Showing 18001 words to 21000 words out of 28383 words
Chapter 7 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
ne masu yawa wanda ake zubawa a ciki Bursunonin su xauka bisa kwanyar kansu suje su zubar.
Gwanar rawa ta iso tana sakin maganganu. “Wai sai mu ne zamu ke zubar da bahayarmu da kanmu? Kai duniyar nan fa tayi mana kancal
da yawa, ana ta mulka mu tamkar mu ne kaxai masu laifi.”
Gandirobar ta harare ta cikin jin haushin maganarta inda ita kuma gwanar rawar ta soma taka rawarta. Aka cika bokitan da bayan-garin, Bursunan suka soma xauka a kansu.
Rose da Beeba suka xauka inda itama baquwarsu da ke ta zubar hawaye aka xora mata ba tare da duba baquntarta ba.
Suka soma ficewa don zuwa zubarwa inda gwanar rawa ke ta taka rawarta tamkar dai
wahayi aka yi mata da rawar, nan ko duk cikin shaixancinta ne.
Gandirobar ta dubeta ta ce, “Ke ‘yar iska me ki ke nufi da ba za ki xauki bokitin ba?” Itama ta ce, “To ranki ya daxe naga dai ni ba kashin nan nike yi ba, masu yi su ya kamata suyi jigilar abinsu, ni kam ba zan xauki kashin wasu qarti ba, rawa zan taka idan ke ma za ki taka sai ki zo mu danse.”
Gandirobar ta ida zuciya ta zabga mata doguwar bulalar da ke hannunta. “Ke kam dama can tsinanniya uwarki ta haifo ki, shi yasa ki ka diro inda za ku haxe da tsinannu ‘yan uwanki, maza ki xauki bokiti nan. Don ubanki da akwai wanda ya kai ki yin kashi a gidannan?”
Gwanar rawa ta dubi Gandirobar cikin jin zafi, kafin tayi kwafa ta suri bokitin ta xora a kanta. Gandirobar tabi bayanta.
Sai da gwanar rawa ta bari sun iso inda Gandirobobi suka yi majalissa ta saki bokitin kashin kif! Ya watse da kashin wanda ya vata su da kayan jikinsu, musamman Gandirobar nan da ta zunkuxa mata bulala.
Ai ko suka yi faca-faca da kashin. Bisa dole aka sauya Gandirobar da wata wadda zata raka
sauran Bursunan, inda ita kuma gwanar rawa ta daku tamkar kurar roqo. Amma ko a jikinta, sai ma rawar da ta xora abarta, dama ai ta ce ba zata je zubar da bahaya ba
.
Tsinuwa kuwa yanzu ta soma nunawa.
Su ko sauran Bursunan sun isa har sun zubar inda su Rose da Beeba suka jero tare da baquwa wadda har suka dawo idonta da ruwan hawaye suna ta hira tsakanin Rose da Beeba, inda suke sako baquwa.
Sai dai bata cewa ko uhum har suka kawo bakin titin da zai maido su qiri-qiri road, babban titin da ke da yawaitar motoci da Mashina, kawai sai ganin baquwar suka yi ta saki bokitin ta kwanta shame-shame a tsakiyar titin da fata da burin mota ta bi ta kanta.
Saura kaxan qatuwar motar (
IVECO
) wadda ta xauko siminti taci burki da sauri, ji ka ke quuuu!
Kan ka ce me
go slow
ya haxu abu ga babban gari irin Legos.
Da sauri Beeba da Rose suka kai mata xauki, “Ku bar ni don Allah, ku qyale ni motar nan tabi ta kaina in mutu in huta.”
Gandirobar ta soma tsula mata bulala, da sauri suka janyeta inda mutane ke ta sheqo mata
zagi da yaruka kala-kala, saboda
go slow
xin da ta haxa musu.
Rose da Beeba suna riqe da ita har suka qarasa gidan Kason, inda suka iske gwanar rawa na ta abinta kafin ta qyalqyale da dariya.
