Showing 18001 words to 21000 words out of 42346 words

Chapter 7 - DR SAGEER BOOK COMPLETE BY NANA DISO.txt

05 Oct 2025

1222

kwata saboda bama kufara zama guri daya ba kissa zaki koya karki zama ballagaza, kina gani dai ni mahaifiyar ki kwata kwata banda kishiya amma kinga dai da idonki abunda facaloli sukeyi min ko kadan basa sona kina dai ganin sharri kala kala.

Akwai lokacin da mamee tacewa mahaifin ki wai nasatar mata kudi yadauka yabiya Yazo yanata bala'i ko uffan banci ba sai ma hakuri dana bashi lokacin da yazo cin abinci muna hirar mu mai dadi sai ce masa nayi tunda muke da kai ai bantaba yimaka sata ba kuma duk halin da muke ciki ai bangayawa kowa, kinsan me yace?? Sai cewa yayi sai daga baya naga bankyauta miki ba Amma kiyimin afuwa wani sa'in in aka gayamaka wanda kafiso yayi maka laifi burin ka kayimasa hukunci adaidai lokacin...

To kinga ita rayuwa tagaji haka hakuri zakiyita yi kuma ki tararrayi mijinki kinji...

" inshaa Allahu mamata inasonki tunda natashi baki taba yimin hudubar tsiya ba ba ki taba cewa in zagi wani ba baki taba cewa muyi wane mugun abu ba tabbas kincika uwa tagari Allah yasaka miki da Alheri...

" Ameen auta

Yasmin na zaune tasaka wata blue rigarta irin sun matseta mikewa tayi ta dau wayarta suna magana da wata 'yar ajin alokacin dr sageer yayi sallah dawowar sa daga asubuti kenan babu kowa adak'in sai ita daya...

Tashi tayi ta cigaba da wayarta batare da tace masa uffan ba tashiga daki...

Dr sageer gaba daya hankalin sa ya tashi wai yasmin dinsa itace take bada dashi yau through out yakasa cin abinci yasan yayi kuskure but yasmin time ne da zatayi masa uzuri...

" Aa dr kaine agidan namu? " eh wallahi mama daga office na biyo yinwa nakeji please kunyi abinci... " Tausayin sa mama taji sannan tace munyi bari nakira yasmin ta zuba maka ni zan lika makota anyi rasuwa... " yasmin fito ki zubawa yayanki abinci ni nafita... " Toh kawai yasmin tace sannan tayi banza da zancen yafi 30minute azaune dakin ya shiga yaganta akwance tana chatting dayayi sallama a hankali ta amsa ko daga kai batayi ba ballantana ta kallesa...

" zama yayi gefenta sannan yace yasmin DanAllah kiyi hakuri wallahi nayi kuskure kaidin ramlat ce kuma itama tagane kuranta, wallahi tunanin ki yana kokarin nakasa ne please my yasmin sannan ya durkusa please yasmin ki saurari ne...

" Kaga is better ka rabu dani daman ai naga so iriri na shafama, kanunamin gidanka yafi karfin ka ko kiyashi akace maka nakashi bada dalili ba ai ka tuhomeni ballantana dan zalunci na dak'ar mata ciki goge hawayen dake fuskarta tayi sannan tace ahaka kuma ka mari ne, Ni ba marin ne matsalata ba aa yadda dakayi zanyi mata wannan muguntar...

" yasmin am your husband to be, yakamata ki fahimce ni please wallahi inasonki ina kaunarki but nasan nayi kuskure ga fuskata rama marin to...

" tashi tayi zata fita sai ya rik'ota jiyo tayi sai idanuwan su sukayi arba da juna kusan minti uku kenan a hankali yariki hannunta sannan yadaga shi to rama marinki...

" cikin shagwaba tace ni kacika ni bazan rama ba kakyaleni sai tasa kuka...

" To kice kin yafemin cikin wani yanayi yayi maganar aikuwa sai ta fuzge hannunta yakara dankota wallahi in bakiyi dariya ba sai nayi kissing din wannam hot lips dinki...

" cikin tsoro tace sai kace...

Kafin takarasa yakai bakinsa sauri tayi ta turesa Allah ba ruwana sai Allah yasaka min ni ba'yar iska bace ba sannan takara saka kuka....

