Showing 15001 words to 18000 words out of 42346 words
bye...tana fita rabia tasa dariya tare da fadin ai sai na kashe miki aure bake kawa ba...
Karfe 5 yasmin ta dawo daga skull abinci tace sannan tazauna bakomai take ba sai tunanin dr sageer tabas tabbas tana tsoron shiga tarkon soyayya Amma kuma gwara tayi aurenta itama ta huta cikin wannan tunanin hajiya tashigo tace yasmin?..
" Naam hajiya .... " wai meke tsakanin ki da dr ne? Naga duk ya mutu akanki ko soyayya kukeyi...
" Murmushi tayi tace lahhh hajiya bakomai fa kawai jinin mu yazo daya ne... " Da bakyason sa bazakiyi wannan murmushin ba bazakuma kiyi magana a hankali ba abunda nakeso kigani shi miji nagare shine wanda zai soka koda mutane na zagin ka kuma kigane cewa ita soyayya masu hankali akan saba kuma a daidai ta, kuma ki daina tunanin sai wanda ranki yakeso aa kiyi adduar nagari mai addini wanda zai tararrayi ki, tabbas nasan sageeru yana sonki Amma kuma ya kamata ki amince bawai ina goyan bayansa bani aa kinsan yana da matsalar zuciya kuma zanso ki kasance akusa dashi...
" Ita dai yasmin batace komai ba har hajiya tafita palour...
" wayar ta ta kunna hotonan sa ta shiga dannawa kallonsa takeyi cike da kauna..
Mama ce tace daman hajiya inaso muyi magana kafin ki tafi?
" Akan me fa?
" A kan sageeru ne dayace a nemar masa mata ni kinga ba harka nake da mutane ba kamar ki ko ke zaki duba masa dannaga yana bukatar karin aure...
" To ke banda abunki ga yasmin nan me zai hana ahadasu...
" Nasan halin yasmin hajiya ba lallai ta soshi ba kuma kinga shima dr sageer din ba lallai yasota taba kina ganin yadda ake sokarta cewa taki auruwa nafeson daidai da'ita ya aure ta....
" Mama kenan ne zanyiwa baffan magana inyaso sai abasu lokaci zakiga in suna son junan su...
" Mama ce tatashi tashiga daki nan takira aisha tagayamata...Aisha ce tace ai mama kece baki saniba yasmin ta dade azuciyar dr ai ke dai kawai kiyimata addua Allah yasa alkhairi ne ...." inshaa Allah sannan ta goge hawayen ta dama zanga auren yasmin Allah nagode maka...
Alhaji haruna ne yafito yaga baffa ya chanja mota tsayawa yayi yana kallon ta can yace kace kafara sayar da kawonan mutane kazama dan fashi ko dan mafiya in ba mafiya ba uban wa zai baka kudinnan dakake samu...
" Baffa babu abunda yace sannan ya huce bangarensa....
" Nan hankalin su isa haruna har su khalil ma duk yatashi sai jafa'i suke jawo mada... matar isa inna itace tayi magana tace ai bakuga komai ba tunda zalunci kuka saka agaba...
A lokacin dr sageer ya shigo kallon motar yayi tayi bala'in kyau sannan yace musu sannunku ya shiga part din baffa bayan sun gaisa da baffa sannan ya shiga cikin palour hajiya da mama suna zaune suna hira yayi musu sannun su sannan yace mama ina yasmin?
" hajiya ce tace me zakayi mata da tsohon daren nan?
" hajiya sak'ona zan karba
" Tana daki bari na kirawo ta tana fitowa yarasa me zaici mata sai kallon ta yake sai kuma yace turamin suratul bakara please...
" hajiya tace ina na wayarka? " hajiya nayi deleting dazu bansaniba....
" Yasmin tace bari na dakko maka memory din sai kayi copying...
" sauri nakeyi please ki mikomin mota..
Tana fita ta tarar dasu carko carko suna ta gulma karasawa tayi tace ya dr gashi karba yayi yace wallahi nakasa sukuni kwatakwata so nakeyi kawai naganki shiyasa na biyo domin naganki zani gayamiki son da nake miki cikin raina zankula dake please ki kula dani...
" Shiru tayi tana kallonsa domin kalar tasa kaunar tana burgeta...
