Showing 9001 words to 12000 words out of 42346 words

Chapter 4 - DR SAGEER BOOK COMPLETE BY NANA DISO.txt

05 Oct 2025

1230

    Tana shiga daki mumy ta kirata tace mumy kuna lpya??

    " lou tambayarki zanyi daman mijinki yayarda kidinga aikine kullum kina tafe? Banson hauka ramlat ina gayamiki gidan ki shine rufun asirinki kuma kawaye ba nakibani ba in bahaka ba sai sun kashe miki aure...

    " mumy yafa yarda har kaini yakanyi..

      " to Allah yarufa asiri...

  '" Nan takirawo rabia cikin rawar murya tace ke wai aure zai kara dr fa???

     " haba? To kidaina gyara gidan kidaina girki kidaina komai kizama kazama hakan zai taimaka miki sosai yace yafasa??

     " Tohm kawata angama!!!

  Yasmin ke kusa da mama tana karatu sai wayar mama tayi ringing tana dauka tayi salama yusra ce ta dauka tace kawata kina lafiya???

     " yasmin tace kwana biyu shiru baki da kirki!

     " kinsan ina benin sai next 4month zan dawo dama kiranki nayi ingaya miki wata magana Amma inaso ki fahimce ni kikuma yarda cewa matar mutum kabarinsa kuma mijin wata baya aurar matar wani, soyayyar da kukayi abaya ki dauka kaddara ce kuma kidaina damun kanki akan abu domin Almah kadaine keyi...

    " Nifa bansan inda kika dosa ba?

      " uncle nafee'u yayi aure suntafi tare da matar sudan tun 4days back!..

       " Tohm nagode Allah yasaka min yaudarata da yayi...

     " kitsaya ki saurare ni yasmin sannan ta katse wayar kan kafadar mama ta kwanta tana kuka nan tasanar da'ita...

     " mama tace bakomai Allah yabaki wanda yafisa...

     "Tun daga ranar ta rage magana tama daina kula kowa sai gaisuwa yau baffa yana kan kujera mama tace kaga yasmin zata kashe kanta fa kullum kuka!

      " Dak'in ta yashiga da kansa yace auta??

       " Naam baffa..

Ki shirya zamuje benin gobe kuma kada nakara ganin ki kina wani tunanin kinji..

     " tohm baffa inshaa Allahu fuskarta ta kumbura saboda kuka...

    Dr sageer yana zaune a office yace kai khalifa karin aure dole fa...

     " please kabar zancen nan menene aibun ramlat???

    " fitsara karya kazanta ....dan haka soon zankara aure...

   " Toh Allah yabada tagari...

    "Daga nan ya dauki motarsa direct sai gida bayan yagaisa dasu ummi sai yayi hanyar su yasmin yana shiga tazo fita zata karasa kenan ya riko hannun ta tajiyo tace lafiya???

        " Yasmin zaki aure ne danAllah ki taimakawa zuciyar data dadi tana begenki tana kaunarki...

       Kada kasoma kada kafara uncle yana cikin zuciyata bam tunanin akwai mai ciremin sonsa kagane...

    " yasmin pleass kitsaya taja hannunta sannan tafice...

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

  

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 25-30

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dr sageer da yafi minti talatin atsaye bak'omai yake tunani ba face in Allah ya rubuta yasmin ba martar sa bace ba dole ne ya hakura, cikin yanayi yaja numfashin sa sannan yace ya Allah ka dubi ne, motar sa yakarasa ya bude bai isa ko'ina ba sai asubuti nan ya duba wasu marasa lafiya sannan ya huce office yana zama yana kokarin cike wasi files sai wayars tafara ringing dauk'a yayi yace hello ramlat ina lafiya??

     " eh lafiya! Please ka tawo mana da abinci a resturant cuz bazan dawo da wuri ba!...

     " wai ke ramlat zamanki nakeyi kokuma zamana kikeyi?? Tunda kikazo gida 3times kika dafa abinci kullum ina hanyar gidan ABinci yanzu abunda kikeyi adalci ne??