“Wai ita wannan baquwar auta ce ko ko shagwava ce da ba ta gajiya da hawaye sai ka ce kabewa? In nan gidan take wa hawaye ai zata saba ne har ma taji nan xin ya zamo mata Aljanna.
Ni nan gidan ya fiye min komai da kowa don ko fidda ni aka yi sai na dawo.”
Baquwar ta dubeta inda Rose ta ce “Rabu da ita kin ji.” Suka wuce don wanka da aje bokitan. Sai da suka yi wanka kafin Rose ta dubi baquwar ta ce da ita.
“Wai ya sunanki ne?” Da kyar ta buxe baki ta ce, “Sunana Deena.” “Haba Deena, me yasa ki ke haka ne? dukkanmu nan da ki ke gani ba daxi muke ji ba amma muka yi haquri. Ki daina neman halaka kanki don Allah kin ji? Ni sunana Rose
”
,
ta nuna Beeba “Wannan
kuma sunanta Beeba, mu zamo qawaye mu taimaki juna duk
da ni xin ba addininku ni ke ba, na komo addinina da na gada.
Amma ke da Beeba addini xaya ku ke, duk da ba mu san zaman da aka yanke miki ba, shin zaman shari’a ki ke ko ko zaman wa’adi ko zaman din-din-din (life in prison)?”
Ta ce, “Wallahi ban sani ba, na dai tsinci kaina ne a gidannan kawai
,
lokacin da aka yanke min hukuncin bana cikin hankalina, tunanina yana ga uwata da ubana da na rasa…” sai ta rushe da kuka.
“Mutuwa suka yi?” In ji Beeba. Ta gyaxa musu kanta. “Ba kuka za ki yi musu ba Deena, addu’a ita ce gatan da za ki nuna musu a yanzu.”
Ta dubi Beeba. “Dole in yi kuka Beeba, na tabbata idan ki ka ji abinda ni ke yi wa kuka kema sai kin taya ni kuka, ki kuma ce in ta kuka har in koma ga Mai duka Allah. Domin ko abin kukan ne ya same ni.”
“Allah dai yasa namiji bai shigo a cikin abinda ya same ki ya sa ki kuka ba?” In ji Rose. Tabi Rose da ido kafin ta furta.
“Ta ya ya ki ka gano da hannun namiji a cikin abin da ya same ni?” Ta ce, “Ban hango ba Deena, na dai yi hasashe ne kawai saboda sanin da na yi wa maza a kan son yaudarar mu.
Maza suna son cutarmu alhalin ba su yi ba
bu mu. Ba su jin daxi in babu mu, amma kash! Burin maza su kashe mata. Ina me tabbatar miki da babu abinda ke kashe mata irin maza.
Nasan za ki yarda dani idan ki ka je asibiti, qaramin alhaki a ciki shi ne wadda taje awon ciki, wata hawan jini, wata yara ta kai. Ke matsaloli na tashin hankali.”
Deena ta share hawayenta ta ce, “Ni na ga baqin cikin xa namiji, ni naga sharrin xa namiji, ni naga illar maza. Da abin ya tsaya a kaina to da ban damu da yawa ba, amma uwata da ubana duk sun shigo sahu, shin kema haka aka yi miki? Kema haka namiji yayi miki?”
Sai suka haxe kawunansu suna ta sheqa kuka tamkar dai ace Alqiyamarsu ce ta gaggauto.
BABI NA SHIDA
G
andiroban ya shigo yana tambayar “Wace ce Fadila Tanko?” Gwanar rawa ta dube shi a sheqe ta ce, “Ga wata
.” Ya ce, “Ki zo kina da baquwa.”
Da sauri Gwanar rawa ta biyo bayanshi don tasan baquwar da ya ke magana a kanta. Suka iso inda ake karvar baqi, inda Gandiroban ya ja ya tsaya a kan su don doka ba ta yarda da kevancewar baqo da Bursuna ba sai dai suyi maganar a kan idonshi.
