Showing 21001 words to 24000 words out of 28211 words

Chapter 8 - GOLD DIGGERS HAUSA NOVELS COMPLETE BY PENDING AMARYA.txt

ba, babu wani alamun tsufa a tattare da shi amma kallo ɗaya zaka masa kasan kuɗi sun zauna ta ko ina.

"Welcome to my home."
" Dan Allah ka bar ni na koma gida please."
" Nooo."
Daga haka ya shiga cikin gidan, tsayawa ta yi ajikin motar tana tunanin a way out for her.
"Na zo na cicciɓe ki ne?." " A'a Uncle."
" Don't call me that again."
Sharɓe majinarta tayi haɗe da binsa a baya.
Sai da ya shiga banɗaki ya yi wanka, a lokacin ruwa mai mugun ƙarfi ya fara sauka, dan daman da akwai hadari a garin.

Wani murmushi ya yi mai kyau haɗe da faɗin " Weather for two wahala for one."

Ɗagowa da kanta tayi sannan ta sauke da sauri sakamakon towel ɗin dake jikin sa........




Is a paid book a hanzarta biya.
Free pages saura uku kuma bazamu ƙara ba.



9068269975.
Opay.
Faridat Aliyu Ibrahim
Shaidar biya via WhatsApp
0816 5842571
[9/29, 22:38] PRETTY SK NOVERLIST (PRETTYN JAJIRTATTU CE): https://whatsapp.com/channel/0029VbAoXYzId7nDgA2Tcr40💫💦GOLD DIGGERS💦💫
(BA JARI 💰SAI UWAR RIBA💎)

COLLABORATIVE EFFORT BY.....

PENDING AMARYA👰🏼‍♀

PRETTY SK🥰

AND.....

YOUNG WRITER ✍️

UNITED PENS 🖋️
THREE VOICES 🔊 IN ONE STORY 📘


💫💫💫💫💫💫💫


CHAPTER 8️⃣


*******Emm dakata habibu yi parking," wani alhaji dake bayan mota ya fada, ba wani shekaru ya tara ba kawai dai Allah ne ya bashi arziki da jajayen sawun sa dan irin su ne akewa take da yaro da kudi abokin tafiyar manya.

Parking habibu yayi tare da fitowa ya budewa alhaji kofar sai da yaja wasu mintuna kafin ya sauko yana gyara babbar rigar sa idonsa akan anayah dake Kuka tana gyara yagwalgwalallen gyalen data ke yafe da shi mai kama da abun tatar Koko.

Abbas na ganin sa ya bar inda yake ya karasa wurin da sassarfa yana fadin alhaji yunus yau Kai ne a gari kuma a layin mu gsky yau mun tashi da saa.

Kasaitaccen murmushi alhaji yunus yayi tare da fadin whl kuwa Malam ummmm......shuru yayi dan bai ma san sunan abbas din ba, karashe masa yayi da fadin Abbss alhaji Abbas nake.

"Yauwa Malam Abbas kana lpy sunan ne ya kwanta min."

"Lpy kalau alhamdulillah ya kokari ya fama da mutane."

"Alhamdulillah...." dan shuru yayi kafin yace "ahh meke faruwa ne na ganku tsaye a waje."

"Eh ah whl wata yar matsala ce anayah zo ki gaishe da alhaji yunus mana ko baki gane shi ba."

Cikin kokarin danne bacin ranta ta karaso tare da Dan risinawa ta gaishe shi cikin sakin fuska ya amsa yana binta da kallon kasan ido.

"Alhaji mu shiga daga ciki mana kasan unguwar tamu akwai yan sa ido yanzu sai a fara Kai kawo."

"Tho ba damuwa, habibu Ka jirani a nan yanzu zan fito." daga haka suka wuce ciki shi da Abbas anayah a bayan su.

Tabarma ta shimfida musu sannan ta koma daki ko zama batayi ba Abbas ya shiga kwala Mata Kira anayah anayah!

Fitowa tayi tana fadin gani.

" Haka akeyi anayah sai ki shiga ki zauna ki kawo masa ruwa mana."

"Ah ba komai Malam Abbas ba sai anyi wata wahala ba."

"Eh tho dake ma dai ban sani ba ko zaka iya shan ruwan namu dan ruwa ne na pampo."

"Karka wani damu ma bana jin kishin ne kawai ina yaran ko kuma dai har yanzu Allah bai kawo ba."