    " Kaga dr gwara kadaina bata bakin ka cuz ba fahimtar maganganun ka zanyi ba danhaka sai kadaina yimun ihu aka idan kaga dama sai kasiyo wa kanka ni zanci anan...

    " Dr sageer ne yace yayi kyau ramlat zaki gani k'urunki..

    " wane tsaki taja mtseww na dade banganiba...

Juyawa yakeyi akan kujerar sa cike da tunanin mafita can nurse kwankwasa kofar..

   " sir akwai marasa lafiyar da zakagani fa sunata jiranka..

    " okay zasu iya shigowa wata matashiyar   ce ta shigo tace ina yini dr?

    " Lafiya file name?

" fatima idres.." meke damunki??

   " wallahi dr inada matsala bakina sai ya dinga wari kuma gabana shima wani wari dr mijina bakaga yadda yake wulakanta ne ba doctor please ka taimaka min..

    " okay zanyi miki abunda zan iya amma nafarko kinayin brush??

    " eh doctor wane sa'in inayi amma ba sosaiba..

    " to kice ke kazantar ki kikeyi kinsan kuwa babu abunda namiji ya tsana irin kazanta kidinga kokarin wanke bakinki ko sau biyu ne kuma kisiya mouth frshner kina kuskurewa kuma kada kici abinci kikwanta batare da kin kuskure bakinki ba inatunanin inkika bi hanyar nan bakin zai daina wari inshaa Allahu...

     " Tohm likita zansiya brush ina fita inshaaAllahu sai dai kuma warin da gabana yakeyi likita...

    " kafin nan amsamin tambayoyin nan idan kina shaving din gashin gabanki??

    " Wallahi likita banayi tunda nayi kafin haihuwata naga kuraji sunfito min sai kawai nadaina...

    " Ai ko amusulci babu kyau barin gashi yahuce 40days kuma babban abunda ke kawo warin gaba harda rashin aske duk wata kazanta ta dank'are agurin kuma dazarar kinsa pant zakiga yayi datti dan..kuma zancen kuraje dakikeyi halittane wane idan ya aske bayayi wani kuma yanayi dan haka yanzu sai ki aske sai kishafa mai agurin kuma kina askewa akai akai...

    " tohm likita inshaa Allahu...

   " idan kikayi fitsari bayan kinyi tsarki kidinga barin ruwan yana kafewa saboda wannan danshin da ragowar ruwan da zai jika miki pant dinki shima yana saka wari sosai kuma zaiyi miki illah..yana da kyau kidinga canja wando sau biyu kuma kidaina zama akasa kokuma guri mai danshi kidinga wanke gabanki da ruwa sosai kina canja sabon wando akai akai..kuma kidinga wanka janaba da wuri dan rashin wank'an da wuri kan iya saka warin gaba shima kodan ka kasance cikin tsarki da rahamar Allah kayi wankan da wuri..kuma ki daina yawo babu takalmi kina saka safa inda hali kuma kidinga yawan shan kayan marmari wayo fruit zasu taimaka miki inshaa Allahu in dai kika lura da wannan to zaki daina wari...

     " To likita hammata fa?

    " ita kuma menene matsalarki??

     " wallahi babu wuya nayi wanka ko 1daya banayi sai wari har banaso nashiga cikin mutane kuma koyaya nasaka kaya wari mai idan nasaka turaren warinsa daban warin hammatar daban warin sure daban...

    "eh gaskiya abunda ke kawo warin hammata shine rashin askewa dazarar gashi yafito mutum sai ya aske zaiga baya irin warin nan amma idan gashi yayi yawa kowanne irin sure zaki saka bazai dauka ba, Amma idan kinayin wanka kisa soso kidirje hammatar sai ki aske kikara wankewa inkika fito ki shafa turaren hammatar ki ko baki shafa ba indai bakya barin gashi yayi yawa to zakiga bakya warin nan dan haka sai kikula da aske da kuma shafa turaren hammata da dirje hammatar idan anje wanka kuma ku masu miji kudinga daurewa kuna wanka sau biyu...

