Showing 21001 words to 24000 words out of 28383 words

Chapter 8 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx

Kai hanyar vata dai ashe yawa gare ta a duniya.

Suka gama kwaramniyarsu, wasu suka kwanta suna munshari, wasu kuma suna ta buga wasa da karta, dare yayi nisa inda mafi yawan Fursunan suke ta jan munsharin bacci inda kuma Deena idonta yake biye babu bacci.

Can ta jiyo nishi wanda ya sata waigowa, inda ta iske Gwanar rawa da wata qabilar Igala suna ta shafe-shafe.

Gabanta ya sara dasss! Tayi saurin runtse ido tana jan tasbihi, Allah ka kiyashe mu tavewa.

Washegari Gwanar rawa ita ba wa qabilar nan abin kari inda haushi ya cika Atika, don me Fadilar zata yi mata kishiya?

Deena ta fito inda Rose ta iso inda take tsaye, “Ya ya dai Deena?” Ta ce, “Lafiya qalau Rose, an tashi lafiya?”

“Wallahi qalau ne, ina Beeba ne?” Tana banxaki. Gata nan ma ta fito.” “Ya ya ne in zo ta samu?” In ji Be

ebar. Suka gaisa a mutunce, inda Beeba ta rage murya.

“Kun san jiya nayi mugun gani a kan Gwanar rawa?” “Ahab!” In ji Rose “Ai kaxan ma ki ka gani, ko ma in ce yanzu ki ka fara gani. Babu yadda Gwanar rawa bata yi ba a kan ta neme mu ni da Beeba muka nuna mata mu ma qwallayen ‘yan iska ne.

Ai shi yasa za ki ga bata fiye shiga harkarmu ba. Ke xin ma na san ta xana miki tarko, shi yasa ki ka ji na ce kar ki yarda da ita ‘yar

luwaxi

ce

.”

Beeba ta qyalqyale da dariya “Kai Rose

manya! Maza su ne ‘yan luwaxi, mata kuma ‘yan maxigo ake cewa.”

Ta ce, “Ke bar su haka Beeba duk tsinannu ne, fushin Allah zai tabbata a kansu.”

“To Allah ya shirye su in masu shiryuwa ne.” Cewar Beeba. Rose ta ce, “A yadda na samu labari wurin wata Barira da na iske gidannan, wadda a yanzu shekararta biyu da rasuwa. Ta sanar da ni itama nan ta iske Gwanar rawa amma ta samu labarin ‘yar neman mata ce, wadda ta shahara ta bunqasa a kan harkar.

Matar da tazo mata jiya har ta kawo mata kayan nan itama abokiyar harkarta ce. Ita ce ma ta saka gwanar rawa a harka, don ga yadda ta faxa min ta ce min har qasar waje suke fita suyo harkarsu da Turawa.

Da na tambaye ta to me ya kawo ta gidan Kaso? Sai ta ce min wai wata yarinya ce ita Gwanar rawar ta gani tana so, to ita yarinyar sai aka yi sa’a irin ‘yan islamiyar nan ne, sai ta nuna ita Allah ya kashe ta in dai zata yi wannan baxalar.

Don haka kar a qara yi mata wannan maganar. Duk yadda Gwanar rawa taso ta yaudaro yarinyar abin ya gagara, domin ko Allah ya wanke mata zuciyarta.

Sai dai a gefe xaya kuma aka jarabci Gwanar rawa da son yarinyar nan saboda an ce wai idan suna sha’awar mutum idan ba lalata shi suka yi ba hankalinsu ba ya kwanciya.

Don haka sai hankalin Gwanar rawa ya yi masifar tashi, babu abin da take so face wannan yarinya. Ita kuma ta kafe kan ra’ayinta.

Wannan harkar ta kawo musu kuxi ba na wasa ba, shi yasa Gwanar rawa me kuxi ce, don haka sai tayi amfani da basirarta da kuma kuxinta inda ta nemo wani kyakkyawan matashi me haibar da mata suke buqata, ta tsara mishi abinda take so

ya yi mata.

