Showing 21001 words to 24000 words out of 42346 words
....
Abida ce tace ai daman idan kun kita wasu zasu sota...
Barister ramlat gida taje ta yini mumy sai tausar ta takeyi gashi har andaura aure yau jumma'a akan sadaki dubu dari da hamsin, hankalin ta bai tashi ba sai dataga part din yaamin yafi nata kaya nan dady yace anjima zaa zuba mata sabbi karta damu Amma kina ganin barstr kin san bata cikin hankalin ta sai kuka....
Bayan ansakko daga sallar jumma'a yasmin tasaka wani hadaddan les dinta tasaka head pink sannan tasa sarka pink jakarta da takalmin ta kuma farari kasancewa yusra ta iya kwalliya nan ta rangada mata mashaa Allah maganar kyau ma ba'ayi mamace tace auta kece??
Dariya tasa ta rungumeta akayi yimusu hoto daga nan ango da abokanan sa sukazo kallonta kawai dr yakeyi ji yakeyi kamar ya rungumeta sai da suka gama hotonan su sannan sukaje cikin gidan su mamee dakyar akayi hotunan saboda habaici idon yasmin gaba daya yakawo hawaye bayan sunfito yatsaya asoro tazo shiga gidan yace yasmin anjima da da daddare zaayi dinner tsaki taja sannan tasa kuka bazanje ba bazanje ba bai san lokacin da yafara kissing dinta ba gashi ta kasa tureshi sai bayan mintuna ya saketa idonta sai hawaye yake fitar sau nawa ina baka hakuri baka damu dani ba...
" kissing din bakin ta yakarayi kin tabbatar ina sonki ina kaunarki matata na yarda dake ko'ina nashige ke zan nuna, ke tawace, na soki zuciya ta daya, rungumeta yayi sann kara da cewa bana nadama nasan sona ne yakamaki...
" Hawayen ta ta cigaba da zubar sannan tace wazai tabamin kai na barshi akanka zanyi komai, rayuwa da kai zanyi ta so zama farinciki dan yakore damuwa ta, ina kaunarka mijina, Ni dai taka ce danAllah kada ki yadani, kai kadai nabawa yarda cikin zuciya...
" To ki daina kuka kinji? Zanyi alfahari dake in kika zamo acikin gidana..anjima ki shirya za'ayi dinner..
" To ta tacemasa tare dayimasa wani rikitaccen kallo sannan ta shiga cikin gidan...
" yana isa mota khalifa yace yau dai burin ka yacika yakamata kaje gurin ramlat bakaji muryarta ba ...
" Dole natafi gurinta na lallashi matata...
ASSALAMU ALAIKUM
~INa gaisuwa da jinjina gareku d'inbin masoyana, adduo'in dakuke min nagode sosai....Nayi tafiya Nakuma dawo lafiya!
*Tell me your opinion about this page!*
~*...Again apologized for the spelling and grammar mistake....bansamun cikkakin lokaci na kara bin labarin...ballantana nagyara...*
_Rayuwa tafi take da matsala da jarabawa kalakala...hakurin ka shine kawai nasararka... Ba za ka sauka tashar nasara ba sai ka hau motar hakuri da kokari da sadaukarwa..... Yana da kayu ka yafe idan aka yi ma laifi. Abin da ya fi haka kyau shi ne ka manta da laifin da aka yi ma ka......Rayuwa komai me wucewa ce..._
*Please do vote comments and like..your comment give me more courage to continue writing my story...and it helps me to write better...#TEAM...DS....DSLOVER'S*
Alqur'ãni mai girma shi ne tushe na farko cikin abubuwanda suka shãfi shari'ar Musulunci, kuma zuwa gare shi musulmai ke kõmawa yãyin da wani abun ya rikitar da su cikin lamarin duniya da lãhira.
Mumini na qwarai yana yin duba zuwa ga Alqur'ãni a matsayin abin d'auke kewa ta yarda yake karantã shi kullum, sã'ilin nan yake tin-tin-tini cikin izinar da ke cikinsa da misãlai da ya qunsa, kuma ya nemi fahimtar Alqur'ãnin da hukunce-hukunce da ya qunsa.
