Showing 1 words to 3000 words out of 36194 words
Chapter 1 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx
1- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_ The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
________________________________
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
___________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
03/04/2025
*ANYI SALLAH LAFIYA? ALLAH UBANGIJI YA MAIMAITA MANA DA RAI DA LAFIYA, AMEEN YA RABB*
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*P.1*
*FARKON LABARI*
“ Meerah wai sai yaushe za ki fito ne? Kin san rana yana yi fa, kar muje ya hana mu shiga.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ta faɗa tana duba wayan hannunta.
Yarinyar da aka kira da Meerah ɗin ce ta fito, sanye take cikin hijab blue me ratsin fari a jiki, matashiyar da ba za ta wuce a kalla shekara sha takwas ba a duniya, dogon fuska ce da ita wanda ya ɗauki manyan idanunta masu ɗauke da zarazarar gashi, hancinta ba dogo ba kuma ba gajere ba, sai ƙaramin bakinta da ya ke pink, tana da tsayi dai-dai misali, sai dai kuma bata da jiki irin slim din nan ce, kallo daya zaka mata da wacce ta yi magana ka gane cewa su ƴan biyu ne. Amma sai dai daya fara daya kuma chocolate colour.
Isowa gurin da take ta yi tana ɓata fuska, kamar wacce bata son magana ta buɗe baki a hankali tana cewa. “ Meemah gani fa.”
“ To ai kinsan halin mutumin yanzu sai ya ce baza mu samu ganin shi ba.” Meemah ta yi maganar tana fita daga gidan sun.
Biyo bayan ta Meerah ta yi tana jan ƙofar gidan ta rufe da lock, ta jefa key din a jaka.
Tafiya suke Meemah tana ta zuba, har suka iso bakin titi Meerah bata kula ta ba, ganin bata da niyar yin magana ne ya sa itama jan bakinta.
Mai adaidaita sahu suka tara suka masa ƙwatancen inda za su je, nan suka shiga ya ja suka tafi.
A dai-dai bakin kamfanin ya yi parking tare da cewa. “ Hajiya kuyi sauri ku sallame ni kafin mutumin nan ya fito dan ya hana tsayawa a nan.”
Meemah ce ta buɗe handbag dinta tana cewa. “ Ciro maka nake yi ai, malam ka yi hakuri mana.” Da haka ta ciro dari biyar tana miƙa masa, ƙarɓa ya yi ya tada machine ɗin shi yana barin gurin, su kuma suka nufa get din.
Dake ana ɗaukar sabbin ma’aikata ne hakan ya sa kullum get din kamfanin a buɗe, gaishe da security ɗin suka yi suna nufan katafaren kamfanin.
Ta ko’ina mutane ne kowa yana harkan gabansa, ciki suka shiga suka tambaya ina ne office din MD, nuna musu aka yi, da haka suka hau bene na uku, nan ma suka kuma tambaya aka nuna musu office din, direct office din suka nufa.
Ƙwanƙwasawa suka yi aka basu damar shigowa, da sallama a bakin su suka shigo, gaishe da mutanen gurin suka yi suma suna samun guri suka zauna.
Meemah ce ta tashi ta miƙawa PA takardun su tana komawa ta zauna.
Sun daɗe kafin aka kira sunan su, tashi suka yi a tare zasu shiga, PA din ta yi saurin dakatar da su ta hanyar cewa. “ One person please.” Ja baya Meerah ta yi tana komawa ta zauna.
Da haka Meemah ta shiga, kusan minute goma kafin ta fito, ita kuma Meerah ta shiga.
Tana buɗe office din kamshin turare ya kai mata ziyara, a hankali ta shigo bakinta ɗauke da sallama.
Yana zaune a kan kujera yana ta faman danne-danne a laptop, gashin kansa ya rufe masa fuska bakinsa kaɗai ka ke gani.
Ba tare daya ɗago ba ya nuna mata seat, a hankali ta zauna tana miƙa masa takardun ta, amsa ya yi yana ganin photon dake manne a jikin takardan, a hankali ya buɗi baki yake cewa.
“ Yanzu fa ki ka fita, me ya dawo da ke kuma?.”
“ Mutum daban-daban ne.” Ta faɗi hakan tana ɓata fuska.
