Showing 24001 words to 27000 words out of 36194 words
Chapter 9 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx
din shi ne 2800, akwai kudi isheshe a ciki da zai ishe ki.” Ƙarba ta yi tana gyaɗa kai saboda kukan da yake shirin kufce mata.
Key din gida ya bata yana cewa. “ Na gidan da muka zauna ne, idan kina neman kaɗaicewa za ki iya zuwa ok.”
Numfashi ya sauƙe yana jawota jikinsa, kukan da take riƙewa ne ya subuce mata, runtse ido yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, wani siririn sarƙa ya ciro daga aljuhun wandonsa yana saka mata a wuya.
“ Duk abunda zai fayu kay ki ciye wannan saykan.”
Taɓa sarƙan tayi tana cewa. “ To.” Alex ne ya ƙwanƙwasa motan yana shiga.
Mika masa kwalin wayan yayi yana cire sim nashi daga dayan wayansa ya saka mata, kunna wayan yayi yana miƙa mata.
Kallon wayan tayi tana cewa. “ Wannan fa?.”
“ Naki ne.”
Saurin rungumarsa tayi tana sake fashewa da kuka, cikin kuka take cewa. “ Nikam mu koma banason komawa gida.”
Dariya ya fashe dashi wanda yasa dimple nashi lotsawa yana cewa. “ Ni da ake cewa an shiga uku.”
“ Ni fa wasa nake maka.”
“ To ai Nigeria zan bayi.”
Da sauri ta ɗago tana kallon shi. “ Ina zaka je?.”
“ India zan je zanyi kusan 1 year ko 8 months haka.”
Shuru ta yi kawai tana jin ba dadi, ganin kamar sun shigo unguwar ne yasa shi cewa. “ Ban da kula samayi, ni kuma tun da ba’ason yayuwa da ni is okay ba matsala.” Murmushi ta masa ganin sun tsaya a ƙofan gidan.
Fita Alex yayi yana basu guri, da sauri ya jawota jikinsa yana haɗe bakin su guri daya yana kissing, ita ma taya shi tayi suna kissing din junan su, ganin yana shirin barin hanya ne ta yi saurin zame jikinta daga na shi.
Numfashi yake sauƙewa a hankali ya ƙwankwasa jikin glass din motan, buɗe boot Alex yayi yana ciro mata akwatin ta kafin ya zagayo ya buɗe mata ƙofa.
Kallon shi take cike da jin ba dadi, wayan da ya bata da Atm ta ɗauka tana cewa. “ Allah ya tsare hanya, Allah yasa kaje a sa’a ka dawo a sa’a.” Da haka ta fita daga motan.
“ Amiin Best choice.” Da haka Alex ya koma ya shiga motan yana tadawa, tana tsaye a gurin har suka ɓacewa ganin ta.
Kallon Atm din ta yi da wayan ta saka a gefen akwatin tana ɗauka ta nufi cikin gidan tare da tsoro da fargaban mai zai faru.
Da sallama ta shiga cikin gidan, Meemah da Yasmeen da suke parlon ne suka amsa, Meemah na cewa. “ Kamar muryan Love fa.”
“ Nima haka naji.” A guje suka fito har suna buge junan su.
Tsayawa suka yi suna kallon ta, ƙare mata kallon Meemah ta yi tana cewa. “ Meerah!!!.”
Kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Na’am.” Da gudu taje tana rungume ta cike da jin dadi…
*Ni ma cike da mura nake cewa sai anjiman ku😒*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
17 - 18 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*P.17 & 18*
NOT EDITING🥹
Kuka ta fashe da shi tana cewa. “ Na’am.” Da gudu taje tana rungume ta cike da jin dadi.
“ Love ina kika shiga? Naga yanayin ki kamar ba sace ki akayi ba, ga akwati a gefe kuma…” Shuru tayi lokacin da ta lura da kayan jikin Meerah din.
“ Meerah waye ya baki kayan nan?.”
Kallon kayan tayi tana dagowa ta kalli Meemah, Yasmeen ce tazo tana daukar akwatin tare da cewa. “ Ki barta ta shiga ciki mana sai kuyi magana, amma mutum daga dawowar ta har kin fara tambaya.”
Kallon tuhuma Meemah ta bita da shi wanda hakan yasa Meerah kasa dagowa ta kallo twins natan, dan duk karyan da Meerah zata yi Meemah baza ta taba yarda ba ne.