" au bazakiyi shiru ba sokike ki nakara???

" Cikin wani yanayi da ita kanta batasan irinsa ba tayi dariya sannan tafita zama tayi kan kujera yafito ya zauna kusa da'ita ni nasan kanwata bazatayi fushi dani ba....

A daidai lokacin maryam tashigo yasmin ita kuma tana cewa aikaini baka...

" dr sageer ne yasa dariya kinsan Allah wannan shagwabar taki tana rikirkita ni sosai kyau kuma kikeyi in kikayi fushi... amma fa kin azabtar dani sosai 9days please karki karayimin irin wannan....

" Da yasmin ta lura maryam tana tsaye sai ta kashe ido tace tabbas inasonka amma narasa ta'inda zan fayyace maka soyayyar danake maka....

" Murmushi yayi yace nifa dazasu taimaki ne 4 month yayi nisa abarshi 2 please...

" mik'ewa tayi tace nidama 1year akasaka.... " Ai sai ajawo na zuzuce..." bari nazubo maka abinci...

" Tana fita maryam ta gudu takoma bangaren su kuka tasakawa mamee wallahi mamee soyayya sukeyi kuma kinsan ina bala'in son yaya mamee zaku iya rasani wallahi...

" ki kyale marasa mutunci zanyi maganin su aure kuma basu isa ba...

Yasmin na zaune tana chatting dr sageer yace tashi muje ki rakani mota...

" Batare da musu ba ta rakashi sai da taga khalil yana kallonta sannan tace sai anjima yayana take care of your self please...

" ki kunna wayarki da daddare...

Khalil ne yace an asirce shi kenan asashi yaso 'yar iska irinki...

" kai iya bakin ka babban mara mutunci kuuu da kuke kiran wasu 'yan iska uban wa yakaiku iskanci...

" Ni kike gayawa haka hahaha ki zuba ido kiga wallahi sai na bata miki rayuwa...

" jahili kawai jahilci ke damunka banza kakoma skul please....

" Alhaji haruna ne yace ubanki ne zai koma ba khalil ba...

" Dariya tasaka tace Alhaji ai sai ku koma tare tayi shigewarta cikin gidana tana dariya...Nayi alwashin duk wanda yayimin sai nai masa tunda basuda kirki....

Assalamu alaikum

BARAKALLAHU FIYKUM BAZAN KUMA DAINA GODIYA AGAREKU BA BISA SAKONNIN KU ALLAH YABIYA BUKATU NA ALHERI.._

*_How was the page???_*

_*I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's*_

_Please do vote comments and like.. And I call my silent readers please do vote and comment my story really need your comment and vote#TEAM .....DS....DS LOVER'S__

Kuma ya zo a hadisin da aka kar'bo daga Abi Sa'eed da Abi Huraira (RA) cewa Manzon Allah (SAW) yace:

*Bãbu wata musiba/jarraba da zãta sãmi musulmi na daga gajiya/wahala da rashin lãfiya ko dãmuwa ko baqin ciki, ko cuta ko bacin rai...*

*...Har - qayar da zai tãka- fãce sai Allah ya rufe/kankare masa da ita - musibar/jarrabawar - wasu daga cikin kusa-kuransa )Bukhari & Muslim.*

Wato yin haquri abu ne mai girma, don haka Malamai suka ce haquri ya kasu kaso uku:

*1- Hakuri wajen biyayya ga Allah, ko da rai ba ta son hakan.*

2- Hakuri wajen gujewa sã'bon Allah, ko da rai na matuqar buqãtar hakan.

*3- Hakuri kan duk wasu abubuwa da ke kai-kawo, domin Allah ya rigã da ya tsãra yadda rayuwa zã ta kasance tun kafin halittar Annabi Ãdam da shekaru d'ari biyar (500)*

*Sa'an nan yana daga cikin addu'ar Manzon Allah SAW ya yin da farin ciki ya sãmu:( Dukkan gõdiya ta qara tabbata ga wannan da ni'imarsa ce ta ke cika dukkan kyãwawan abubuwa )*.

*A halin baqin ciki kuma: (( Dukkan gõdiya ta qara tabbata ga Allah a bisa ko wane hãli )*


*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 55-60

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Lokacin da dr sageer ya koma gida brstr ramlat yatarar sai kuka takeyi cike da rashin mamaki yazo ya huce ta gabanta..