Ɗago da kansa ya yi yana kafe ta da manya idanunsa masu cike da ƙwarjini, idan ka gan shi zaka ce ba a nigeria yake ba, da sauri ta kau da kanta gefe tana sake tamke fuska, danna telephone ya yi yana cewa. “ Wacce ta fita yanzu ta shigo.” Kafin ya sauƙe telephone din yana komar da kansa ga laptop.
Meemah da ke waje PA ta ce mata ta shiga ana neman ta, sai da zuciyarta ya tsinke, cikin ranta kuwa cewa take ‘ Allah ya sa ba kinyin magana Meerah ta yi ba.’ Da haka ta tashi ta shiga office din.
A hankali ta iso gurin tana cewa. “ Sir gani.”
Ɗago kai ya yi yana kallon su, cikin cold voice ya ce. “ Are you twins?.”
Kafin Meemah ta yi magana Meerah ta yi saurin cewa. “ No cousins ne.”
Duban ta ya yi, kai ka rantse ba ita ta yi maganar ba saboda yanda ta tsare ta ɓata fuska, yasan sarai gatsai ta masa hakan yasa ya ce. “ Oh I think you’re just a neighbors ai.”
Meemah dake tsaye tana kallon su ce ta danyi murmushi tana cewa. “ Sir sorry mu ƴan biyu ne, ni Meemah ita kuma Meerah.”
Taɓe baki ya yi yana nuna mata hanya alamun ta tafi.
Hararan Meerah ta yi tana juyawa ta fita, cikin ranta kuwa jira take Meerah ta fito su tafi gida, sai ta gaya mata a gurin wa ta koyi gatsai da rashin kunya, ga miskilancin tsiya, duk surutun da zaka mata sai dai ta ce maka uhm, hmm, mmm. Amma ta buɗe baki ta maka magana zaka daɗe.
Bayan fitan Meemah sun ɗauki kusan mintuna biyar babu wanda ya yi magana a cikin su, shi yana danna laptop ita kuma tana danna wayarta.
Ganin bata da niyar yin magana ne yasa shi ɗago kai yana cewa. “ Keee!!!.”
Taji sarai amma sai taƙi ɗago kanta ta yi kamar bata ji ba, hakan ba ƙaramin bata masa rai ya yi ba, a hassale ya kuma cewa. “ Keee!!!.”
Nan ma bata nuna alaman taji ba, shuru ya yi bai kuma cewa komai ba. ‘ Ko dai ta saka ear phone.’ Ya tambaye kan shi.
Chan kuma ya dube takardan da ta bashi, kafin ya dago yana cewa. “ Meeyah.”
Har cikin ranta sai da tayi dariya, ta lura bashi da R ko kaɗan, kamar ba za ta ɗago ba sai kuma ta ɗago tana cewa. “ Na’am.”
Tamke fuska ya yi yake cewa. “ Kina jina ki ka mantan da ni, wai ba neman aiki ki ka zo yi ba?.”
“ Shi dai.” Tana cigaba da danna wayanta.
“ Ok you can go, gobe ki fara aiki a matsayin mai gyara min office da toilet, make sure 7 o’clock ta same ki a nan.” Ya faɗa a gadaran ce tare da zuba mata manya idanunsa, dan ya lura tana da rashin kunya.
Ɗago da kanta ta yi tana cewa. “ Idan banyi kuskure ba neman aiki nazo yi ko?.” Ta tambaye shi tana kallon kwayar idanunsa.
“ Uhm.” Ya bata amsa ba tare da ya yi magana ba.
“ Kuma dole sai an dube gurin da ya cancanta kafin za’a bani, to akan wani dalili zaka mayar dani cleaner?.” Ta yi maganar a dan ɗaga murya.
Dafe kan shi ya yi yana nuna mata hanya tare da cewa. “ Please get out, idan kin ga dama ki fara zuwa idan kin ga dama kar ki zo, is your on cup off tea.”
A hassale ta janye takardanta dake gabansa, ba shiri tea din dake gefen takardan ya zube a jikinsa, ko tsayawa bata yi ba ta fice daga office din.
Tana fitowa ko kallon inda Meemah take bata yi ba ta fice fuuuu, kai ka ce tayi missing din flight ne.
Da sauri Meemah ta mara mata baya.
Tsabar zafin tea din bai san sanda ya cije lebben shi ba tare da rufe ido da ƙarfi, sai ji kawai ya yi an banko ƙofa alamun ta fita.
