Showing 30001 words to 33000 words out of 36194 words
Chapter 11 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx
mata kuwa, idan ban kashe yarinyar nan ba Luby bazan ji dadi ba sam.” Cewar wata budurwa da take tsaye taci uwar bleaching ita da kawayen ta biyu.
Dayar ce me suna Zuby ta yi dariya. “ Kee ai nemo gardi zamuyi ya mata kaca-kaca ta yanda bazata ganu ba, ko kuma a watsa mata acid.”
Tafawa suka yi Sumy na cewa. “ Shiyasa nake ji daku kawayen arziki, amma nifa nafi so a mata fyade ko ya kuka gani?.”
Luby ce tayi murmushi tana cewa. “ Amma kar garin nemo kiba a samo rama fa.”
“ Ke babu ramar da za’a samo ku shiga mota muje.” Cewar Sumy tana tada mota, Zuby ce ta zauna a gurin me zaman banza ita kuma Luby ta zauna a baya, kida ta kunna musu suna tashewa.
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
23 - 24 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*BOOK ONE*
*FREE PAGE 23 & 24*
Har suka isa gida bata musu magana ba, Meemah ce ta biyo su ɗaki tana cewa. “ Kin san ta ne dama?.” Girgiza mata kai tayi.
Yasmeen ce ta shigo ɗakin tana kallon su kafin ta ce. “ Ya dai? Akwai matsala ne na ganku duk a tsaye?.”
Numfashi Meerah ta sauƙe kafin ta ce. “ Kinsan Laylerh ne?.”
“ Na santa mana, department namu fa daya.” Cewar Yasmeen tana zama a bakin gado.
“ To bani labarin ta mana ko kaɗan.” Meerah ta faɗa tana zama kusa da Yasmeen, ita ma Meemah zama tayi a kusa da Yasmeen din sai ya zamana sun saka ta a tsakiya.
Kallon su tayi tana cewa. “ Da matsala ne naga kuke tambayar labarin ta? Ko kunsan wani abu akanta ne?.”
“ Laaa kawai fa inaso naji ne bayan haka kuma babu komai ko Meemah?.” Ta faɗa tana warewa Meemah ido.
Ita ma tayi dariya tana cewa. “ Eh fa Yasmeen babu komai nikam ta burgeni ce.”
“ Kun tabbata babu abunda ta muku ko?.” Cewar Yasmeen tana sake kallon su, dan ita bata yarda da su ba.
Kau da kai Meerah ta yi tana ɓata fuska, tana cewa. “ Idan ba za ki faɗa ba shi kenan ai.”
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa. “ Sunan ta Amina Junaid Dala, amma anfi saninta da Laylerh ko kuma ƙanwar big bro… Saurin juyowa Meerah tayi tana cewa. “ Waye ne Big Bro din?.”
“ Yayanta ne wanda kwanakin baya kuke aiki a company shi, abokin Yaya Mansoor wanda ya taba zuwa wajen ki, ana kiran shi da Alyan abokanan shi suna kiran shi da Bobo wasu kuma su ce masa Mama’s Boy.” Meerah ce ta katsai ta ta hanyar cewa. “ Yana da aure ne?.”
“ A’a bayi dashi kwanakin baya dai har za’ayi auren sai kuma aka fasa, dan gidan nan ma yazo yayi kwana biyu.”
“ Yasmeen ko kinsan me ya sa aka fasa auren?.” Cewar Meerah tana zuba mata ido.
“ Eh dai to kamar naji wai akan yayi wa wata yarinya fyaɗe ne, amma shi kuma ya ce baiyi ba sharri aka masa dan maganar har ya taɓa siyasar shi.”
Ta ƙasan ido Meerah da Meemah suka kalli juna kowa da abunda ke rayawa a ransa, maganar Yasmeen ce ya tsorata ta inda take cewa. “ Ai har budurwarsa din ta haihu ta kawo masa yaron, amma yaron ko kama dashi bayayi sai ma da akaje akayi gwajin genotype aka ga jinin kwata-kwata bai hadu ba, nan fa aka shiga court ita tace sam nashi ne shi kuma ya dafa Qur’ani akan cewa bai taba ko kama hannun mace ba bare ya kai da yi mata fyaɗe har tayi cikin shege, sai da aka sha wahala fa kafin ta yarda bashi bane uban yaron.”
Numfashi Meerah ta sauƙe zuciyarta cike da tsoron da bata taɓa jin irinsa ba, gaba daya hankalinta ya tashi ta rasa me ke mata dadi.
