Showing 9001 words to 12000 words out of 28383 words

Chapter 4 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx

“Uhum! Lafiya qalau na tashi. Suna kuwa zan amsa kowane daga gare ka.”

“To amsa Beauty kawai.” Ya faxa a taqaice.

“To na amsa Sir!”

Yayi dariya sosai. “Haba dai Sir, maimakon ki ce min

Darling

sai ki ce min Sir? Gaskiya ko zan amsa Sir to ba dai ke ba,

Darling

kawai za ki ce min in amsa.”

Suka dubi juna saboda a

Handsfree

tasa wayar. Deena ta tave baki tana zubawa Rose ido tamkar wata

TV

. Rose ta ci gaba da magana. “Kenan dai za ka fi son

Darling

xin a kan Sir?”

“Haka nake nufi.” Ya bata amsa.

“To an gama



My Darling

…”

“Yanzu naji daidai, wai Xanfulani ya ji wuta. Ina fa son ganinki ko zai yiwu?” Ta ce, “Me zai hana?” Ya ce, “To faxa min inda ki ke zan turo a xauke

ki.”

“A’a ba sai ka turo ba, faxa min inda zan same ka kawai.” Ya ce, “Da kin bari na turo zai fi nuna darajarki a gare ni.” Ta ce, “Nima xin don in darajaka yasa nayi hakan, baban mutum irinka fa sai da sirri ko?”

Ya ce, “Wannan haka yake Beauty, to ki iske ni a Sheraton, ai ya yi miki ko?” Ta ce, “Eh yayi ai

zavinka shi ne nawa.” Ya ce, “To ina jira.” Da haka suka sallama. Ta dubi

su Deena da suka zuba mata ido.

“Oh ni Rose! Na zama

TV

ne irin wannan kallo haka?” “Ai nayi mamakin yadda ki ka saki baki kina ta zubo zance tamkar babu wani tabo na namiji a zuciyarki. Ai inda ni ce ina mai tabbatar miki sai nayi suvutar bakin xurawa uwarshi ashar, musamman wancan tsinannen sunan da ya ce ki kira shi da shi (Darling).

Ya tuno min da lokacin da ake faxa min shi a cikin yaudara. To da daga nan zan xura ashar.” Ta ce, “Kina mantawa da Mage mai kwanciyar xaukar rai Deena? Ai matuqar zai ji daxin kalaman nan to tabbas zai ji daxin ratsa maqoshin shi da wuqa zata.”

Rose ta miqe “Ni dai bari in je mu gama da My D.P.O in dawo, azal ko tsautsayi ya aiko wani.” Cikin shigar ka gani qwalelenka ta fice tana zuba qamshi.

Bayan ta fente fuskarta da

make up

. Rigar

body hug

ta saka wadda ta matse ta, ta bayyanar da tsarin halittarta. Sai dogon wandon fensil tare da flat xin

cover shoes

na (TOMS). Yadda take taku ko ina na jikinta rawa yake, dole ta burge wanda ya kalleta, bare wanda tayi don shi. Don ta kula da

kallon da ya dinga qare wa qirjinta a ranar

, don

haka ne

tayi nufin yaudararshi.

Taxi

ta dire ta a

Gate

xin Sheraton, ta sallame shi ta doso cikin otal xin, tana tafe tana kissima yadda

film

xin zai qare.

Ta zaro wayarta ta kira shi.

“Gani fa na iso Sir,

…wai!

Darling

.” Ya ce, “Yauwa, ya ki ke mantawa ne, ai ko zan amsa Sir, to sai dai na qasa da ni ba ke ta sama da ni ba.” Ta ce, “Uhum! Haka dai ka ce…” Ya ce, “Haka ne mana, ba ki san ko Sarki a waje yake Sarki ba, idan yazo ga masu gidan shima abin sarauta ne ba?” Ta ce, “Haka ne kam.” Ya ce, “To bari in zo in tarbi kayana.” Ta sauke wayar tana tunanin abinda yasa maza suke yaudarar mata, namiji shi ya koya wa mace yaudara har tazo ta zarta shi iya yaudarar.