Haka ma ba a yarda me zuwa ziyara ya kawo wa Bursuna abu ba tare da ya ci a gaban Gandiroba ba da Bursuna ba.
Hamshaqiyar mace ce wadda kallo xaya za ka yi mata ka san tayi hannun riga
da talauci. Sanye take da atamfar
super
exclusive
me ruwan tsanwa da
yellow
. Hannunta da zobban
Gold
wuyanta da kunnenta.
Fara ce tas, bakinta xauke da haqorin Makka irin matan nan dai da ake wa laqabi da ‘MANYAN MATA!’
Gwanar
rawa ta zube a gabanta tana murmushi. “Hajiyata yanzu ki ke tafe?” Ta ce,
“Uhm, yanzu ni ke tafe Fadila, fatan kina lafiya?”
“Lafiya qalau Hajiya, ya ya su Hafiz?” Ta ce, “Suna lafiya, sun ce na gaishe ki.” Ta ce, “To na gode.” Ta miqo mata ledar da tayo mata guzuri, ta miqo mata bayan ta gama xanxanar duk abinda ke cikin ledar.
“Idan kina buqatar wani abu sai ki faxa min in kawo miki.”
“Babu abinda ni ke buqata Hajiyata, na gode sosai, Allah ya qara so da qauna.”
“Kar ki damu Fadila ai ke xin kin wuce komai a gare ni, bari in tashi naga qab da kaki ya zura man ido babu damar ayi sirri.” Ta faxa murya a qasa-qasa.
Da haka Hajiyar ta fice, inda Fadila Gwanar rawa ta kwaso kayanta ta shigo inda Atika ta taho da sauri tana faxin.
“Shi ne ko kirana ba kiyi in yi miki dako?” Ta karvi ledar zuwa xaki suka haye kan gadon Fadila, wanda ke kusa da na Atika, suka soma buxe abubuwan da Hajiyar ta kawo wa Fadila. Biredi ne da madarar
Peak
da kifin Gwangwani, da soyayyar gyaxa, da garin rogo da sukari, da
man gyaxa, da garin quli-quli, kai kaya masu yawa dai.
A gefe xaya kuma ga
Ice Cream
da
Cake
, da soyayyen nama me yawa. Atika ta xauki naman xaya ta jefa baki, kafin ta buxe robar
Ice Cream
ta kamfanin (FAN MILK), inda Deena ke kallonta, itama Gwanar rawar idonta na kan Deena saboda tunda aka kawota idonta ke kanta.
Ta xauko robar (Fan Milk) da soyayyen naman ta zubo a kan murfin na (Fan Milk) ta kawo mata. Da sauri Deena ta kaxa kanta alamar a’a ta gode.
“Haba dai baiwar Allah, ni fa na ba ki ko ba ki so mu taka rawa wata rana?”
Deena ta ce, “Kiyi haquri bana buqatar komai a rayuwata, shi yasa ba zan ci ko na sha abinda zai xorar da rayuwata ba.”
“Ayya! Ai ni in na bada abu bana waiwayenshi, kamar yadda in na bada so da qauna bana amshewa.” Ta juyo ta bar Deena da binta da kallo, yayin da Atika take jin tamkar ta shaqe Deena.
Rose da Beeba da ke waje suna ta
tiqar wankin da suka amsa saboda su samu na siyen Gyaxa da Garin Kwaki, saboda ba su da me zo
musu ziyara bare su saka ran da wanda zai tallafe su da wani abu.
Dama shi aikin yana danganta ne da wanda ba shi da me zuwa inda yake, bare ya samu wani abu. Amma masu gata irin Gwanar rawa bata aikin komai sai dai a kawo mata abinda duk take buqata.
Ba Gwanar rawar kawai ba, da akwai masu gatan da ya zarta gwanar rawa, wanda ko ruwan gidan bata sha bare abincin gidan. A kullum sai an kawo mata abinci sau uku a rana.