Sai kula da aikata duk abin da Alqur'ani yayi umurni da shi, da nesantar abin da ya hana, don shi ne kad'ai litattafin da ya dãce ga rayuwar d'an Ãdam kuma yana nan a kiyãye kamar yadda Allah SWT ya fad'a cewa:
(( Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alqur'ãni), kuma lalle Mu, haqiqa, Mãsu kiyãyewa ne gare shi )).
Bisa ga haka mumini na qwarai shi ne wanda ba ya nesantar karatun Alqur'ãni a kõda yaushe, sannan kuma yake qõqarin bibiyar ma'anar abin da yake karantãwa da neman sanin wasu darussa wad'anda suka shãfi Alqur'ãni.
Shi Alqur'ãni igiyar Allah SWT ne wanda yake miqaqqe, duk wanda ke son Allah SWT da gaske, to, zai so littafin Allah ya kuma girmamã shi da ma'abõtansa.
*Urs Nana diso*
Deejarh berver
http//:deejarhberver.wordpress.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 60-65
*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_
_NA NANA DISO_
http://deejarhberver.wordpress.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Anty najiba ce kanwar mumy tace haba barister menene abun damu ak'an kishiya common sai kace jahila kinfi yarinyar nan komai da komai fa akasari ba ke ba'ajin ta bace ba ki manta da'ita tashi muje kiyi wanka ki shirya kema kinji my barister...
" Har cikin ranta ramlat ta d'anji dadin kalaman ta goge hawayen fuskar ta tayi sannan ta shiga wanka...
Dr sageer ne yakaraso cikin gidan su ramlat mumy yafara tarar wa sannan suka gaisa cikin farin ciki tace Allah yasanya Alheri doctor ya hada maka kansu...
" Har cikin ransa yarasa irin mumy tabbas wata suruka ce da babu ruwanta gata dai 'yar boko Amma tafi masu ilimin dayawa aiki dashi cikin murmushi yace Ameen mumy....
" Ramlat din tana cikin daki kaga ko abinci tun safe ta kasaci narasa irinta wallahi sai kana hakuri da'ita dr kana kuma yimata wa'azi...
" Murmushi yayi yace inshaa Allahu mumy sannan yashiga dak'in da take nan yaganta zaune ko kaya bata saka ba tayi tagumi rufe kofar yayi yazauna kusa da'ita cikin bacin rai yajanye hannun sannan yace haba matata haba sirrin zuciyata, ke tawa ce iyalina sannan ya rungumeta wane kuka tasaka mai cike da tausayi dagota yayi ya goge hawayen sannan ya kalleta haba ramlat so kikeyi ki illata kanki da baby din cikin ki???
" Shiru tayi batai magana ba sai da yagama goge hawayen fuskar ta sannan tace ai duk kai kajawomin da kakoyamin soyayyar ka kasaka min dafi acikin raina, yanzu itama haka zaka tararrayi ta kenan??
" Haba my wife haba ramlat ba dan bana sonki yasa nayi miki kishiya ba badan in muzanta miki ba wallahi ina mutukar son mata biyu wannan kaddarace daga Allah kici abincin sai kisha maganin ki kinji?
" Wane murmushi tayi da yakaraso da hawayen fuskarta tace ni sai dai k'abani bazan iya ci ba...
" Uwargida rangida duk yadda kikace haka za'ayi ai karbi to kici...
" Kallon sa kawai takeyi tabbas sageer dole mace ta sosa cikin maza dare kadan ne irinsu yadda yake tararrayar matarsa sai da tagama ci sannan yabata ruwa..
" kwanciya tayi kan kafadarsa sannan tace yau zakuyi dinner ko?
" Eh yau za'ayi ga kayanki can apalour zakije ko??
" cikin murmushi mai cike da boye damuwa tace kanaso naje?
" Ai abunda kikeso shi nakeso in hakan zai haifar miki da damuwa ai bai kamata kije ba...
" kumatun sa tashafa tace farin cikin ka shine nawa inasonka da yawa mijina...
" Bakinta ya sumbata yace nima haka matata uwar 'yayana ina bala'in sonki...
" yana shafata yana danyi mata hira har bacci ya kwashe shi sallar azahar yayi sannan yanufi asubuti dan yanada aiki...