"Au su naem suna makaranta ai su biyu ne naem da zahrah."

"Allah sarki Allah ya raya, ni bari nazo na tafi dama sauri nake sai na hango Ku na dauka matsala ce k.........."

"Eh alhaji ai matsalar ce ma whl Ka ganta nan kullum cikin korafi take Abbas babu kaza, kaza ya kare waye² sai kace ni kadai ne me gida a unguwar nan."

Hannu yasa cikin aljihun sa da fadin ai dawainiyar gida haka take Malam Abbas haka duk muke fama whl ga wanna a rage hidimar gidan a Kara da hakuri."

Da sauri ya dafe wai dan Kar anayah taga adadin nawa ne yana fadin nagode alhaji Allah ya Kara girma in sha allah zanzo na maka Allah huta gajiya." ya fada yana miqewa ganin alhaji ya tashi.

"Karka damu duk lokacin da kake da wata matsala in dai ina gari kana iya zuwa."

"Nagode nagode Kai ni har bansan da wani bakin zanyi ma godia ba."

"Ahh karka damu ai yiwa Kai ne."

"A gaida su aunty afrah." Anayah ta fada.

Zasujiiiii in sha allah ya amsa yana sa kai waje tare tare da Abbas din.

Sai da yaga tashin motar su sannan ya koma ciki saurin tarar sa anayah tayi da fadin ina kujeru na? hannun ta ya riqo ya jata suka koma Kan tabarmar kallon ta yayi bayan sun zauna yace haba rabin ran Abbas kiyi min hakuri whl ba wani dalili yasa na sayar da kujerun nan ba face ina so na samu jarin da zamu riqe kan mu ke ma fa me bani ce in bani dashi ai duk taimakawa kai ne kuma nayi alqawarin canza Miki wasu sababbi da zarar na juya kudaden nan sun ribanya kimin hakuri kinji riqe wanna ya fada yana ware dubu goma ya Kara Mata ki ajje a hannunki yanzu zan fita na mana cefane me kike so na siyo zakara ko zabo?"

"Duk Wanda Ka gani ."

"Haba gimbiyar ki daina fushi mana kinsan in kina murmushi kinfi kyau ni naga jan bakin ki ma ya kare in na fita zan biya na siyo miki da barbada kumatu."

Yar dariya tayi yace tho ko ke fa tawan yanzu bari naje ko zamuje tare kafin su zaran su dawo.

"Ah ah kaje kawai ."

"Tho shikenan bari naje ya fada yana tashi ya fita.

Tun daga ranar Abbas ya samu aikin yi da an kwana biyu yaga aljihun sa yayi low zaije yayi sallama da alhaji yunus wanda zai tare shi da mutunci ya kuma jikashi da kudade masu nauyi amma dukda haka naira biyar baya nunawa anayah iyaka ya basu na abinci shi ma na maneji...........







*******


Washegari ko bayan sun farka, ba su da aiki sai shafe-shafen juna, duk cikin su Nunu ta ɗan fi dakewa dan a yau ko sau ɗaya ba tai ba, hannu ta sa ta ɗauki wayarta sannan ta kunna gidan Sim tare da kunna data sannan ta hau whatsApp, take saƙonni suka dinga shigowa kaman me, duk yawanci na group ɗin ƴan iskane, number da ke sama ta lasa dan dama shi take jira, 'Abba' shine sunan da ke saman number, tana shiga ta saki murmushi dan ya ga abin da ta tura mai, shedar kuɗin da ta siyar da mota ne, kimanin Naira Miliyan talatin, ta san dole zuciyar Abba ta buga. Ganin dogon voice ɗin da ya mata yasa ta latsa tana kai kunni dan saurara.

"Nusaiba! Nusaiba !!, Wallahi ki dawo min da mota ta, na baki kwana uku in ba haka ba zan sa ƴan sanda su ne moki, idan mota ta wani abu ya sameta to sai na miki matsiyacin duka, shashasha mara ɗa'a da tarbiyya, kin ci sa'a Amina ta gudu da akan ta zan fara fanshewa dan station zan miƙa ta, na kusa miki baki wallahi." dariya ta kashe dan yadda ya yi magana cikin ɓacin rai, sannan ta lura da ƙyar ma yakai aya. Abu ɗaya ne ya dawo mata kai Ummi.

