Showing 15001 words to 18000 words out of 28211 words

Chapter 6 - GOLD DIGGERS HAUSA NOVELS COMPLETE BY PENDING AMARYA.txt

ka je kasuwar ba ta wani abu cikin kazar _ kazar, rayuwarta kawai ta ke a sanyaye har suka siyar su ka dawo gida.

Yau da bata ga Ahmad a kasuwa ba ta shiga damuwa sosai, ga pressure ɗin Mama Rabi da tazo bayan dawowarsu ta nace sai sunyi waya da ɗanta a what's app. Yaron ma wani iri alamar yana bleaching duk bai kwanta mata ba.

Zuciyarta na maƙale da Ahmad har goman dare ta gota bata ga kiransa ba, shahada kawai ta yi tare da dialing, wannan matar ta MTN ta sanar mata ba ta da kati.

Tsaki ta ja akaro na ba adadi.
Sannan ta kunna call record ɗinsu ta na saurara har bacci ya kwashe ta.

Da sassafe ma haka ta tashi ta gama komai because kuɗin hayansu ya kusa ƙarewa she gats to hustle sosai, a gaggawce ta yi komai dan yau Maami na hutu bazata samu daman zuwa ba dan batason mahaifiyyarta ta wahala, bayan ta gama ta fita ta kira mai napep ya ɗauke ta ya kai ta har kasuwar, yau ma shagonsa a rufe ya wuni ba'a buɗe ba abin har ya fara sa ta a damuwa.

Har yau dai akai sati biyu Ahmad bai buɗe shago ba babu wani labari kuma a kansa, ta san inma kaya zai sara ya kan je Ghana bai fi yayi kwana biyu ba ya ke dawowa ana ukun.




Hankalinta ba ya jikinta ga biyan kudin haya ga damuwar Ahmad ga neman admission , ta ma rasa ya zata yi.

Sunday afternoon

Zaune ta ke kan bench ta na wanki earpiece na kunnenta ta na jin waƙar _Play boy _ na wannan mawaƙin fireboy.

Wayarta ta ɗauki ringing ko da ta kai dubanta kan wayar number Maami ya fito _My Hope _ .

Bayan ta ɗaga wayar wata muryar da ba ta taɓa jin irinta ba.

Murya Kamar saukar aradu, cikin muryarsa ya ce "Mai wayar nan ta yi collapse yanzu bata cikin hayyacinta."


Daga ita daman sai underwear da vest, hannunta kawai ta ɗauraye tare da ɗaukan hijab mai ɗan faɗi da tsayi sannan ta zura slippers.


Tunda ta fara falfala gudu ba ta tsaya ba sai data zo shagon da babanta ke kwana da guy ɗin ya faɗa mata.

Mutane sai kallonta suke bata wani damu ba ta hankaɗe ƙofar shagon, wanda cousin sister ɗinta ke ciki ƙanwar Nafisat tana durƙushe a wurin sai kuka take yi.


Bata damu da ganin Babanta da ke ta smoking ɗinsa ba ta fara kiciniyar ɗaga mahaifiyyarta daga kan ƙasan ledar shagon wanda babu wani alamun numfashi a tattare da ita.


Sai da ta samu taimakon matan da ke unguwar da ta ke ɗan mutumci da su sannan aka taimaka mata suka kaita Waraka Clinic dake bakin titin unguwar na su.

Bayan sun je ma cewa sukayi su ba su da gado Tawa na kuka haka suka ƙara ɗaukan Maami zuwa Clinic ɗin Hamdala da ke gaba da Waraka.


Ƙarin ruwa su ka fara sa ka mata sannan suka ce zata farfaɗo nan da ƴan awanni.


Ita kanta ta shiga tunanin mai Zainab ƙanwar Nafisat ke yi a shagon kwanar Baa, meke sa ta kuka kuma, menene dalilin sumar da Maami ta yi.

Yanzu ita ta ina ma zata fara neman kuɗin treatment har dubu hamsin?, anya ba cika mata kuɗi aka yi ba?? .


Kuka ne ya kuɓce mata ta shiga rairaiwa ta na tuna yau da safen da Maami za ta fita.


Ashe tana ajiye kuɗin haya ta tara har fifty thousand, shine dillali ya zo amsa ta duba wurin ajiyarta ba ta gani ba kuma tasan babu wanda zai ɗauka sai Baa.