    " likita me zance maka da wannan sharawa naje asubuti da yawa babu wanda yagayamin gaskiyar daka fadamin nagode nagode kuma inshaa Allah zanyi yadda kace daman sonjiki ne irin nawa Amma yanzu naga son jiki baidace ga mace ba...

    " juya kujerar sa yayi sannan ya danna bell dinsa next person ya shigo...

Yasmin ke zaune k'an sallaya tagama sallar walhar ta sai jin wayatayi cikin rashin kulawa ta dauka tace yaya aisha kuna lafiya??.

    " bansaniba wai meke damunki kowa yazo kice bakya sonki abunda makiya sukeso kenan wayagamiki asiri akai miki ke ma harda halinki idan anyi miki asirin kema sai kina kokartawa ai amma kowa yazo sai kice bakyaso ba dole suji dadi ba sudinga tunani mugun tuggun da suka hada yayi ba..

   " Haba yaya aisha ke fahimce ne mana wallahi...

    " dakata yasmin dazu mama takirani kin dage ke sai nafee'u mutum makaryace mara sonki wanda yayi miki karya yace karatu zaitafi bayan aure zaiyi kina tunanin miji to wallahi kiyi tunani kuma kikula kada mama ciwon ta yatashi akankk kowa ai mijinsa yake aure inma abun duniya kike hanga sai ki daina shi arzuki na Allah ne kiyi fata kisamu mai addini mai kuma rufin asiri ba mai kudi ba...

    " Cikin kuka tace nagode sannan ta katse wayar cikin kuka mai ban tausayi tace yaAllah in zunubi nakeyi dan yarasulillahi ka yafemin kayimin afuwa ya Allah kazabamin abunda yake alkhairi agareni...

     " mama ce ta liko au kukan kikeyi uwar kuka kidaije kisawa kanki ciwo...

    " sauri tayi ta goge fuskar tace aa mama..

   " To ki bari kije ki doramana abinci Allah yana sane dake!..

     " tashi tayi ta sun kuyar dakanta..

     "  Mama da hawaye ya wanke mata fuska ta goge tace Allah yayi miki albarka yasmin..

K'wance take kan gado tana faman danna waya cikin zafin nama ya k'wace wayar ramlat wai ni banida lokacin ki ne??

     Haba ya zaka kwacen waya wai sokake na goyaka?? Kokuma sokakeyi na daukeka naga kwance nake akusa dakai..

     " Amma kinsan ina bukatar hankalij ki ko ina bukatar ki yanzu...

     " Tsaki tayi tace to gani ai kabani please nakarasa chat dina...

     " Shiru yayi mata sannan yace kiyi ahankali ramlat banjin dadi sosai fa, rungumeshi tayi sannan ta sumbace shi cike da son mijinta tace sannu husby Allah yasawake yakara sauki...

     " Rungumeta yayi cikin yanayin soyayya yafara kissing dinta cikin soyayya tafara mayar masa da martani daga nan suka wada wata sabuwar duniyar...

   Da asuba dakyar yasamu yaje masallaci saboda zazzabin da yarufeshi bayan karfe 6 ramlat tatashi tana kokarin hada tea sai kuwa cewa tayi jikin nakane??

   " Daga mata kai yayi tace bari ta kira dr yace aa basai ta kiraba nan ta shiga kitchen takirawo rabia tace kwalliya yaufa bazan zoba jikin dr yayi tsanani...

    " ke brstr bakida hankalin namiji zaki tsaya kina kulawa dashi ki wacce irin shasha sha ce??

    " Kina nufin natsallake shi nafito?..

  " kwarai ma kuwa ai namiji ba dangoyo bani inda kece bakida lafiya fitarsa zaiyi kifito muje gurin bikinnan kinji?

    " hahha angama aminiya yanzu zan shirya sai natawo...

    " tea din data dora takashe sannan ta shiga wanka tana shirayawa dr yace ina zakije?

     " Office mana akwai abu mai mahimmanci da zanyi but kafin 3 ma zandawo sannan tadauki jakarta cikin zafin ciwo ya lalubo wayar mama bugu daya ta dauka tace lafiya sageeru???

    " Mama danAllah ki dafamin abinci akawomin kinji...

