Showing 6001 words to 9000 words out of 42346 words

Chapter 3 - DR SAGEER BOOK COMPLETE BY NANA DISO.txt

05 Oct 2025

1222

tayi tace babu kowa baba.." To kinji ankafe sunanki amasu zana jarabawa ran monday zaku fara sai ki shirya. " cikin mamaki tace baffa wa yabiyamin? " sageeru ne sai kiyi masa godiya. " inshaa Allahu. " Mama tace aikuwa angode.

   " Aisha ce tace kasan ina koyarwa baffa kuma ina daukar kudi masu yawa gakuma business da nakeyi wallahi baffa bana taba komai acikin kudin sai dai ko idan zanyi taimako Allah yabani miji nagare komai shi yakeyi min bana siyar komai kuma nasan gar da adduar da kukeyi min duk da bana kusa daku domin ku iyaye nagari masu koyar da hakuri da yadda da kaddara.. " yasmin ce tace hakane yaya Aisha. " wannan jakar million 4 ce aciki da dubu dari 3 duk kudin aiki na da sana'a tace nakusan shekara 10 danake tarawa wannan gaba daya nabar maka baffa kaja jari domin tarbiyar da kake bani wallahi banda abunda zangode maka duk da bana kusa dakai komai kanwata tasa sai ka turamin duk da munyi nisa kuma mahaifiyata batasaniba, hatta kudin makarantar da kabiyawa yasmin naga kasiyamin atampa duk dan karka fifita wani acikin mu, kaja jari baffa ina fatan wanna kudin yazama dukiyar da Al'umma zasu amfana da'ita ..

    " yasmin ce tasaka kuka ta rungume aisha tare da fadin tabbas nayi wani sabon karatun Anan idan kanason d'anka yatashi cikin tafarkin gaskiya to kasanar dashi ilimin addini kakuma zama babban misali nagurin koyar tarbiya,kar kuma kanuna masu bambanci , abunda zamuci miki shine Allah yayimiki Albarka yaya inasonki wallahi...

    " Mama ce tasaka kuka tace tabbas mai hakuri shikeda riba, ako da yaushe baffa kana fadan Allah yana sani damu kuma zai dubimu yau gashi ranar tazo ranar da mai hakuri zai ci riba, Allah yayi muku albarka aisha Allah yasaka muku da Alheri halinki nagari yasa 'yar uwarki tagado halinki...

    " Baffa ma yayi musu addua tare da godiya sannan yace yadda kikace naja jari zan koma sana'ar mahaifina wato atampofi tunda tun ina karami na iya sana'ar daman ba lallai kayi ilimi kakuma samu sanaar da kake tunani ba wane sain sai kaga alkhairin ka yana inda baka tunani especially idan kana addua ...

   " Tabbas hakane..

Yau Aka kai lefen dr sageeru akwati goma sha biyu kaya masu kyau, wani satin za'a fara biki yasmin kuwa ta hada kayanta zata koma boarding tun karfe 8 baffa yasa aka kaita gida ya cika da hidimomi kalakala..

    " Da daddare dr sageer yaje gurin ramlat taci kwalliya bakace ita bace ba daman irin siraran matannan ne ga ido amma batada hanci sosai kuma ita chocolate colour ce sai dai iyayi acikin ta kamar me tana zuwa tace ya muradin zuciyata..  " Cikin kayataccen murmushin sa wanda ya bayyana hushiryar sa da hakorin makka yace Amincin Allah ya tabbata agareki ya ruhin zuciyata amaryata kuma muradi
na...

    " yauwa mummy tace in gayamaka kayafa sunyi sai sai Allah yabiyaka kuma gobe zasuje jiran kayan dak'i ..

    " Dariys yayi yace tohm shikenan na riga nacika saman ku kwacika kasan kitchen dinki katoto kinsanni da son abinci...

    " Haha lallai kam..

   To ni inada aiki yanzu sai zuw gobe in Allah yakaimu..

   " kagaida gida sannan tashiga cikin gida..

 
Baffa ya bar aikinsa yasamu babban shago ya zuba kaya aciki, da magriba yana dawowa yayi sallah, Dr sageer yana shigowa yace baffa naga yanzu kana yin yamma??

