Showing 1 words to 3000 words out of 31066 words

Chapter 1 - HAKURI DA KIYAYYA COMPELET BOOK by Aisha Wakili.txt

27 Sep 2025

529

[19/11 10:35 pm] ‪+234 813 630 9911‬: 👰HAKURI DAKIYAYYA👰
Written by aysha wakili
"(Mrs ahmed)"
*bismillahi rahamanir raheem,,,,,inagodia ga Allah dayabani ikon rubuta wannan littafi inarokonsa yabani ikon karewa lafiya*

*inamika godiata ga dumbin masoyana masu karatun littafina hardama makiyana masu karantawa suna kushewa ngd*

~Gargadi~
*wannan labarin kagaggen labarine banyarda wata kowani yajuyamin ba danhaka akiyaye*

*DEDICATED* *TO Oll reader's*
Page1⃣➖5⃣
Malam zubairu shine asalin sunansa mai almajirai shine asalin sunansa yanada mata biyu da ya'ya biyar uku maza biyu mata ,,,uwargida saude itace me ya'ya uku biyu mata sai namiji daya ,safiya itace babba sai hauwa sai autansu kabir,,,Mairo itace tabiyu ya'yanta biyu duk maza salihu da usman ,,, malam zubairu haifaffen garin katsina ne akaramar hukumar danmusa ,,,,,,gidan malam zubairu gidane nadattako sannan yana tsaye kan iyalansa ,,shiyasa suke zaman lafiya inkagansu bazaka zaci kishiyoyin juna bane ,,,,ya'yan malam zubairu duk sunyi aure autansu kadaine yarage baiyiba wato kabiru kasancewar shine karaminsu gabadaya tunyana yaro yataso dason karatun zamani saidai abun yagagara kasancewar basuda karfi sosai iya secondary yatsaya baicigaba ba yafara kasuwanci ,,cikin ikon Allah lasuwanci yafara bunkasa ,,,nan yabude karamin shago nasaida kayan masarufi ,,,,,,,,,,,ranar yana shago wata budurwa tazo tace masa tanason madara yadauko yamika mata bayan tajuya zata tafi yace malama inbazaki damuba inaso nasan sunanki murmushi taimasa sannan tace sunanta halimatu sadiya ,,,yace ngd malama sadiya kozan iya sanin gidanku babu 6ata lokaci taimasa kwatancen gidansu ta tafi bayan yazaunane yafara tunanin anya zaisamu kar6uwa agunta kuwa saidai bazaiyi kasa aguiwa ba ,,,
Da daddare bayan sallar isha yashirya yabi sahun kwatancen da sadiya taimasa yaisa gidansu yasamu yaro ya aika ba'afi minti gomaba saigata tafito tana ganinshi tai murmushi tagaisheshi nan yagabatar mata dakansa dakuma kudirinsa itama bata wani ja ajiba ta amince suka kulla soyayya ,,,,,,,saidai kabir yana tunanin gidansu sadiya bazasu amince ta aureshi ba sbd bambamcin dasuka samu tawani fanni ,,,,,domin gidansu sadiya masu arzikine shikuma gasu talakawa masu rufin asiri ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,bayan watanni dafara soyayarsu gidansu sadiya suka nemi daya turo magabatansa domin ayi maganar aure yacika da mamaki domin shi atunaninsa bazasu ta6a amincewa ya auri yarsu ba ,,,,,,_nan Yakoma gida yafadawa yan'uwanshi abinda akeciki suka shirya suka tafi gidansu sadiya balaifi antarbesu kadaran kadahan ,,,,mahaifinta yafara dacewa na amince zanbaku auren sadiya kamar yadda tabukata amma inaso kusani cewa nibazanyiwa sadiya doleva sannan bazance karta auri Wanda takesoba saidai inaso kushaida masa daya riketada amanah yakula daita ,,,,,,,,,,,,,,nan dai akayi komai akasa rana ba'adauki lokaciba akayi biki ranar daza'a kai amarya mahaifinta yajaddada mata maganarshi nacewa