Showing 6001 words to 9000 words out of 28383 words

Chapter 3 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx

ni ka karya min alqawari? Yaudara ce fa sanadin da ka ganni a gidan Yari, shi ne kai ma kayi min? wai dama haka ku ke maza? To na roqe ka yadda muka haxu lafiya to mu rabu lafiya.”

Bai ko saurareta ba, ya doka kiran waya inda ya bada umarnin a zo da mota yana da me laifin da yake so a wuce mishi da ita.

Kafin ya sauke wayar daga kunnenshi kasancewar ya bata baya yana amsa wayar. Bai aune ba ya ji shigar harsashi a kwanyar qeyarshi, bata ida ganin yadda ya qare ba ta fice daga xakin. Da sauri ta bar otel xin.

Ta dire gida inda ta iske Deena da Beeba cikin jimamin yadda take.

“Ah! Me ya faru ne na ganku jugum kamar ma su zaman makoki?” Deena ta rungumeta da tambayar.

“Ya ya ku ka qare da shi?”

“Kai Deena, sai ka ce naje qiyama na dawo, irin wannan tambayoyi haka?”

Beeba ta ce, “Nima fa jinina a kan akaifa yake Rose, nasan mutumin can mugu ne.”

Rose ta ce, “Ai na kawo qarshen muguntarsa Beeba, tunda na lura manufarshi a kaina ta ya sake

quga min baqin ciki a karo na biyu yake. Shi fa da tsiya sai ya maida ni yari da jarin kafin su xora binciken yadda aka yi na tsere, kin ji shege ko, wa ya faxa mishi tserewa nayi?”

“Ya gane ki ne?” Cewar Deena.

“Ya gane ni, kuma ban voye mishi kaina ba. Kai tsaye na amsa mishi ni xin ce.”

“Ya ya ku ka yi to har ya bar ki ki ka taho?” In ji Deena.

Ta zaro bindiga daga qugunta. “Ai yanzu ina jin ya kai babban birnin lahira.”

“Shi kenan kuwa.” Cewar Beeba. “Gobe ma ya kira me alewa

ba shi da kuxi…”

Qararrawar ta xauki qara alamar da baqo a waje. Deena ta leqa ta Taga inda ake hango wajen gidan, in da tayi arba da wani Gandiroba da wani me kayan gida riga da wando na farar shadda.

Da sauri ta juyo tana faxa musu abinda ta gani. “Mits! Aikin banza.” In ji Rose. “Je ki Deena ki ji me ke tafe da su?”

“Bari ni da su matsiyata.” Ta zura zumbulelen hijabi ta doshi

Gate

xin, yayin da Beeba ta miqe akan doguwar kujera tana danna ‘IPAD’ xinta tana wasan

Game

. Ita ko Rose kicin ta nufa tana zuba abinci.

Deena ta buxe

Gate

ta isa inda baqinsu ke.” “Ku ne ke

door balt

?” “Eh mu ne.” Gandiroban ya faxa yana zare ido.

“Ayya, gashi kuma maigidan ba ya nan…”

“Dama ba shi muke nema ba, ke ce matar gidan?”

“Eh ni ce, in ce dai lafiya?”

“Wacece ta shigo nan gidan, kuma tana ina?”

“Ban gane ba?”

“Eh, wata ta shigo nan gidan yanzu ba da jimawa ba, ita muke so ki fiddo mana…”

“Wa ke nan?” Ta tare shi.

“Wata matashiyar budurwa mai sanye da doguwar rigar

fashion

kalar

Green

.”

“Gaskiya ba nan ta shigo ba, sai dai ko gida na gaba.”

“A’a nan naga ta shigo, in dai kin voyueta to faxa mana.”

“Ribar me zan ci idan nayi maka qarya Malam?”

“Ban ce kin yi min qarya ba Hajiya, amma ni na san nan matar nan ta shigo. To bari in faxa miki ko me tayi, kisan Gandiroba tayi me riqe da babban muqami. Don haka idan kin amince muna so mu dubata a cikin gidan, me yiwuwa ko ta shigo ba ki sani ba.”