Yasmeen ce ta wuce daki da akwatin tana ajiyewa, kafin ta biyo parlon ta same su suna zaune, sai idon da Meemah ta zuba mata tana jiran taji me zata ce.
“ Meerah ina kika je?.”
“ Meemah ya kina min wani irin tambaya ne, me ya sa zan gudu haka kawai me aka min.”
Kallon Yasmeen Meemah ta yi tana cewa. “ Sis kamar karar motan Yaya Mansoor.”
Duban agogo ta yi tana cewa. “ Zai iya dawowa tunda ana neman four ai.” Shuru duk suka yi kowa da abunda yake cin ransa.
Da sallama a bakinsa ya shigo parlon yana cewa. “ Meemah zo ki karbi chocolate na…” Maganar ne ya makale lokacin da idanunsa suka sauka akan Meerah wacce ta sunkuyar da kai.
Da sauri ya karasa shiga yana cewa. “ Yaushe ta zo?.”
Yasmeen ce ta ce. “ Bata dade da shigowa ba ka shigo Yaya.”
“ Meerah!!!.” Dago da kai tayi tana kallon shi.
“ Waya dauke ki?.”
Shuru ta masa tana tunanin karyan da zata yi, sake tambayan ta yayi a karo na biyu. “ Waya sace ki?.”
“ Ni ma bansani ba.”
“ Meerah kiji tsoron Allah, Wallahi kinsan wanda ya dauke ki.” Meemah ta fada kamar ta kai mata duka.
Kallon su Mansoor yayi yana cewa. “ Meemah taya za ki ce ta sani, idan ta sani ai zata fada.”
“ Hmm Yaya tun muna yara nasan wacece Meerah fa, Wallahi Wallahi kaga Meerah tasan waye ya dauke ta.” Ta fada tana kallon cikin idanunta.
Da sauri ta janye idanunta daga cikin nata tana cewa. “ Ni bansani ba nace muku.” Juyar da zancen Meemah tayi zuwa yaren su Igala ta yanda su Mansoor baza su ji ba, tana cewa. “ Meerah babu wanda zai yarda da karyan kin nan, kawai ki fada gaskiya ko Wallahi na miki ba dadi.”
Ita ma ta yaren ta mayar mata. “ Babu abunda za kiji daga bakina kuma tunda ke kin gane ai shikenan.”
Da ido kawai Yasmeen da Mansoor suke bin su, dan babu abunda suke ganewa.
Masifa Meemah ta fara mata. “ Ojo Meerah yaushe kika chanja ne, wannan kwata ba dabi’ar ki bane kin koma wata daban kuma kayan jikin kin nan nasan waye ya siya fa.”
“ Idan kin sani sai me? Ba nikam na dawo ba ai shikenan ki daina damu na.”
“ Hmm kenan tun da kuna tare da shi ne ko me?.”
“ Kin manta haifarmu akayi tare da shi, ni banma san waye kike magana a kai ba.”
Dakatar da su Mansoor yayi. “ Wannan wani kalan rainin hankali ne, kun wani koma yaren da duk bamu sani ba. Shuru suka masa ba tare da sun ce komai ba.
“ Idan bakwa so muji me kuke cewa zaku iya kebewa a wani wajen ai.”
“ Nace mata bansan waye ya sace ni ba, ta wani dame ni.” Meerah ta fada tana kallon Meemah ta kasan ido.
“ Yaya Wallahi ta sani ka yarda da ni, nafa san wacece Meerah idan bata san abu ba shuru take yi amma idan ta sani ta rin ga muku kwana kwana kenan da surucen da ba kai.”
“ To ki barta mana kawai, ai tunda ta dawo lafiya mun godewa Allah.”
“ Hmm.” Meemah ta ce kawai tana shuru.
Ana haka ne Mama ta shigo da sallama a bakin ta, amsawa duk suka yi kafin ta iso cikin parlon tana bin su da ido.
“ Wa nake gani kamar Meerah.”
“ Ita ce dai Mama.” A cewar Meemah tana hararan Meerah.
“ Ikon Allah, Allah mun gode maka da ka bayyana yarinyar nan.” Kallon Meeran tayi tana cewa. “ Biyo ni daki.”
Tashi tayi tana bin bayan Mama, da ido suka bi bayanta Mansoor tuni ya daura tantama akan ta. ‘ Gaskiyar Meemah ce yarinya daga sacewa sai tayi jiki ta wani koshi tayi fresh, dubi fa yanda ta ajiye duwawa kamar ba ita bace wacce take a bushe, har wani hips ta yi.’ Saurin katsai zancen zucin nashi yayi a fili ya furta. “ Astagfirullah.”