   " brstr dataga bai kulata ba sai cewa tayi ai daman namiji hankaka ne gabansa fari bayansa baki, har ka kai kudin aure amma baka sanar dani ba me nayi maka da zaka yimin kishiya menene bana yi maka??

    " Baki da hankali ramlat kije kiyo karatun tanuzu tukunna, kuma bari in gayamiki babu ke babu yasmin wallahi naji ance kinyi mata abu sai na sassaba miki nagaya miki...

    " Wallahi sai nayi mata ta aure mijina tagani tsabagen rashin mutunci naka wacce irin bukatar kace bana biya maka?

    " Tsaki dr sageer yayu yace ina abinci na??

    " ban dafaba? " baki dafa ba? Allah yaso naci awaje da haka zaki barni da yunwa ke bari kiji duk duniya babu abunda namiji yake bukata sama da kulawar mace amma ke ko ohoo babu abunda ya dameki sannan yashiga daki.....

     " kuka tasaka sannan takira rabia awaya sannan tace wallahi rabia auren yaki yafasa narasa yadda zanyi zuciyata sai bugawa takeyi please i need some advice please...

    " dariyar mugunta rabia tayi sannan tace kije kikara yimasa masifa zama zakiyi kina kallonsa idan kika bude masa huta zakiga yafasa....  " cikin kuka tace toh sannan ta kashe wayar dak'in tabisa cikin masifa tace wallahi tallahi kai dai ba d'an halak baniba kuma baka haifu ba, ko haihu banyi ba zaka karamin kishiya sannan tasa kuka...

    " k'allon ta kawai yakeyi sannan yace tabbas inason ki rike hannun ta yayi kafin yayi magana ta fizge sannan tace wallahi zakaga tashin hankali indai kayi auren nan don wallahi sai na takura mata...

    " Murmushi yayi yace ai ba jahila zan auro ba nutsetsiyar yarinya wacce tai ilimi kuma tana aiki dashi wacce zata kula dani da ita...

    " Kuka tasaka wanda har sai da ya tausaya mata amma ina brstr ramlat jitakeyi kamar zuciyarta zata buga saboda kishi...

Yasmin tana kwance bacci yana kokarin kwashe ta sai kuwa jitayi an kirata dauka tayi tare da sallama...

    " wallahi bakida kirki yasmin wato ankawo kudin auren ki ko kisanar dani to nagode sosai...

    " DanAllah kiyi hakuri yusra wallahi nakira wayar mamanku bansamu ba kuma inata kokarin kiran daya layin naki amma wayar ki akashe kiyimin afuwa please aminiyata...

    " dariya tasa tace Matar doctor bada kanki asare amarya gidan sageeru Allah yasa kina shiga ki haifi twins...

    " Dariya tasaka sannan suka cigaba da hira bayan wasu mintuna sukayi salama...

     Yasmin yasmin kiranki kifa naketayi...

    " mama ina waya banji ba wallahi bari nafito tana sanyi da kayan bacci sannan tafito takarbi wayar...

    " ke yasmin ki biyo hajiya kutawo kizo muyi miki irin gyaran jikin mu kuma akwai abubuwan da zamu tattauna dake...

    " Au yaya aisha ygida? Gaskiya ni garin nan naku bana sonsa ayimin anan...

     " Nifa dadi na dake shirme please kibiyota kinji 'yar kanwata wallahi ina missing dinki gasu umar nan sai kuka suke kinki zuwa...

     " Karki damu 'yar uwa zan biyota inshaa Allahu...

    Tana kashe wayar sannan ta nufi dakin da hajiya take bayan tayi mata sannu sannan tace hajiya gobe zaki tafi ko?

    " eh wallahi bansan halin da yayanki suke ciki ba gashi anyi rasuwa sai gab da bikin ku zandawo...

    " DanAllah hajiya zanbiki zanje gidan yaya Aisha kinji...

     " Hajiya ce tayi murmushi tace ko kefa?? Sai ki shirya jirgin 12 zamu bi nagaya babanki anjima...

   " yauwa hajiya tamu nagode sosai...

     Mamee ke faman sintiri a palour can tace wai Alhaji babu wani boka akasa ne?? Da za'asa ya hana auren nan...