Shiyasa ta je har wurin da yake domin tuhumarsa akan kuɗinta.

Ƙara runtse ido ta yi tana faɗin "Duniyata mai sa kike min haka?? Ƙaddarata mai na miki haka??. Ga Ahmad ga Maami ga abubuwa duk sun min yawa a ɗanyan shekaruna?." Wata Doctor ce ta ce "ba kuka za ki yi ba, ki tuntuɓi relatives ɗinki a kawo kuɗi ayi mata abin da ya dace shi ne kawai mafita". "Thanks Maa." Tawa na faɗan hakan ta sa ƙafa ta fita daga Clinic ɗin ta yo gida.

Wanka ta yi sannan ta ɗauki ɗari biyar a kuɗin kayan miya ta wuce ƙofar ruwa gidan Saddiƙa domin ta taimaka mata amma unfortunately Saddiƙa ba ta nan.

Wayarta ta ɗauka ta kira ta is not reachable, a ranar talauci sai da ya sha tsinuwa a wurin Tawa ba adadi.


Wayar ta ƙara ɗauka ta yi dailing numbersa a hankali ta fara ring, picking akayi tare da sallama amsa sallamar ta yi sannan ta sakar masa kuka, hankalinsa a tashe sukai magana ta sanar da shi in da zasu haɗu.

A cikin minti ƙalilan ya ƙaraso wurin da ta ke tsaye cikin shigarta na jeens trouser da hijab iya gwiwa.
Farar fuskarta ta yi jaa alamar ta sha kuka sosai.

A hankali ya yi parking motar sa a gabanta ta buɗe ta shiga ta ƙara sakar masa kuka.

Bai tayar da motar ba ya ɗago haɓarta tare da kallon fuskarta ya ce " she will be fine okay?."
" Buh ya Ahmad kamar ta mutu faa ba ta motsi am scared of losing her, am really scared.'' ta ƙara fashewa da kuka.


Ajiyar zuciya mai zafi ya furzar sannan ya tayar da motar suka nufi bachirawa.
Wani go slow mai ƙarfi suka tarar a kurna wan da ya sa ba su ƙarasa ba sai bayan isha.


Asibitin har sun fara tashi. Maami kuma a waje suka ajiyeta dan babu kuɗin da Tawalkaltu ta kawo bare su ɗan fara abin da za su iya.


Ko da suka ƙaraso Tawa kamar za ta yi kuka.

Sai da ya bawa doctors ɗin kuɗi sannan suka saka masa ita a ambulance suka nufi hajji camp da ita Khadijah memorial hospital.


Taimakon gaggawa aka bata sannan sukai mata abubuwa da dama, sai asuba dai ta fara buɗe ido a hankali.

Ahmad na zaune a ɗakin sai Tawa da ke kusa da shi amma ba sosai ba.
Tawa!! Tawa!!, a ruɗe ta ƙaraso wurinta ta kara kunnenta a bakinta.

Magana ta ke mata a hankali cikin yaren Igala.

" Tawa ki kula da kanki kar ki bari wani Namiji ya ruɗeki bansan ko zan kai wayewar gari ba amma ina umartarki da ki kula da budurcinki karki bari daɗin bakin ɗa namiji ya ruɗeki haƙika naga mahaifin ki da ɗan yayansa Zainab a cikin yanayi da ba zan iya faɗa ba amma nasan za ki iya fahimta...........

9068269975
Account number opay
Farida Aliyu Ibrahim
0816 584 2571
Shaidar biya via WhatsApp
[9/29, 22:38] PRETTY SK NOVERLIST (PRETTYN JAJIRTATTU CE): 💫💦GOLD DIGGERS💦💫
(BA JARI 💰SAI UWAR RIBA💎)

COLLABORATIVE EFFORT BY.....

PENDING AMARYA👰🏼‍♀

PRETTY SK🥰

AND.....

YOUNG WRITER ✍️

UNITED PENS 🖋️
THREE VOICES 🔊 IN ONE STORY 📘

💫💫💫💫💫💫💫


CHAPTER 6️⃣


Kamar yadda ya saba yau ma haka ya shigo Yana yan wake waken sa tashi tayi da fadin Abbas gsky abinda kake min cikin gidan nan ya fara isa Kai baka mana ba kuma mun samu Ka kwace wanna adalci ne cin mu da shan mu fa duk a kanka yake amma Ka kasa sauke nauyin dake kanka munyi hakuri kuma muna kama kama nan ma kabi Ka hana, ba dan ba dan ba ni da sai nace kana da bakar zuciya Abbas."