tunda ita tazabi zama dashi toh kowani Abu yafaru kartai kuka dashi sannan kartazo gurinshi Neman taimako SADIYA ko azuciyarta cewa take insha Allahu baba zanbaka mamaki kuma baza'ata6a jin sirrin aurena va tunda kahadani da masoyina ,,,,,haka aka kai sadiya gidan mijinta ,,,,,suna zaune klw babu tashin hankali saima soyayyarsu dasuke zubawa cikin ekon Allah tana cika wata goma ta suntulo kyakkyawan jaririnta maikama da babansa sunyi murna da wannan haihuwar sosai bama kamar zaid dan gidan yaya salihu daya dawo gidan dazama waiyasamu sabon kani ,,, ahaka akaita kulawa da mejego har ranar suna tazo yaro yaci sunan kakansa zubairu amma sunace masa abba nan sadiya tacigaba dakulada danta da mijinta ,,,,,,,
Batasake samun cikiba saibayan shekara biyar Inda tasake haihuwa saidai wannan karon mace tahaifa jaririyar farasol kyakkyawa daita aiko sadiya tayi murnar haihuwanta koba komi itama tasamu wacce zataringa yiwa kitso ,,,,ranar suna yarinya taci sunan kishiyar kakanta wato maryam amma sunace mata Yasmin,,,,, aiko inna Mairo tadauki son duniya tadaura akan maryam takwararta wato Yasmin haka tunda aka yayeta tadauketa tace itazatayi rikonta badan sadiya tasoba amma sbd alkunya tahakura tabarwa inna Mairo ita koba kome ita meson jinintane ,,,,haka goyon Yasmin yakoma gun inna Mairo ,,,,,,,,Yasmin ta taso cikin gata dakulawa sosai sangartacciya ce afannin shagwa6a amma hakan baishafi tarbiyarta ba ,,,💃💃💃
[19/11 10:35 pm] ‪+234 813 630 9911‬: 👰HAKURI DA KIYAYYA👰
Written by aysha wakili
"(Mrs ahmed)" Page5⃣➖1⃣0⃣
Tundaga haihuwar Yasmin sadiya batakara samun cikiba ,,,,,,,,,,,,Yasmin yargatan inna Mairo bata bari adoketa intashiga cikin yara tana wasa batajimawa zata nemi fada ta arta aguje ta6uya bayan inna Mairo tana zuwa ko inna zata 6oyeta abaynta kuma tace bawanda yaisa yata6a mata jika akwai ranar da Yasmin taje tasami gwaggo saude tana tankaden gari tazauna kamar abin arziki tanai mata fira gwaggo tace yauwa Yasmin danzauna anan karki tashi bari naje nadubo ruwan danasa awuta koya tausa karfa kitashi Yasmin tace toh aiko gwaggo namikewa Yasmin ta kwashe garin tazuba cikin ruwan dake roba agefenta tanagama juyewa tamike sadaf sadaf tashige dakin inna takwanta bayan inna kamar itama baccin takeyi gwaggo nafitowa taga mugun aykin da yasmin tayi mata tasaka salati tana tafa hannu tabi bayanta tashiga dakin inna hangota tayi bayan inna wai ita adole bacci takeyi aiko gwaggo tajawota dakarfi tasauko daita bisa gadon datake tadaga hannu zata mareta kenan inna tafalka baki bude tace metayi dazaki daga hannu kidoketa da yamma haka gwaggo tadubeta tace kifito kiga aikin datayi yausai kinci gidanku yarinya kamar mai hannun roba sai shegen 6arna nan inna tabi bayan gwaggo suka fito koda inna taga mugun aikin da Yasmin tayi batai mamakiba cos tasan zata aykata abinda yafi haka cikin Sauri inna ta6oyeta abayanta taceda gwaggo tayi hakuri barita debo mata wani garin haushi yaturnuke gwaggo batace komeba tawuce tadebo wani gari tana tankadewa tana cewa wlh duk ranar dakika shiga hannuna zaki gane kurenki inna tace bazatama shigo hannun nakiva ,,,,,,,,,,