“Babu damuwa, sai dai ku fara neman izinin maigidan tukuna. Don haka ga

phone number

xin shi ku kira shi kuyi mishi bayani.”

Suka kira wayar amma a kashe.

“Wayar nan fa kashe take.”

Ta sake

basu wata lambar ta bogi, ita kam an yi sa’a ta shiga sai dai ba a xaga ba.

Ta dube su “Ina ga bari in kira shi a

Landline

.” Ta faxa tana qoqarin juyawa ciki.

“To mun gode.” Suka faxa.

Ta koma cikin

gidan. Jim kaxan ta dawo tana shaida masu cewa, “Ya ce, ku shigo ku duba.” Tayi gaba suka bi ta a baya.

Sai dai iya bincike da dubawa babu abin da suka gani, har quryar xaki ta kai su amma babu komai. Ba don sun yarda ba suka yi mata godiya suka fito da qudirin saka ido a kan gidan.

Deena ta buxe kafet xin tsakiyar falon, in da wata qofa take wadda zata sada ka da gidan qasan inda Rose da Beeba suke.

“Ku fito sun tafi.” In ji Deena.

Rose ta kaxa kanta ta ce, “A’a Deena, kema dawo qasan nan kafin qurar ta lafa, don ba qyalewa suka yi ba sai sun sake dawowa.”

Haka suka koma rayuwar gidan qasan, wanda akwai komai na rayuwa har ya soma yafi na saman haxuwa.

Tsayin sati xaya ido na kan gidan, inda ake fakon wani motsi daga gidan, sai dai shiru amma a gefe xaya ana ta zuzuta kisan Olu Kayode, wanda Tukur Sambo ya tabbatar da Aisha ce (Rose) ta yi kisan, saboda ya sanar da shi ya ganta. a otel xin ma an tabbatar da mace ce tayi kisan

.

Kuma tare suka shigo otel xin da ita, a take Tukur Sambo ya gama kissima lallai ya zama dole a tsaurara bincike a garin Abuja don gano Aisha (Rose). Take ya xaura xamarar zaluqo Aisha domin ko laifin ta hawa hawa ne. To ko zai dace da ganinta?

**

Ta zubawa

TV

xin ido har bata qyaftawa, a zatonta idonta ne ke mata Gizo. Da sauri ta miqe tamkar wadda aka tsirawa allura, ta isa gaban

TV



xin ta tabbatar da idonta ba Gizo yake mata ba.

Bata tsinke da lamarin ba sai da taji an kama sunan shi ta tabbatar shi xin ne. babban abinda ya girgizata shi ne jin wai shi ne ke son kujerar Senator da ya kwanta dama, wato Shehu Usman Shehu.

A take komai ya shiga dawo mata tamkar a fai-fan Garmaho. Hawaye ya shiga zuba a idonta. Rose da Beeba suka iso gareta.

“Mene ne Deena?”

“Babu komai.” Ta faxa muryarta na rawa.

“Na zaci babu bata a tsakaninmu.” Cewar

Beeba. Ta durqushe ta saki wani irin kuka me ban tausayi. “Ban voye muku ba na tuno abinda wancan mutumin ya yi min sanadin shi ne silar shiga baqin cikina. Shi ne silar haxuwarmu a inda muka haxu. Shi ne silar rasa uwata da ubana, sai gashi na gani an hasko shi a

TV

wai shi ne zai maye gurbin Senator Shehu Usman Shehu.

Shi rayuwa ta haska shi ni kuma ya jefa ni a duhun tashi ya ci ribar rayuwa ni na faxi warwas!.”

Rose da Beeba suka maida idonsu a kan mutumin da ya yiwa Deenarsu sanadin baqin ciki. Rose ta maida dubanta ga Deena.

“Kiyi haquri Deena, nayi miki alqawarin sai kin xauki fansar abinda ya yi miki, ko ma fiye da abinda ya yi miki. Bana jin zan iya rama abin da ya yi min Rose, bare har fiye. Uwata da ubana duk a sanadinshi suka hallaka. Rose ko kashe shi nayi wallahi ban ci riba ba.”