"Ehh lalle anayah bakin ki yayi kauri tho ai duk bakar zuciyar tawa ban Kai iyayen ki ba da suka san halin da kike ciki amma suka gaza taimakon ki."

Cikin mamaki tace Abbas iyayen nawa ? Yau iyaye na ne suka zama abun zagi wurin Ka."

"Tho karya nayi ai gskyne dole a fada."

"Ina so Ka sani a karkashin Ka nake baa karkashin su ba kuma lokacin da ina karkashin su ai ban rasa komai ba har Ka ganni na birgeka kaji kana so."

"In suna son ki ai zasu so abinda kike so har su taimaka miki yadda kike so na din nan kamata yayi ace da mukayi aure sun bani gida da mota tare da wani dan jarin miliyan biyar amma basu yi haka ba suka barki nan kina cin bakar wuya su sunacan cikin raba suna yawo Kan hazo ya karashe yana Kadai bakin rigarsa yayi shigewar sa ba tare daya Kara kallon ta ba, binshi tayi tana fadin whl sai dai kazo Ka san yadda zakayi dani dan bamuci komai ba yaran nan ma dakyar na samo musu bashin gari ko isarsu baiyi ba."

"Tho ni ce miki akayi naci wani abun ne kuma ma bana barmiki tsaki ba da rana ya akayi dashi."

"Kaji tsoron allah Abbas."

"Ikon allah tho da tsoron ki zanji uwata, kinga anayah a rayuwar nan yanzu kowa maleji yake duk gidan da kika ga ana zaune lpy gurgurawa ake ayi amfani da abinda aka samu kiyi hakuri tunda yanzu dare yayi da safe in sha allah zanje na samo Miki wani abu yanzu zo ki zauna muyi magana ya fada Yana zama tare da zuba mata yaudararrun idanun sa yana kallon ta tare da tuno tattaunawar sa da abokin sa inda yake ce masa mahaifin anayah ya samu Karin girma."

Ajiyar zuciya ta sauke tare da karasowa ta zauna riqo hannun ta yayi tare da tausa murya ya Kira sunan ta, "anayah daddy ya samu Karin girma ya kamata ace munje mun masa murna."

"Daddy wani Daddyn kenan?"

"Daddyn Ku mana."

"Amma dai Abbas ina fatan baka manta da dokar Daddyn a Kan mu ko."

"jiya fa ba yau ba anayah yaci ace zuwa yanzu zuciyar daddy tayi sanyi a Kan mu, kawai abinda nake so ki shirya gobe da safe muje kafin ya fita."

Dan shuru tayi tana tunano furucin mahaifin ta a gareta kafin tace a gsky Abbas bazan iya zuwa ba, ba kuma dan bana son na gansu ba sai dan ina tsoron abinda zaije ya zo amma in har Kai kaga zaka iya zuwa kaje din."

Tsaki yayi kafin yace saiki ta zama da fushin mahaifa ni dai da safe zani yauwa." Ya karashe yana miqewa ya kwanta Kan katifar.

Da sassafe kamar yadda ya fada yaje ya samo musu kunu da kosai cikin wasa da dariya suka zauna suka ci kamar ba komai sannan ya shirya yasa yaran a gaba dan kaisu makaranta da kansa kallon anayah yayi da fadin tho mu zamu wuce a sa mu a addu'a."

"Allah ya tsare ya dawo daku lpy ya kuma baka saa...."

"Yauwa tho kin gani wato ita wanna saar ita nake nema ido rufe ina gamo da ita tho kun warke kema zaki shiga sawun manyan mata wanna manyan motocin duk shekara sai an canza muku kije Madina garin manzo kema."

Murmushi tayi kawai Shi kuma ya kama hannun yara suka fita suna mata bye bye.

A yadda Abbas ya fita ba haka ya dawo ba da sauri anayah ta tashi daga bakin kofar dakin da take zaune tana tsifa ganin yadda ya shigo yana fada ga jikinsa jage jage da kwata ya sata tambayar Abbas me ya faru?