Zaid ne da abba suka dawo makaranta Yasmin nabayansu da sallama suka shigo gidan Yasmin ko batayi sallama ba tawuce dakinsu tanacewa inna tadawo zaid suka wuce shashinsu suka gaida ummansu sadiya ,,,,,,,,bayan awa daya Yasmin tashigo sashin su abba tanacewa umma dan vani naira goma insiya alawa umma tace batadashi nan tafara buga kafa tanacewa ai inna tace kibani zata maido maki abarki umma tace bazan badava yarinya sai shegen kashe kudi ,,,,,zaid yace ketafi kibamu guri anan sai danbanzan shagwa6a ni wlh natsaneki haba, umma taji maganar harzuciyarta sbd ai Yasmin yartace kamar abba amma zaid yadauki karan tsana yadaurawa Yasmin haka kurum,,,,,,itakuma takasa taka masa birki ,sannan bataso tafadawa abbansu kar asamu damuwa tanadai addu'a Allah yashirya tsakaninsu yadena kin yasmin ,,,,,,,,,,6angaren Yasmin dai tsokana sai abinda yai gaba kuma inna tahana adoketa saidai batada wasa afannin karatunta tanada kokari irin yarannan ne masu kokari basuda mantuwa she's very clever ,,,,, matsalarta daya tsokana bata kyale kowava hatta inna dake goya mata baya wataran tana takalarta insuna kusada juna ne inna taita zuba mata dundu ,,,,,akwai watarana da duk anazaune inna gwaggo da malam zubairu Yasmin tadubi gemunshi tafashe da dariya tace mai almajirai sunan datake kiranshi dashi kenan ,,,wannan gashin naka kaman na akuyan ilu maishago ,,habawa su inna mezasuyi banda dariya shiko yamurtuke fuska yace Mairo wato tsokanar taki yau akaina ta tashi kenan ,,baki tazun6uro sbd ta tsani acemata Mairo shiyasa shima yakirata dasunan sbd tarabudashi ,,aiko taishiru batakara cewa komaiba ,

Haka rayuwa tacigaba da tafiya yayinda Yasmin ke kara girma da sangarcewa babu ko6o domin inka ta6ata tokarma kashigo gidan danko kana shigowa zaka gamu da inna ,,,,mai almajirai kuwa intaje gunsa awaje tadinga zuba mai tambaya kenan wannan menene meye wancan me akeyi dashi ,haka zaita bata amsa sbd acewarshi ba'a kwa6on yaro alokacin dayake tambaya amsa yakamata abashi sbd basirarshi zata karu ,,idan aka kwa6eshi toza'asa shi dakikanci kenan danhaka Yasmin ta taso da baiwar sanin abubuwa dayawa,💃💃
[19/11 10:35 pm] ‪+234 813 630 9911‬: 👰HAKURI DA KIYAYYA👰
written by Aysha Wakili
"(Mrs ahmed)"
Page1⃣5⃣➖2⃣0⃣
Bayan fitar baba adaki tasa kanta cikin cinyiyinta tana kuka maiban tasauyi ,,inna tashigo taisketa sai kuka take'inna tace yasmin meyasameki kike kuka zonan kifadamin innata jawota jikinta tana shafa mata kai,,,,duban inna tayi tace inna wai babane yace zasu hadani aure da ya zaid kuma kinsan halinshi baya kaunata ko kadan toya za'ai nazauna dawanda kenuna min tsantsar kiyayya,,,inna yace share hawayenki indai bakisonshi kigayamin ynxu inje insamu mai almajirai infada masa Yasmin tadubi inna tace inna ainariga na amsawa baba na amince kukan nan dakikaga inayi inatunanin yadda zamana zaikasance da ya zaid ne nasan bazan kwashe tadadi ba '''inna tadubeta tace kidaina cewa haka kiyita addu'a shiyafi Inda ba ace mai almajirai ne yayi wannan hukunci ba da iyayenku ne wlh saisun kwance amma dashike mai almajirai ne bayadda zanyi kiyita addu'a kinji kai tagyada takwanta cinyar inna itako sai lallashinta take harta samu tasake kamar baita va
************************
Sati biyu dayin maganar mai almajirai yasaka ranar biki wata daya cif yasaka danhaka akafara shirye shirye '""""""""""""afannin amarya kuwa babu wani shiri datakeyi asalima ita batadamu da zancen auren ba tsakaninta da ya zaid kuwa daga harara sai tsaki shikenan abinda kehadasu yana ganinta kamar yaga mutuwarshi zai murtuke fuska itakam ko kallonshi batayi balle tasan yanayi