    " Alhaji haruna ne yace ina wani boka ina kudin ai boka sai da kudi ki duba yadda kullum yarinyar nan take cigaba gashi sageeru sai kantuna yake budewa...

    " Na shiga uku na lallace to yanzu ga dankune na kasiyar DanAllah ahana auren nan...

     " To yace sannan ya karba yana fita waje alhaji mukhtar yace ku dai anyi asararru kabiya ni kudina dubu sittin dita wallahi sai kabiya ni...

     " Wallahi banda ko sisi...

     " Dallah yimun shiru ku ba abun atausaya bani malam bani kudina kokuma yanzu nasa atara maka gajiya...

     " Ga dank'une dubu hamsin ne kudinsa zan ciko maka dubu ashirin...

    " kai baka isaba malam bani cikon kudin bai ankaraba yaji ankifa masa mari gaba daya mutane sun tsaya kallonsa baffa ne ya karaso gurin da mota yana zuwa yace haba bawan Allah me yayi zafi haka .....

    "  Alhaji mukhtar ne yace kudina yakarbar min sama da shekara daya amma yaki biya na wannan mutumin ba abin tausayi bani wallahi...

    " To sakeshi nawa ne kudin naka?

     " Dubu ashirin ne sauran...

    " Kayi hakuri danAllah ga kudinka...

     Wallahi kayi sa'a anbiya maka da kaga yadda ake gunduwa gunduwa da mutum banza mai bakar zuciya...

    " Cikin borin kunya yashiga gida baffa ne shima ya biyo bayansa Alhaji haruna ne yace kai baffa banson munafurci kudin da ba'asan asalin su ba kada kakara kwatar mana riga ko ance maka mu fak'irai ne? Banza mai kudin yankan kai banza mai yarinya karuwa...

    " Abunka da mutumin kirki baffa murmushi yayi sannan ya huce cikin gidansa...

    Yasmin da ke faman shiryawa tasa wata blue atampha riga da siket gaba daya shape dinta yafito kayan ta ta'iba sannan tafito palour nan ta tarar da baffa sannu da dawowa baffa...

    " Yauwa sannu auta sai ki kasance cikin shiri sai karfe 5 jirgen zai tashi...

   Tohm baba kwana biyu ni zanyi fa kasan basan benin din nan nake ba...

    " Tohm shikenan dan soyamin danKali da kwai...

   Tashi tayi tashiga kitchen tana cikin soyawa taji sallamar dr murmushi tayi sannan tajiyo...

   " kallonta kawai yakeyi saboda kyan datayi masa ga halittun ta duk sun fito ina zakije kika cancada wannan adon??

     " benin zamu tafi nida hajiya...

     " aikowa sai dai nima atafi dani...

    " dariya tayi tace kafiya tsokana aikin naka fa??

     " yasmin kenan kinki ki fahimce ni kenan??

    Hajiya ce tace au hirama kika tsaya yi bazaki maza ki gama ba???

     " durkusawa yayi har kasa yagaida hajiya...

     " lafiya lou yajikin mai dakin naka??

    " Alhamdulilahi hajiya DanAllah nima zanje benin din sau mu tawo tare da yasmin...

    " haba sageeru aikin naka fa nibanason sha shanci kayi zamanka kaga zai iya yuwa akawo mara lafiya...

     " Toh hajiya itama tayi zamanta yasmin din menene amfanin zuwan nata...

    " Kasan Allah sageeru babu inda zakaje kazauna kaje ka duba kanin babanka ance zaayi masa aiki babu kudi...

     " haba hajiya kin manta abunda sukayi min?? Irin tsanar da suka nunamin?? Shine fa...

     " haba sageer kaifa ba yaro bani ai zamani yazo idan mutum yayi maka sharri sai kayi masa alheri kamanta dabaya ka fuskanci gaba Allah yayi maka albarka...

    " Ameen yaa hayyu yaa qayyum sannan tafita yasmin tace yanaji kayi shiru yaya??

      " Please ki hakura da zuwa banson kiyi nisa dani please...

     " Dariya tasaka sai kace wata matarka?? Lallai kai dinnan zuwana babu fashe sannan ta fita gurin misalin karfe hudu suka shirya dr sageer ne ya kaisu har airport amma ko kulata baiyi ba sai hajiya da yabawa uban kudi tana ta shimasa albarka harsunyi gaba tayi sauri tadawo tace yaya lafiya kaki kulani...