Idan kuma da abinda take so za a kawo mata, don haka su Rose da Beeba da suka tabbatar ba su da wannan gatan suke amsar wankin kayan har ma da na
mashinan.
Don haka ba su samu kansu ba sai da rana tayi sanyi, bayan sun karvi haqqinsu suka shigo xakin inda suka iske Deena ta zabga tagumi.
Rose ta dubeta ta ce, “Halan kukan ki ke?” Deena ta ce, “Uhum! Rose kuka fa shi ya dace in ta yi har in mutu, na rage ne saboda na lura ba kwa jin daxi.”
Beeba ta dubi (Fan milk) da naman da ke gabanta ta ce, “Ina ki ka samu wannan abin
Deena?” Ta ce, “Wannan me rawar nan ta bani…”
“Me yasa ki ka karva Deena?” In ji Rose. “Wallahi sai da na ce mata na qoshi ta aje min.” Rose ta rage murya ta ce, “Kar ki yarda da duk abinda za ta ba ki, yaudararki zata yi neman mata take.”
Deena ta zaro ido “Ba ki ga tana ta rawa ba? wannan rawar da take wani salo ne na jan hankali, da kuma gane wanda za a yaudara
kin gane? To kar ki kuma karvar wani abu daga hannunta.
Ke ko magana kar ki yarda ta haxa ku, in ma ta haxa ku to kar tayi tsayi eh a’a kawai.” Beeba ta tanka “Ni dama nasan tunda ta soma saka baki a harkar Deena nasan da akwai abinda take nufi
.”
Deena dai sai binsu da ido take tana mamakin sauyin rayuwar da ya same ta, wai ita ce a gidan Kaso, inda baragurbi irin ‘yan maxigo ke rayuwa, lallai Allah Gwani ne a kan dukkan komai.
Gata na gidan duniya babu irin wanda bata da shi, amma yau gata a inda babu me tuno ta bare
ya ziyarce ta. To me zata xauka a wannan baqar duniyar da ta gama yi mata duhu.
Ta soma share hawaye…. “To to za ki fara ko?” In ji Rose. “Ban ma fara ba Rose, ina ma ace za ki fahimce ni? Ina ma ace a kan idonki komai ya faru? Ina ma ace kina ganin abinda ke zuciyata?
Kuyi haquri da yawan kukana, don ina jin babu wanda ya xanxani baqin ciki irin nawa a wannan duniyar da zan samu natsuwa da na faxa muku abinda aka yi min wanda ku da kanku za ku ce kuka ya zame min dole, kuma ku taya ni kokawa.”
Suna cikin haka, Fadila Gwanar rawa ta shigo tana faxin “A’a, me aka yi miki Auta? Ke dai kam ina ga kuka baya miki wahala, ni kam ai ban iya tuna tsawon lokacin da na xauka ban yi kuka ba. Kai an daxe gaskiya. Ai ni tunda na gane wannan duniyar sai mutum ya zama jan gwarzo na daina yiwa komai kuka.
Kema zamo jaruma ki daina yiwa komai kuka, in ba haka ba to za ki haxu da ciwon zuciya, da kuma hawan jini. Kin ga ko ba ki mutu ba to wahala kawai za ki qarawa kanki
Deena.”
Tabbatar da maganar Gwanar rawa gaskiya ne sai dai don me za a ce ta bar kuka. “Ai ku manya ne Gwanar rawa.” Cewar Rose.
Ita ko Deena bata tanka ba sam, duqar da kanta da tayi tana sharar hawaye. Beeba ta jiqa Garin Kwaki ta zuba sukari da Gyaxa, inda ta kawo musu suna sha ita da Rose suka dubi Deena.
“Ba za ki sha ba Deena?”
“Na qoshi.” Ta faxa.
“Ina
fa lura da ke Deena ba kya cin komai sai baqin ruwa, yunwa ma fa ciwo ce. Don Allah ki bar wa Allah komai har ki ga abin da zai yi a kanki.”
