Showing 33001 words to 36000 words out of 42346 words
cewa irin wannan kwalliya ina zakije??
Matsowa tayi ta karbi boy tace yarona sannan ta sumbace shi..
Juyawa tayi tace ina kwana yaya??
" sai da yadan jima sannan yace lafiya lou..
" yadda ya amsa mata ita kanta bataji dadi ba ramlat kuwa sai faraa takeyi...
" yasmin kuwa tahada komai na breakfast sannan ta zauna..
" ramlat tace yaushe zakije gidan su mama ne??
" Yau zanje inshaa Allahu..
" Ki gaishe su in kinje please.." dr sageer dake danna waya yajiyo yace babu inda zakije fa..
" wani malolo ne yatsaya mata a wuya cikin takaici tace Tohm...
Tashi tayi zata hau sama.." dr ne yayi saurin kiran sunanta sai tajiyo zo ki zauna ina zakije??
" Bacci nakeji idonta cike da hawaye zo to kikwanta kusa dani..
" Shiru tayi bataci komai ba.." ramlat tace karfe nawa jirgin zai tashi ne??
" karfe biyu yanzu karfe 12 ai...
" To bari naje nayi wanka nima...
" Yasmin da takasa magana tashi tayi itama dak'inta tashiga wayar ta ta dauka ta kirawo hajiya tana kuka...
" Lafiya yasmin lafiya??
" Hajiya yaya sageer yahanani zuwa inga su baffa tunda suka tare banje ba babu magiyar da banyi masa ba yaki, kuma ni banason nabishi kasar wajen nan danAllah kiyi masa magana sannan tasaka kuka...
" Daina kuka tagurina inshaaAllahu zan kirasa kuma kwana 2 ma zakiyi agidan..." goge hawayenta yasmin tayi tace hajiya nagode sosai...
Yasmin na zaune akan gado taje dr sageer yaturo kofa yace mata au baki shirya ba??
" Tace ina zanje?? " Au Tambayata kikeyi? Wato yasmin ban isa nasaka ki abu ba ki bazanji dadinki ba kenan? Da ramlat ce nace tashirya datuni tashirya ko so kikeyi indinga neman mata?? Kinsan yanayi na...
" kuka tasaka ta fara ciro kayanta sai kuma wayar hajiya ta shigo cikin murna ta kallisa dataji yana gaidata...
" Ko amsawa batayi ba takamashi da fada kuma kabarta taje ta gaida iyayenta taje tayi kwana biyu in zakadawo sai ta dawo... " doctor bashir da ransa ya bace yace hajiya amm... " Umarni na baka ta kashe wayar...
" Kallon yasmin yayi idonsa duk yayi jaa yace kishirya kije kiga su umma..
" Cikin fara'a tace kwana nawa zanyi???
" Duk yadda yayi miki... "har da dantsallen ta nagode my habiby...
" Tsako yajaaa sannan yafita shiryawa yayi sannan ya rungume ramlat yace inasonki uwargida na kiyimin addu'a kinji...
" Ramlat cikin mamaki tace ina yasmin din?? " No ni kadai zantafi sai nadawo 3days kawai zanyi tunda babaa tananan to sai ku zauna ita yasmin zataje gurin baffah..
" Ramlat ce take kokarin yin kuka ni kadai?? ... " DanAllah Ramlat kada kisani cikib tunani pls.." tohm Allah yatsaremin kai yadawo dakai lafiya...
" Yasmin kuwa sai ibar kaya takeyi ta dauki kusan kala 7 sannan ta rufe koina ta sakko bata tarar da kowa a palour din ba abunda yabata haushi ko sallama dr sageer baiyi mata ba tana isa gida ta rungume mama lallai baba ya zuba dukiya agidan nan mashaaAllah..
" Yasmin yanaganki da akwati??
" sati daya zanyi mama ..." haba auta sati daya yayi yawa kwana biyu dai...
" Toh mama nan tashiga dakunan..
Mamee ce tace yanzu Alhaji babu wani boka dakasani ma aiki kamar yankan wuka???
" Alhaji isa ne yace to inma akwai bokan ina kudin aikin...