Suka zuba mata ido suna tausaya mata. Rose ta kamo tana faxin “Kiyi haquri Deena ki daina kuka don Allah, wallahi bana jin daxin ganinki cikin hawaye.”

Ta ce, “Rose kuka kuwa shi ya kamace ni, kuka ya kamata in ta yi har in qare rayuwata. Wace ce a ka tava yiwa abinda aka yi min ba zata yi kuka ba? Kar ki fa manta Rose, uwata ta mutu sanadin xa namiji, ubana ya mutu ta dalilin xa namiji. Na shiga garari, da takaici, baqin ciki. Meye amfanin farin ciki a gare ni? Meye amfanin dariya a gare ni?

Ku duba ya cuce ni, ya yaudare ni amma wai yau shi ne a matsayin Senator, ya manta da wata halitta Deena, ya manta da Ubangiji ya tsiri halittata a duniya.

Farin cikinshi yake ta yi, walwalarshi ya ke ta yi, yana can shi da matar da yafi qauna…”

“Sai farin cikinshi ya koma baqin ciki, sai walwalarshi ta koma damuwa, sai damuwa ta kewaye shi gaba da baya in dai ina numfashi

. Idan har ya ci riba a kanki kenan Allah baya sakayya? Sai ya zamo shi da duniya ba kuma ba lahira ba? sai ya zamo rasa komai? To ina me tabbatar miki ba zamu rasa xaukar fansa ba, ko za ki yafe komai ni ba zan yarda ki yafe jinin Mahaifanki ba.

Ko da ta Allah zata kasance a kanki (mutuwa), to ni zan maye gurbinki tunda Allah yasa na ga fuskarshi. Duk da ina jin ku duka babu wacce ta kamo ni xanxanar baqin cikin xa namiji. A kullum na runtse idona ina hango illa da zamba cikin aminci, da kuma gorin ni sabon tuba ce. Ni Arniya ce, Musulmai ba su yi min kara ba.

Ko da ya ke wanda nayi don shi bai karanta min ba. hakan yasa na dawo addinina da na bari (kiristanci), wanda barinshi ya jawo min abubuwa masu yawa, kuma marasa daxin tunowa.

Duniya da mutanen duniya ba su da adalci, mutanen duniya su suka ba mu lasisin zamowa qwallayen shegun da zamu buwaye su. Ba ma da kowa ba mu da komai, to me zamu jira? Kan me uwa da wabi a kan maza sai mun zamo ‘MANYAN MATA’ a wurin maza, sai mun zama manyan mata a duniya da cikin al’umma gaba xaya. Don haka Deena idan kina muradin wancan mutumin ya gama kwana a duniya…”

“Ba yanzu ne ya kamata ya mutu ba Rose, sai duniyar ta gama yi mishi daidai har ya zamo qawar duniyar ta ruxe shi ya ji ba ya da burin da ya wuce duniya.”

Rose ta dubi Beeba “Kin kawo

Good idea

, amma ki sani tunda aka motso min abin da ya

shuxe bana jin zan iya runtsawa ba tare da na tankaxa qeyar maza zuwa barzahu ba. wallahi sai naga bayan maza. Sai duniyar nan ta zamo babu sauran wani namiji sai mata.” Ta faxa da idonta na vulvulo hawaye.

Ta miqe da

sauri ta sauya kayan jikinta. Deena ta ce, “Jira ni Rose.” Itama Beeba ta miqe “Ai ba za ku barni ba.”

Suka yi kwalliya ta neman fitina da shiga wadda za ta fizgo zukatan mazan da ajali yayi kira. Deena ce ke jan motar yayin da Rose da Beeba ke baya.

“Wane irin iskanci ne wannan sai ka ce wata direbarku?” In ji Deena. “Yi haquri Hajiya Deena girman ne muka baki, wa ya isa ya jera kafaxa da ke?” Cewar Beeba.

Ita ko Rose cewa tayi, “To da mece ce? Ai ga zahiri nan ta gani.” Ta ce, “Idan ban varar da mu ba ki ce min tsinanniya.”

