Showing 27001 words to 30000 words out of 36194 words
Chapter 10 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx
da cewa. “ Da nasan haka zai faru Wallahi Allah da banje neman aiki a company ba.”
Ita ma Meeman kuka take tana cewa. “ Ni banga laifinki ba Love, kuma ai komai da ya faru Allah shi kaɗai yasan me ya boye a tsakanin ku.”
Tana kuka ta ce. “ Tamkar karuwa fa ya ɗauke ni, ya mayar dani tamkar abinci.”
Jawo ta jikinta ta yi tana rarrashin ta, ta ɗaura da cewa. “ Da ciwo abun amma idan za ki iya komai mai sauƙi ne, ki cigaba da rayuwarki kamar komai bai faru ba, amma aiki kam a company ki bari ko ince mu bari, tun da har ya baki Atm din shi kin ga sai ki biya kudin Makaranta na part three sai ki cigaba da yi.”
Da sauri ta ɗago kai tana kallon ta. “ Wai na cigaba da yi ke kuma fa?.”
“ Nima ai Allah zai kawo.”
“ Yanda zanyi haka za kiyi.”
Murmushi Meemah ta mata tana cewa. “ Yanzu ya soyayyar Yaya Mansoor din a gurin ki?.”
Da mamaki ta ce. “ Wani Mansoor din?.”
“ Wanda kika sani.”
“ A’a babu soyayya kuma ni a rayuwata ai, an rushe min komai, abun da nake taƙama da shi an ƙarbe ta ƙarfin tsiya, ni yanzu maza ma kallon daya nake musu da ni…”
“ Kar ki sake faɗan irin wadan nan kalaman, idan bakya son Mansoor ai akwai Jameel.” Ta ƙarashe tana dariya.
Murmushi kawai Meerah ta mata tana cewa. “ Kin ga har an fito daga magariba bamu yi sallah ba.”
“ Ai na mai da kina off ne, dan nasan tare muke yi.”
“ Aa bana yi nikam kila ya chanza ya koma ƙarshen wata, bari na tashi nayi sallah.”
“ To bari naje gurin Yasmeen ko ta gama.” Da haka Meemah ta fice ita kuma ta shiga toilet dan ɗauro alwala, ta dan daɗe a toilet din tana tsaye duk tunanin duniya ya ishe ta, ga maganar Mama da ta mata wai ta mishi biyayya sai kace ubanta ko mijinta, ta gefe guda kuma har cikin ranta tana kewarsa amma idan ta tuna da cewa ita karuwarsa ce kamar yanda yake faɗa sai taji ba dadi.
Ganin tunanin babu abunda zai haifar mata ne yasa ta yi alwala tana fitowa, sallah ta gabatar tana addu’a sosai a ciki.
**************
INDIA / DALHI
**************
kwance yake akan makeken gadon shi suna video call da Ammy, duk damuwa ya bayyana akan fuskarsa, Ammy ce ta lura da hakan tana cewa. “ Babana ko akwai matsala ne.”
Shuru yayi ba tare da yace komai ba, sake tambayar sa ta yi yayi saurin firgita yana cewa. “ Meeyah!!!.”
Da mamaki Ammy ta ce. “ Wace ce ita Babana? Ƴar wace ce haka da ta rikita ka kake tunanin ta?.”
Shafa sumar kansa yayi yana cewa. “ Ammy sai da safe bacci nake ji, bye love you.” Da haka ya rufe laptop din.
Gyara kwanciyar shi yayi yana faɗawa duniyar tunani, ya dade a haka kafin ya tashi ya shiga yayi alwala ya dawo yana sallan nafila, sai kusan ƙarfe uku kafin bacci ya ɗauke shi, yana kwanciya ba da daɗewa ba aka kira sallan asuba.
Idanunsa duk bacci ya farka yayi alwala ya wuce masallacin dake ƙofar gidan shi, sai da alfijir ya fito kafin ya fito daga masallacin, kansa a ƙasa ya nufa ƙofar gidansa.
Buguwa yayi da mutum hakan yasa ya ɗago kansa yana kallon ta, hade rai yayi yana ja baya.
“ Beb.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ce ta faɗa tana masa murmushi.
Ta gefen ta yabi zai wuce, saurin rungume shi tayi ta baya cikin yaren turanci ta soma magana. “ Beb kasan yanda zuciyata yake min kuwa na rashin ka.”
Bantare ta yayi daga jikinsa yana magana a fusace cikin turanci shi ma. “ Keee!!! Ki yike kanki okay, banason hauka da gidadanci ba sonki nake ba ki fahimta!!!!.”
Da gudu ta nufa gidan dake facing din nashi tana kuka, tsaki yaja yana shiga gidansa, kallon security’s din yayi yana musu warning ⚠️ akan kar a bar kowa ya shigo, da haka ya nufa cikin parlon.
Ɗakinsa ya nufa yana ɗaukar wayansa ya duba agogo, 8:02am dot ya nuna kenan a nigeria 12:32pm, danna kan sunan da aka rubuta best choice yayi yana mannawa a kunne.