Har ga Allah wata macen babu yaudara a ranta, amma namiji ya ga tsarinta ya burge shi to sai ya ga bari ya yaudare ta. To ita kuma daga nan zata xora xan bar yaudarar maza, saboda ta gama shata musu layi. Idan namiji xaya ya yaudare ta to ita sai ta yaudari goma. Me yasa to?

Maza! “Mits!” Taja tsaki saboda takaici. Ta hango shi ya taho cikin farar jallabiya me dogon hannu, ya kusa cimma shekara hamsin amma bai

bar mayatar bariki ba a ranshi. Ya miqo mata hannu wai suyi musabaha. Ta miqa mishi nata hannun yayi saurin janyewa.

“Au! Ashe fa ana kallonmu kar a kai ni gaba a ce an ga ina musabaha da Beauty.” Ta ce, “Uhum! Ai naga kamar ba ka son sirri…” Ya ce, “Ke! Ai nafi kowa son sirri

, ke dai shigo daga ciki.” Ta bishi a baya a zuciyarta tana tsine mishi.

“Tsinanne, matarshi na gida ta tsare mishi kanta da ‘ya’yanta da gidanshi da dukiyarshi, amma shi yana otal yana sheqe ayar shi da qadangarun Bariki, kai! maza? Uhum, ai in dai ina raye a duniya maza sun gama jin daxi kafin mu tankaxa qeyarsu zuwa babban birnin barzahu…”

Suka isa xakin da ya kama yana gaba tana

biye. Sai dai me?

Maimakon ta same shi shi xaya, sai ta iske shi su wajen biyar. Ba ta tsinke da lamarin ba sai da taga ya yi wa qofar

key

ya datse.

A take ta gano abinda hakan ke nufi. Ko a fuska bata nuna tsananin razanar da tayi ba, ta basar. Ya ce, “Kin ganni baqi nayi kafin ki iso, da na san za su zo ai da ban kira ki ba. Amma ai yanzu zan sallame su don na lura takura min suke son yi. Bayan sun san idan nazo otal hutu ne ya kawo ni ba.

Ai ina jin aje aikin Xansandar nan zan yi. Haba! A yi aiki kullum mutane ba za su qyale ka ba. shiga ciki ki jira ni in sallame su.” Duk wannan dogon surutun da yake yi bata tanka mishi ba, don haka da ya bata umarnin shiga ciki kasancewar xakin ciki da falo ne, sai ta shiga ciki ta bar su a falon, amma fa kunnenta a buxe da son ta ji abinda za a tauna, domin ko ta fahimci tarkon da aka xana mata ya gama kama ta a wuya.

Kamar daga sama taji ya ce, “Ina wayar nan ta Olukayode? Duba min cikin

recording

xin da ya yi da wannan, ai kun shaida fuskarta ko?” “Eh.” Suka tabbatar mishi. “Ina so ku duba ta cikin wayar Olukayode don ku tabbata ita ce ko ba ita ba ce?”

“Ai ranka ya daxe ita ce babu ko ja.”

“To gata nan mu mun gama aikinmu

, sai ku sanar da shi Tukur Sambon in yaso gobe ko

Monday

sai su zo su wuce da ita. Amma kafin nan zamu aje ta a

Station

kafin zuwansu.” “To shi kenan Sir, muna iya tafiya?” Ya ce, “Eh kuje amma ku bani wayar shi marigayi Olukayode don in tabbatar mata da abin da ke ciki.”

Suka miqo mishi wayar suka yi mishi sallama, bayan sun sara sun kuma qame qam! Har da bushewa.

Tana ji suka fice tayi wani banzan murmushi tare da godewa Allah da yasa suka fice

su ka bar shi shi xaya qwal, yadda zata fanshe yaudarar da ya yi mata.