Yasmeen ce ta ce. “ Akwai wani abunda kuke so kuji?.”
Girgiza kai Meerah tayi tana cewa. “ Babu iya wannan ma ya ishe ni.”
“ Shi kenan bari nikam naje gurin Mama.” Da haka Yasmeen ta fice daga ɗakin.
Matsowa kusa da ita Meemah tayi tana jawota jikinta, kamar jira take kuwa ta fashe da kuka mai tsuma zuciya duk da bata san kukan nata akan me bane, rarrashin ta take tana bata hakuri.
Buɗe baki tayi zata yi magana amai yazo mata, da gudu ta tashi ta nufa toilet Meemah na mara mata baya, sosai take aman kusan duk abunda taci sai da ta zubar, tuni ruwan jikinta ya ƙare.
Riƙe ta me kyau Meemah tayi tana tayata gyara jikinta, sai da ta taimaka mata ta cire rigar jikinta dan ya ɓaci kafin suka fito.
A bakin gado ta ƙwantar da ita tana komawa toilet din ta wanke rigar ta fito taje ta shanya, dawowa tayi tana zama kusa da ita ta zuba mata ido tana karantar yanayin da take.
Haɗa ido suka yi Meerah na cewa. “ Meemah ya kin zuba min ido haka fa.” Saurin ɗauke idanunta tayi tana fatan ba abunda take zargi bane.
*MILLIONAIRE CITY*
Ammy ce da Laylerh a parlon suna hira, Laylerh na cewa. “ Ammyna na yiwa Big Bro fa mata.”
Kallon ta kawai tayi tana cigaba da danna wayanta, tasowa tayi daga gurin da take ta dawo gurin Ammy tana cewa. “ Ammy da gaske fa nake, yarinyar akwai hankali sosai ga nutsuwa ga kyau.”
“ Kee matsa chan da shirman ki.” Cewar Ammy tana ɗaga kiran da ya shigo mata vc.
“ Wallahi Ammy da gaske nake yarinyar ƙyaƙƙyawa ƴar gidan mutunci nasan Big Bro zai so ta sosai, dan naga kaman su sosai.”
Yana zaune a parlon shi ya kira video call din, sai yaji Laylerh na cewa ta samo masa mata, murmushi kawai yayi yana cewa. “ Ammyna wancan yayinya lafiyanta kalau kuwa?.”
Saurin ɗurowa daga kan gujeran Laylerh tayi tana kallon Ammy, tana mata magana da hannu alaman tace bata nan, murmushi Ammy tayi tana cewa. “ Babana nima haka naji wai an maka mata.”
“ Hmm ai Layleyh bata jin magana ko kaɗan, ni ban mata miji ba ita zata min mata ko.” Ya faɗa yana dan dariya.
“ To dai gata ko takamamman saurayi bata da shi duk wanda yazo sai ta kore shi ko tace zata haɗa shi da kai.”
“ Ai Ammyna ina dawowa za’a mata auye.”
“ Babana kai din fa?.”
Shafa sajen shi yayi yana murmushi kawai, kafin ya ce. “ Lokaci muke jiya Ammyna idan yayi zamu yi mu ma.”
“ Haka kullum kake faɗa fa Babana, ko acan din ka samo mana wata ne?.”
Girgiza mata kai yayi yana cewa. “ Ban samu ba tukun, sai aikin da nake yi kawai.”
“ Naga ka rame sosai ma kuma kayi baƙi, ko akwai abunda kake tunani ne?.” Ammy ta fad’a fuskarta ɗauke da damuwa.
“ Ammyna babu komai aiki ne kawai.”
“ Kana hutawa mana to.”
Murmushi ya mata daga haka sukayi sallama.
Shuru yayi yana tunanin ta, number ta yayi trying amma switch off gashi baya so ya tambayi Mansoor, Laylerh ya kira ta normal call, lokacin ta koma ɗaki tana charting.
~Big Bro~
Shi ne sunan da ya fito a gaban wayan. “ Na shiga uku yanzu zai min masifa ko.” Ta faɗa tana ɗaukan kiran.
“ Yaya ina wuni.”
“ Yau din kuma, ko dai baki da kudi ne naji kina gaishe ni?.”
“ A’a Yaya kawai na gaishe ka ne.”
Taɓe baki yayi yana cewa. “ Siyyi zamu yi dake, amma idan kika faɗawa wani sai naci ubanki.”
“ Bazan faɗa ba Yaya nayi alkwari.”
“ Better…. Gidan su Man za ki je ki dubamin wata yayinya.”