"Dole zaki tambaye ni meya faru mana munafuka masu kudin lukudi ni zaayiwa wulakanci a garin nan ni ni ni Abbas har nayi lalacewa da wani zai kame daga sama yayi umarnin a hadani da karnuka......."


Paid book ne
9069269975
Farida Aliyu Ibrahim Opay
Shaidar biya via Whatsapp 0816 5842571

*********


Ba komai ne take tunawa ba sai rayuwar baya, ƙara kallon Abba ta yi wanda yake sauke ajiyar zuciya a hankali, kulle idanuwanta ta yi take abin da ya faru shekara 14 baya ya haska a cikin kanta.................

*Flash back*

Tin tana cikin napep ta hangesa, a kallo ɗaya ta ji ya shiga cikin ranta, kuma ta ya ba da shi dama haka take fatan samun wanda a kallo ɗaya za ta ji ya mata. Bama a kai in da za ta sauka ba, ta umarci a sauke ta. fitowa daga napep ɗin bayan ta biyasa kuɗinaa sannan ta nufi in da yake tsaye, sanye yake cikin ƙananan kaya masu kyau, shigan ya mai kyau sosai, kuma ga dukkan alamu motarsa ce ya fito a ciki dan yana jingine a jikinta.

"Assalamu alaikum." ta faɗa tana isa in da yake, kallon ta ya yi sannan ya saki fuska ya amsa gaisuwan.

"Dama tambaya zan ɗan yi dan Allah."

"To Allah yasa na sani." ya faɗa yana gyara tsayuwar sa.

"Uhmmm shagon lalle na ke nema, da yake ba'a nan nake ba ne, kuma na duba ban gani ba, kai kaɗai na hangi za kai mutumci shine na zo na tambaya." ɗan dariya sannan ya ce.

"Allah sarki, na gode da yabon, nima kam baƙone a nan amma hau mota na rage miki hanya ko Allah zai sa mu dace." ba musu ta hau, sai bayan da ya amsa saƙon da yake jira sannan suka bar gurin.



Time to time take ɗan satar kallonsa ta gefan ido, ɗan hira suke ɗan yi kafin Allah ya kaisu wani shagon lalle, a bakin gurin ya tsaya.

"To Allah ya kawo mu, zan iya sanin sunanki?."

"Yana da tsada gaskiya." ta faɗa ta na mai fatan su tsawaita suratu har su yi exchanging number.

"Uhmmm ai abu mai tsada daga gani ake ganesa, a kallo ɗaya na san ke mai tsada ce, faɗa min farashin sa." Ɗan fari ta yi sannan ta ce.

"Kodan mutumcin ka, na baka kyauta, sunana Aisha."

"Ma sha Allah Humairah, suna mai daraja da daɗi, suna wacce ta za ma mafi soyuwa a zuciyar manzan Allah (S.A.W).”

“Na gode.”

“Ahhh ba wani godiya sunan ya kai ya yi tsada ai.”

"Tom sai anjima." ta buɗe motar ta, shima buɗe wa ya yi, har ciki ya rakata sannan ya biya kuɗin lallen, godiya ta mai sosai sannan ta ce.

"A gaskiya na daɗe banga mutum na gari ba sai yau, ina godiya sosai, ɗan ban numberka dan na dinga kiranka muna gaisawa."

“Har ga Allah kin sani farin ciki, kinsan akwai daɗi ya ba mutum, amma dan Allah na miki, ina matukar daraja mata a rayuwara." ba musu ya ba ta sannan ya wuce.


Tinda wannan lokacin ta kulla aniyar aurensa koma ta ya ya ne, suna waya dan tana yawan kiransa tin ba ya ɗauka har yake ɗauka, bayan ta fahimci yana mata wacce yake mutuwar so da yara biyu, a ranan da ba ta iya barci ba, haka ta kwana, aikam washegari ta nufi gun wani boka, shi ya mata aiki har ya fara sonta kaman ransa, dan kusan ɗan hauka ya yi, balle in ba su yi waya ba, ba a ɗau lokaci ba a ka yi auransu, har lokacin ta lura yana son kishiyarta fiye da komai nasa, komawa gun boka tai aka cire mai soyayya Amina da yaransa Musa - Nusaiba. ta lura ya na da tattali da ba kuɗi daraja, dan haka nan ma aka mata aiki a kansa da haka ta take jan kuɗaɗe a wakanda sannan take juyasa kamar waina.