Shahid matashi ne xan qarya, duk da kasancewar ya fito daga gidan talakawa, akwai son qarya da fantamawa, gashi ba shi da kuxi sai dai yana karatu wanda ya tara dukkan burinshi a kan karatun.

Sai ga Fadila da son yayi mata aikin da za ta biya shi kuxi ba na wasa ba. Da azamar shi ya amsa da zai yi kowanne irin aiki ne, duk da bai san irin aikin ba.

Ta fuskance shi ta ce, “Ka gane ko Shahid, wata yarinya ce ni ke masifar so, saboda ban tava ganin irinta a duniya ba, komai ta haxa. Ga

ta fara ce tas! Ga qira irin ta mata, kai duk yadda zan fasalta maka ita ba za ka gane ba sai ka ganta kawai.

Babu abin da ban yi ba, amma ta qi aminta da ni. Babu irin alqawarin da ban yi mata ba, babu irin kuxin da ban juye mata ba amma ta qi saurarena.

Ni kuma na lashi takobin samunta ko ta wace hanya, shi ne ni ke so in yi amfani da kai, nasan babu macen da za ta ganka bata yi wa kanta burin aurenka ba.

Ina so kaje kuyi soyayya da ita a zuwan aurenta ka ke so kayi, idan ta baka haxin kai to sai ka san yadda kayi ka yaudaro min ita gidana.

Idan ko bata yarda ba, to in ma auren ya kama sai ayi, burina dai in same ta. Zan biya ka kuxi ko nawa ka ke buqata matuqar dai kayi nasarar kawo min ita.

Don haka zan gwada maka gidansu da kuma ita kanta, in yaso sai ka xora daga yau ma.”

Ta xauki Shahid a motarta zuwa gidan su Asma’ul Husna wadda ake kira Husna ta nuna mishi gidan, in da ya ce ta bari tunda ta faxa mishi sunan in yaso idan yazo sunan kawai zai yi amfani da shi, haka kuma aka yi.

Washegari Shahid ya nufi gidan su Husna, bayan wanka da ya xauko. Husna ta fito da xaurarriyar fuska saboda bata son suntirin maza

.

Sai dai me? Duk yadda Fadila ta fasalta tare da zuzuta mishi Husnar, sai yaga ashe bata faxi komai a kyawunta ba.

Lallai dole ta ruxe, itama kenan mace da ta ganta ta ruxe to wane namiji ko zai ganta ya kauda kai? ya yi murmushi wanda yake siye imanin mace.

“Naso a ce ta sama na biyo wurin tallata kaina, sai dai na kasa haqurin zuwa gare ki. Amma zan xora da ban haquri kasancewar ban sanar da ke zuwana ba bare ki bani izini.” Ya tare ta da wannan maganar.

Ta dube shi inda taji zuciyarta ta buga dam! Saboda kwarjininshi, amma da yake mace ce sai ta maze.

“Malam wa ka ke nema ne?” Ta tambaye shi cikin dakewa. Ya sake faxaxa murmushin da ke maqale a fuskarsa ya ce da ita.

“Husna nake nema, kuma na gan ki, da fatan kin wuni lafiya?” Ta waigo tamkar tana neman wani ko wata kafin ta maida kallonta a gare shi.

“Malam ina da uziri don Allah ina son in koma gida.” Ya ce, “Babu laifi Husna, amma don Allah ki bani lokacin da zan dawo saboda a yanzu dole nayi miki uzuri kasancewar ban sanar da ke ba.”

Ta sake dubanshi a karo na biyu. “Kayi haquri, don ni matar aure ce!” Yayi murmushi “To ba damuwa, zan je ga Baba in sanar da shi kin ce min ke matar aure ce, nasan shi zai faxa min gaskiya.”

Da sauri ta ce, “Ban aike ka ba.” Ta tari numfashinsa. Shima xin ya tare ta “Nima ba cewa zan yi kin turo ni ba.” Ganin zai ja ta da tsayuwa yasa ta shige gida. Yana tsaye kafin ya wuce Dattijon ya iso inda suka gaisa a mutunce, ya nemi sanin wa yake son gani? Inda ya nemi izinin zuwa qurin Husna.