"Nasan ka Abba, wato na dawo kasa a ka ma ni, nasan Ummi na cikin ƙoshin lafiya." ta faɗa tana miƙe wa ta shiga bedroom ɗin da suke, ganin Feaz da Reemah har lokacin suna jiki juna suna aikin na su ta ce.

"Wai ku bakwa gajiya, nan da 1h su Alhaji Bukar za su iso fa.?" ba ma ta jira amsar suma ta aje wayan sannan ta shiga wanka, bayan ta fito suma suka shiga a tare, wayar ta kuma ɗauka ya shiga massage dan ganin saƙo na 'Ya Musa nah' tana shiga taga ya rubuto.

'Nusaiba, ina kika shiga, sannan mai ya sami wayarki? Idan saƙona ya iso gareki ina son ki kirani.' take ta cire sin ɗin ta karya sannan ta sanya wani.

"Kar ka damu Ya Musa soon zan dawo gida da ƙatuwar mota har gida zan siya mana." Sai ta saki murmushi dan tina, jiya ta turamai 5M, shine yake so ya mata tambaya aka kuɗin.



Wow, kamar ba su ba, tsaye suke su ukun ko wacce ta sanya ɗaya daga cikin sababbin ɗin kunan da ta yi, Reemah wata atamfa ta sanya mai kyau wanda aka mata ɗinkin riga da skirt, ta hau ta sannan ta haska atamfar, haka ɗaurin ma ya hauta sosai. Feaz ita ma cikin wata shadda mai zuma ƙamari, doguwar riga ce irin ɗinkin da ake ya yi sannan ya ji uban aiki. Sai Nunu wanda ita ma atamfa ce mai golding, fitted gown ce wanda ya bi ko ina na jikinta ya yi mugun kyau, ta hau atamfar sai wani wal-wal suke, ba abin da ke tashi sai faman ƙamshin turarikan da sukai wasa da su. Agogo Reemah ta kalla wanda yake nuna 8:12pm na dare, ita ta fara gaba sai suma suka bi bayanta dan tin ɗazu suka iso.


Maza uke ne zaune kan sofa suna kallo a tv, take suka ji sallama Reemah cikin zazzaƙan mutunta, amsawa suka yi suna mai bin su da kallo. Kamar sun haɗa baki suka ce "Ma sha Allah." zama suka yi sannan suka kaisa, Reemah dai kusa da Alhaji Bukar ta zauna, Feaz ce ta ɗago dan satar kallon mazan da ke zaune, wanda duk ƙamshin da suke zubawa sai suka ji na su kaɗan ne.



Da Alhaji Bukar ta fara kallo dan shi dama ta sanshi sosai, ya na sanye cikin irin shigar da ya saba ta manyan kaya da babbar riga, shaddar sai shining take, sai na biyu wanda a kallo ɗaya da ji sa har ranta, mutum ne kamili, mai ɗan shekara kaman Alhaji Bukar, kana kallon sa kasan kuɗi sun zauna mai sosai, dan har haƙoran makkah biyu ne a bakin sa, sannan ga gazna da ke zuba musu ƙamshi ita wallahi ya mata. Sai na ƙarshen wanda matashi ne dan ba zai haura 30yrs ba, saurayi mai jini a jika, ƙananan kaya ya sanya amma sun haushi sosai, sannan ya fisu haske sosai, kana ganinsa kasan Fulani ne, ka hancin ɗan siriri mai kyau. Muryar Alhaji Bukar ne ya dawo da ita cikin natsuwar ta.

"To Alhamdulillah, Allah ya kawo min wannan lokacin da muka daɗe muna kiransa, tin lokacin da muka haɗu da ke Reemah a wannan group ɗin (Musha daɗi whatsApp group) na ji kin burge ni sosai, dan haka har na samu na ziyarce ki sau biyu, kuma na ji daɗin kasancewa da ke sosai, da haka abokinsa shima ya Umarci samun wata a cikin ƙawayen ku, gashi mun ganku yadda muke so dama." take na tsakiyan ya capke da ce wa.

"Tom ni dai sunana Alhaji Naira, nasan kun sanni dan ni ba ɓoyayyen mutum ba ne, akwai abubuwa da yawa wanda za kuga Company shine ya ƙera, a wannan gidan mun sha kawo ƴam mata amma sam ba su mana ba, duba da wasu ba su san mai ke damun su ba, amma daga gani za kuyi dan naya ba da hankalin ku, kunsan ance Kano ko da mai kaje an fika, to na yadda dan kunfi matan Kaduna waye wa, sannan a gaskiya kin kwanta min a rai." ya kai maganar yana kanne ma Feaz ido ɗaya. Sai Reemah ta ce.