" Khalil ne yace DanAllah mutuba mudaina abunda mukeyi tun ina yaro kuke illatar da baffa Amma kullum gaba yakeyi...Dr sageer kunyi masa asiri kan kar yasamu karin girma gashinan asirin ya karye kukallah ya kunna musu wayarsa yadda turawan America suka girmamashi tare da kyaututuka...
" Basu gigice ba sai dasukaji uban kudin da suka bashi tare da motoci..
Alhaji haruna ne yayi cilli da wayar tare dacewa wallahi sai munga bayansa bazaiyi kudi ba...
" inna ce tace kudi na nawa kuma ku dai da zuciyar ku ta mutu kai kuma isa Allah ya'isa tsakanina da kai khalil katashi mutafi ka koma makaranta kayi noma agarenmu idan kasamu mata sai kayi auren ka Ai yanzu kaji jiki kakuma gane sharri dan aike ne ko karufe kofa sai ka bude masa...
" Khalil ne yace tabbas hakane inna zan biki kukuma Allah yaganar daku...
" Mamee tace to waya rikiko?? "Ku tafi mana kunga Alhaji isa asaida gidan dasuka tashi sai akaiwa boka ko???
" Alhaji isa yace gaskiya kin kawo shawara mai kyau sai Haruna ya samo dillalai...
Bayan Angama karrama Dr sageer da karamasa girma wani hotel suka kaishi yana kokarin cire safa wata baturiya tashigo tasaka wasu shaidanun kaya bakinta dauke da red lipstick tana bude kofa tace...excuse me please Dr sageer...
Dagowa yayi da kansa yace ...hope fine??
" she smile and say am happy for your success...
" he reply to her by saying thanking...
" am juliet am here to help you sleep well..
" I don't understand...
" she just smile and started to remove his shoes...
" cikin gigicewa yace thank you please i appreciate...
" she smile again and say okay let me bath you please....
" Dr sageer shout and said i don't need any it please u can work out...
" she reply to him by saying do u need some kiss???
" cikin zafin nama yace getout...
" cikin tsoro tafita innalilahi kawai yake ambata da'irin shigar datayi...
Wayansa ya dakko yafara neman lambar yasmin har zai buga yakatse..yakirawo ramlat sukafara video call...
" Mashaa Allah dr na yazama tauraron taurari Alhamdulilahi naji dadi..
" nagode matata kinyi wankan tsarki??
" No kofa sati baayi da haihuwar ba banyi ba meke damunka??
" Hawaye ne ke zuba a idonsa tare da fadin kinsan matsalata kinsani ai...
" Cikin rashin jindadi tace shiyasa nace ka tafi da yasmin ai... " yasmin batasona bata kaunata ba nine agabanta ba...
" Shiru tayi tace ai jibi zaka tawo dear kayi azumi mana...
" Tohm nagode kikularmin da kanki da muhammad kinji...
" Tohm tace tare da fadin ilove u so much... sannan ta kashe..
" Hoton yasmin yafara kallo yana hucewa cikin jindadi yace Allah ne yasamin sonki... wasu magunguna ya hadiya sannan yayi sallah yayi bacci...
Fadila ce tashigo gurin mama ta zauna tanata dariya mama yau baki nemi ne ba...
" yasmin ce tace sannu..
" mama tace fadila ga yarinyar tawa laa itace yasmin din kice kinzo mana..
" mama ce tace yasmin wannan yarinyar kanwata ce hadiza kinganeta kusa damu take kullum tana tayani aiki da zama...
" Murmushi yasmin tayi hankalin ta duk yana kan dr sageer bai kirata ba har ynzu...
Mama ai kallo natsaya yi ingayamiki wani matashin mutum america ta karrama kinga yadda kawaye na suketa ihu dama zai aure su gaskiya yayi bawan Allah kinsan ya sunansa??
Mama tayi dariya tace dr sageer ko??? " fadila ce tasaka dariya tace ashe kema kinkala..
" D'a nane ai , shine mijin yasmin...
" yasmin wani kishinsa taji , " fadila tace wallahi ki rikeshi hannu bibbiyu don baki yadda yanmmata ke sonsa ba...
" shiru tayi tashiga daki duk sai taji ta tsane gidan ma tabbas miji wani niima ne daga Allah wayanta dauka ta dinga kiranshi amma bai dauka ba message babu wanda bata turaba bai kulata ba..