Bayan ‘yan tambayoyi irin kai waye? Dattijon ya ce yaje sai bayan kwana biyu ya dawo.

Da ya dawo bai voye wa Fadila yadda suka yi da Husna da ubanta ba.

Don haka ta ce “Kai dai ka jajirce Shahid, yaqin yaxa manufa yana da wahala, musamman ga mace irin Husna. Kayi

duk yadda zaka yi aikin kuxi ka ke. Don haka

ka koma bayan kwana biyun.”

Haka ko aka yi, inda ya koma ga Mahaifinta ya tako sa’a uban ya amince mishi zuwa wurinta. Sai dai inda matsalar take shi ne Husna.

Domin ko ta nuna mishi ta rufe babin so, tunda aka yaudareta. Yayi murmushi duk a cikin son ya siye zuciyarta.

“In ban da abinki Malama Husna, don wani ya yaudare ki sai aka ce miki duka kowa ma mayaudari ne? zan so ki bani dama ki ga irin nawa salon, idan ki ka ga abin da bai yi miki ba to ki kira maza da kowane irin suna.

Ki kuma yi masu jimlar su xin mayaudara ne.” Ta ce, “Ni dai haquri zan kuma baka, don ba zan tava bari namiji ya sake yaudarata a karo na biyu ba, na kuma kyautata zato a kanka. Amma dai uhum umm!”

“To Malama Husna kenan, ba za ki fidda miji ba haka za ki yi ta zama?” “Haka!” Ta faxa alamar ta soma qosawa.

“To ai ko kamar Baba ba zai bar ki ba.” “Haka ni ke nufi idan ya gaji da jirana sai ya xauko ko ma wane irin namiji ya bani, na tabbata zavin shi ba zai cutar da ni ba.”

Ya ce, “To in ko haka ne ai ina ga kamar ni xin zabinshi ne, tunda ya bani izinin zuwa gare ki.” Ta dube shi idonsu ya haxu, inda ya sakar mata wani kallo me tafe da saqonni masu yawa.

Ta duqar da kanta tana nazarin maganarshi. Uhum Husna? Ta kasa tankawa. Da dai ya tabbatar da ta zo hannu sai ya soma gabatar da kanshi gare ta.

“Sunana Shahid Shu’aibu, na ganki ne bayan kin dawo daga Makaranta, na kasa tunkararki ne saboda kwarjini har dai na fidda tsoro da shakka na iso gare ki, mayar da qoqon barar qaunata Husna yana nufin shiga kowane irin hali, ki tausaya min don Allah kar in zube miki a nan.” Ya qarasa maganar da salon zolaya.

Tayi murmushi “Uhum!” Ya dubeta “Ban ji abinda ki ka ce ba my Husna?” A hankali ta ce mishi “Allah ya zava alheri.”

BABI NA BAKWAI

“T

sinanne kenan, kiji zai kuma yaudararta a karo na biyu, kai maza sai sun shiga uku!”

Rose ta dubeta ta ce, “Bari kiji yadda ake qarewa mana.” Suka bita da ido suna baza kunnuwa, inda Rose ta xora daga inda ta tsaya.

“Soyayya ta yi nisa a tsakanin Husna da Shahid, wani irin so Husna take wa Shahid, babu inda sunan Shahid bai zagaye ba.

Tun daga gidansu zuwa qawayenta, wadda duk take son su daidaita da ita to taso Shahid, wadda kuma ta kushe Shahid to ko gaisawa sun gama da Husna.

Duk abin da ake ciki Fadila tana sane, wani abun ma ita ke xorawa. Yawan zaryar Shahid yasa Baban Husna ya nemi da manya su shigo saboda duk yadda ya xauki Husna da kamewa ta zarta nan.

Domin ko duk yadda yaso ya yaudareta ya miqota ga Fadila abin yaci tura, domin ko ya gane mata suna suka tara, matuqar mutum ya samu Husna a matsayin matar aure to ko shakka babu Allah ne ya azurta shi da mace tagari.