Anty najiba ce tashigo taga yadda ya kwantar da'ita ga kuma kayanta da rafar 'yan dari bibbiyu akusa da'ita murmushi tayi tace dama mijin mu muma zai dinga yimana adalci kamar yadda dr yake yiwa su ramlat tana cikin tunanin nan taji wayar ta text ya shigo tana budewa taga rabia tana cewa wai ke meke damunki da baki kashe auren ba tabbijan kina gani yana rawar jiki akan yarinyar kina zaune su hada miki hawan jini bikin ma kiyi zaman ku agidan ku karki je... najiba bata tsaya ko'ina ba sai dak'in mumy nan tabata takaranta mumy ce tafara blocking dinta kafin nan tace...
" Wallahi narasa irin ramlat tarasa kawar da zaau dinga mu'amala sai rabia shiyasa in ramlat tayi wani abun nake tunanin sata akai zata kashe min yarinya....
" najiba ce ta kada kai tace abunda kawaye sukeyi kenan su kashe maka aure su aure mijin naka, kuma su saka ayawon duniya, ai duk mai hankali yasan kawa ba abar anemi shawarar ta bace...
" Wallahi kam bani wayar tata boyeta zanyi..
" Ai dr sageer sai son barka wallahi ba'acewa komai saboda namiji ne mai kokari...
" mumy tace shine ai suje mata bakin cikin su rabata dashi...
Anty barira ce taja hannun yasmin tayi cikin daki da'ita ke zo kikaebi tawa tsarabar...
" Turo baki tayi tace nifa tsarabobin nan sun 'isheni gaskiya...
" Dariya anty barira tayi tace ke tawa ta dabance shanye wannan zallar aya da dabino ne da zuma ki shanye duka roba biyun..
" dakyar ta'iya shanyi wa sannan tace wash cikina fa yacika...
" karbi wannan kazar da nonon nan kishanye ma..." dakyar ta karasa sannan tace yau kinsa nayi over ci...
" Zakiji ajikin ki ai da kanki zaki nemi ne...Anty aisha ce ta shigo tana cewa haba anty barira 'yan ubanci zaa nunamin ne ansata a dak'a ana gyara mu anshanya mu...
" Haba aisha jiya zuwa yau nawa kikasha...
" hahaha ai ni nafeson wanda zai burkice in muka hadu....
" Toh uwar magana kyalemu nayiwa 'yata wa'azi ke yasmin ki saurari ni kijini shi namiji ke zaki gyarashi duk kazantar sa zaki gyara abunki, Amma fa sai kina gyarawa kema duk wani lungu da sako na jikin ki ki tabbatar kina dirjeshi da sabulo, warin baki kada ki sake kice zaki zauna dashi ki dau makilin kiwanke hakoranki, duk yadda kika kai da son jiki kada ki bare gashin hammata dana mara su tarar miki su sukesa warin jiki ki aski kina ta ammali da turari in mijinki yaji wari ajikin ki to kin kade, kishiyar ki 'yar gayu ce kema sai ki dage da gayu, kuma kada kice zaki zauna da faso ki wanke kafarki ke kada ki zauna lebenki ya bushe dinga shafa ko basilin ne kuma girki kikara dagewa kada kisake mijinki ya dawo ki barshi da yunwa kinji...
" Inshaa Allahu Anty barira zan kokarta inshaa Allahu...
" Yauwa 'yar gidana Allah yasa Albarka a auren naku...
Karfe 7 da rabi nadare yasmin tafito sanyi da gown dinta red and white tayi masifar kyau ga kwalliyar zamani ta dauki fuskarta jambakin ta ma abun A kallane ga jikinta yajik'o da tsumi jitakeyi kamar tana jik'ewa, Dr ta sageer da yasha farar shaddar sa mai adon ja tayi masa kyau koya ya murmusa sai kiga hushiryar sa ta bayyana kallon ta yatsaya yi kai mashaa Allah matata ta takaina...
" Mota tashiga sanadiyar babu kowa aciki su yusra basu karasa fitowa ba yace yasmin cikin jin kunya takasa kallonsa...
" Gaskiya kinyi bala'in kyau mashaa Allah... " da karamin bakin ta da yaaha jambaki tace nagode..