Sai dai kaxan ya rage ta zube a qasa a sume saboda shafawa tayi inda ta soke bindigarta taji wayam! Ya aka yi haka? garin ya ya? Shi kenan ta mutu! Tana cikin tsaka me wuyar fita ya shigo. Amma da yake jaruma ce duk irin ruxanin da ta ke ciki bai hanata binne abin a ranta ba.

Koda wai ba zai tava gani a fuskarta ba. Ya miqo mata wayar Olukayode yana murmushi. “Ko kin san wannan?” Ta karvi wayar inda tayi arba da hirar da suka yi da Kayoden, wai ashe

recording

yake ita bata sani ba.

Ta zuba wa hoton me motsi (

V

edio) ido, inda yake zubo mata tambayoyin tana bashi amsa har zuwa inda ta sakar mishi harsashin, da faxuwar da wayar tayi saboda sakinta da Kayoden yayi a qasa sakamakon bankwanan da yake da duniya.

“Ehem! Kin san shi?” Ta amsa kanta tsaye. “Qwarai na san shi.” Ya ce, “Labarin mutuwarshi fa? Ko kin sani?” Ta sake amsawa da ta sani. “Me yasa ki ka kashe shi?” Ta ce, “Saboda ya yaudare ni.”

“Ya yi miki me?” Ya tare ta saboda ya sava alqawarin da yayi min…”

“Kamar wane kenan?”

“Irin wanda kayi min.”

Yayi murmushi “Ni ai ban yaudare ki ba…”

“Shigo-shigo ba zurfi kayi min?”

“Yanayin aiki ne kawai.” Ya faxa yana murmushi.

“To Allah ya qara

qira.” Itama ta faxa, ta miqe “Idan ka gama min jaridar ina da abin yi a gabana.” Ya sake yin murmushi. “Jarida fa ai yanzu aka soma! Ba a ma fara ba.” Ta ce, “Ban gane ba?” Ta faxa idonta a nashi. “Eh, ina nufin ke me laifi ce da ba zan iya barinki ki tafi ba. Yanayin aiki ne yasa nayi miki abin da nayi, amma ni ba irin wanda ki ke tunani ba ne, ban tava sanin

wata mace bayan tawa ba, bare har in faxa bariki.”

Ta ce, “Me yasa ka yaudare ni a karo na barkatai? Yaudara ce tasa na kashe Kayode bayan ya karya min alqawari. Yaudara ce sanadin da Kayode ya sanni har yake nemana. Yaudara ce ta jefa ni a baqin cikin da har in mutu ba zan yafe ba. Shi ne kaima ka xora a kan ta waxancan?

Me yasa maza ku ka xauki yaudara ado? Me yasa ku ka zavi ku yaudare mu a kan ku tarairaye mu ku bamu farin ciki a rayuwa? Me yasa ni bani da sa’a duk namijin da zai rave ni sai ya yaudare

ni? Me yasa rayuwa ta zo min da maza mayaudara? Allah na gode, Allah na gode.

Amma me ka ke nufi da ni? Me yasa ba ka fito min a me bincike a kaina ba? me yasa? Me yasa..?” cikin sauri ya tari numfashinta da cewa, “Kar ki damu fa, na faxa miki yanayin aiki ne, babu abu xaya da zan miki wanda

zai nuna na yaudare ki, ko

station

ba zan kai ki ba bare sauro ya ciji kyakkyawar fatarki har kiyi tunanin na kai ki

Cell

har sauro yayi miki illa.

Don haka zan xauke miki duk wani abu da zai cutar da ke ta hanyar kulawa da ke, ke a otal xin nan za ki kwana har zuwa inda zan miqa ki ga su Tukur Sambo, ki kuma faxi abinda duk ki ke buqata zan sa a kawo miki shi. ban dai so ki jefa ni a layin mazan da suka yaudare ki.”