Kallon shi suka yi Meemah na cewa. “ Yaya me ya faru?.”
Mikewa yayi yana cewa. “ Babu.” Da haka ya fice daga parlon.
Suma komawa dakin su suka yi, Meemah na cigaba da zargin yar uwar tata.
Ko da suka shigo daki rufe kofan Mama tayi tana kallon Meerah. “ Fadamin me ya faru?.”
“ Mamana babu abunda ya faru.”
“ Kar ki daukeni karamar yarinya Meerah, ko ban haife ki ba na haifi irinki ko ince wanda ya girme ki, saboda haka nasan wannan bai yi kama da sacewa ba.”
“ Ma… ma dagaske sace ni akayi.” Muryanta tuni ya fara rawa ganin irin kallon da Mama ke mata.
“ Idan sace ki akayi waye ya sace ki Meerah!!!.”
“ Mama bansan shi ba.”
“ Kiji tsoron Allah fa Meerah.”
Shuru tayi tana kallon yatsun hannun ta, cigaba da magana Mama tayi. “ To shi ya fadamin komai ai idan ke bazaki iya fadamin ba.”
Da sauri ta dago kai tana kallon ta cike da mamaki, cigaba da magana Mama tayi. “ Meerah taya har namiji zai miki wayo ki yarda, idan da farko aka ce tsautsayi sauran kuma me za’a kira su uhm?.”
Kuka ta fara yi tana cewa. “ Mama yafi karfi na ne, kuma kuma…” Sai ta sake fashewa da kukan.
Zaunar da ita tayi a bakin gado tana jawota jiki tare da bubbuga bayan ta. “ Ki dauke ni tamkar uwa kamar yanda ya dauke ni tamkar mahaifiyarsa, ke din marainiya ce kuma amana ce a hannuna, duk wata damuwarki ki rin ga fada zan share miki kuka kuma duk lokacin da kike buk’atar shawara ki dauke ni a matsayin kawarki wacce zata baki shawara.”
Gyada mata kai Meerah tayi tana jin dan sanyi a ranta, goge mata hawayen fuskarta tayi tana cewa. “ Cewa yayi dan Allah Mama kar ki bari hawayen ta ya zuba, to taya zan bari ya zuba bayan tun da akamin huduba sosai.”
Dan dariya tayi tana cewa. “ Mama fada miki komai yayi?.”
“ Taya zai fadamin komai, kawai dai abunda baza’a rasa ba ya fadamin bayan shi kuma babu.”
“ Amma Mama idan na nemi yafiyar Allah zai yafe min?.”
“ Allah a ko da yaushe shi mai yafiya ne, amma ai ku baku aikata wani zunubi ba.”
Sunkuyar da kanta tayi tana cewa. “ Mama mu kuwa muka aikata zunubai.”
Tallafo da habarta tayi tana cewa. “ Ki dena dauka zunubi kuka aikata.”
“ Mama tamkar matarsa haka ya maida ni, baya tunanin hukuncin da Allah zai mana ranar gobe kiyama, baya tausayi bayi da imani ko kadan, nayi alkawarin cewa har nayi aure bazan taba bari ruwan zina ya shiga jikina ba, sai gashi ya karyamin alkawari na, nasan yanzu babu namijin da zai aure ni.”
Murmushi kawai Mama tayi tana cewa. “ Shi kuwa yake da tausayi Meerah, kuma ya tambaye ki ko zaki iya zama dashi a matsayin miji me ya sa kika ki yin magana.”
Da sauri ta dago ido tana kallon ta, kafin ta ce. “ Kenan ya gama fada miki komai?.”
“ Ai yarona ne taya bazai fadamin komai ba.” Shuru ta mata tana wasa da yatsun ta.
“ Kibi duk umarnin da ya baki kinji Daughter.” Gyada mata kai tayi tana tunanin me ya sa Mama ke fadan haka.
“ Idan babu abunda za ki fada na sallame ki.” Kamar jira dama take da sauri ta mike ta fita.
Tafiya take tana tunanin maganganun da Mama ta fada mata, dakin su ta shiga tana kallon su kafin ta samu guri ta zauna.