    " Eh da yake yanzu nakoma shago nazuba kaya.. " shago baffa? Ina kasamu kudi?? " Wanda ya yarda da Allah ai shi zaisha kallo, ga dubu dari tukwuicin bikin ka Allah yasaka albarka a auren ku kuma kaji tsoron Allah kariketa dakyau..

    " To baffa nagode Allah yakara budi sannan yatafi, " mama tace gaskiya nayi dacen miji wallhi mai boye sirrin gidan sa akwai da babu..

   " Murmushi yayi baice mata komai ba...

    Yau jumma'a yau aka fara biki sunyi kamu da dinner sai dauren aure abun ba a magana sai wanda yaje biki dai yayi kyau sosai kuma manyan mutane sun halacci bikin su abida da maryam da bilal basu haukace ba sai da sukaga gida kowa baisan yana ginin ba kallon kolo sukeyiwa dr sageer nan suka dawo gida suma zagin. " mumy da dady sunyiwa ramlat fada abisa gaskiya da amana sannan aka tafi da ita hajiya suwaiba itama tayi mata sannan akayi gidanta..

   Lokacin da aka kaita bayan kowa ya watse tayi kwanciyar ta sai bacci lokacin da dr sageer ya shigo yaganta ta kifa cikinta sai bacci takeyi yana kokarin tashinta sai kuwa tace please darling bacci sai da safe shima haka yayi shafa'i da wutir sannan ya kwanta da asuba kuwa bayan yafita tayi sallah rabia ta kirawota tace kada fa kisake kice zaki zauna kiyi tawowarki office kinga munada case mai zafi..." eh daman zanzo sannan ta kashe wayar...

   " Hajiya suwaiba tare da aisha suka koma benin , yasmin kuwa batasan abunda ake ba tana can tanata karatun ta..

    Su abida kuwa yanzu aka kara samun kofar yawo, mamee tace kowannen su yaje ya dangwalo mata babban arzuki dan bazata aurawa talaka ba..

   Ina zakije ramlat??

" wacce irin tambaya ce dr inada aiki mai mahimmanci a office i neef to live kafin na makara..

   " Ai ban baki izini ba ko ni na dauke hotu a office.." sai ka koma kaga matarka tafita itama..

    " Ramlat ban baki izini ba nagaya miki...

    "  hmm kaga sai nadawo...

   " zama yayi kan kujera tare da takumi...

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   *WANNAN SHAFIN SADAUKAR WANE GAREKU FACEBOOK READER'S ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI SAK'ON NINKU SUNA ISA TA, INA KUMA GODIYA SOSAI...*

   GOD BLESS YOU OLL....

Ya zo a hadisin Mu'ãz d'an Jabal (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:
(( Ka ji tsõron Allah a duk inda kake, sannan ka bibiyar da kyakkyãwan aiki a kan mummuna; sai ta shãfe/guge ta -ita mummunar-, kuma ka yi mu'ãlama da mutãne da kyãwawan d'abi'u )).
Imãm At-tirmizy, kuma yace: "Hadisin Hasan ne".

Wato ana son bãwa ya yawaita kyãwawan ayyukan alheri, musamman ma ace ya yi wani aikin kuskure ko sã'bo, to, sai yayi sauri ya tuba kuma ya yi kyakyyãwan aiki.

Sai jin tsõron Allah a duk inda mutum yake, kuma inda tsõron Allah yake, shi ne zuciya; sai dai ayyukan fili suna nuna abin da mutum ya qudurce a zuciyar, dã wani zai ce shi yanã tsõron Allah, sai kuma aka ganshi yanã abin da ya sã'bãwa taqawar; to, qarya ya fad'a kenan !

Abin da ke sanya bãwa yin taqawa kuwa shi ne tsananin kulãwa da zuciya da hanã ta bin son zuciyar, sa'an nan a tilastã mata wajen tsantsar biyayya ga Allah da kuma Manzon tsira (SAW).

Ana son bãwa yayi kyakkyãwar mu'amala da 'yan uwansa 'yan Adam kai har ma dabbobi, shi Allah (SWT) yanã duba aiki mai kyau ne wanda zuciya ta tausaya yayin gudãnar da aikin, sannan duk wanda aka kyautatãwa su ne suke yiwa mutum adda'a musamman bayan komawa gidan gaskiya.