Ta ce, “Sai dai kar a kuma, dole ne sunanka ya fito a cikin waxanda suka yaudare ni. Amma babu komai lokaci na zuwa.” Bai kuma bi ta kanta ba sai ma ya kira wayar matarshi ya sanar da ita kar taga bai dawo gida ba yanayin aiki ne ya tsaida shi, amma yana lafiya. Suka gama wayar inda ya kira wani Xansanda ya ce a kawo wa Rose abin tavawa da na sha.

Haka ya tara mata ababen buqata amma ko ruwa bata sha ba. Washegari motar

Black Maria



wadda ake wa laqabi da shiga ba biya fita da Allah ya isa, ta shigo harabar otal xin na Sheraton. Gandiroba biyar suka fito, xaya daga cikinsu ya soma kiran wayar D.P.O Xanjuma ya sanar da shi gasu sun iso.

Yasa aka kawo su xakin da suka kwana shi da Rose, wadda tana cikin uwar xakinshi yana falon, sai dai su duka babu wanda ya runtsa. Shi dai yana tsoron ya kwanta Rose ta sulale. Ita kam takaicin yadda rayuwa zata yi da ita idan aka maida ita Lagos a gidan kason qiri-qiri, alhalin yanzu laifinta ya qaru, koda laifin kisan Olukayode kaxai aka tsaya to hukuncinta me girma ne.

Idan aka yi duba da muqamin Olukayode. Sai dai kuma a gefe xaya tana jin bakin rai bakin fama ba zata tava bari namiji ya yi nasara a kanta ba.

Tausayinta xaya su Deena da za su shafa su ji babu ita babu dalilinta, tasan hankalinsu zai tashi alhalin bata san inda rayuwa ta cillata ba.

D.P.O ya buxe musu xakin suka shigo. bayan sun kai gaisuwa da cike-ciken takardu ya damqa musu Rose da wayar marigayi Olukayode. Suka yi godiya tare da sarawa gare shi suka xaurawa Rose ankwa suka ingizata cikin motar ta shiga ba biya wai fita da Allah ya isa.

Tafiya me nisa zuwa Lagos, sai misalin biyu na rana suka iso Lagos, Rose ta gama jigata na farko dai ga gajiya ga yunwa, ga kuma duhun da ke shimfixe a cikin motar. Rabonta da abinci tun

break first

xin jiya da safe aka buxe ta haske ya haske mata ido inda taji wani tsam! Kai tsaye aka wuce da ita zuwa ofishin Gandirobobin

.

Tukur Sambo wanda

case

xin mutuwar Kayode yake hannunshi, shi ne kuma wanda yafi me kora shafawa a kan

case

da kuma Rose, shi ne ya soma kewaye Rose xin yana qare mata kallo da jinjina qarfin halinta na yin laifi

kashi biyu ko ma uku.

Laifin guduwa daga gidan kason da kuma laifin kisan Kayode, wanda shi yafi komai zafi a cikin laifukanta, da kuma laifin da ya kawota gidan yarin tun farko. Koda ace za a iya yafe mata laifinta biyu, to ba za a yafe mata laifin kisan Kayode ba.

Ya gama zagayeta tamkar me son ya gano yadda aka faro da yadda za a qare. Fuskarshi a gimtse tamkar wanda aka yi wa albishir da makomar Jahannama.

“Ina so in ji abinda Kayode yayi miki ki ka kashe shi? Koda yake wannan alhakin kotu ne amma duk da haka ina son in ji yadda aka yi ki ka mutu kuma ki ka dawo duniya?”

Tayi murmushi kafin ta xauke kanta “Ni fa ban tava jin wanda ya mutu ya dawo ba ko a cikin addininmu mutuwa guda xaya ce.” Ya ce, “Na fi ki sanin mutuwa guda ce, amma ke da akwai wani mugun qulli a ranki. Ta ya ya ma ki ka mutu kuma ki ka vulla a garin Abuja?”

“Ta iya yiwuwa ko uwata ce ta sake haifata, tunda ka yarda ana mutuwa a dawo

.” Ya ji matuqar zafin baqar maganar da ta gasa mishi, tamkar ya damqi maqoshinta har sai ya ji ta daina numfashi.