"Insha Allah ba ku da matsa akan mu."

"Haka dama muke fata, ni dai sunana Alhaji Rapass mai dollars, shugaba hukumar sugo da komai cikin ƙasar nan, idan babu sign ɗin na to ko hukumar nafdac ba ta danna stam, a gaskiya ko sati banyi da shiga wannan group ɗin ba, sai Allah ya haɗani Alhaji Bukar, su ne sukamin tallan ku sai na umarci a kawoku wannan gidan nawa, idan zaku riƙe mana sirri shike nan, duk weekend za ku dinga zuwa sannan ku wuce Monday, in dai kuɗi ne kunzo gidan." Ya kai maganar ya na satar kallon Nunu wacce ko ɗagowa ba tai ba.

"Ba ku da matsala guys." Feaz ta faɗa suna kallon juna da Alhaji Naira.

"Ni kam wata Madam ɗin ba ta magana ne, ko ita ma sabon shiga ce." ya faɗa yana murmushi sai Feaz ta ce.

"Aikam amma in ta jima da kai za ta sakema jiki." Sai a lokacin Nunu ta ɗago ta kallesu, murmushi Alhaji Rapass ya mata sai ta mai da mai sannan ta ce.

"Ku gafarcen zazzaɓi ne ke damuna."

"Subuhanallah, sannu gaskiya ta shi muje asibiti." ba musu ta miƙe dan jikin ta ya ɗau zafi, su kuma sauran kowa ya tsaɓa ɗaki ɗaya dan aikata abin da ya kawo su........






********




Wani murmushi ya yi mai kyau haɗe da faɗin " Weather for two wahala for one."

Ɗagowa da kanta tayi sannan ta sauke da sauri sakamakon towel ɗin dake jikin sa.

Hamma ya fara yi sannan ya samu ya sanya kayan bacci ya kulle ƙofar ya kwanta.
Sai da ta bari baccin yayi nisa, sannan ta tashi a hankali ta ɗauki key ɗin a hankali.

Kama hannunta yayi tare da faɗin "am not sleeping, you want to sneak out right?."
" No am starving."
" Kin san kitchen ɗin ne?."
"Please let me go, mahaifiyyata tana asibiti dan Allah."
" Ga fili ga mai doki, ai mukulli na hannun ki, darajar ki ɗaya am not in the mood." Daga haka ya gyara kwanciyar sa.

Ajiyar zuciya ta sauke, duk da ruwan da ake bai hanata barin gidan ba, tana tafiya tana waigensa.


Ta na fitowa gate man ya buɗe mata ƙofar, ta fita da gudu.
Ta na cikin gudun wasu karnuka suka biyo ta ga ruwa anayi mai mugun ƙarfi, ga layin na masu kuɗi ne sosai, babu alamun abun hawa.
Gudu take bana wasa ba.
A hankali ta fito bakin titin unguwar, da ƙyar ta samu napep dan ƙarfe 12 saura.

A take wani zazzaɓi mai mugun ƙarfi ya rufe ta, ko da ta isa gidan har an kulle ƙofar a hankali ta ƙwanƙwasa aka buɗe mata ƙofar.
Ɗakinsu ta shige tare da kullo ƙofar.
Cire jiƙaƙƙun kayan tayi tare da saka wasu, ta haɗiyi Panadol.
Sai da tayi kwana uku zazzaɓi na ɗawainiyya da ita sannan ta ɗan warware.
Bayan ta warware, ta shirya tsaff domin zuwa ziyartan Mami.

Bayan taje ma doctor request ɗin wani x-ray da za'a yi wa Maami yayi mai mugun tsada.

Babu wani wurin da take tunanin zata samu kuɗi face wurin Saddiƙa she has no choice than to went to her again.
" Ya rabbi am dying, mutuwa nake a hankali, zanje ba dan son raina ba Allah karka kama ni da laifin hakan, please ya rabbi.'' ta ƙarashe maganar tana goge hawayenta da bayan hannunta.


Tana gama yanke hukuncin hakan ta ƙara goge hawayenta tare da barin hospital ɗin ta kama hanyar zuwa gidan su Faridat.