Da safe suna tashi Meemah ta kama girki, Yasmeen shara Meerah kuma wanke-wanke, kafin ƙarfe takwas duk sun gama kowa yayi wanka anzo cin abinci.
Ganin babu Mansoor ne yasa Meerah tashi tana cewa. “ Mama bari naje na kira Yaya.”
Murmushi kawai Mama ta mata tana gyaɗa kai, part din Mansoor ta shiga tana sallama, amsawa yayi yana fitowa daga ɗaki, murmushi ya mata yana cewa. “ Meemah gani ma fitowa ai.” Ganin Meerah ce yasa yayi shuru.
Kallon junan su suka tsaya yi na mintuna, a hankali ta janye idanunta daga nashi tana cewa. “ Dama abinci ne nazo kiranka.”
Shi ma dauke idanunsa yayi daga gare ta yana cewa. “ Muje to.” Da haka suka nufa parlon.
Abinci akaci kowa ya tashi Meemah ta tattare gurin, Mansoor ya nufa gurin aikinsa, Yasmeen ta shirya ita da Meemah suka nufa gidan kawarsu dake unguwar, ba yanda ba suyi da Meerah ta bisu ba amma tace sam babu inda zata je haka nan suka bar ta ba dan sun so ba.
Ɗaki ta shiga ta gyara ta hau kan gado ta kwanta, bacci ne ya ɗauke ta, guraren ƙarfe 12:32pm wayanta ya fara ringing, farkawa ta yi a dan razane tana ɗaukan wayan.
Ta cikin wayan taji ya sauƙe ajiyar zuciya yana cewa. “ Meeyah.”
Cikin magagin bacci ta ce. “ Na’am.”
Sauƙe wayan daga kunnen sa yayi yana duba sunan, ganin eh lambar ne yasa shi mannawa a kunne yana cewa. “ Bacci kike yi ne?.”
“ Uhm Baby.”
Da mamaki ya sake duba number kafin ya ce. “ Kina saka hijabin a gida?.”
“ Uhm uhm ni haka nake yawo.”
Murmushi yayi dan ya lura bacci ke sa take fallasa, hakan yasa ya fara cewa. “ Kin yi missing dina ne?.”
“ Eh sosai.” Ta faɗa cikin bacci.
“ To bani labari?.” Ya faɗa yana zama a bakin gado dan ya lura zaiji dadin hiran.
“ Ni ka dawo kawai.”
“ Kina kewa na ne?.”
“ Eh har da kwanciyan da muke yi....” Ware idanunta tayi da sauri, jin sautin murmushin sa yasa ta ce. “ Kaji me nace ne kake dariya.”
“ Aa babu abunda naji.” Kashe wayan ta yi tana tashi ta zauna a tsakiyar gadon, tagumi ta yi tana jin kunyar maganganun da tayi, kira ne ya sake shigowa wayanta, ganin shine yasa ta kashe wayan gaba daya tana jan tsuki.
Shafa sajen sa yayi yana murmushi kafin ya tashi ya watsa ruwa ya shirya cikin suit baki da fari, takalmi ya saka baki yana ɗaukar jakarsa ya fito, da sauri daya daga cikin driver dinsa ya ƙarba jakan yana nufan mota da shi, buɗe masa back site yayi yana shiga shi ma ya shiga yana tadawa, buɗe get akayi suka fita.
A haka su Meemah suka dawo suka same ta tayi tagumi, kallon junan su suka yi kafin Meemah ta isa gurin ta tana cewa. “ Love me kuma ya faru.”
Kallon ta ta yi tare da cewa. “ Nayi babban casting….
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
21 - 22 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝🤝
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*BOOK ONE*
*P.21 & 22*
A haka su Meemah suka dawo suka same ta tayi tagumi, kallon junan su suka yi kafin Meemah ta isa gurin ta tana cewa. “ Love me kuma ya faru.”
Kallon ta ta yi tare da cewa. “ Nayi babban casting.”
“ Na me kenan?.” Cike da fargaba ta tambaye ta tana kallon cikin idanunta.
Ganin Yasmeen tana dakin ne yasa ta mata maganar ido, gyada kai tayi tana cewa. “ Allah ya kiyaye gaba.” Ta fada tana dariya.
*Bayan sati biyu*
Sosai hankalin Meerah ya koma ga Makaranta, dan hutun da aka basu an dawo, taje ta cire kudin tayi registration ita da Meemah ta hada har da Yasmeen, da Mansoor yazo yi musu registration yaga sun biya, yayi mamaki sosai dan kusan duba dari hudu ne, amma wai sun biya kuma bai tambaye su ba dan ba gaskiya zasu fada ba sai dai ya bisu da addu’a.
Tun ranar da sukayi waya dashi ta cire sim din ta ajiye ta cigaba da harkan ta, sosai tayi kyau tayi haske abun har mamaki yake bawa su Meemah da Yasmeen, dan shi Mansoor sai dai ya bita da ido kawai yana ganin yanda take kara kyau, duk da kuwa kullum cikin hijabi take.
Yau ya kama Wednesday kuma suna da lecture daga karfe goma zuwa sha biyu, sauri sauri suka gama aikinsu suka fice daga gidan dukan su uku.
