Showing 27001 words to 28383 words out of 28383 words
Chapter 10 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
/>
Da haka suka yi sallama, Rose tana mamaki. Ta kwashe kayan ta shiga ciki, inda Deena da Beeba suka taya ta xauka.
A jikin kuxin da ubangidan Sintia ya bata taga wata guntuwar takarda, ta warware inda tayi arba da guntun rubutu wanda bai wuce layi uku ba. amma ma’anar sai tafiye mata daxi fiye da komai.
Ga abin da ta gani a rubuce.
Kina buqatar a kuvutar da ke Rose? Idan kina buqata idan Sintia tazo ki sanar da ita, nayi miki alqawarin kuvutar da ke nan da sati xaya.
Da sauri ta soke takardar a qugunta, sai ta shiga xokin tasan ta inda za a kuvutar da ita. Shin ta wace hanya ita da aka yankewa hukuncin zama na din-din-din?
Amma duk da haka sai ya zamo bata da burin da ya shige wata yayi Sintia ta zo. Sai ga shi Allah ya turo mata da Sintia kafin cikar wata xayan.
Da azama ta iso ga Sintia. Bayan sun gaisa, Sintia ta rage murya ta yadda Gandiroban ba zai ji abinda za su faxa ba.
“Kin ga saqon ogana?”
“Na ga saqo Sintia, kuma ace mishi ina so don Allah ku agaje ni Sintia, bani da kowa sai ke da oganki.”
Sintia tayi murmushi “Kar ki damu Rose, nan da sati
xaya kin bar gidan nan…” Ta ce, “Ta ya ya Sintia? Alhalin an yanke min hukuncin zama na din-din-din, sai fa in na mutu?”
“Ko hukuncin kisa aka yanke miki Rose, ogana zai fidda ke ba tare da anyi nasarar zartas da hukuncin a kanki ba.”
Rose ta bi ta da ido, inda Sintia
ta miqe da shirin tafiya, suka yi bankwana inda Sintia ta ce mata sai gobe zata dawo.
Mamaki ya baibaye Rose, ta inda za a fara da kuma yadda za a qare. A tsorace Rose take har su Deena suka lura da hakan. “Wai lafiya kuwa Rose?” Ta ce, “Bani da lafiya ne.” Ta basu amsa.
“To bari in sanar a kawo miki magani.” Da sauri Deena ta sanar Rose bata da lafiya. A take aka zo aka dubata aka bata magani.
Haka Rose ta kasance a kwance inda take tunanin gobe da abinda Sintia zata zo mata da shi. Lafiyarta qalau fargaba ce kawai ke damunta.
Deena da Beeba sun damu matuqa da rashin lafiyar, Rose xin da ta motsa za su ce mata me take so? Har suka bata tausayi, sai dai tayi murmushi ta ce ba komai. Haka ta kwana tana dakon zuwan Sintia.
Misalin
sha biyu na rana Sintiyar ta iso inda aka sanar da Rose. Ta fito gabanta na sarawa. Ta iso ga Sintia suka gaisa. Sintia ta miqo mata kular me xauke da jalof xin kus-kus, inda Sintiyar ta xanxana saboda doka ce in dai ka
kawo wa Bursuna abinci, ko abin sha sai ka xanxana.
Sintia ta rage murya sosai tana raxawa Rose cewa, “Da akwai wani abu a cikin abincin har ma da rubutacciyar wasiqa, don haka ta kula sosai kar ta bari kowa ya ga abinda ke cikin abincin.”
Da haka suka yi bankwana, Sintia ta tafi. Rose ta xauko kular abincin ta iso xaki, inda
tayi hikimar
aje kular da nufin
sai dare zata ci abincin.
Ta koma ta kwanta gabanta
na harbawa
. Sai kuma aka yi sa’a babu wanda yabi ta kan kular. Tana kwance lamo tana zullumin abinda ke cikin kular, wanda Sintia ta sanar da ita.
Deena da Beeba suna zagaye da ita suna jero mata sannu. Tana amsawa har zuwa lokacin da aka kawo musu abincin rana.
Wake ne gurguzu babu komai sai xan banzan gishiri zau! Rose ta dube su “Ga fa abinci nan a kula da na bar shi sai dare idan kuma za ku ci gashi nan.”
“A’a bar shi sai daren.” In ji Deena. Duk yadda suka so su nuna jarumta a kan rashin
lafiyar Rose abin ya gagara. Shi yasa bata abinci suke ba.
Da ta lura da hakan sai ta qarfafi kanta don su ci abinci, su kuma saki ransu. A gefe xaya kuma Allah-Allah dare ya raba take don ta bincike abincin nan na Sintia.