    " tsaki yayi tare da fadin tunda ban isa dake ba sai kije kiyi abunda kikeso in har kinaso na sai ki fasa tafiya...

     " Nafasa tafiya?? Cikin mamaki tazaro idanuwanta haba doctor karkayimun wannan hukuncin...

     " shiru yayi yana kallonta hajiya tace yasmin yi sauri mana...

     " tafiya ta dinga yi tana kallonsa tana jiyowa har yatafi ahanya yatsa yana cin abinci sannan ya zauna tabbas yana son yasmin soyayyar da bazata fadu ba amma shi yayi rashin sa'a bata sonsa...

Lokacin da suka isa mijin ya Aisha yazo ya dauke su suna karasawa gida yasmin ta rungume aisha kai haka aka gyara gidanki??

    " zama sukayi suka ci abinci hajiya gidanta ta huce tana isa tatarar dasu dukkanin su agida kudin da dr yabata ta kasa musu sannan tace ku daure ku samu sana'a DanAllah kuduba kuga fa yaranku duk sungirma amma kullum sai dai abaku...

    " Murmushi sukayi duk'an su...

     Yau aka kawo lefen yasmin akwati 10 gashi biki har yarage saura sati daya a bikin yasmin doctor bakaramin fushi yayi daita ba har takai baya daukar wayarta tana zaune akan kujera tace ya Aisha nifa gaskiya tafiya zanyi dr yaki daukar wayata...

     " Haba yasmin please kibari sai gobe ke akwai abunda nakeso kisani namiji kamar jariri ne sai kina tararrayar sa kuma idan kuka samu matsala babu ke bagayawa wasu mutane hakuri zaki kishiyarki tsakanin ku sallama kuma ki cire kunya ki farantawa mijinki kinasa fitinannun kaya kikuma dinga sarrafa masa girkuna kinji...

     " Ita dai hankalin ta ba akwance yake ba kawai binta takeyi da to...

   " Mama ce takira waya tace aisha wai menene hakane mazamaza yasmin tatawo banson shirme...

    " Toh mama nan suka shirya gaba dayan su sukabi jirgin rana suna isa yasmin wanka tayi kawai tayi sallah sannan takira doctor da wayar mama Kuka tasaka masa lokaci daya jikinsa ya mutu cikin zafin nama yace wacece??

    " Kuka tasaka bazan iya jure fushin ka ba, bazan iya boye soyayyar ka ba ina sonka dr sageer, nasan nayi laifi please kayi hakuri, ...

    " Kashe wayar yayi sannan yayi ajiyar zuciya wata sabuwar soyayyar tace take harbawa a kirjinsa...

     Tun daga ranar baizo ba mama tabata kayan da zata kai dinki washe gari aka shirya ayimata jire kannin mama dasu baffa duk sun cika nan yasmin ta dan mikawa kawayenta kati wayanda bata samu zuwa ba tayi musu text a
Wayarta yusra ce tayi sallama suna zaune apalour rungume juna sukayi sannan anty barira kanwar mama da sakina sukace irin wannan kiba yasmin ko zaki 'yan mun...

    Nifa namanta daku ace kuna dangin mu amma ko kuzo inda muke sai yanzu dayake biki ne zaku kwaso kafa...

    " mama ce tace banson fitsara ne goggo babar su mama tace haba jikalle kiyi musu afuwa mana kema babar taki ai bazuwa takeyi ba...

    " Dariya suka saka sannan akatafi jira kayan dak'in ta mashaa Allah part din yasmin yayi bala'in kyau dan baffa yayi mata orders din kaya masu bala'in kyau kowa sai yabon kayan yakeyi da gidan...

    Tun safe su yasmin suke gidan kunshi basu gama ba sai yamma sannan suka nufi saloon ta karbo dinkinta kuma wayar yusra takarba takira dr bugu daya ya dauka sannan ya katse cikin rashin jindadi aka gyara mata jikinta...

    Abida dake faman fadin ai wallahi indai baku cire mugunta ba to nasara ma yanzu kuka fara gani ku dubi mutane da suka cika gidan sai kace bikin yarinyar shugaban kasa..

   Mamee ce cikin kuka tace wato sai an daura auren nan wayoo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login