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 1:45 PM] Aysha Galadima: 20-25

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dr sageer da yakusan rabin awa azaune ya rasa me yakeyi masa dadi,tabbas wahalar da yasha acikin rayuwarsa bazata faduba shi a tunaninsa yasamu mata tagari wannan zaiji dadi da'ita Amma ina brstr ramlat ta yaudari shi da k'alaman ta Yana, cikin sanyi jiki yace ya Allah kaganar da Matata tabbas inason ramlat....

     " sallama tayi acikin office din tace kawata kinga nafito ko?

    " rabia ce tace yaya kukayi da mutumin naki??

     " Wallahi baiji dadi ba harda cewa bai bani izini ba...

    " Dallah kyaleshi ke kike tashi ai yanzu lokaci ne da account dinki zai kara nauyi fa?

   " kamar yaya??

     " Rabia ce tace ke komai bakya kawo wuta ina nufin lokacin da zaki tatse kudi agurinsa yazo ke hatta dariyar ke kice sai ya siya if not ki kuntata masa...

    " haba kawata mijin nawa?? " lahh kinjiki sai kace ba barister ba ai tahaka ake kwace miji ai abinci ma kice baki 'iya ba..

    " Hahaha rabia kina bala'in sona fa ina godiya kudin adinga yimiki transfer kema koba haka ba??

     " yauwa bestie kokefa bari mu tattauna akan wane case...

Mamee ce ta kalli abida da maryam tace shigen raina mutune da kukeyi kukalli dai gidan da dr sageer yagina yadda kikasan 'dan shugaban kasa...

   " maryam ce tace wallahi mamee har Allah yaisa sai danayi azuciyata da ban aureshi ba ashe yanada kudi sosai da sosai...

    " Alhaji haruna ne yace ai sageeru babu maijin cikinsa ba'asan me yake samu ba shiyasa Amma nasan ta yadda za'ayi zan rance kudin nasa sannan mucinye mu hanasa...

    " abida ce tace yauwa Alhaji gwara haka dan mu gaskiya bama jindadin da yakeji kwatakwata naga mama ma sai sababbin kaya take sawa inaji shi yabata...

    " Aikuwa zaizo yasameni inji mamee..

   Mama ke zaune ak'an tabarma ta kalli baffa tace ya cinikin naka kuwa???

    " Murmushi yayi yace Alhamdulillahi wallahi muna samun riba sossi da sosai mun hadu da wasu 'yan chana mun basu kaya munsamu riba mai tsoka sai dai Allah yasa musu akbarka...

    " Alhamdulilahu har naji dadi muna nan dai muna addua sai kaima kadage saboda makiya yanzu kuma zasuyi maka chaaa akai!

    " Ni bazan iya kare kaina ba Amma Allah yafiso ai duk abunda sukaga dama suyi nidai dogarona Allah kuma shi zai tsaremu mu dai kada Allah ya kawo ranar da zamu cuce wani...." Ameen yaa Allah baffa..

   " jiya naji makarantar su yasmin tace agaida ki sosai kuma takusa gama jarabawar saura guda biyu2...

     " To Allah yabada saa..  " Ameen

Yusra ce tace lallai yasmin soyayyar ku da uncle nafee'u karfi takeyi fa dubi yadda kika damu ak'ansa....

    Murmushi yasmin tayi tace duk da malamin irs dinmu ne wallahi addinin sa yana burgeni kinga tun lokacin da yace yana sona shikenan naji ya kwanta mini...

    " yasmin kenan ina guje miki fadawa tarkon da bazaki iya fita ba kicere soyayyar nan yanzu...

    " Tohm kawata zanceri inshaa Allahu bari naje na tambayi shi littafan mu koya gama dubawa kinga gobe exam din muke dashi ..

    " Yauwa tohm shikenan...

   " sallamar dayayi ita ta doki kunnan sa cikin murmushi yace yasmin?

    " Naam daman nazo naga ki kagama marking din books din ne?

     " Daman inason muyi magana dake ina fatan bazaki daukeni mai son zuciya ba??