Da sauri ta gyara zaman ta tana cewa. “ Yaya wacce a cikin su?.”
“ Dama akwai wanda kika sani ne a cikin su?.”
“ Eh fa Yaya ai ita ce nace na maka mata, Makarantar mu daya ma dazu Alwan yake mata maganar aure ni kuma na kore shi nace matar Big Bro ce, kuma wallahi Yaya idan ka ganta fara sol ka rantse baturiya ce, ga hankali da nutsuwa, kuma har na nuna mata photon ka nace shi ne mijinki tace wai sam bata sanka ba, nace kina Kaduna baki sannan wannan ba tace wai bata sanka ba, amma sai satan kallona take ta gefe idan muka haɗa ido sai ta ɗauke kai, kuma…”
Katsai mata zancen nata yayi yana dafe kai, kafin ya furta. “ Ya isa haka keee!!! Ai su biyu ne wacece kika sani?.” Ya faɗa duk da kuwa yanzu ta masa bayani yasan ita take nufi.
“ Meerah shi ne sunan ta, Allah yasa dai itace in-law namu dan naji jinina ya hadu da ita sosai har na fara ce mata In-law, ita kuwa sai dai ta bini da lulu eyes nata, gata da packaging tana tafiya kana ganin yanda hips nata suke rawa…”
Da mamaki ya furta. “ Layleyh abunda kike kallo ke nan?.”
“ A’a Wallahi.”
“ Kin kyauta, amma da hijabi take yawo ko gyalle?.”
“ Wallahi Yaya kullum cikin hijab take, kuma hijab din har ƙasa yake ja amma sai jikinta ya nuna tsabar irin surar da Allah ya mata.” Har wani bayani take da hannunta tsabar gulma nacin Laylerh.
Haɗiye yawu yayi mai ƙauri na ɓacin rai yana cewa. “ Gobe idan tazo Makayanta ki haɗamu waya, idan kuma bata zo ba ke kije gidan ki bata waya.” Daga haka ya kashe kiran.
Murmushi Laylerh tayi sai kuma tayi shuru. ‘ A ina suka hadu to? Kenan tasan shi amma tace bata san shi ba?.’
*UNGUWAR DOSA*
Da daddare kowa na parlon Mansoor ya shigo da leda a hannun shi, gaishe shi suka yi Mama na cewa. “ Yau kayi dare.”
“ Ammy wata mara lafiya aka kawo duk jini jikinta, shiyasa na tsaya har na bata kulawan gaggawa.”
“ Ayya.”
Tun da ya shigo taji kamshin nama cikinta ya hargitse, ɗaurewa tayi kawai tana zama bata tashi ba.
Miƙa ma Meemah leda daya yayi yana cewa.” Gashi ku raba.”
“ Mun gode.” Ta ƙarɓa tana buɗewa.
Kamshin ne ya daki hancin ta a take amai yazo mata, da gudu ta miƙe ta nufi toilet din dake parlon tana amai, da sauri Mansoor ya mara mata baya zuwa toilet din su Meemah ma suka biyo su.
Sosai take aman ya rike ta ganin bata da ƙarfin tsayawa, sai da ta amayar da duk abunda taci kafin ya tara ruwa ya wanke mata baki suna jera mata sannu.
Ɗaukarta cak yayi zuwa parlon ya ƙwantar da ita akan three seater, toshe hancinta tayi tana rufe ido, kallon ledan kajin yayi yana cewa. “ Yasmeen fitar da ledan waje.” Da sauri ta fitar ta dawo.
Meemah ce tazo kusa da ita ta zauna tana kama hannunta, cike da tsoron abunda zai biyo baya take kallon ƴar uwarta ta.
Mansoor ne ya fice bai dade ba ya dawo, tashi Meemah tayi shi kuma ya zauna, buɗe idanunta yayi yana kallo kafin ya duba tafin hannunta, kallon ta yayi na wasu mintuna kafin ya bada wani ƙaramin abu yana cewa. “ Meemah rakata tayi fitsari.”
Kamata Meemah tayi suka nufi toilet, zama Mama tayi tana mai tagumi, shi ma ɗafe kansa yayi yana yin shuru, Yasmeen kuwa sai bin kowa da ido take.
Dawowa suka yi yayi sauri ya ƙarba yana kallo, a dan tsorace ya dube ta yana sake kallon type din, Mama ce ta ce. “ Mansoor me ya faru?.”
“ Mama yarinyar nan cike ne fa da ita.”
Da sauri ta kama hannun Meemah tana girgiza kai idanunta sun ciko da hawaye, kallon ƴar biyun ta ta tayi tana cewa. “ Meerah!!!.”