" Darajarki a zuciyata tana karuwa, Wahalar sonki nashata sam bana damuwa, wallahi banki ace yau zaa daura auren mu ....
" Murmushi tayintace kayi ahankali karsu mamee suji please...
" To yaushe zaki bani amsata??
" zanbaka ga wannan sannan ta juya tana zuwa gurin su mamee maryam tace iyayan asiri za'a asurce shine, khalil ne yace ai dr bazai aureta ba komai nacinta a daije akare da masu faskare....
" Yasmin ce tace Allah ko ke ai zai soki sai kije ki aure shi tunda ansaba bin dutse...can tace ko bahaka ba Alhaji....
" Nace ubanki ne yake bin kan dutsen banza masu yankan kai....
" ubana yafi karfin ku wallahi nangani nan bari nagaba yayi gaba sannan nan tashige....
" Hajiya tace ke dawa yasmin nida wayannan 'yan rainin hankalin...
" Mama tace banson tsokana salan suzo su zazzageki...
Dr yana shiga brstr ramlat tace munafiki tsinanne mai bin mata kagama kazantar taka shine kashigo???
" Cikin zafin rai yakifa mata mari mara mutunci naga take taken ki wallahi sai kingane kuranki mara mutunci duk hakurin danakeyi dake??
" hakurin me to wallahi sai dai kazaba ko kafasa kara aure kokuma nabar gidan ....
" Waya hanaki bari tafi yanzu ma sai kindawo kuma aure nan da 2month sannan yashiga daki kuka takara saka gashi tajawo sunyi fada gashi tana bukatar mijinta dakin ta shiga ta kwanta akan gado kusan awanta 2 tanata juye ahaka har dr ya fahimce ta nan yafara sarrafata har hankalin ta yatashi daga nan tafara kissing dinsa cikin kidemewa har sai da suka shiga wata sabuwar duniya....
Da asuba rabia ta kirata tace lallai kibar gidan kitafi gida yazaba ko ke ko aure...aikuwa ta biyewa rabia da safe tatafi....
" ya shirya zai tafi aiki ya kirata ta gaggaya masa magana cikin zafin rai dakyar yake tukin har ya'isa kofar gidan ya kira yasmin yace please tafito zata ga black mota...
" Mayafin ta ta yafa sannan tafito ta bude motar tashiga cikin damuwa da idanun sa sukayi jajir yace zaki aure ne yasmin please kada namutu...
" Yasmin ce tace so ai baya kisa...
" Amma kema kwanakin baya aikin san zafin soyayya da masoyin ki ya gujeki ko??
" Shiru tayi tana kallonsa...
Dani dake akwai alak'ar mu ta 'yan uwa, zuciya tawa ke ta kama, komai wahala dake zani kasance, Alkawari ki rik'e komai wuya kar mu rabu kinji... rashin yarda dani zaisa nafada halaka ki taimakawa ruhina kisoni danAllah ni ke nake so yasmin...
" Cikin hawaye tace kai daya na yarda muyi soyayya acikin ruhina, banyi zaton zan kamu da soyayya a nan kusa ba, Na baka dama kasan kaunar ka, tabbas nagani bani da tamka kaine kadai zabina, kai kagwadamini son da kakemin dan na shaqu da da kai, sannan ta rike hannun sa tace na baka amanar kai na...
Assalamu alaikum
Kuyi hakuri masoyan wannan littafin tabbas ina cikin busy ne shiyasa banayin post akai akai Kuyi min afuwa masoyana ina tare daku....
Ko yakuke ganin wannan soyayya???
Yasmin da dr sageer sun dace??
Barister ramlat wane hali zata shiga in taji labarin yasmin zai aura???
Wacce irin k'awace rabi'a??
Ko yaya auren su dr zai kasance???
*WANNAN SHAFIN SADAUKAR WACE GAREKI MATAR KIRKI MATAR K'WARAI UWA GA 'YAN BIYU WATO ANTY MAI JIDDA ALLAH YASAKA MIKI DA ALKHAIRI YAKARA SOYAYYA DA MAIGIDA*
_I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's_
*How was the page???*
_Please do vote comments and like my story really need your comments and vote#TEAM....DS
*Wadãtar zuci {Qanã'a}*
Duk wanda ya wadãtu da abin da Allah SWT ya bã shi; to, zai sãmu nutsuwar zuciya da kuma dãcewa a rãyuwar duniya da qiyãma.