Ganin haka yasa ya kasa yin nasarar kaita ga Fadila, sai gashi kwatsam saqo ya riske shi na manya su shigo cikin lamarin. Ya amsa da insha Allahu, suka rabu gabanshi na sarawa, inda ya dire a gidan Fadila ya sanar da ita abinda ke faruwa.

“An zo wurin Shahid, har auren sai ayi ai in dai kuxi na magani to sai na cika burina a kan Husna. Zan shirya maka waxanda za su je a matsayin masu neman aure.”

Ya zuba mata ido yana nazarin wasu al’amura da ke tunkaro shi. fadila ta dire mishi kuxin a gabanshi. “Sai ka soma shirin biki da xinkin kayan da za ka saka yayin hidimar.”

Ya xauki kuxin yana sakawa aljihu. Ya miqe da shirin tafiya

“Ji mana Shahid.” Shahid ya juyo yana kallonta. “Na manta ban sanar da kai ba.”

Ta xan saurara kafin daga bisani ta ci gaba da cewa, “Shahid ina so koda Husna ta fuskanci manufar aurenku, duk abin da zai biyo baya bana son ka saki aurenta, saboda nasan idan tasan ba sonta ya kai ka aurenta ba dole ne zata nemi ka sake ta, musamman idan na bayyana mata manufar aurenta.

Don haka duk tsallenta ka riqe qaryar aurenta koda sun yi barazanar kai ka kotu, ni zan tsaya maka amma fa bana son ka tava min ita, tawa ce ni xaya.”

Shahid ya ce, “Kar ki damu, ni ina jin ma idan aka xaura auren zan samfe ba zata sake ganina ba, sauran ya rage tsakaninku.”

Ta ce, “Yauwa, ashe kana ganewa.” Don haka ya fice daga gidan Fadila Gwanar rawa. Sai dai an samu tsaiko wurin samo waxanda za su je gidan su Husna a matsayin manyan Shahid.

Don haka shi da kanshi ya samu manyan da za su wakilce shi aka tura su gidan su Husna, inda aka tsaida wata biyu masu zuwa.

Tuni Fadila ta haxo lefe na garari inda ta ce ai ita za a yi wa kwalliyar, hatta da gidan da za a zauna ta kama gida na ke ce raini.

Don haka lokaci kawai za a jira, inda kuma a gefe xaya soyayya sai gudana take tsakanin Husna da Shahid, inda kuma a gidan su Shahid ba a san wainar da yake toyawa ba, kasancewar shi maraya ubanshi ya mutu.

Sai dai mahaifiyarshi wadda tsufa ya soma kamawa, kasancewarshi Shahid xin yana da manyan yayu sai qanwarshi da ke binshi wadda

ta zamo auta. Hakan yasa suka zama su biyu a gaban mahaifiyarsu, inda ‘ya’yanshi suke aure a gidan wasu mazan.

Hakan yasa ya zamo shi ne namiji mataimaki ga uwarsu. Aka ci gaba da shirye-shiryen biki, amma fa uwarshi bata sani ba.

Kwanci tashi aka ce asarar me rai, inda aka shiga

biki. Hidima kala-kala sai dai Amarya ta ce bata buqatar bidi’a, walima kurum ta shirya.

Duk yadda Ango yaso ayi koda faty kala xaya amma ta ce su nemi albarkar aure ta hanyar wa’azi da walima.

Bisa dole ya bari ya kuma tabbatar da Husna samunta ba qaramar nasara ce a rayuwa ba a matsayin mace tagari. Bisa dole ya bita da yadda take so.

Anyi varin kuxi saboda Ango Shahid Fadila ta riqe mishi kan macijin har zuwa ranar da aka xaura aure aka kuma kai Amarya a gidan da Fadila ta kama musu da tsadar gaske.

Saboda a cewarta babu abin da ba zata iya yi ba a kan mallakar Husna. Kashegari aka yi walima

, inda Fadila ta soma shirin zuwa gidan Amaryarta ta kwana don ba zata yi saken bari a xauki dogon lokaci ba.