     " Tohm shikenan ta kashe wayar ta kalli yasmin tace dora couscous da miyar hanta sai ki hada salad da lemon kankana...

    " cikin biyayya tace baffa me kace nahada maka ma??

     " auta kiyi duka iri daya sai azubamin...

      " baffa ne yace lafiya naga wayar sageeru??

    " to dai lafiya ba lafiya ba tabbas yaronnan yanada wata matsalar wallhi dan bakaji muryarsa ba,abinci yace adafa musu...

     " To in zanfita sai yasmin tabini sai takaimasa, yanzu bari naje nayi wanka dan hajiya suwaiba tana hanya amma gidan dr zata sauka...

    " Tohm shikenan

Alhaji isa ne yace kai bilal ina kudin daka dauka?? Banson iskanci fa yanzu alhaji mudi ya dauke motata abashin da yake bini.

    " Bilsl ne yace haba baba ai kudinnan munriga mun kashe tuntuni...

    " mamee ce tace oho muku dai nidai abani kudin ankon dana fada...

      " Abida datazo tace gaskiya baba da kaida Alhaji kubawa baffa hakuri ko kwasamu wani rangwamen...

    " Alhaji ne yace zakici ubanki mahaukaciya sai mun wuhulakanta shi kuma kitsaya kigani...

    " Shi dai alhaki kwikwiyoni duk abunda kayi babu makawa sai anyi maka kuma wallahi babu ta inda azzalumi zaiyi gaba gashinan nayi auren amma kullum ina gida abunda kuka shuka sai bibiyarmu yakeyi...

    " Mamee ce ta rufeta da duk'a tana zazzagenta har tashiga dak'i..

  Dr sageer daya jingina ajikin gado sallamar hajiyarsa yaji cikin rashin karfi yataso da daddafawa yakarasa..

     " Sageeru lafiya dai subhnlhi ina ramlatun??

    " Dakyar yazauna akan kujera sannan yajingina yace sannu da zuwa hajiya..

    " Ai kai zanyiwa sannu sageeru yaushe jikin yayi haka???

    " dazu ne.." toh ina ramlatun??

    " Ta tafi gurin aiki..

" yanzu dan rashin imani da tausayi ahaka tafita tabarka subhanallahi anya kayi sa'ar mata kuwa??

     " Sallamar yasmin sukaji tasaka doguwar riga blue da farin mayafinta sai k'wandu na a hannun ta ahhh hajiyarmu yaushe kika karaso??

    " Ja'ira bayan kinki zuwa garin namu?

   " hajiya kenan bazaki gani ba garin nan fa banason sa kwata kwata yanzu dai yagida ya hanya??

    " Lpyalou ....ina samarin naki??

     " Murmushin karya tayi tace samari sunanan sannan ta kalli dr cikin dakewa tace ina kwana ya sageer...

    " dakyar yace lafiya sannan yayi shiru abunka da mai haske duk fuskarsa tayi ja gakuma idonsa dayayi jajir sai dan karamin nishi dayakeyi...

    " hajiya ta kalla tace bashida lafiya ne??

    " Yanzu nazo naganshi ahaka tunda kinzo taimaka wa yayan naki kibashi abinci wannan wawiyar matar tasa tafita...

    " Dan shiru tayi sai jitayi yace DanAllah..

    " Ni bari nashiga gidan hajiya hansatu mugaisa...

    " yasmin ce ta zuba masa abincin sannan ta ajiye masa akusa dashi amma sam yakasa motsawa sai dakyar yadau cokalin yana dauka ya wadi saboda rawar da hannun yakeyi...

     " Yasmin dake satar kallonsa ta tausaya masa sosai aranta tace wannan wacce irin matace mijinta na wannan halin zatafita?

     " zai dakko cokalin yasmin ta tashi ta dau abinci cikin sunkuyar da kai ta bashi sai da yagama ci tabashi lemon riki hannunta yayi da hannunsa dake dauke da zafi yace yasmin DanAllah kisoni danAllah..

    " Shiru tayi tana tausaya masa tace yaya so fa kace?? Kaima yaudarata zakayi kenan?