Allah SWT yana fad'a cikin suratun Nahl ãya ta (97) cewa:
(( Wanda ya aikata aiki na qwarai daga namiji kõ kuwa mace, alhãli yanã mumini, to, haqiqa, Muna rãyar da shi, rãyuwa mai dãd'i. Kuma haqiqa, Muna sãkã musu lãdarsu da mafi kyawun abin da suka kasance sunã aikatãwa )).
Manyan Malaman Tafsirin Alqur'ãni da yawa sunce game da wannan ãyar shi ne:
( Rãyuwa mai dãd'i a duniya shi ne wadãtar zuci ).
Sannan kuma duk mai wadãtar zuci yã rabauta bisa ga abin da Allah SWT ya bã shi, kuma ya kasance arziqinsa dai-dai buqãtunsa, wato ya kasance tsakãnin yalwar kud'i da kuma talauci.
Don kasantuwar komai tsakã-tsaki shi yafi; Nawa nawa ne mai kud'in da kud'insa ya shagaltar da shi ga barin sanin Ubangijinsa ! Kuma nawa nawa ne talaka wanda talaucinsa da neman abincinsa ya shagaltar da shi ga barin bautar Ubangijinsa !!!
*Urs Nana diso*
Deejarh berver
http//:deejarhberver.wordpress.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 50-55
*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_
_NA NANA DISO_
http://deejarhberver.wordpress.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Doctor sageer ne gaba daya ya gigice don bai taba tunanin wayannan zafafan kalaman daga yasmin ba kallonta yayi sannan yaja motarsa sai wane babban super market Nan yadinga kwasar mata kaya har sai da tace doctor lafiya kuwa...
" kallonta yayi yace samun mace irinki sai an tona yasmin bansan me zanyi na faranta miki ba nidai nasan banda kamarki ina cikin damuwa Amma gaba daya k'in yayemin ita lokaci guda ina kaunar ki matata to be...
" wane murmushi tayi dayakara fito da kyanta tace Lallai dr ma yanzu da k'a dakko ne me zancewa su mama in nakoma?
" yasmin kenan har yanzu soyayyar tawa batayi nisa cikin zuciyar ki ba kenan?
" Bahaka bani kasan dai da kunya nagaya musu ai...
" oyaa muje kisha drinks wane bakery suka shiga suna zaune kowannen su yana kallon juna yasmin kuwa mamaki duk ya rudeta wai dr sageer ne ke sonta tabbas ta yarda wane hanin ga Allah baiwa ce babu irin kalar soyyayar da bata gani ba daga karshe suka gujeta...
" baby yasmin me kike tunani??
" Murmushi tayi tace rayuwa.. " banson kina dogon tunani please tohm shikenan...
" Barister rabia adaidai lokacin ta shigo bakery din ba mamaki dr sageer tagani da yasmin, dariya tayi sannan tace lallai nasamu babbar hanyar kashe miki aure ramlat, zama tayi nisa dasu sannan ta kirawo barister ramlat tace ke hau whatsapp yasmin tanata murmushi ta daukesu ta tura mata..." kai rabia ai yasmin ce wannan..." To koma wacece gatanan sai soyayya suke da mijinki laahhh kinga ma yakusa kissing dinta subhanallahi.. " kuka ramlat tasaka sannan tace wallahi sai anraba auren mu tasa kuka...." rabia tace koni ce ai saina sa yasakeni daman nace miki iskancin sa kawai yakeyi kuma aikin gani...
Mumy ce tace Yarinyar banza da wofi ni banga amfanin ilimin kiba ramlat tayaya miji bazai karo aure ba? Kinzama kazama mara ladafi ga dinbin hauka to wallahi ni bazaki zauna agida na ba adinga zagina ana nunani da baki ana kirana da asararriyar uwa sam kafin ubanki yadawo yayi miki duka kitattara ki koma danni ba irin sha sha shen iyaye bani...
" Mumy bin mata fa yakeyi yanzu ma rabia taturomin hotonsa da wata...
" koba kawaba ai sai takashe auren zata hutu sau nawa ina miki kashedin rabuwa da rabia baki jiniba ko? To wallahi nakarajin kincewa dr dan iska sai kingane kuranki ..
" Ai dama bakwa sona yana cutata amma kun goyi bayansa...