    " kada idonta tayi cikin rashin fahimta tace kamar yaya uncle?

   " kindai san inasonki kuma ni ba dawasa nakeyi ba tabbas ina kaunarki inason kisani acikin zuciyar ki bangare mafi daraja please!!!..
  
    " Murmushi tayi tace Allah ya zabamana abunda yafi alheri...

    " Ameen tauraruwar taurari...

    " Murmushi tayi tare da jin wani zafin soyayya acikin zuciyarta tace ban san so ba Amma ina daf da kamuwa dashi sannan ta shiga class.

Dai dai shigowar ta cikin gate sai wayar ta tafara ringing bata dauka ba sai da takarasa cikin gidan nan ta tarar da dr sageer yana kallon film zama tayi kusa dashi tace darling am back ...

     " Kallonta yayi cike da kauna yace sannun ki yaya aikin??

    " wallahi lafiya am hungry akwai abunda zan danci???

   " Ga tea nan da burger sai kici...

     " Dauka tayi sai data gama ci sannan taje tayi wanka nan tasaka kayan bacci tayi sallah yana zaune k'an gado sannan taci darling yanaji kayi shiru???

    " Murmushi yayi yace nayi tunanin ke macece tagari da kowanne namiji yake bukatar yasamu? Duk kyan mace in bata bin umarnin mijin ba mace bace ba kinyi kirari cewa kina sona amma kuma bakyason abunda nakeso anya kuwa ke na kaunata??

     " Rungume sa tayi tace please darling dina kayi hakuri inagama case dinnan zan ajiye aikin domin ina mutukar son naga nasamu damar taimakon sa please ina gamawa shikenan zan ajiye...

    " Shiru yayi mata can yace mata babu komai Allah yataimaka....

   " yadda yayi magana yasa ta tabbatar yana sonta sosai da sosai cikin shaukin soyayya ta rungume sa nan tafara gigitasa daga nan kuma suka fada wata sabuwar duniyar...

Kai baffa kai baffa uban wani ne yabaki kudi ne naga har kasiya mota...

    " baffa ko kallan sa baiyi ba sannan yaja mota yafita..

  " Kai isa kanacan wannan makiyin namu sai kudi yakeyi musan abunyi???

   " bilal ne yace motar da yake hawa mu kanmu bamu da'ita bakuga yadda mutane suke bashi girma ba...

    " alhaji haruna ne yace zanyi bincike akan lamarin..

    Yana fita yaga abida tafito tana kuka tace baffa ina kwana?

    " lafiya lou ya karatun?

" ban biya kudin makaranta ba gashi saura 1days kuma last semester ce...

    " Baffa ne yace nawa ne kudin makarantar??

    " dubu 50 ne kuma Alhaji ya hanani!!

    " To munafika ke wannan mutumin kike sanarwa me zai baki kudin sata kokuma kudin yankan kai??

    " baffa ne yabata kudin yace gashinan Allah yataimaka abida...

     " Kuka tasaka tace tabbas nagani wallahi mutumin kirki daban yake tabbas kai mutum kirkine baffa har ka'iya biyamin kudin makaranta Amma lokacin da baka dashi babu wanda ya taimakawa yarinyar ka???

    " ba dan kowa nayi ba nayi dan Alkah ne sannan yashiga cikin gida yana zaune suna tattaunawa sukaji sallamar yasmin tare da akwatinta...

    " baffa kuna lafita??

" mama ce tace sannu da hanya yasmin Allah yasa kici jarabawar sai kuma jami'a...

    " baffa ne yace jami'ar lafiya sai dai aure miji yana fitowa zatayi aurenta...

   " ita dai dariya tayi tace Allah ubangiji yayimana zabi nagari..

    " Ameen auta..

Shekaru sai wakana sukeyi yasmin kullum cikin kuka domin baffa har yagaji tafara makaranta tunda babu maganar miji da sunzo sai aji shiru ga abida tayi aurenta sai maryam kadai ga barazar da kullum khalil yake mata na yana sonta yauma kamar kullum uncle nafeeu yazo tashirya kenan sai ta zauna k'an kujera...

    " mama ce tace wai yasmin ba baki kikayi ba??