Washegari ana karyawa baffa yace gobe mijinki zai dawo misalin 6 na yamma sai ki tafe gida da wuri koh?
" sauri tayi tace inshaa Allahu baffa...
" baffa yace kunyi waya ko??
" Cikin sauri tace eh munyi azuciyar ta kuma kuka take kokarin yi...wayan mama ta dauka ta shiga wani room takirawo shi bugu daya ya dauka yace mamata ina yini??
" kuka tasaka tace yaya nicefa danAllah kayi hakuri wallhi nayi kuskure.. " sauri yayi yakatse wayar sannan yace yasmin bazaki illatamin rayuwata ba sannan yafita...
Washegari da safe tasa fadila ta nemo mata mai kunshi da kitso sannan tasa aka siyo mata kwakwa tayi lemo dayawa sannan tayi white rice da farfesu tayi hadin salad duk tasa aka kaimata gida ita gurin 5 ta shirya tsaf mama tace kiji tsoron Allah yasmin kije tsoron Allah kikula da dr kiyimasa biyayya danAllah...
Tohm mama inshaaAllahu..." Allah yayimiki albarka.." Ameen!!!
Yasmin nakarasawa cikin gidan taga ramlat tanata video call da dr harda su kiss cikin kishi tace sallamata nakeyi...
" ramlat tace ina nan muna soyewa da mijina banjiki ba sannunki da zuwa...
Tsaki tayi tahau sama ta bude dak'inta turaren wuta tasaka sannan ta gyara dakinsa tayi waka wata riga da siket tasaka duk saman kirjinta abude siket din duk yadameta dankwali ta daura tanajin shigowarsa ta rungumesa tureta yayi ahankali sannan yace ina muhammad gobe suna inshaa Allahu...
Ramlat ya sumbata ta mika masa yaron yasmin kuwa duk jikinta yayi sanyi dakyar tace sannu da zuwa ya hanya??
Banza yayi mata ya kalle ramlat sunata hira..
Yasmin da batasan lok'acin da kuka yacita ba tatashi ta hau sama kallonta kawai yakeyi dr duk jikinsa ya mutu, kuka tayi sosai sannan tayi sallar isha'i tafesa turare ta nufi dak'insa tana shiga taga yana kwanci cikinsa nata ciyo sa juye yakeyi a tsoraci tace lafiya yaya tasaka kuka...
Maganin da yake nunawa ta dakko tabashi...kuka tasaka tace DANALLAH kayi hakuri wallhi nayi kuskure DanAllah kada kayi fushi dani zanshiga wani hali...
Bakyasona ko? zan iya shiga mugun hali yasmin bakya kaunata? Zan sakike sai ki aure wanda kikeso... sai ya sume..
" A furgice ta mike tana A'a A'a A'a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo....
Assalamu alaikum
*Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!*
*_Sak'onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..
Please do vote comments and like 👏
Urs *Nana diso*
Email:kabba43@yahoo. com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 85-90
*DOCTOR*
*SAGEER*
_NA NANA DISO_
http://deejarhberver.wordpress.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
A furgice ta mike tana A'a A'a A'a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo....
Hank'alin Ramlat bai tashi ba sai dataga doctor sageer baya motse kwata kwata batasan lokacin da ta ajiye muhammad ba tana kuka takirawo dr khalifa dakyar ya dauka yace matar dr ya'akayi??
" kuka tasaka tace mijina ya mutu, wallahi yasmin ce wayoo ka taimakeni danAllah...
" Kashe wayar yayi yajuya kan motarsa sai gidan dr sageer yana shiga ya hau sama hankalin sa bai tashi ba sai dayaga yasmin akwance bai bi takan dr sageer ba yafara dubata...
" Dr khalifa yazaka biyewa wannan mahaukaciyar yarinyar batason shi bata kaunar shi, itace sanadin komai tasa kuka...
" dakata ramlat karya kikeyi wallahu yasmin bazatayi haka ba da dai kece kowa yasan zaki aikata haka, bazaki fadi kyakyawar kalma ba haba sai kace ba musulma ba...
" Ai daman nasan haka zakace yayi mata banza ya dudduba yasmin nan yasa ramlat ta kwantar da'ita wata allura yayi mata sannan yayi hanyar fita..