Tashi ta yi ta nufa inda akwatin yake ta bude, kallon ta Meemah tayi ganin wayar da ta ciro, Yasmeen ce tayi saurin cewa. “ Ahhhh gaskiyan Meemah, Meerah ba sace ki akayi ba Iphone 15 pro max. “
Ringing wayan ya fara inda suna ke yawo a kai, Meemah ce ta kalli gaban screen din tana cewa. “ Final choice.”
Da sauri ta kashe kirana tana kallon su da manyan idanunta, Meemah na shirin magana ne wayan ya sake yin ringing, the same sunan ke yawo akai.
Fuzge wayan Meemah tayi tana dauka.
“ Are you okay?.” Shine abunda aka fada daga cikin wayan, kashe wayan Meemah tayi tana dagowa ta kalli Meerah wacce ta zuba musu ido.
“ Shi din waye ne?.”
“ Ina zan sani ke fa kika dauki wayan, kina min tambaya kamar ke ce babba ko kin haife ni, duk abunda naga dama shi zanyi rayuwata ce kinbi kin addabe ni tun da na shigo sai kace na tare miki wani abu, sai zargina kike yi.”
“ Ba dole na zarge ki ba Meerah, kin chanja hali gaba daya kamar ba ke ba.”
“ Bani wayata.” Mika mata tayi ba tare da ta ce komai ba.
Ringing wayan ya kuma yi ta dauka. “ Ke da waye ne?.”
“ Ina ruwanka?.”
“ Shikenan na kira ne naji ya kike.”
“ Bansani ba.” Ta kashe wayan.
Bin ta da ido kawai su Yasmeen suke har ta gama wayan…
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
19 - 20 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*BOOK ONE*
*P.19 & 20*
Bin ta da ido kawai su Yasmeen suke har ta gama wayan, kafsewa ta yi tana zama ta juya musu baya.
Kallon junan su suka yi kafin Yasmeen ta ce. “ Meerah nikam ba ni wayan nayi hotuna, sai na tura ta nawa.”
Kallon baki da hankali Meemah ta mata, miƙa mata wayan Meerah ta yi tana fara gyara kayanta, da sauri ta ƙarɓa tana fita daga ɗakin.
Tashi Meemah ta yi ta zagayo ta gurin da Meerah take tana kallon ta, ita ma kallon ta din ta yi tana cewa. “ Meemah bakya yarda da ni.”
“ Meerah taya zan yarda da ke bayan ba ki da gaskiya? Ni fa ƴar uwarki ce kuma ciki daya muka fito sannan a rana daya, waye zai faɗa min halinki kuma.”
Shuru ta yi tana mai kallon yatsun hannunta, zama Meemah ta yi kusa da ita tana mai tallafo fuskarta ta ce. “ Ki faɗamin gaskiya me ya faru, dan nasan wannan baiyi kama da sacewa ba sam.”
Nan da nan idanunta suka cika da ƙwalla, kamar wacce akace ki fara kuka kawai ta fashe mata da kuka tana faɗawa jikinta.
“ Subhanallah ni dama nasan wani abu ne ya faru, kiyi hakuri love komai zai wuce, me ya faru.” Tana maganar tana bubbuga bayanta alamar rarrashi.
“ Meemah me ya sa kaddarar mu take zuwa a haka? Mun aikata zunubi ne bamu sani ba, da nasan haka kaddara zata zo da ban darsu cikin duni…” Saurin rufe mata baki ta yi tana girgiza mata kai.
“ Koman da ya faru rubutaccen kaddara ne, kar kiyi saɓo Meerah.”
Numfashi ta sauƙe tana cewa. “ Idan na faɗa miki komai kar ki ga laifi na dan Allah, hakan zai ƙara saka zuciyata cikin ƙunci.”
Murmushi ta mata tana cewa. “ A guna bakya laifi kuma ba za ki taɓa yi ba har abada, ki faɗamin komai idan na shawara ne zan baki idan kuma na kuka ne sai mu taru muyi tare, kin ji so faɗamin me ya faru da aka ce kin ɓata?.”
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana kallon ta ta fara magana. “ Kin san Alyan?.”
“ Waye Alyan kuma?.”
“ Wanda muke aiki a company shi, wanda yazo ranar har na masa rashin kunya shi da Yaya Mansoor.”
“ Ohhh eh na gane shi.”
“ To tun ranar da na rubar masa da coffee a jiki ya ƙullace ni…. Nan ta bata labarin komai da komai tana kuka ta ɗaura