“To Allah ya tsinewa wanda bai varar da mu ba.” In ji Rose.

“A’a yi haquri Anti Deena kar ki varar damu, akwai buri a gabanmu wanda ba mu cika shi ba.”

“To shi kenan Anty Beeba, ta ci albarkacinki.”

“Uhum! Uhum!! Ku nuna min ni xin bare ce, ku nuna min wariyar launin fata.”

“Ayya! Ai ke ma za ki dawo ne cikinmu, hutu dai ki ka je amma ai ga ki can kin koma Indonki.” Cewar Deena.

“Uhum! Deena ai babu ranar da zan dawo cikinku, kowa dai ya tsaya a kan mazavarshi. Amma ni da addininku ai ba rantsuwa ba baki.”

“Ai ko in dai zaman gaskiya ne dole a tallafi juna Rose mu gudu tare mu tsira tare. Mu fa nan ba mu da kowa sai kanmu, mun zamo dangin juna.”

“Haka ne, amma mu bar maganar kawai.”

“To mun barta a yanzu, amma zamu yi ta nan gaba.”

“To abar wa gaban, don lokaci shi ke alqalanci, shi kuma zai nuna kanshi.”

“To yanzu ina muka nufa?”

“Kai mu ‘JIFATU’ ta Wuse II, idan ba mu

catching

ba sai mu koma titin Asrock.”

Kai tsaye Deena ta faka motar, suka duro qasa suna zagayawa tamkar masu siyen wani abu. Wani mai kakin Xansanda me kalar bula ya dubi Rose fuskarshi a sake da salon zolaya.

Ya ce, “Kamar nasan fuskar nan?”

“Bana zaton hakan.” Cewar Deena da ta tsani Xansanda ko wanne. “A’a wata qila dai kama nayi mishi da wadda ya sani.” In ji Rose. Ita ko Beeba

duk inda me kakin Xansanda yake tana girmama shi, albarkacin Xansanda guda da ya albarkaci mutum guda xaya.

Yayi murmushi yana qarewa qirjinta kallo

, don tun shigowarsu ya zubawa ‘yanmatan ido har dai ya ji tamkar ana fizgar shi zuwa ga Rose xin, kasancewar shi me son fantamawa.

“To in dai haka ne bani sunanki sai in ji in na sanki ko ban sanki ba.” Ta dube shi sosai inda ta gane D.P.O ne na yankin Suleja, saboda gani a rubuce da tayi.

“Sunana ba shi da daxin ji fa!” In ji Rose.

“Amma ai ke kina da daxin gani a ido, bani sunan.” Ya faxa da alama ya iya matan bariki da yadda ake bi da su.

“Uhum! Sunana Duduwa.”

Ba shi ba, har Deena da Beeba sai da suka yi dariya.

Ya ce, “

Amma ko ni yayi min daxi, kin ga ma sai ya zamo irin nawa

wato Dudu.”

“Ka ko ci sunan Dudun.” In ji Deena.

Suka qara yin dariya.

“Me za ku xauka ne in taya ku Duduwa?”

Rose tayi dariya “Wai xan abubuwa muka zo dubawa.” Ya ce, “Ok, to muje in taya ki dubawa.” Suka shiga jidar kaya tamkar za su buxe shago.

Deena da tayi maganar qasa-qasa ta ce, “Uhum! Wani zai siyi ajalinshi da kuxinshi.” Ita ko Beeba cewa tayi, “Wallahi kaya zan xiba kamar ba gobe, tsinanne. Yanzu haka matar shi ta gida a kan xari biyar sai ya tada mata hankali. Ko na rantse ba zan yi kaffara ba, idan na ce rabonta da xinki tun na salla, amma daga ganin mace tashi xaya zai yi mata wahala. Kai! maza ba kyau wallahi, ba ki lura da shi ba ne? xan duniya ne sosai.”