**************************
Ranar wata asabar biki nasaura sati uku ne tafitoh gidansu ihsan kawarta tana dawowa tace bari tashiga gun umma tana shiga soro daidai dakin zaid tafarajin maganganu kamar namashaya batai kasa aguiwava taja kofar tajishi akulle takoma window tanajan window din yabude tadaga labulen ya salam tafurta dakarfinta aiko nan suka dawo hankalinsu ,,ya zaid ne tagani kwance saman wata dabatasan kowacece ba tsirara haihuwar iyayensu aidagudu tasaki labulen taruga tafita agidan dankar yafito yasameta direct gida tanufa dakin inna tafada tanashiga takwanta tafara rera kuka maiban tausayi tana furta magana Mara sauti ,,,,cewa take yanzu da wannan fasikin za'ahadani aure innalillahi ya Allah ka kawomin dauki tana cikin kukan ne inna tashigo yazauna gefenta tace kindawo shine baki ko cedani komeba share hawayenda yakeda niyyar zubowa tayi da dabara sannan tace wlh inna kaina keciwo shiyasa banyi maku magana ba amma kuyi hakuri inna tace kinsha magani ne girgiza kai tayi alamar batasha ba """""inna tamike tadauko mata paracetamol tabata takarba tasha ,,,,,inna tace takwanta tahuta karta fito'""toh kawai tace ,,_

***********************
Bacci ne yadauketa cikin baccin taji anatashinta tanafalkawa taganshi tsaye akanta yana muzurai tadubeshi tace ya zaid lafiya '''harara yawatsa mata sannan yace ita takawo haka dama nazone nai maki gargadi akan abinda kika gani yau karki kuskura kisanar dawani wannan al'amarin domin inkikayi kuskuren sanarwa wani wlh saina ninka ukubar dana tanadar maki bayan aurenmu sbd natsaneki arayuwata """idonta cikeda kwalla tace ayya aidama bakayi wahalar zuwa yimin kashedi bah domin ko bakayimin ba bazan fadawa kowaba tomeye nawa aciki konafada ma ai inaga aikin banza ne tunda bakaji tsoron mahaliccinka ba wazakaji tsoro Dan nafadawa danhaka kasaka ranka aruwan sanyi bazan fadawa kowaba amma Allah yana ganinka duk abinda kakeyi kuma ukubar dakake cewa zaka bani bazaita6a sawa nasa6awa iyayenaba zanyi *hakuri da kiyayyar* dakake nunamin harlokacin da Allah zaisa kadaina ,,,,hannu yadaga da niyyar marinta kome yatuna saiyafasa yayi tsaki yajuya yafita ,,,,,,,,komawa tai takwanta tacigaba da rera kukanta tana mai tausayawa kanta da makomarta domin tasan ya zaid cikakken makiyinta ne kullum tanazama tayi tunanin metaimasa yatsaneta amma haryau takasa gano dalili,,,💃💃
[19/11 10:36 pm] ‪+234 813 630 9911‬: 👰HAKURI DA KIYAYYA👰
written by Aysha Wakili
"(Mrs ahmed)"Page2⃣0⃣➖2⃣5⃣
Inna tashigo dakin ta iske ta yana kuka kusada ita tanufah tace meyafaru kike kuka takwara haka takece mata wani lokacin" Yasmin takalleta tace bkomi ,,inna tace kifadamin me zaidun yamaki lfy lau nafita nabarki ynxu kuma kina kuka fadamn abinda yai maki share hawayenta tayi sannan tadubi inna tace inatunanin irin rayuwar dazanyi da ya zaid ne wani irin zama zamuyi idan natuna haka shike sani kuka,,,,,,inna tadubeta batareda tagamsu da abinda tagaya mata ba tace nagaya maki kidaina tunanin wannan komai kibarshi ahannun Allah yanataredake sannan inaso kikasance mace maijuriya bakomi zaki zauna kina kuka akaiba danhaka share hawayenki karki kumasa damuwa aranki,,,,,,

Inna nafita tanufi dakin zaid ganinshi tayi yanafitowa daga dakin takirashi bayan yakaraso ne tace zaidu inaso inbaka shawara kuma daka cire kiyayyar dakake yiwa Yasmin azuciyarka sbd koka sota koka ki ta itace dai abokiyar rayuwarka danhaka kayi saurin janye kiyayyar dakake yiwa yarmutani inbahaka ba zaka gamu dani ,,,,,,,,,tana wucewa yabitada wani irin kallo yana cewa lallaima tsohuwan nan tarainamin wayau akan waccan yarinyar zatazo waitana bani shawara kuma zangamu daita mtwe tama karasa nakara tsanar yarinyar ,,,,,,,,,,