Yasmeen kam tuni tayi suman tsaye, kallon ta yayi yana magana a tsawace. “ Uban wa ya miki ciki!!!.”
A razane ta buya a bayan Meemah tana kuka, fuzgo ta yayi da ƙarfi idanunsa sunyi ja cike da haushi ya kuma cewa. “ Mara hankali kawai, Wallahi idan baki faɗamin uban wanda ya miki ciki ba sai na kusan kashe ki a gidan nan, kuma a zubar da cikin…
Saura page biyu na gama, ga masu buk’atar su cigaba da karanta littafin *BA KAI NAKE SO BA* Book two dari hudu ~N~ 400🫠🫠🫠, Kun san dai yanzu za’a shiga cikin labarin saboda haka kar ayi tafiyar babu ku🤗😘😘😘. Za’a iya biya via 9031176727 Fatima Isa Opay, idan mutum ya turo da kudin sai ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta WhatsApp number ta 09027308227 SAHIBAR JAJIRTATTU ko DR TEEMAH.
Kar ku bari wannan labarin ayi sa ba tare da ku ba❤️🌹🫠 Yan Nijer kuma su min magana.
*BOOK TWO zai fara zuwa ne on 28th April In Sha Allah kar ku bari ayi baku🤗🤗🤗*
25 - 26 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*BOOK ONE*
*FREE PAGE 25 & 26*
Saura page kadan na gama, ga masu buk’atar su cigaba da karanta littafin *BA KAI NAKE SO BA* Book two dari hudu ~N~ 400🫠🫠🫠, Kun san dai yanzu za’a shiga cikin labarin saboda haka kar ayi tafiyar babu ku🤗😘😘😘. Za’a iya biya via 9031176727, Fatima Isa, Opay, idan mutum ya turo da kudin sai ya yi screenshot ya turo mini da evidence of payment ta WhatsApp number ta 09027308227 SAHIBAR JAJIRTATTU ko DR TEEMAH.
Kar ku bari wannan labarin ayi sa ba tare da ku ba❤️🌹🫠 Yan Nijer kuma su min magana.
*BOOK TWO zai fara zuwa ne on 28th April In Sha Allah kar ku bari ayi baku🤗🤗🤗*
**************************
A razane ta buya a bayan Meemah tana kuka, fuzgo ta yayi da ƙarfi idanunsa sunyi ja cike da haushi ya kuma cewa. “ Mara hankali kawai, Wallahi idan baki faɗamin uban wanda ya miki ciki ba sai na kusan kashe ki a gidan nan, kuma a zubar da cikin tun da na shege ne.”
Kuka take ta kasa magana, Mama ce ta ce. “ Mansoor kabi a hankali da ita zata fada koma waye ne, amma a yanda ka biyo din nan ba lalle kaji wani abu daga bakinta ba.”
Gagara nutsuwa yayi sai ma cigaba da mata masifar da yake yi yana fuzgota. “ Me ya sa kika min haka? Meerah ki fadamin koma waye ne zan tsaya miki a shari’a, me ya sa baki fadamin halin da kike ciki ba, kinsan inason ki to me ya sa zaki sakamin da wannan, me na miki da zaki sawa zuciyata ciwo Meerah?.”
Tuni Meemah ita ma ta fara kuka ganin yanda Meerah ke yi kamar ranta zai fita, nan da nan fuskarta yayi ja tsabar kuka, sake matse mata hannu yayi da karfi wanda yasa ta kara sautin kukan nata.
“ Mansoor ciwo fa kake ji mata.” Cewar Mama wacce ta gagara motsawa daga gurin da take.
Kallon Meeran yake yana huci. “ Har yanzu bata ji irin zafin da nake ji ba, kuma har abada zafin bazai bar zuciyata ba.”
Yasmeen ce ta lura da gurin da ya rike tana cewa. “ Yaya kaji mata ciwo fa!!!.”
Da sauri Meemah ta durkusa a gabansa tana hade hannayen ta biyu tana cewa. “ Na rokeka ka barta dan Allah.”
“ Waye ya miki ciki? Tambayar ki nake waye ya miki ciki!!!.” Ya fada a tsawace.
Kukan ta kara tana kama hannun shi da ya rike na ta, muryanta tuni ya dashe tsabar kuka take cewa. “ Al… al..”
“ Wallahi idan har baki fadamin uban wanda ya miki ciki ba ke da farin ciki kun raba hanya.”
Cike da haushi Meemah ta mike tana shiga tsakiyar su, ta