    " kuka tasaka tace mama kullum ace saurayi in yazo bazai dawo ba mama basa sona ace yayan mahaifinka su dinga korar maka samari gashi har ina kokarin gama jami'a kullum zagin da akemin naki aure sai mai kudi...

     " Nima mahaifiyar ki sai danayi tunanin haka yasmin sai daga baya nagani akwai wani abun akasa yasmin karki damu jinkirin ki inshaa Allahu zai zama Alkhairi ki tashi kije bansanki da wulakanci ba kinji?

    " Tohm tace sannan tafita tanayin sallama yace yasmin lafiya bakida wayane???

    " eh wallahi banda ita baffa ne bai siyamin ba shiyasa...

    " A daidai lokacin dr sageer yayi parking yana fitowa yatsaya amsa waya...
 
     " yasmin daman nazo nasanar dake sai nadawo daga sudan za'a kawo kudin mu inason naje nakara karatu...

      " kallonsa kawai takeyi hawaye na bin fuskarta tabbas tasan zatayi rashin masoyi nai kaunarta mai sonta shikenan tasan kuma balallai ta auru ba tunda shi kadaine yane idan alhaji haruna ko isa sunyi mata sharri sai yace bakomai yana son abarsa...

     " Yasmin menene na kuka kinsan dai ina sonki kuma 5month kawai zanyi nadawo kima kafin lokacin kin karasa makarantar ki dan haka kada ki damu ina tare dake kinji?

     " idonta daya riga yayi jajir tace to Allah yabaka saa tayi shigewar ta tana karasa gate Alhaji isa yace k'arya mai bakin jini yauma yazo ya gudu kenan ke da aure sai dai kiga anayi , aguje ta takarasa gida tana shiga ta kifa kai sai kuka...

    " wai ciwo kikeso kisawa kanki ne so kike nima nakamu da ciwon?? Yasmin ina hakurin naki...

    " kuka takara fashewa dashi sannan tace mama kinji me baban bilal yace min wai bazantaba auruwa ba kullum sai ya zageni kullum kuma samarina basa zama, yanzuma uncle yatafi bansaniba ko shima guduwa zaiyi sannan takara saka kuka tace mama shi kadai nakeso inason uncle nafee'u tayaya zuciyata zata rabu dashi...

   " Dr sageer ne yayu sallama ya shigo amma basuji ba sai tsorata da yayi da irin kukan da yasmin takeyi...

    " mama ce tace to kibar kukan...

    " kukan takara fashewa dashi tare da fadin kibarni nayi ko naji dadi inason uncle nafee'u yaya zanyi yanzu mama??

    " mama ce kwallah suka cikomata idonta tare da barin gurin ta shiga daki...

    " Dr sageer ne ya tuna da irin rayuwar da yayi abaya sannan yazo yazauna akusa da yasmin hannunta ya riki yace haba kanwata me isa kike damun kanki haka???

    " bakinta ta cije tace dr so shakuwa su ba'a boyesu ina mutukar sonsa kamar yadda yake sona shi ya koyamin sonsa in yatafi yabarni yaya zanyi ina zan saka kaina???

     " Yasmin kenan bakisan akwai wanda yakeson ki ba fiye da kanki fiye da masoyanki??

     " shine uncle nafee'u yaya har yanzu bakasan zafin soyayya ba tunda kana tare da wacce kakeso dan haka ka kyaleni kada...sannan tasaka kuka mai cike da tausayi ta shiga dak'inta...

    " yanayin da yashiga yasa shi barin gidab gabadaya yana isa yaga ramlat bata dawo ba tana dawowa ya kifa mata mari ke wai bazakiji maganata ba to menene amfaninki ban isa na baki umarni ba kullum kina titi tunda nayi auren nan gaba daya na rame wai ahaka ina da mace meke damunki wai aikin ince sai da izinin miji???

    " in kagaji ka sakeni kokuma ka auro mai yimaka bauta dan ni bazanyi ba...

      " eh aure babu fashi wannan watan zan kainm kudi zan kawo wacce zan koya mata soyayyata...

     " tsaki tasaka sannan tace kakaro uku idan ka'isa...

 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login