Showing 27001 words to 28211 words out of 28211 words

Chapter 10 - GOLD DIGGERS HAUSA NOVELS COMPLETE BY PENDING AMARYA.txt

ga ƴan adawa ne da ita ta kowani fannin." ya kai maganar cikin damuwa.

"Ban gane ba, wani abun take aikatawa mara kyau, wallahi Nunu na da ƙoƙari, haka satar amsa aka ce tana yi." Murmushi ya ɗan yi sannan ya ce.

"Zuwa latti, ina zuwa." ya faɗa tana miƙe wa, yana kallon yadda yaga hankalinta ya kwanta, dan ba zai iya faɗa mata abubuwan da ya ji akanta wanda yanzu haka bincika zai yi yaji ainiyin maganar.............



Har ƙarfe 12pm na rana, Feaz da Reemah ba su fito ba ana ta aikata baɗala, har Nunu ta gaji da zaryan da take duba su, koma wa ta yi ɗakin in da taga Rapass ya tashi daga barci, murmushi ta sakar mai sannan ta ce.

"Ko dai ka na da sleeping sickness ne?."

"Hmmmm ai ni duk weekend haka nake ban da aiki sai barci."

"Ai naga alama ace tin ɗazu kana abu ɗaya." Murmushi ya yi yana mai ƙare mata kallo dan ta yi masifar kyau, sanye take da Pakistan dress mai launin, baƙi da shuɗi, kayan ba su matse ta ba amma a haka ta yi kyau sosai, ba ta makeup, lipstick kawai ga sha akan pink lips ɗin ta.

"Allah ba miki kyau Nunu." ya furta a hankali sai ta ce.

"Alhamdulillah na gode."

"Bara na shi haka."

"Da yafi maka." Miƙa wa ya yi sannan ya shiga restroom.




Haka dai suka shafe kwana biyu suna cikin gidan a kulle, su Reemah sai dai a huta a koma aiki, haka Feaz da Alhajin ta wanda ya ji ya kamu da ƙaunarta sosai, a ɓangaren su Nunu kuwa sun shaku da Rapass fiye da tinani, har ita ya fara ɗan burgeta. Yau Monday dan haka su Alhaji za su bar gidan.


Ji suke kaman kar su rabu da juna, haka dai Alhaji Bukar ya hau motarsa ƙiran Prado ya wuce, haka ita ma Feaz ta raka Alhaji Naira ya hau tasa mota ƙiran Audi. sai bayan sun jima da fita sannan Rapass shima ya fito cikin sauri ya hau ta sa Rolls-Royce black, mai shegen ɗaukan ido.................











★________________★




Tawa da ta ɗan buɗe ido, wani daga cikin mutanen ya zo dab da ita ya mata feshin jini a fuska wanda a take ta saki wata razananniyyar ƙara, ta saki hannun Saddiƙa wanda hakan yasa tayi tangal -tangal zata faɗi ɗaya daga cikin mutanen ya cafke hannunta itama Saddiƙa ta cafke ɗayan hannun, da Faridat ta ga Saddiƙa ba ta ita ta ke ba ta kama ɗayan hannun Saddiƙar.

Da ƙyar Saddiƙa ta ƙwato Tawa daga hannunsu sannan girgizar K'asar ta daina, ko wannensu ya buɗe ido wanda a take suka ƙara ganinsu a wani wuri da za'a iya kiransa da palace amma ba na sarakunan mutane ba sai dai na blood money.


skulls ɗin mutane ne jere reras kamar kwanukan samira, sai wasu daga saman throne ɗin da ke wurin, ga wani kan mutum da ke fidda jini wasu kuma zallar harshen mutane ne a ka rataya.

Wani nishi da kuma ihun azaba da suke ji shi ya sa suka kalli bayansu wanda a take suka ga mutum akan wuta da ke ci bal - bal ana gasa shi amma da sauran ransa (wa iya zubillah😭).



" Kowa ya durƙusa ba'a ganin zaman Egedege." Inji cewar Saddiƙa, tsugunnawa su ka yi da alamar daff ( wannan rawar da akayi yayi a baya).


Wani kalar iska da ke fita mara nutsuwa ke ta shi kamar guguwa take wannan guguwar, ta zauna akan throne ɗin wanda a take ya zama mutum.

Kayan jikinsa ado ne na ƙwayan idanun mutane.
Sarƙoƙin wuyansa na cike da ƙwarangwal ɗin mutane.
Awarwaron hannunsa na cike taff da haƙoran mutane.
Ƙugunsa sarƙa aka haɗa da zuciyoyi kala mabanta daga halittu mabanbanta.
Duk abin sai wanda ya gani.