*Continuation*

Miƙe wa ta yi sannan ta isa gabansa, kallon fuskarsa ta yi, tana son sa, amma ta fi son kuɗin sa. Tina abin da ya faɗa ta yi. 'Nusaiba' sai ta kuma sakin wani murmushi dan tinawa da ita ta sa aka tusa ma Nusaiba tsanar Abba, kamar yadda shima baya son su a ganinsu. Sumbatar goshin sa ta yi.

“Nasan ina sonka Abba, amma bayan wannan son akwai son kuɗin ka, a gaskiya ina son kuɗin ka.” ta faɗa tana miƙa wa sannan ta nufi waje dan dubo doctor............
******
Not edited


" Tawa ki kula da kanki kar ki bari wani Namiji ya ruɗeki ban san ko zan kai wayewar gari ba amma ina umartarki da ki kula da budurcinki karki bari daɗin bakin ɗa namiji ya ruɗeki haƙika naga mahaifin ki da ɗan yayansa Zainab a cikin yanayi da ba zan iya faɗa ba amma nasan kin fahimta......

Karki ci haram karki ci amana idan an baki.

Ki nisanci kanki da faɗawa halaka, wannan jin waƙar naki ki ragesa.

Sannan zamanki da mahaifinki da zan barki a yanzu saboda hali na jinya ki tabbatar kin kare kanki daga shaiɗancinsa tun da har ya iya kusantar ɗan yayansa toh na ki ma ba zai ƙyale ba amma ki bi ta kan Zainab kiji ya akayi hakan ta kasance dan na san yarinya ce ƙarama kuma ta fiku nutsuwa da tunani, kira min Ahmad."

Ko da ya ƙaraso wurin zama ya yi kusa da ita.

Sannan ta ce "Ahmad na gode sosai Allah ya barka da abin da ya fi maka alheri a rayuwa, Nagode sosai da ɗawainiyya, dan Allah ina neman alfarma ɗaya a wurin ka."
Kallonta kawai yayi alamar yana ji sannan ta ƙara faɗin " ka kula min da Tawa tamkar ƙanwarka." "Maa daman ita ƙanwata ce babu wani abu kuma a tsakanin mu."

Tari tafara sosai da gudu Tawa taje ta kira Doctor kafin ta dawo har ya mayar mata da oxygen ɗin da aka sa mata.

Bayan Doctor ya zo ya ƙara dubata sannan ya ce ta na lafiya ta dai koma suman da ta farfaɗo ne amma ai abin ya zo da sauƙi.


Gida Ahmad ya mai data suna cikin motar Mahaifiyyarsa ta kira shi.
Bayan yayi sallama, ta amsa mai tare da faɗin "Ahmad ka na ina??." " Ina wajensu Adam za muje gaida Mamansa." " You're lying Ahmad, idan ma kana wurin wannan mayyar yarinyar da na rabaka da ita ka dawo yanzu ina nemanka , ko kallonta ka ƙarayi da niyyar ka taimaketa, toh wallahi sai dai ka biya ni nonona da ka sha ba zan yafe ba."


Bata jira cewar sa ba ta kashe wayar, kallon fuskar Tawa da ke zubar da ƙwalla ya yi saboda shi bai iya waya babu handsfree ba.
Kuma ya tabbatar babu munafukin da zai gaya wa Ummi sai Doctor ɗinsu tun da Hospital ɗin suke komai.


Cikin sanyin muryarta ta ce "Ya Ahmad kar ka bijirewa mahaifiyyar ka, nagode maka sosai in da rai da rabo Ya Ahmad naaaa." Ta ja na ɗin tare da rufe baki ta na fashewa da kuka.

Tare da fita daga cikin motar da gudu ta shige gidan nasu.

Sai da ta ɓacewa ganinsa sannan ya tayar da motar ya bar unguwar zuciyarsa na ƙuna.


Koda ta shiga gidan sallah ta yi tare da kwanciya bacci mai nauyi ya ɗauketa.
Bayan ta tashi ma wanka ta yi tare da shiryawa ta bi number Saddiƙa da ta mata miss call.


Ring biyu Saddiƙa ta ɗaga tare da faɗin " wassup.'' ''wallahi i dey fine.'' '' ya kike, ya Maami?.'' ''Saddiƙa I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login