**************************
Biki saura sati daya anatayiwa amarya gyaran jiki itadai batacewa komai saidai tabisu da ido ko kawaentama babu Wanda tasan dazancen auren inbanda ihsan ,,itadinma sbd sunfi shakuwa kuma tare suka taso shiyasa kullum suna tare ,,,,,,,,Yasmin zaune tana aikin nata wato tunani ihsan tashigo tanata magana amma Yasmin batajita ba saida tadafata firgigit tajuyo tana duban ihsan tace yaushe kika shigo ihsan tace tun lokacin dakika shiga duniyarki ta tunani murmishi Yasmin tayi ihsan tace yabatun rabon IV din yaushe zamufara rabawa Yasmin tawatsa mata harara tace lallai ihsan bakida aykinyi harma wani rabon kati kike magana akai ,,,,nikam bainda zani wlh bana gayyatar kowa auren so akewa rabon kati amma wannan auren kiyayya ne danhaka bainda zani ,ihsan tadubeta tace ai watarana zaizama auren soyayya insha Allah Yasmin tai murmushi tace har abadah bazai zamaba,, ,,ajikina babu abinda ke tattare da wannan auren said ukuba saikuma kaddara daya hada,, ihsan ta kalleta tace kidaina fadin haka Allah zai iya aiwatar da ekonsa aduk lokacin dayaga dama kuma alokacin dayaso ,,Yasmin ta gyada kanta tanacewa nasan dahaka amma inarokon Allah dayasanja min ya zaid sbd nasan tarayyata dashi ba alkhairi bane ,,,,,,ihsan dai taga Yasmin bazata yarda sutafi rabom IV dinba tamike tace itazataje tayi rabon Yasmin ta ta6e baki tace Allah yakiyaye hanya ,,,,,,,
**************************
Yau saura kwana biyu biki Yasmin zaune cikin yan'uwanta anata fira saiga zaid yashigo gidan yadubi Inda Yasmin take zaune tawitsiyar ido sannan yawatsa mata harara ,,,,,,,,,sadda kanta kasa tayi yakara dubanta yace ke kizo zaku gaisa da abokaina yajuya yafita ko kallon hanyar dayabi bataiba tacigaba da firanta aunty safiya ce tace Yasmin ba zaid yace kije kugaisa da abokansa bane turo baki tayi tace aunty share shi kawai aunty safiya tace maza kitashi kije kugaisa inbahaka ba ynzu ranki zaibaci mikewa tayi tana bubbuga kafarta taja mayafinta tafita tana isa soro saidata tsaya tashare hawayenta sanna tafito zaune taikesu kan kujerun roba dake wurin ta tsaya agefe sannan tace ina wuninku suka amsa da lfy lau amarya bakya laifi ya kk ya akaji da hidima ta amsa da lfy lau sukace toh Allah yasa ayi a sa'a yabada zaman lfy da zuriah nagari kome bataceva tajuya tawuce abinta ,,bayan tawucene abokan suka dubeshi sunacewa gsky bahba kayi sa'a wannan beautiful angel haka gsky we re happy for u ,,,kallonsu yai sannan yai tsaki yace Ku dallah Ku kyaleni nagaya maku nifa natsani yarinyar nan fiyeda tunaninku mtwe kutashi muhaure club yau am high I need to cool down wit babes ,,,
Nan suka mike sukawuce club gurin chasu ,,,,💃💃
[19/11 10:36 pm] ‪+234 813 630 9911‬: 👰HAKURI DAKIYAYYA👰
Written by Aysha Wakili
"(Mrs ahmed)"Page1⃣0⃣➖1⃣5⃣
bayan shekara goma shabiyar lokacin Yasmin nada shekara goma sha takwas aduniya lokacin abba yayanta nada 23yrs yana karatu A UMYU katsina yana karanta low yayinda zaid tuni yagama nashi karatun yana running business cos dama business administration yakaranta ,,,,,Yasmin koh anzana jarabawar karshe a WTC ,,,anazaman jiran result yafito tacigaba da karatu amma mai almajirai yace baiyadda tacigaba dakaratuva saidai aimata aure kamar yadda akaiwa sauran inyaso mijinta yabarta tacigaba ,,,itakam tace mai almajirai halan kaizaka aureni ne naga dukkawani zake sainayi aure nifah banida kowani saurayi balle ince yafito danhaka karabudani inyi karatuna ehe,,,,, mai almajirai yace toh tsigai zoki saukemin kwandon rashin kunyar dannace aure za'ay maki ko kifito damiji ko karki fito dashi dole aimaki aure mikewa tayi taiso kusa dashi taja gemunsa tanacewa saidai inzaka auramin maigemu irin naka taruga aguje binta yai da kallo yana dariya yanacewa ohh ni zubairu Allah yabani yarbanzan jika kuma bayadda naiya daita ,,,,,,,gashi kuma Allah yajarabeni dasonta shiyasa nakeson hadata aure da zaid nasan zaikula daita sbd banason wani abu yacutar min daita,""