" dallah yimun shiru akwai son da yahuce nayi miki addua kikasami miji nagare wacce kowacce mace take fata nakuma aura miki shi sannan nace kizauna dakinki ki neme aljannar ki??
" Amma ai...
" yimun shiru ja'ira kawai ki dau mota kikoma gidanki...
" cousin din ramlat ce tace aikam kawai wasu neman auren ma sukeyi amma ke kinsamu sai iskanci kikeyi sai ki kaso auren ki dawo kiga ko damai kwasarki...
" brstr ramlat dataga bazata samu goyon baya agurin su ba, cikin ikon Allah sai ga dr sageer ya kirata after magrib yace tafito su tafi cikin borin kunya tafita Amma shi bai ce mata kala ba...
Tunda suka dawo babu wanda yayiwa juna magana sai ma wanka da barister tashiga tana fitowa ta tarar da miss call din rabia sauri tayi ta kirawo ta tace kee lafiya da daddaren nan....
" Dallah kinyi masa zancen yasmin din danagan su tare? To karkiyi kizama mara yanci gwara ki sanar dashi yasan kinsani...
" Ai daman zangaya masa hauka nakeyi nayi shiru aikinsan abunda bazai yihuba kenan...
" bayam ta katse wayar sai tasa kayan baccin ta nan ta kalli cikin ta har yafara fitowa murmushi tayi takara turoshi sannan ta nufi dak'insa, tunda tashiga yake faman kallonta saboda tsabagen kyan datayi masa shi daman doctor yana bala'in son yaga matarsa da sleeping dress...
Zama tayi tace wannan yarinyar ta nuna hoton yasmin awayarta tace menene Alakar ku?
" kallonta yayi yace budurwa tace kuma itace wacce zan aura...
" Ashe kuwa baka siyawa kanka farin ciki ba indai kayi auren nan zaga yadda ake hauka wallahi...
" Murmushi yayi yace au kinfasa tafiya ne? " kuka tasaka masa daman ni baka sona baka kaunata ai shiyasa kakemin abunda kakeso...
" Tasowa yayi ya zauna kusa da'ita ne ina sonki ina kaunarki matata sai dai kuma narasa wa'yanda suke zugamin ke, shafa cikinta yafara yana this my baby endless lurv for you...
" Rungumesa tayi daga nan kuma yafara kissing dinta batasan lokacin datace inasonka dr i can't live without you nan ya shiga sarrafata sai gurin 10 yasaketa yayi wanka....
Mama ce tace Baffa kaga siyayar da sageeru yayiwa yasmin kuwa nidai lamarin nan yana bani tsoro...
" hajiya suwaiba tayimin bayanin zan tambayi yasmin din ko tana sonsa tukunna...
" Allah mai iko kaga sai yanzu Allah yakawo mijin anata abu ashe shi mijin nata yana kusa da'ita ma...
" Ai daman haka sha'anin Allah yake sai dai in mutum baiyi hakuri ba, sai ki kirawomin yasmin din ..
Tana shiga ta tarar da ita azaune tace yasmin..
" Naam mama? " kizo inji baffa yana kiranki...
Tana fita ta zauna akusa dashi tace gani baffa...
" Yauwa auta maganar sageeru ce yazo akan cewa zasu turo sati mai zuwa kuma nayi miki alkawarin bazan yi miki auren dole ba sai ki sanar dani ko kina sonsa?? Banson bata kunya ke 'yatace kina ban shawarwari ballantana kuma maganar rayuwarki ki bude baki kigayamin da kanki banson na zalinci ki...
" Shiru tayi nadan lokaci har sai da yakara maimaita magana sannan tace eh baba sannan tamiki tabar gurin tana shiga ta rufe kofar dakinta tare da murna daman zanyi aure nan ta kwanta cike da murna...
Yau ramlat da zazzabi tatashi sosai har sai da yasaka mata karin ruwa sai shagwaba take masa saboda sha'awa datake tada masa yasa yabar gidan...
Hajiya ce tace yasmin taimaka mini danAllah kije min gidan sageeru ga atampopin matarsa sai kuma kiyi mata sannu...
Gaskiya hajiya matarsa bada kirki kinga kartayi min sharri wallahi...
Mama ce tace au bazaki je ba kike nufi tashi kitafi kafin ranki ya baci, ai babba baya aikin ka kace aa..