Rose ta dubeta ta ce, “Uhum! Deena kenan, kin ganni nan shekaruna biyar a gidan nan, Beeba itama shekaru biyu duk wani abu da ki ke ganin yana damunki wallahi a duniya ne. Daga ranar da ki ka mutu to shi kenan nan gidan ma fidda ki za a yi a kai ki kushewa.
Don haka ki fuskanci Allah da kyakkyawar manufa, me yiwuwa a nan gidan ki samu rabon da baki same shi a rayuwarki ta jin daxi ba.”
Deena ta dubi Rose da kalamanta irin na musulmin da ya yi final da tsoron Allah. Tayi
murmushi na yabawa “Kalamanki Rose tamkar na musulma…”
“Kar kiyi mamaki Deena idan na ce da ke na tava shiga Musulunci har aka raxa min suna Aisha…”
“Me yasa ki ka baro shi ki ka dawo Kiristanci?”
“Saboda na gane Musulmai mayaudara ne. Nayi masu kyakkyawan zato suka munana min zato
, wanda nayi don shi ya cuce ni, ya ha’ince ni, ya yaudare ni, sai naga kawai in koma addinin da aka haife ni a cikinsa, na kuma gada. Shi yasa na watsar da sunan Aisha na koma sunana na asali wato Rose.
Kar kiyi mamaki idan na ce miki na sauke Alqur’ani, na kuma san Hadisai da littattafai da dama.”
Suka bi Rose da ido, “Amma zan so in san labarinki Rose.” In ji Beeba. “Sanin labarina a yanzu Beeba ba shi da amfani, domin ko miki kawai zan tado wa kaina
.
Da a ce ina da tabbas a kan rayuwata, to da na rubuta labarina don in barwa duniya abinda namiji ya yi min, sai dai kash! Rayuwata zata
qare a gidan nan, sai na mutu qiyamata zata tsaya.
Idan har kin ganni a waje to tabbatar bayan garinmu ne zamu je zubarwa Deena ni na riga ki neman mutuwa ido buxe a gidan nan amma yanzu da na saba sai ya zamo ina jin daxi, har ma na riqe a raina ban da inda yafi nan.”
Beeba ta share hawaye “Ina ma ace mu kuvuta daga gidan nan? Ina ma a ce zamanmu a gidan nan ya zamo mafarki? Ina ma ace mu samu ‘yancin yin rayuwa irin wadda muka baro baya?
Wallahi tallahi da sai mun rama abinda aka yi mana.”
“Ai ni sai na rama fiye da abin da aka yi mana ma!”
In ji Rose. “Ni kam bana jin zan iya rama abinda aka yi mana, bare har in zarta in je Deena mu bar abin da ba zai yiwu ba kar mu qarawa kanmu baqin ciki.” cewar Rose.
Bisa dole aka bar maganar inda Beeba da Deena suka tashi don yin sallar Magriba. Suna idarwa me rabon abinci yazo da dafaffen Gero da wake, da kofin ruwa guda-guda.
“Ni dai nawa a kaiwa ‘yan majalissar waje.” In ji Gwanar rawa wadda bata shan ko ruwa na gidan bare abincin. A kullum da abin da take
faxa a kan abinci, wata rana ta ce a ba wa Gandirebobi ko ta ce a zubar ko ta ce a ba wa ‘yan majalissa.
Rose ta karvi abincin saboda tana son Gero
da wake. Inda Fadila gwanar rawa take shan zallar madara da biredi.
Ta iso inda Deena take, “Qawata ga wannan don naga alamar ke xin ‘yar madara ce.”
Deena ta ce, “Na gode sosai na qoshi wallahi.” Ta ce, “Ah! Wai ke komai kin qoshi? To me ki ka ci?” Rose ta qyara mata ido ta karva tayi godiya, ta aje gefe don har ga Allah bata buqatar komai.
Rose ta kurve madarar da biredin in da Deena ke mamakin gwanar rawa a kan neman mata ko ta ji me?