Ta shari baccinta a zuwan ta samu sauqi. Da dare ya yi ma bata ci abincin da aka raba ba ta ce bata jin daxin bakinta. Haka Deena da Beeba suka yi ta tarairayarta har zuwa lokacin da kowa ya kama makwancinshi.
Dare ya raba, ba ka jin komai sai jan munshari. Rose ta tashi zaune ta jawo kular abincin Sintia ta buxe. Kus-kus ne wanda ya ji haxi.
Ta motsa abincin inda ta hango wasiqa a qasan kular. Da sauri ta jawo ta ta buxe inda tayi arba da dogon rubutu kamar haka:
Ki nutsu ki fahimci abinda zamu tsara a kan yadda
za ki kuvuta. Da farko dai a qasan kular nan da akwai allura da sirinji, da kuma ruwan allurar.
Ki tabbatar da kin badda sawun idon da zai ganki yayin da za ki fiddo allurar da kuma
sirinjin ki zuqo ruwan allurar da sirinjin ki tsira a kan jijiyar hannunki.
Ki fa tabbatar da babu idon da ya ga hakan, domin ko
matuqar wani ya gani to shirinmu zai lalace. In ma san samu ne to ki shiga banxaki ki aiwatar da aikin.
Idan ki ka aiwatar da yin allurar da sauri za ki dawo ki kwanta tsayin awa biyu za ki rasa gane kanki kafin daga qarshe kiyi…
Sauran batun ya dame daman cikin abincin, don haka bata ida karanta abinda saqon ke son isarwa ba. Amma duk da haka ta soma fahimtar inda aka dosa.
Don haka da sauri ta yamutsa abincin sai ga allura da sirinji har da ruwan allurar. Da sauri ta kwashe su ta nufi banxaki ta maido qyaure.
A take ta ciro sirinjin ta kuma zuwo ruwan allurar ta tsira a jijiyar hannunta kamar yadda aka sanar da ita a cikin wasiqar.
Da sauri ta buxe shaddar ta watsa allurar da sirinjin ta dawo gadonta ta kwanta. Sai dai me? Bata rufe awa biyu ba ta soma fitar da wani irin numfashi tamkar ranta zai fita.
Hakan da taji yasa ta tuno da rashin jin qarshen saqon wanda wata qila da akwai batun
da ana son sanar da ita sai dai kash! Har asuba tana fama da numfashi, inda su Deena da Beeba suke kanta, daga qarshe dai dole aka sanar da mahukuntan gidan.
Kafin ma suyi wani abu Rose ta daina numfashi, inda suka tabbatar da rai yayi halinshi. Tashin hankalin da Deena da Beeba suka shiga bai faxuwa.
Kuka suke tamkar kukan rashin iyaye, suna ji suna gani aka fice da gawar Rose xin. Duniyar sai ta qara duhunce musu, shi kenan Rose ta mutu?
“Ta huta da baqin ciki.” Cewar Deena
.
Haka aka yi ta kakabin mutuwar Rose, inda ake ta faxar ciwon kwana xaya tal tayi ashe bankwana take yi da duniyar.
Aka gama rubuce-rubuce akan Rose, kafin a kaita kushewa a rufe saboda an rasa duk wata hanyar da zata sadar da wani nata bisa
haka aka binneta.
Su Deena kuwa suna ta jimamin mutuwar Rose, kowace tayi fatan da ma ita ce ta mutu ba Rose ba, saboda baqin cikin da ke wa
lankeluwa da rayuwarsu.
Su kaxai ke jimamin su, su kaxai ke kewar Rose, su kaxai suka damu da ita da rashinta.
Deena ta waiwayo inda ta hango Gwanar rawa sai taka rawarta take yi tamkar Ibadarta.
Ta share hawayenta. “Kin huta Rose, kin huta da baqin cikin duniyar nan, dama nice ke da na ji daxi.” Haka suka kasance cikin alhini da jimami. Idan sun tuno Rose sai suyi kuka.
Ana haka Sintia ta iso da son taga ya ya aka qarke? Ai ko ta samu labarin mutuwar Rose, wadda aka binne a xazu.
Da sauri ta fasa kukan rashin ‘yar’uwarta. Ta fice tana sharar hawaye. Don haka kai tsaye ta wuce maqabarta da ta tabbatar da can ne aka kai Rose don su xora karatu na gaba.
Mai karatu a nan zan tsaya domin in xan numfasa, don haka sai a biyo ni a cikin littafi na biyu, tare suke da na xayan.
Taku har kullum;
HADIZA BARAU (GIDAN IKO)
(Maman Assibi)
08035191669 – 08078500055