Tashi ya yi ya nufa hanyar ƙofar yana saka key, kafin ya juyo ya nufa toilet, jim kaɗan ya fito bayan ya chanja trouser, wayoyinsa ya ɗiba yana kashe laptop dinsa, ransa a matuƙar ɓace ya fito.
Ko gaisawa da mutanen gurin bai yi ba kamar yanda ya saba, lifter ya hau ya danna last floor, da haka ya kai shi.
Yana fitowa bodyguard din shi ya hango shi, da sauri ya buɗe mota, tun kafin ya iso mutane suka fara gaishe shi, wasu kuma suna mamakin yanda yau yaƙi kula kowa.
Mota ya shiga, aka wangale musu get driver ya ja suka fita.
Tun da suka fito Meemah take tambayarta me ya faru, amma ta yi burus da ita, har suka tara mai adaidaita sahu ya kawo su bata kula ta ba.
Ciro key din ta yi tana bud’e gidan, gida ne na irin ba masu ƙarfi ba, amma a wani gurin gidan masu kuɗi ne, ɗakuna uku ne a gidan da parlon babba, ko wane ɗaki da toilet nasa a ciki, sai kitchen dake gefe, ga bishiyar mango a tsakiyar filin gidan.
Buɗe ƙofar parlon ta yi tana wucewa ɗakinta direct ranta a ɓace.
Biyo bayanta Meemah ta yi, tana shiga ɗakin ta zauna a kan katifa, dafa Meerah ta yi tana cewa. “ Calm down Love, ki daina saurin fushi please.”
Ko kula ta bata yi ba, sai ma ajiyar zuciyar da take sauƙewa akai-akai, da sauri Meemah ta kuma cewa. “ Za ki saka ciwon ki ya tashi ko, wai me ya miki ne?.”
Kallon ta ta yi tana ɗauke idonta, kafin ta ce. “ Wai ni zai ce ya ɗauke ni aiki as a cleaner.”
Da sauri Meemah ta sa hannu tana rufe bakinta dan kar dariyar ya subuce, ta witsiyar ido ta ganta, kafin ta ce. “ Are you laughing at me Meemah.”
Girgiza kai ta yi, ƙwafa Meerah ta yi tana cewa. “ If i go make i d…” Da saurin Meemah ta rufe mata baki tana cewa. “ Please Meerah don’t say no, bamu da wani hanyar da zamu biya kudin hayan nan, ga school zamu shiga part two, kinsan dole za muyi registration, and babu wani kayan abincin da muke da shi bayan indomie daya rage guda biyar; babu wanda yake taimaka mana tunda Dad da Mom suka rasu, gidan mu na gadon ma su Uncle sun ƙwace. Kin ga dole mu yarda da duk gurin da ya ajiye mu.”
Ta ƙarashe maganar a raunane.
Sanyi jikinta ya yi, cikin wani irin yana yi ta dube ƴar uwarta ta tana cewa. “ Shi kenan, but ki sani bazan yi tolerate din ko wani wulaƙanci ba.”
Murmushi ta sakar mata tana cewa. “ Babu ma wanda zai miki wulaƙanci Love, and nima ai ya ɗauke ni aiki a company.”
Da sauri ta juyo tana kallon ta, alamun tana son karin bayani, murmushi ta yi tana ɗaga mata kai tare da cewa. “ A matsayin mai duba shiga da fita na office din accouter.”
Waro ido ta yi tana cewa. “ So ni ya rainawa hankali ke nan, ni ce cleaner ko.”
“ Love ki ɗauka ke ce me kamfanin bashi ba, kar ki kawo tunanin ke cleaner ce a company ok.”
Lumshe ido ta yi tana tashi tsaye tare da cewa. “ Bari na watsa ruwa na gaji, sannan ki dafa mana indomie din ko guda biyu ne, gobe kafin mu fita sai mu dafa uku.”
Gyaɗa mata kai kawai tai, da haka ta wuce toilet, Meemah kuma ta fice.
Yana ƙwance akan makeken gadonsa ya yi ruf da ciki, idanunsa a rufe kamar wanda ya ke bacci, ringing din wayansa ne ya dawo da shi cikin hayyacinsa.
Hannu ya miƙa ya ɗauka tare da mannawa a kunne, ta cikin wayan ne ake cewa.
“ Sir munyi bincike sosai akan yaran, gidan da suke ciki ma na hayane, sannan su biyu kawai suke rayuwar su basu da kowa.”