" Dr mijina fa dr kataimaka, mijinki nan da minti biyar ma zai watsake matsalar sa mai sauki ce wallahi kuji tsoron hakkin yasmin kuji tsoron hakkin ta yarinya karama ace jininta yana hawa...
" Ramlat ce tajaa tsaki ta mutu mana sai me sai me kuma ai nasanar dasu mama duk abunda takeyi..
" Bai saurareta ba yatafi...
Mama ke faman sintiri apalour tana innalillahi..
" fadila tace haba mama wallahi yasmin bazatayi haka ba sharrin kishiya ce wallahi bazatayi ba, to kinkirawo ta kinji ta bakinta???
" Mama cikin fada tace ai tasan tayi laifi bazata dauka ba...
" DanAllah mama kidaina fadin haka please...
" Wani numfashi mama tajaa sannan ta goge hawayenta so kikeyi ace ninake zugata idan ta kashe musu yaro fa...
" Makiyi ai duk abunda bayaso babu sharrin da bazaiyi ba kiyi hakuri danAllah...
Tunda doctor sageer ya tashi idonsa yayi jajir wanka yayi ramlat sai sannu takeyi masa...
" Kallon yasmin dake kwance yayu yace wannan fa??
" ina tunanin bacci takeyi, tsaki yajaa sannan yace yunwa nakeji sosai cikin murmushi tace katashi muje kaci abinci..
" murmushi yayi yace ina babyna??
" yana gurin iya bari nakarbo shi suna hira yace abinci sannan ya zauna kallo nan ramlat da matsa kusa dashi tana ta bashi labarin budirin da za'ayi gobe yanata dariya...
" wasa yake tayi da muhammad yace ita bazata tashi ba kenan???
" ramlat ce tace uhm kaikama damu da wanda bai damu dakai ba..
" Shiru yayi baice komai ba..
Yasmin dake kokarin bude idonta hawaye ne yabiyo bayan budewa tashi tayi zaune tace tabbas da namiji hankaka ne gabansa fari bayansa baki, yaya baya sona baya kaunata gashi yace zai sakeni yanzu in yasakeni ina zanje mama bazara barni na zauna gurinta ba hajiya kuma yaronta ne tasaka kuka mai cikin da kuna, A hankali tace inshaa Allahu bazan sake cewa komai ba daga gaisuwa sai kuma in yace nayi wani abun... hannun ta tazata daga taji alamar alura zafi taji nan taje dakinta tayi wanka sannan ta zauna ga yunwa da takeji...
Hijjabi tasaka har kasa sannan ta sakko daga benen tana kallon su sunta hira ramlat rungume da muhammad dining ta duba taga shinkafa jallop haka ta zuba ta zauna taci, wata kasala taji sannan tace sai da safenku...
" Ramlat tasa dariya tace yauwa...
" yasmin tana shiga dakinta tace tabbas dr baya kaunata baya sona har yaushe mukayi auren yafara wulakanta ni wayoo Allah na tasaka kuka mai cike da kunci tare da fadin tabbas wannan shine KUNCIN RAYUW ramlat bata kyauta ba tunda tasaka SON ZUCIYA acikin aikinta wayarta tadakko number mama tagani kusan kira 20 cikin tashin hankali ta bi kiran to ko ya sakeni naga bai kalleni ba shikenan nashiga uku takara saka kuka ....
Alhaji haruna ne ke cikin dokar daji yanata wasu abubuwa har ya'isa bayan wani dutse yana zuwa boka yace nasani nasani ka ajiye dubu hamsin zamu gama maka dasu..
" Murmushi alhaji haruna yayi yace ga dubu hamsin nan muna godiya boka..
" tashi katafi zamuyi hahahaha...
" yana tafiya boka yace ai ku matsalar ku kenan kada wani yafiku bansan komai ba yasa dariya yau dilu zataci kaji inba da harkar karyarba babu mai bani dubu hamsin haha yashige gida...
Alhaji haruna tunda yakarasa gida yake fadin ai kawai sai dai kuji labarin mutuwar baffa da sageeru...
" mamee ce tayi guda tace damun zama masu arzuki...
" Alhaji isa dake faman washe baki yace ai bokan yafa'iya aiki sosai karku damu..