Suka jidi kaya sosai, wani abun ma babu abin da za su yi da shi amma a cewarsu wai raba mugu da makami…Ya biya kuxin ta hanyar (ATM Card) xin shi, aka cire ta (P.O.S) kuxi ba na wasa ba. Aka xura masu kayan a mota inda yaso ya kai su gida. Sai dai Rose bata yarda ya bi su ba.

Ya ce, “Yo ta ya ya ma za ayi haka? kar ki damu muje in sauke ku, ba ki san ke xin kaffa-kaffa ake da irinku ba

kar rana ta riqa dukanku ba?”

“A’a rufa min asiri, ai da an ganni da kai cewa za’ayi me laifi ce.” Yayi dariya “Alhalin ke xin kuma ba me laifi ba…”

“To ka gani!” Ta tare shi. “To yanzu ya zamu yi?” Ya tambaya. Ta ce, “In ba ka

phone number

ta in yaso sai ka kira ni.” Ya ce, “Ok, to na gode

my Duduwa.” Ya dubi Deena ya ce, “Kuyi haquri fa zan canjawa qawarku sunan zata tashi daga Duduwa ta koma

Beauty

.”

“Gaskiya sunan ya yi kyau.” In ji Deena.

Rose ta karanto mishi lambar wayarta ta bashi ya shigar, sai dai tayi qwangen xaya, don haka ba ta shiga ba. Da sauri ya miqa mata wayar tashi ta sake zuba mishi. Sai da ya kira ta shiga kafin ya tabbatar mata da zai kira ta a

week end

Asabar ko Lahadi.

Suka yi bankwana Deena taja mota.

“Amma kash! Na so a ce mutumin can ya nuna zalamar shi ta zahiri don lahira tayi baqo!” In ji Rose. “Deena sauya hanya zai iya biyo mu a baya fa.” In ji Beeba.

Da sauri Deena ta xauke kan motar suka nufi wata hanyar. “Ni fa ban yarda da Xansandar nan ba.” In ji Beeba. “Kamar ya ya?” In ji Rose. “Idan kin kula D.P.O ne na yankin Suleja, idan har irin shi suna nuna zalama irin haka kin ga akwai matsala. Koda suna tava barikin to za ki same su a sirri suke abin su.”

“Maganar ki Beeba abin dubawa ce.” In ji Deena. “Kar ku damu, in har taqamarshi zafin kai to ni ashana ce, Allah yasa ajali ya kira shi ya nemi ganina. Ta haka ne zai gane a garin makafi

mai ido xaya Sarki ne, Daji kuma bai gama cin wuta ba ba a yi wa Fara barka, ku bar ni da xan banza.”

BABI NA UKU

R

anar Asabar tana zaune tana

Breakfirst

wayarta ta xauki qara, inda su Deena da Beeba suka bi ta da ido da son sanin me kiran. Har tayi qararta ta tsinke bata xaga ba. A ka sake kira, shima bata xaga ba sai da aka jera biyar bata xaga ba.

“Ai ko da kin xaga wayar nan Rose, ina jin fa Xansandanki ne.” Rose ta ce, “Eh, nima haka ni ke zato Deena.” In ji Beeba. “A’a kar ta xaga Deena, ta bar shi har ya gaji ya qyaleta.”

Deena ta ce, “Bana zaton zai qyale ta Beeba. In dai numfashi ne ya qare mashi to zan iya cewa Allah ya jiqanshi

.” Tana rufe baki wayar na sake shigowa a karo na shida. Rose ta kai hannu zata xauka, Beeba ta riqe hannun “Don Allah ki rabu da shi ya gaji da kiranki ya qyale ki.”

“Uhum! Beeba kenan, kina mantawa da ni xin Tauraruwa ce me wutsiya? Ina me tabbatar miki wannan mutumin wallahi ya ci karya ya kwana da yunwa yayi nasara a kaina.”

Jiki a sanyaye Beeba ta sakar mata hannu. Daidai da wani kiran ya sake shigowa. Da sauri Rose ta danna amsa kiran, inda a take ta shaida mai sallamar. Ta amsa da “Amin wa’alaikas salam.”

“Beauty ko in ce Duduwa, fatan kin tashi lafiya?” Ta ce,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login