Jijjiga kai ya yi yana cewa. “ A nemo me gidan da ya basu hayan ya kore su nan da kwana biyu.” Da haka ya kashe wayan ba tare da ya jira ya ji me wancan din zai ce ba.
Tashi ya yi yana zura jallabiya ya sauƙo ƙasa….
*COMMENTS AND SHARE FISABILILLAH🙏*
09027308227 chart only
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
2- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny _
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
________________________________
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*P.2*
Tashi ya yi yana zura jallabiya ya sauƙo ƙasa, wata ƙyaƙyawar mace ce zaune a kan haɗadɗan two seater, ta ɗaura ƙafa daya kan daya tana kallon labarai, fuskarta ɗauke da murmushi take ganin ɗan nata, kafin ta ce wani abu ya ɗurkusa yana cewa. “ Ammah ina wuni.”
Murmushin nata ta faɗaɗa tana cewa. “ Lafiya Babana, ya aikin?.”
“ Alhamdulillah.”
“ Ka shigo ɗazu ina maka magana baka kulani ba, kuma naga ranka a ɓace, hope everything is fine.”
Sosa keya ya yi dan yasan sarai ɗazu ya jita amma ya basar, saboda ɓacin ran daya dawo dashi daga office, cikin lallaba ya ke cewa. “ Kiyi hakuyi Ammah, dazun ne yai na a bace.”
Murmushi ta masa tana cewa. “ Ya wuce ai, kaci abinci kuwa?.”
Ƙarɓan remote din hannunta ya yi tare da chanja channel zuwa na ball, kafin ya ce. “ Ammah am okay bana jin yunwa.”
“ Kai ka sani kuma, tv din ɗakinka bai ishe ka bane zaka zo ka hanani kallo.”
Dariya ya yi yana cewa. “ Ammah ɗakin ne ba daɗin kallo, kuma yau ake buga World Cup shi ya sa.”
Taɓe baki ta yi tana tashi ta nufa ɗakin ta.
Ringing wayansa ya ke yi, hannu ya sa ya ɗauka yana mannawa a kunnensa, ta can bangaren ne ake cewa. “ Sir mun bashi million biyar din, sannan ya ce yau zai kore su daga gidan.”
Murmushin gefen baki ya yi yana buɗe baki cikin rashin son magana irin nashi ya ke cewa. “ Good, and make sure kay a kuskuya wani ya taimake su.”
“ Okay.”
Da haka ya katsai wayan yana murmushi.
“ Ya Alyan yau kai ne da wannan maganar.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ta faɗa, kai daga gani basai an maka dogon bayani ba kasan ƙanwarsa ce, duba da irin kaman da suke sosai.
Zama ta yi kusa da shi tana cewa. “ Ma waye din ne kar a taimakawa Bro.”
Tamke fuska ya yi kamar ba shi bane ya ke murmushi yanzu, kafin ya dube ta a tsare yana cewa. “ Laɓe ki ke min?.”
Saurin girgiza kai ta yi tana cewa. “ Nazo wucewa kitchen ne naji kana waya.”
“ And sai aka ce ki tsaya kina sauyayan abunda nake faɗa?.” Nan ma ya yi maganar fuska babu annuri.
Tashi tsaye ta yi tana turo baki tare da cewa. “ Daga tambaya sai a fara min masifa.” Tana maganar tana nufan kitchen.
Tsawa ya daka mata ta hanyar cewa. “ Laylah!!!.”
Da sauri ta juyo tana rufe bakinta, kafin ya yi wani magana tuni ta gudu ɗakin Ammah, ƙwafa ya yi yana tashi ya haura sama ran sa fesss.
Suna zaune a ƙasan bishiya suna dan taɓa hira, amma duk rabi da ƙwatan hiran Meemah ce ke yin ta, ita dai Meerah sai dai ta bita da uhm.
Sallama aka musu daga waje, duban juna suka yi Meemah na cewa. “ Waye kuma da mangarib nan?.”
“ Ki zauna bari naje na duba.” A cewar Meerah tana tashi tsaye, veil din dake kanta ta warware ta yafa tare da saka takalmi ta nufa ƙofa.
Fitowa wajen ta yi tana gaishe da dattijon.
Fuskan mutumin babu alamun tausayi ya ce. “ Ina ƴar uwar taki.”
Dan ɗaga gira Meerah ta yi tare da kama ƙwanƙwaso tana cewa. “ Wani abun zaka mata.”