Ko da ta shigo cikin gidan kowa ya baje Maman Farida ta tafi ƙosai, sai su kaɗai a gidan.
Jiki a sanyaye ta shigo cikin ɗakin tare da kallon Zainab da jin muryarta ya sa ta kauda kai ƙwalla na ƙara ziraro mata.
Tawa bata kula ta ba ta nufi wurin Saddiƙar tare da faɗin



'' we go fit go now I don dey ready.''

Dariya suka yi tare da faɗin ''iskanci ne daman tun da can.''



''Gobe da sassafe za mu ta fi sai kowa ya shirya in ta yuyu mu kwana a wuri ɗaya yadda zai yi sauƙi wurin shirin.''
Na'am su kayi da zancan Saddiƙa sannan suka kama hanyar zuwa gidan nata, ba kuma tare da sun faɗawa iyayen su ba .

Da yamma Saddiƙa ta sa Tawa ta shirya ta kaita hospital ɗin, ta ga har yanzu Maami ba ta tashi ba, sai da ta rungumeta ta sha kuka, sannan suka dawo gidan Saddiƙa suka fara shiri.

Da sassafe suka bi tashar jirgin ƙasa suka wuce Enugu, ba su sauka washegari ba sai da suka kwana a hanya sannan suka fara ƙeta hanya suka fara shiga dajin, da ake kira da _Egedege forest_ forest ɗin da ba'a shiga a fito da rai dole sai wanda ya san kan dajin.

Ko 'wa sai da ya sha jinin jikinsa ban da Saddiƙa da ke magana ta na faɗin "kamar yadda na yi wa Egedege alƙawarin dawowa da mutane har guda huɗu ga ni yau na dawo dasu alƙawarin linkamin arziƙina sai acika min su." Tana gama faɗan haka ta yanka babban yatsanta na hagu tare da barin jinin ya ɗiga a ƙasan ciyayi.



Wani kalar hayaƙi ne ya turnuƙe wurin wanda su da suke wurin, suka daina ganin Saddiƙa, wani duhu ne ya ƙara mamaye wurin da suke su da rana ne amma duhu ne bana wasa ba.
Gaba ɗayansu ƙanƙame jikinsu suka yi a wuri ɗaya suna ihu, barimma Tawa da jikinta ke mugun ƙyarma, wani kalar ihu suka ji da ya amsa wurin da suke ba ki ɗaya wanda hakan ya ƙara firgita su.

Ta ke kuma wurin ya washe ya dawo rana, Saddiƙa kuma kayanta su ka dawo jajaye mai hula.
Ta yi musu murmushi, tare da riƙe hannunsu, ta ke su ka ɓace daga wurin, wani ƙaton rafi ne da ke fitar da Walƙiya adaidai wurin suka bayyana, sakin hannunsu ta yi tare da shigewa cikin rafin da ke ɗauke da tiriri.

Ta ke wani kalar hadari ya taso ko ina ya ƙara zama baƙi, istigfari kawai Tawa ke yi a cikin zuciyarta.....


Paid book ne a hanzarta biya
9068269975
Opay Farida Aliyu Ibrahim
Shaidar biya via WhatsApp
0816 5842571
[9/29, 22:38] PRETTY SK NOVERLIST (PRETTYN JAJIRTATTU CE): 💫💦GOLD DIGGERS💦💫
(BA JARI 💰SAI UWAR RIBA💎)

COLLABORATIVE EFFORT BY.....

PENDING AMARYA👰🏼‍♀

PRETTY SK🥰

AND.....

YOUNG WRITER ✍️

UNITED PENS 🖋️
THREE VOICES 🔊 IN ONE STORY 📘

💫💫💫💫💫💫💫


CHAPTER 9️⃣


********Da sallama ta shiga, jin shuru ya sata kwala sallama sosai alhaji yunus ne ya sauko da waya a kunne idonsa ya sauka Kan anayah da sauri yace zan Kira Ka ina zuwa kafin yayi magana mero ta fito tana amsawa da waalaikis ina wuni Anayah ta fada ba tare data lura da alhaji yunus ba .

"Ina wuni anayah ya gida."

Alhamdulillah ta fada tana karasawa ta zauna, su aunty afrah fa?

"Basa nan whl."

"Basa nan kuma? Sunyi nisa ne?"

Kafin mero ta bata amsa alhaji yunus ya amsa da ba dadewa zasuyi ba ai mero kije sashena ki gyara yanzu kafin su dawo.

Tho Alhaji ta amsa tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login