     " yasmin ke dai ki aminci min kigani inhar da yaudara nazo...

      " hmm tatashi zata tafi sannan tace kanemi wata ba dai niba kagani..

     " haka tatafi tabarshi yana wani irin tare mai gigicewa...

     " mumy din ramlat ce  tana sallama taganshi acikin jini caba caba aguje takarasa tana innalillahi wainna illahirrajiun dr sageer??


    *Assalamu Alaikum*

_Tabbas kun cancanci yabo da kuma godiya masoyana nagode da irin kaunar da kukeyiwa wannan littafin ina kuma fatan kuna amfana da abunda ke cikinsa? Kuma ina neman afuwarku abisa jimawa danayi banyi rubutuba wani uzuri ne ya rikine...lurv u oll_

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   _Mumini na qwarai shi ne wanda yake yarda/amincewa da duk abin da Allah SWT ya tsãra kuma ya zartar, abin da yafi alheri shi ne duk abin da Allah SWT ya zã'barwa bãwansa mumini; bã abin da shi muminin ya yake so ba ko ya zã'barwa kansa.._

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 35-40

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yasmin dake faman kokarin  samun mota sai ga hajiya suwaiba nan ta karaso cikin karamci da dadtaku irin na manyan mutane tace yasmin har kin fito??

    " Eh hajiya naga dare yanayi kuma zan shiga makaranta da safe kinga na kwanta da wuri ko??

     " Eh nima din tare zamu tafi sai kitsaya su baffan su fito ko?

    "Au ai nayi tunanin ke zaki zauna dashi tare da ramlat?

     " aa mamanki zata zauna dashi ramlat gida zata koma...

  Suna tsaye sai ga baffa sunfito bayan sunyi sallama suka shiga mota sannan suka tafi suna isa suka bude gidan bilal ne yazo hucewa yace yasmin dama magana zamuyi?

     " tsaki tayi tashige gida can sai yayi ihu yace daman rufamiki asiri zanyi tunda babu mijin aure sai kizo a taimake ki in aure ki shine zakiyi min iskanci to indai muna gidannan maga masu kwasar ki....

   " Hajiya suwaiba ce ta rufe kofar tare da fadin ohhh su dai sun tsotso tsiya marasa kunya da tarbiya Haka zaku kare dai....

    " brstr ramlat tunda tabar asubutin ta tafi gida sai take ganin kamar mumy zasu kashe mata aure can sai ta kirawo rabia awaya cikin yanayin bacci tace lafiya??

    " ke ina lafiya ana cikin wannan hali miji ba lafiya iyaye sunyi fushi dani sosai fa...

    " To aikece doluwa aikin banza sai me in anyi fushi dake wayasani ma ko matar da zai aura ce tayi masa wani asirin? Kinga ki watsar dasu kitawo aiki gobe in bahaka ba ina tabbatar miki sai sun haifa miki ciwon zuciya waye kula da namiji yanzu? Sai sokuwar mace?

    " Haba rabia mijina shine rayuwata fa banda kamarsa shida iyayena kina nufin na bujere musu?

    " kaji banza tsaya su hada miki damuwa kema ace ciwon hauka ya kamaki kifito mu shakata yarinya....

    " kumafa hakane kawata shawarar ki ta karbu kinga kinfine iya case fa??

    " hahaha..sannan rabia ta kashe wayar cike da dariya acikin fuskarta can tayi wani tafe tare da fadin ai wallahi sai na kashe miki aure sai kingane kawance ba da kowa akeyi ba...

   Cikin ikon Allah jikin dr sageer yayi dadi dan har sallar asuba yayi suna 'yar hira da mama yace mama aure nakeson karawa Amma kuma ina tsoron matan...

    " Murmushi tayi tace sageeru kenan yaushe kasamu lafiyar ma? Kabar zancen nan sai an kwana biyu..

   " Tohm na amince amma ke nakeso kisamo min yarinya mai tarbiya mai ilimin addini DanAllah kinji??

    " To Ni yaya zanyi sageeru dama hajiya kagayawa tafini hulda da mutane ai...

    " Ai duk maccen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login