"Jiya yi gabadaya jikin sa ya mutu yasmin please ki goge janbakin ki wallahi kina sakani cikin wani hali ga wata muguwar sha'awa, yana daga cikin abunda ke tayar min da hankali especially innaga ansa kuma ana magana kingA kada acikin mutane nayi abun kunya ko??
" Murmushi tayi sannan ta dakko tushu ajakarta za goge..
" Basai kin wahalar da kanki ba yasa bakin sa yafara kissing dinta tas sai da ya goge...wani numfashi yasmin ta sake jikinta har wani yar yar yakeyi..
" Turo baki tayi tace to ai duk ka kwashe...." kibarshi haka yafi kyau daga nan suka huce gurin dinner kai ramlat ma tayi bala'in kyau har inda suke taje ta rungumesu aka dau hoto ya'ilahi tace saboda kawai kokartawa takeyi amma zuciyarta kamar ta buga intaga yana yiwa yasmin magana, baau tashi ba sai 12 dinner tayi kyau sosai....
Washe gari tun karfi biyu akayi kamu da yamma baffa yayi mata waazi bayan karfi 6 mutocin kai amarya sunzo mama tace yasmin kije kuyi sallama da mamee mana dasu maryam ...." tohm mama tana shiga mamee ta dinga jawo mata bala'i kala kala amma bata kulasu ba nan tayi wanka sannan tashirya daga nan aka dau motoci sai gidan yasmin....
Barister ramlat ke zaune duk abun duniya ya isheta sai jitayi ance ke kin isa nakiraki kiyi blocking dina...
" Ramlat ce tace banza wayake ta waya ina cikin bala'in nan narasa inda zansa kaina...
" Karki damu aminiyas shiyasa na tako nabaki shawara wacce zaki hanasa kusantar ta koma suyi soyayyar yau ki ruguza musu farin cikin su yadda kema yayi miki...
" Ramlat ce tace barister rabi'a wacce shawara ce wannan???
" Hmmm bayan kowa yatafi ki fito tsakiyar palour kisa kara sannan ki fasa kwalba ki caka ahannun ki yadda jikin zaita zuba...
" Yauwa rabia wannan ce kam mafita dannasan inyaga jinin hankalin sa zai tashi sosai...
" eh mana bari ni natafi sauri nakeyi...tohm sai kinjini...
" Dariya brstr rabia tasaka ahanya tace ni ai ban taba ganin jakar mace irin ramlat ba komai dauka takeyi hahaha ai sai nakashe auren nan kuma na aure doctor namijin mazaje...
Bangaren yasmin badai kyau ba duk irin gudar da akeyi duk ramlat tanaji sai karfe 1 sannan doctor ya shigo yana shigowa ya fara shiga dakin ramlat nan sukayi sallah har da tuntuben sauri...
" Amarya yasmin mata ga doctoe sageer yau Allah yayarda...
" Murmushi tayi cike da sonsa...
Sai kitashi muje muyi sallah ko? Sai da sukayi alwala sukayi sallah yana tayi mata addu'oi tace nifa bacci nakeji...
" to ai yanzu sai kijirani ko ya watsa ruwa ita kuma ta riga ta kwanta bacci har yana kokarin surarta can taji mutum abakin ta dakyar yakarasa adduar ma cikin kidemewa yafara shafata yana kokarin rabata da riga sai kuwa wani mahaukacin ihu sukaji....
" da sauro ya fito yasmin kuma mayafi kawai tasaka...
" ramlat da 'idonta yayi faman ja tafasa kwalbar sai caccakawa takeyi ahannun ta....da gudu dr sageer yazo ina yana kokarin kwacewa har ta suma....
" Yasmin kuwa cikin gigicewa tace anya lafiyar ta kalou da daddaren nan zata...
" dakko min jakun kunana yasmi i sauri ramlat ramlat daki yayi da'ita sai da ya gyara gurin sannan ya saka mata robar ruwa ya kwantar da'ita ya lullubeta ....
" yasmin da macce ki ibarta doctor yace jiki kwanta yasmin...
" Tunda ta samu bacci ai sai ka taso kaima...