**************************
Tana fita kofar dakin abba tanufa taleka ta window taga sai bacci yake danhaka dasauri takoma tadebo ruwan sanyi tadawo da niyyar watsa masa tana isowa taganshi yatashi yanazaune ajiya roban ruwan tayi takama hanyar Shiga cikin gida tazo daidai dakin zaid kenan tafarajin wani irin nishi batai kasa aguiwa ba taisa taja labulen dake window tanalekawa innalillahi abinda tafadi kenan ynxu dama ya zaid Dan iska ne no wonder shiyasa baya bari ashigo masa daki Ashe iskanci yakeyi dasauri tasauka takoma gida dakin inna tashiga takwanta tai lamo amma hoton videon da zaid yake kallo ne yadawo mata lallai kam ya zaid Dan iska ne mtwe tomeyada menima nanta manta da batun abinda tagani tacigaba da harkokinta,,,,,
Kawarta ihsan ce tashigo nansuka hau fira da labarin in result dinsu yafito wani makaranta zasu shiga wani course zasuyi haka dai sukaita firansu ,,,,,,

*****************;bayan sati biyu mai almajirai yakira baba kabiru da baba salihu da baba usman yafara dacewa inason kuhada ya'yanku aure wato zaidu da yasmin sbd ni banaso yasmin tai nesa dani sannan banason wani bare ya dauketa sbd yarinyace sangartacciya afannin shagwa6a shiyasa nakeso zaidu ya aureta sbd shiyasan halinta kuma dan'uwanta ne koyatake zai kula daita """nan su baba salihu suka jinjina maganar sannan suka amince amma baba kabiru baice komeba sbd yariga yasan irin tsanar da zaid yakewa Yasmin amma badamuwa insun hadu inuwa daya yana ganin komai zaidaidaita watakilama yakaunaceta ,,,
Bayan baba kabiru yashigo gidane yaiske umma sadiya zaune tana shan iska nan shima yazauna bai6oye mata komeba yafada mata gabanta saida yafadi sannan tanisa tace babansu kana ganin babu matsala awannan hadin kuwa 'girgiza kai yayi yace nafiso kiringa zaton alkhairi koma wani irin kiyayya yake mata wataran zaizama soyayya mubisu da addu'a dawannan magana yakashewa umma jiki,,_,,,,,,,,,,,,,,,,,,
Bayan kwana biyu dayin maganar baba salihu yakirawo zaid yafada mashi kudirinsu nahadashi aure da Yasmin,,,,gabanshi yai mugun faduwa yadago kai yadubi babanshi yace amma baba ai yarinyar batace tana sona ba,baba salihu yace aimukeda iko daku danhaka munriga munyanke shawara ba amincewarku muke nema ba danhaka tashi kabani guri ,,sum sum yamike yafita yana hada hanya dakyar yaisa dakinshi kan katifa yafada yashiga duniyar tunani ,,,,,shikam yasan baita6a kaunar yasmin koda daidai da minti dayava àsunan yan'uwantaka balle kuma ynxu da'akeso ahadashi daita lallaikam inya amince ya aureta yacutu gsky da tunanin bacci yai awon gaba dashi,,,,,,,,,,********

Itako yasmin tana dakin inna tana kallo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login