" Hajiya ce tace ai yasmin da gaskiyarta ramlat bata da ta ido kwatakwata daman sageerun yace bazai fito ba yau ramlat din ba lafiya shiyasa...
" yasmin dai ba'ason ranta ba ta yafa mayafi daman wata duguwar rigace ajikinta tana fitowa ta dau kayan...
" Hajiya tace kiyi shatar abun hawa kina kaimata sai ki dawo...
" Tohm hajiya...
Lokacin da yasmin tafita ta tarar da ahmadu mai adaidaita ko zaka kaine sabuwar unguwa??
" Muje mana yasmin sunatafi suna hira har suka isa dataje gidan shiru tayi sallama yayi sau 10 apalour din amma ramlat batace uffan ba...
" yasmin aranta tace ai wallahi ni bazan dau rainin nan ba sannan tace gashi inji hajiya in yadawo abashi...
" ramlat ce tace to dan mikomin wannan bazan iya tashi ba..
" ita kuma yasmin taga daidai cikint ne shine taji tsoro amma dataganta akwance sai ta taimaka mata ai kuwa tana durkusawa zata miko mata sai ga dr sageer nan ihuuu ramlat tasaka sannan tace wayoooo zata kashemin baby muguwa azzaluma....
Yasmin da gaba daya tatsorata sannan ta jiyo taga dr sageer ya shigo idonsa har wank jayayi...
" ramlat ce takara da cewa wayyoo cikina nashiga uku wallahi indai da'ana ya mutu sai nima na kashe ki kuka tasaka ramlat yasmin kuwa da ta miki sanin kanta dr yans bala'in son yara bata ankara ba sai taji mari...
" Daga aiko ki cikin gidana shine zaki gular mata ciki da hannu yasmin kashemin ita zakiyi da baby na???
" ramlat ce tace Allah yaso kagani da idon ka da sai ace sharri nayi mata...
" yasmin batace komai ba sai kuka haka tabar gidan mota ta hau sai kuka take har ta'isa gida mama da hajiya na palour tazo ta hucesu tana kuka hankalin mama yayi mugun tashi amma sai tayi ta maza ta dake...
" Hajiya tace ohh ni suwaiba me kuma yafaru?? Duk sukayi dak'in...
" yasmin tace daga nashiga gidan sai takarasa musu labarin tana kuka amma batace dr ya mareta saboda mama zata iya shiga damuwa hajiya kuwa sai tace sai ta rama mata...
" Mama ce tace Allah yasawake ke kuma da kuka bayayi miki wahala ai sai kiyita yi....
" Hajiya tace yi hakuri auta kinji aniyarta ta bita Allah ai baya zalunci...
Abida kenan cewar Amal irin wannan kyau haka kinsa rake da zuma sai sha kikeyi inci dai dawani sirrin???
Wallahi amal ban cushe cushen kayan matan nan wannan fruit din idan nadinga sha sun isheni ke bakiga oga yadda yake gigicewa ba wallahi, kuma kinsan wani abu harda rashin tsafta yakansa maza suja baya da kai ke dana gyara bakiga yadda yake mutuwa akaina ba...
" Ke wallahi gaskiyar ki wata makociyata zainabu bata rabo dasu kwakwa da aya ke har kantu kullum cikin tauna da lemo takeyi innaci mata ke bakya gajiya da cinsu sai tacemin ke gyarane ba kadan ba ai sirrin su sai mai yi...
" Wallahi kam ai indai mace ta dage da biyayya da kula da kanta ai sai sambarka wallahi...
Hakane wallahi..
Yau kusan sati guda kenan yasmin ko wayarsa bata dauka bama tabari su hadu gashi ankawo kudin aurenta dubu dare biyu ansa biki wata 4..
" mama ce takira yasmin dak'in tace lallai yasmin nalura fushi kikeyi da dr kenan?
Mama goyan bayanta fayayi kuma yasan karya takeyi..." haba yasmin mutum akan abunda yakeso ai makaho ne kin manta son yara irin na sageeru to bari kiji wata rayuwa zaki fara wacce gaba dayanta hakuri indai kinason ganin daidai kinaso kuma ki dace, dole sai kin kau da kanki kinyi kuma hakuri sosai kuma ki tsaya ki karanci mijin ki sosai, bakiga komai na makirci ba kwata