Ya ce, “Daga kanki ko uwar taki zata gane asarar haihuwa take yi.” Itama ta ji zafin hakan fiye ma da shi. Amma da yake duniya ta koyar da ita abubuwa masu yawa, sai tai ta maza. Ta ce, “Uhum!

‘Yallavai ba fa shegu ta haife mu ba, duk da ubanmu take haifar mu. Da ace a shegu ta haife mu da ban musun maganarka ba. a ganina a haihi shege ba uba shi ne asarar haihuwa…” Dau! Ya dalla mata mari me shiga jiki.

“Lallai na yarda ke tsinanna ce, ni za ki duba ki ce min shege?” Ta dafe inda ya mareta tana kallonshi. Ta ce, “Saboda ka tambaye ni na baka amsa? To ya zamo na qarshe, wallahi don na rantse da Allah ka sake gigin kai hannu fuskata sai kayi nadama. Babbar mace ce ni da na zarta

tozarcinka, in don nayi kisan kai ka soma gana min azaba ta hanyar mari to ai hukuncina ba a hannunka yake ba.

Sannan kuma ba Gyatuminka na kashe ba bare ka huce haushinka a kaina.” Ya ce, “Yo ni ki ka kashe Gyatumina ai ba zan xata da nisa ba. A yanzu ma da ki ka kashe ubangidana ai ba zan sassauta miki ba…”

Ta tari numfashinsa cikin fushi, “Allah Ya tsinewa wanda ya yi min sauqi…” Kafin ta rufe bakinta ya sake auna

mata wani marin wanda ya zarta na farko. Ta ko qurma wani irin ihu me qarfin gaske, kafin ta zube a qasa.

Sauran ma’aikatan suka shigo a ruxe suna kallon Tukur da yake mazurai, ga kuma me laifi a zube a sume.

“Ya aka yi ne? me ya faru?” Ya yi shiru yana bin Rose da ke shimfixe qasa da ido. Aka soma kuza mata ruwa amma ‘yar duniyar tayi bakam ta qi ko motsawa. Duk da tana jin duk abin da ke faruwa a nufinta na qullawa Tukur Sambo mugun qullinta, don ya kiyayeta nan gaba.

Sai da ta ji ana batun asibiti kafin ta kawo numfashi. Ta miqe cikin nuna ta galabaita, ta dubi Gandirebobin da ke zagaye da ita sai ta soma faxin “Wayyo qirjinta.” Sai kuma ta fashe da kuka tana ita ba zata yarda ba don tayi kisa a tozartata ba.

“Me ya faru ne?” In ji wani daga cikinsu. Ta dubi Tukur Sambo “Qirjina ya kama don kuma naqi yarda ya soma kwaxa min qaton takalminshi a cikina har yana taka

min ciki. Wallahi-tallahi ba zan yarda ba, sai na nemi haqqina.”

Zufa ta karyo mishi. Duk da ba halinshi ba ne kula mata barkatai, to amma idan aka dubi shigar Rose xin wadda ba kowane namiji zai iya xauke kai ba sai aka yarda, kasancewar ana samun bara-gurbi a cikin ma’aikatan, musamman ma su kula da Gidan Kason na mata, shi yasa ba a musa qagen Rose a kanshi ba.

Kowane da abinda yake faxa na rashin daidain Tukur Sambo, wanda ya kasa furta ko uhum, wanda hakan ya tabbatar da zargin yayi abinda ta ce ya yi. Suka soma bata haquri a kan ta bar maganar.

Ta ce, “In na bar maganar kama min qirji da ya yi fa? Kuma ni yanzu nan zuciyata da cikina ciwo suke.” Kawai sai ta koma ta kwanta qasa tana birgima. Bisa tilas suka kwasheta zuwa asibiti

, inda aka rubuto magani me yawa don qarya da gaskiya ta haxu, ciwo ko kala-kala ta furta. Kuxi kusan dubu sha biyu ta ciwo bayan an ce tasha

Tea

me zafi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login