Cikinsu Saddiƙa ce kawai ta ɗago tare da faɗin "Akabalé kî yá shà bà lé." ( Mai faɗa ya cika)."
Yau gashi na zo Egedege forest, na wuce garuruwa fiye da 9, sannan na wuce ƙalubalen shaiɗanun Egedege, na zo har Egedege wurin Egedege mai cike da arziƙi ta ko ina, ga ƙawayena na kawo maka suma za suyi abin da na yi.

Kallon kowaccensu ya yi tare da ƙafe idanunsa akan kyakkyawar cikinsu da ta sidda kanta jikinta na ƙyarma.

''Tawa!." ya kira sunanta da ƙarfi wanda ya sa dajin amsawa, fashewa ta yi da kukan da bata shirya mai ba ta ɗago kanta a hankali, kallo ɗaya ta masa ta ƙwalla ƙara tare da duƙunƙune Saddiƙa da ke gafenta da jajayen kaya.
''Nutsu.'' shi ne abin da Saddiƙa ta raɗa mata. Natsuwa ta aro da jarumta tare da kallon Egedege da ke kan karagar sarautarsa, cikin muryarsa mai bawa mutum tsoro ya ce ''Kinga wancan da aka rataya, gardama ya yi min shiyasa na rataya shi tare da babbaka sa, kin ga wannan kan da ke zubar da jini?." Dubanta ta kai ga kan da ke ɗigar jini sannan ya ƙara faɗin,''umarnina ya tsallake.''

Ajiyar zuciya Tawa ta sauke sannan ya ƙara faɗin ''Saddiƙa!." , kallonsu ta yi sannan ta ɗauko wani ƙwarya da ke cike da ruwa tare da wani ɗan ƙaramin pin a hannunta, ta kan Zainab ta fara tare da caka mata a hannunta jini ya fito, ta ɗiga a cikin ƙwaryar, ta bi kowaccan su sannan ta zo kan Tawa da ke ta zirarar hawaye aka ɗibi jininta tare da bawa saddiƙa ordern ta bawa kowaccen su ta sha a haka suka runtse idanunsu suka sha har da Saddiƙar.

Sannan kowa ya samu confidence zuciyarsu na barin gangar jikinsu, Tawa babu abin da ta ke faɗa a zuciyarta sai kiran sunan Allahn ta, wanda a take ta samu natsuwa.




Mauryarsa ce ta doki kunnansu '' Duk wadda ta san ba ta taɓa sanin ɗa namiji ba ta matso gaba.''

Tawa jikinta ya yi sanyi ita da ta ke Allah da Annabi ba budurci mai aka yi kenan?.

Nafisat da Faridat suka matsa gaba tare da yafuto Tawa da ke tsaye ta sidda kanta a ƙasa .

Kallonta suka tsaya yi baki sake sannan Egedege ya fara Magana '' Kee! Ya nuna Nafisat da wani sanda da ke hannunsa '' za ki kwanta da kare kuyi mu'amala irinta ma'aurata da shi sannan babu ƙyanƙyami babu san jiki, idan kika gama ki tabbatar ki binnesa tare da barbaɗa masa wannan maganin.'' ya faɗa tare da cilla mata maganin ta iska.

''And then you.'' ya nuna Faridat '' za ki kwanta da namiji tare da cire masa manhood ɗinsa (gabansa), ki dafa ki cinye sannan ki barbaɗa maganin da na baku, sannan in kun kwanta da namiji ko mace kar a baki kuɗi sai dai ku ku bada .'' ''ku koma baya na gama da ku.''

Su Tawa su ka matso gaba tare da siddar da kansu Madubin da ke wani ƙaton bishiya ya nuna da sandarsa take Maami da ke hospital da doctors ke ta ƙoƙarin ceto ranta ta gani, sai panic take kamar za ta mutu.
Juyowa ya yi ya dawo da kallonsa kan Tawa, yana wani kallonta sannan ya ce '' ita mu ke da buƙata........"





Anan zamu kawo ƙarshen free pages ku biya ku karanta namu ba kalar nasu bane ba 🤴💎🦋

9068269975 Opay Farida Aliyu Ibrahim
Shaidar biya via WhatsApp
0816 5842571



Ku biya ku samu sauran 😌

Mu bama haka 🌚🥴

GOLD DIGGERS 💎💦

(Ba jari 💰 sai uwar riba 💎).


Let's start the Journey ah paid pages.
Anan za muyi clashing 😊🫵

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login