" Sai kace mara imani kina ganin ta suma taza'ayi natafi na barta ko farfadowa batayi ba?
" Tsaya wa tayi tana kallonsa can tace ince ita tajawowa kanta ai naga...
" to kitafi ni anan zan kwana kije ki kwanta ke daya, danyan ciki ne fa da'ita...
" Yasmin ce tace Allah yabata lafiya sannan ta huce dak'inta tabbas ramlat ba karamar makira bace ba.. Amma indai akan mijina ne muzuba mugani...
" Ramlat dake kokarin bude idonta tace mijina mijina ina sonka please...
" Gani akusa dake ramlat me isa zakiyiwa kanki haka nifa nakine har abada ...
" kanta tasaka kan cinyarsa sannan tace karka tafi kabarni tsoro nakeji...
" karki damu anan zan kwanna kusa dake...
" Murmushi tayi sannan tace to karufe kofar kazo ka kwanta...
" tohm yace mata sannan yayi yadda takeso cikin jin zafin hannun ta tace banzan nayi ba...
" Haba my sweety kwanta kiyi baccib ki kinji ni nakine har abada....
" Murmushin mugunta tayi sannan tace acikin zuciyar ta ai yasmin bakiga komai ba ma...
Yasmin dake faman zubda hawaye da kyar bacci ya kwashe ta...
Assalamu alaikum
Gaisuwa gareku masoya ina godiya da addu'oi Allah yabar kauna...
Ya kukaji shafin nan??
Menene ra'ayin ku dangane da shafin nan??
Anya zaman yasmin da ramlat zaiyi dadi kuwa zaman doya da manja??
*Please do vote comments and like..your comment give me more courage to continue writing my story...and it helps me to write better...#TEAM...DS....DSLOVER'S*
Nana Aisha RA tace: Na tambayi Manzon Allah SAW -game da wannan ãyar-:
(( Da wad'anda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu )).
Shin shi ne wanda yake sãta yake zina yake shan giya? Sai yace:
(( A'a, Mutumin da yake azumi yake sallah kuma yake sadaka, amma yana jin tsoro kada - Allah SWT- yaqi kar'bar aikin da yayi )).
Sã'ilin nan bãwa yaji tsoron tãlãlar da Allah SWT ke yi masa, a duk lõkacin da bãwa yaga alãmun dãcewa da nutsuwar zuciya, to, kada ya rud'i kansa da hakan, A'a abin da ake so ya qãra dãgewa wajen biyayyar Allah SWT.
Domin shi shaid'an yana iya 'batar da bãwa ta kõwace hanya, idan muna aikin alheri sai ya zo mana ta 'bangaren da nuna mana cewa ai mu wasu na musamman ne a gurin Allah SWT.
Abin da ya wajaba ga mumini shi ne jin tsoron zunuban da ke aikatãwa, komai qanqantarsu, in kuma shaid'an ya rinjãye shi sai ayi saurin tuba zuwa ga Allah SWT.
Kada bãwa ya rud'u da yawan aikin alherinsa; don wani laifin guda d'aya zai iya sanya rushewar ayyukan bãwa a tsawon shekarunsa har ya kai kansa cikin wad'anda Allah SWT yake cewa:
(( Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra ! ))....
*Urs Nana diso*
Deejarh berver
http//:deejarhberver.wordpress.com
Email:kabba43@yahoo.com
Gmail:nanadiso100@gmail.com
Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 65-67
*_DOCTOR_*
_*SAGEER*_
_NA NANA DISO_
http://deejarhberver.wordpress.com
© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*
Yasmin tun karfe 6 na safe ta farka jitayi gabadaya jikinta yana ciwo ga wani ciwon mara dake da wainiya da ita cikin salati da zikiri tatashi wanka tashiga tana fitowa ta saka wani material dinta da akayi mata riga da siket rigarta irin mai buda d'an saman nan wato rabin kafada awaje, kayan sunyi carasras ajikinta kwanciya tayi tana karewa da'kin kallo yayi bala'in kyau can kuma tafara lalubar wayar ta tanata kiran mama bata dauka ba sai takira yusra tace ta kaiwa mama wayar..
" salamu alaiki auta kuntashi lafiya? " lafiya