Yau kwana 5 kenan tsakanin yasmin da dr sai kallo tun tana sakkowa taci abincin har ta daina takama azumi tabbas mai samun kulawar miji dan gatane don ranar suna ma sai da momy tace tazo ayi hoto da ita sannan ta dan sakko...
" Hankalin dr sageer baitashi akan yasmin ba sai dayaga bata bude ko kofarta tabbas yasan bai kyauta ba amma kuma haka shine daidai kodan ya hukuntata kuma irin kalaman da ramlat take gaya masa yasmin tace abun nabasa tsoro...
"Bayan sallar isha'i yasmin na zaune akan sallaya takara kiran wayar mama dakyar ta dauka tace lafiya kiketa kirana mara kunya???
" Mama kitsaya ki saurari ne wallahi banyi komai ba Allah inason yaya Allah mama inasonsa shine...
" dakata shine me kice kullum cikin kuntata masa har dacewa ramlat wai tace abaki takardar sake to baffa zangayawa wallahi wallahi kika kaso aurenki sai dai wata uwar bani ba haka kika inayi eh...
" Nashiga uku nashiga uku wallahi mama ban fada ba yaza'ayi nace haka wallahi...
" ki cigaba da duk abunda kikaga shine daidai kuma kika kashe sageer kema kashiki zaayi...
" ummata ke kike fadin haka ke dakikafi kowa sanin halina tasa kuka...
" yasmin ta da nasani ba yasmin ta yanzu ba mara jin magana takashe wayar...
" Wani abune ya tokari mata awuya sai hawaye dake zuba a idonta ahankali ta kwanta soyayyar su da dr sageer kawai take tunawa to ita kuwa me tayi masa haka yatsaneta bakomai ji tayi tana son cin indomie...
" Doctor sageer ke faman kallon hotunan yasmin can yace ramlat yasmin ta sakko yau???
" Ta sakko tabani sako ingayamaka wai in kanada zuciya ka saketa tunda ku ba dangin mayu bani...
" Kallonta yayi da mamaki ita tagayamiki haka...
" hmmm ai yafi haka kadan nagayamaka...
" Baice komai ba yacigaba da aikinsa a system..
" Cikin hijjabi har kasa yasmin ta sakko bataci komai ba ta huce kitchen indomie tayi da shayi tahadu indomie din taji vegetable palour ta zauna tabbas duk dr sageer ya rami ta lura kallon plate dinta kawai yakeyi ramlat tace bari na dakko muhammad...
" Dr sageer yace kidaina barinsa shi kadai...
Tashi yasmin tayi zata tafi sama ramlat tace ina zakije?? Ai baki ci ba...
" in kinaso ke kicinye bana sha'awar su yanzu..
" Dr sageer ne ya cinye har da tea din cikin ransa sai son yasmin kara bugar ransa yakeyi ba shiri yaja mota yaje yasiyo mata gashashiyar kaza da yogurt da yadawo duk sun kwanta sama yayi direct dakin yasmin yana shiga yaga ta rufe kofar da mukulli babban mukulli ya dakko ya bude yashiga ta cikin bargo ta dugungune kallonta kawai yake yana me nayi miki bakyasona yasmin? Idan na rabu dake zanshiga mugun hali hannunta ya riki alokacin duk tanajin abunda yake cewa amma tayi luf sai hawaye...
" cikin kakkausar murya yace yasmin yasmin yasmin tayi masa banza...
Hannunsa yasa abargon yana kokarin shafata tayi saurin tashi tana kuka banaso kabari..
" To tashi kici kaza gashi nasiyo miki...
" banaci banaci tasaka kuka..
Cikin murya mai sanyi yace haba kanwata danAllah kici ko kadanni banson kina kwana da yunwa wallahi dazu baki koshi da indomie ba kinyi hakan ne don kinsan banci abinci ba yasmin ni fa ina sonki wallahi wallahi amma kuma kalaman dakike gayawa ramlat kullum tagayamin suna batamin rai jiya harda ce mata ni asalin mu mayu ne?
" hawaye takeyi kawai tabbas me ramlat take shirya mata dole wasan yazo karshe...
" karbi kici danAllah.." karba tayi tanaci