Ta xauki wanka na tashin magana, da wani matsiyacin leshi m

e ruwan goro (Orange), fuskarta da kwalliya irin ta gwanayen da suka iya tsara kwalliya.

Inda ta fito tamkar ‘yar tsana. Kai su Fadila an iya gayu. Ta doshi motarta ta shiga ta fizgeta da son ta isa gidan Amarya saboda xokin ta xora ido a kan fuskar Husna. Tayi wani murmushi na mugunta.

Ita fa nan a dole ga ta Allah ko me ta xauki kanta? To ai yau zata gane wayonta bai fice a kira shi a cikin cokali ba. Ai ita in dai ta haxiyi yawu a kan mace to duk runtsi, duk wuya sai ta biya buqatarta.

Ita gidansu ma ta baro ta shigo bariki sai Allah yayi mata gam-da-katar a cikin bariki ta faxo a cikin masu neman mata har ta fito duniya ta santa, ta kuma samu kuxi na ban mamaki many an mata ko babu wadda ba sa harka.

Har ta zamo jan

wuya, sai ga shi wata ‘yar jaririyar yarinya zata kawo mata cikas da matsala, ai sai dai ta ce ba a haife ta ba.

Ta iso katafaren gidan wanda har Maigadi sai da ta aje saboda tsaro. Ta faka motar ta fito tana

taku irin na manyan mata, inda Maigadin ya taho da sauri ya karvi jakarta yana gaisheta.

“Yauwa Hambali, na gode.” Ta buxe Jakarta ta xebo kuxi ta bashi ta shige cikin gidan. Sai dai me? Gidan tsit babu motsin kowa da komai.

Mamaki ya kama ta, ta bankaxa xakin inda take zaton ganin Amarya sai dai babu ko allura a xakin. “Ah! Me ke shirin faruwa?” Ta kewaya xakunan gidan baki xaya amma babu motsin komai.

Ta dawo inda Maigadin yake. “Hambali ina mutanen gidan suka je?” Ya ce, “Hajiya babu kowa ne a ciki?” Shima ya tambaye ta.

“A’a babu kowa. To wallahi ban san babu kowa a ciki ba tunda aka gama h

idima mutane suka watse ban sake sanin abinda ke faruwa ba.”

Ta dube shi ta ce, “Shahid ya zo gidan a yau?” Ya ce, “Shahid bai zo ba. Gaskiya ina jin rabon da in gan shi tun ranar da kuka zo tare da ke.”

Tayi shiru tana tunani. Can kuma sai ta zuge Jaka ta zaro waya ta doka kiran Shahid, tamkar ba zai xauka ba. Tana dab da tsinkewa ya xaga, inda ta tare shi da tambayar.

“Kana ina Shahid?”

Ya ce, “Ina gida, ya ya ne?”

“Ka zo gidan Husna a yau?”

“Ai na faxa miki ni da an xaura zan samfe, na ma manta da wata Husna a rayuwata, meye?”

“Na zo gidan nan ban tarar da ko tsinkenta ba. Kar fa yarinyar nan ta gane gadar zaren da na haxa mata?”

“Bana zaton haka.” Ya tare ta. Ta ce, “To in ba haka ba tana ina? Amma abinda za a yi jeka gidansu ka binciko min yadda abin yake.”

“To shi kenan, bani minti biyar.”

Da haka

suka aje wayar.

Tana zaune a cikin mota tana dakon Shahid, har tsayin awa xaya da ta sake kiranshi sai ta samu wayar tashi a kashe.

Tayi ta kira amma a kashe, bata tsinke da lamarin ba sai da ta qare yininta a motar tana bulayin neman wayar Shahid, tafi buqatar taji inda Husna take bata samu wayar Shahid ba sai da tsakar dare shima tamkar ba zai xaga ba, a kira na huxu ya amsa.

“Wai ya aka yi ne Shahid ina ta jiran ji daga gare ka amma shiru, ya ake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login