Meemah da Yasmeen gyale suka saka ita kuma ta saka hijab blue wanda ya haska farin fatarta da ya kara haske sosai, hira suke suna tafiya ita dai Meerah sai dai tayi murmushi idan na yi ne, idan kuma na shuru ne tayi, da haka suka isa bakin titi, mai adaidaita sahu suka tara suka fada masa inda zai kai su, da haka suka shiga yaja suka nufi bus stop.
Suna isa bus stop Meerah ta bashi kudinsa, Napep suka shiga su uku ya jasu suka tafi.
Kowa hanyar department nashi ya nufa, ita Meemah ta nufa Physiology department, Yasmeen kuma Computer science , Meerah kuma Law.
Sauri take dan baifi saura minti biyar a shiga ba, buguwa tayi da wata budurwa har ta watsar mata da takaddu.
“ Yi hakuri dan Allah sauri nake ban ganki ba.” Ta fada tana durkusawa ta fara tattare mata takardun ta mika mata.
Karba tayi tana mata murmushi tare da cewa. “ Bakomai Nagode.”
Murmushi Meerah ta mata tana k’ok’arin wucewa.
Budurwar ce ta dafa ta tana cewa. “ A wani department kike ne.”
“ Law.”
“ Ok ni kuma ina Computer science, sunana Laylerh.”
“ Ayya ni kuma Meerah.”
“ Wow suna mai dadi, sorry fa na cika ki da surutu ki tafi kar lecture ya wuce ki idan kika fito zamu hadu.”
Murmushi Meerah ta mata tana mai wucewa, ita kuma Laylerh ta tafi wajen zama ta zauna.
Tana shiga lecturer ya shigo, nan aka fara lecture bai barsu ba sai da suka yi kusan awa biyu da mintuna kafin ya fita.
Duk ta bi ta gaji ga yunwar dake dawainiya da ita, tashi tayi zata fita. “ Meerah Abdulrazak Alhassan.” Da sauri ta juyo dan ganin wani isheshen ne.
Kyakyawan saurayi ne wanda akalla bazai wuce ashirin da tara ba, dogo ne sai dai kuma ba fari bane, murmushi ya sakar mata yana isowa inda take tare da cewa. “ Ina ta miki magana tun last week shine kike min yanga ko, irin mun kusa gamawa din nan.”
Murmushi ta masa kafin ta ce. “ Ai kasan ana tests ne duk hankalina ya koma kan karatu, amma kayi hakuri.”
Kafada ya daga tare da cewa. “ Ya na iya, dole nayi hakuri dake ai muje ko.”
Fita sukayi daga hall din suna hira, cikin hiran ne yake ce mata. “ Meerah wai ina Meemah ne bana ganin ta 2days fa.”
“ Kuma yau tare muka shigo da ita ba.”
“ Haba dan Allah.”
“ Da gaske, kila tana ta wajen department na su.”
“ Meemah gidan surutu ba, nikam yaushe zan turo ne?.”
“ Waye zaka turo?.”
“ Magabata na mana, so nake ayi maganar gemu da gemu in yaso kina gaba Makarantar sai muyi bikin.”
Cak ta tsaya tana kare masa kallo, nan da nan ta hade rai tana cewa. “ Ko zanyi aure ba yanzu ba Alwan, sai na cika muradai na kafin nan.”
Kasa yayi da kansa yanda zai kalli cikin idanunta, kafin ya furta. “ Tare zamu cika muradin naki, idan ban aure ki ba Meerah to har abada bazan yi aure ba.”
Sauri kallon shi tayi, kai ya daga mata alamun eh abunda kika ji shi na fada. “ Banaso mutum ya cutu ta dalili na ne Alwan.”
“ Nasan bazan taba cutuwa ba inde ke ne.” Ya fada yana kallon hararan da Laylerh take masa, murmushi ya sakar mata zai yi magana ta karaso gurin da suke tana cewa. “ Kai kam ka boni, sai ace ai baya kula mata yanzu namiji kake kulawa ko.”
Sosa keya yayi yana cewa. “ Laylerh me ya kawo ki nan kuma?.”
Tabe baki tayi tana kallon inda Meerah take tana cewa. “ Gurin In-law nazo, dan kaima kasan idan kai ne bazan taba zuwa ba.”
Murmushi Meerah ta mata kawai, shi kuma ya ce. “ Waye ne In-law naki?.”
“ Mu nawa ka gani a nan da kake min tambayar iskanci?.”
“ Idan Meerah ce to na kai sadaki tun tuni.”
“ Allah tsinewa mai karya, kuma idan ban fadawa Big bro ba cewa ka zage shi.”
Saurin cewa ya yi. “ Laylerh kina yi kina tsoron Allah.”
“ Kama ce bana tsoron Allah kawai.”
“ Ban fada ba ni.”
Murguda masa baki tayi tana jan hannun Meerah da ta zama yar kallo suka bar gurin tana cewa. “ Kar ki biyewa yaran nan, dan ke matar Big bro ne.”
“ Ikon Allah.” Ta furta lokacin da suka zauna a karkashen bishiya.
“ Ni sunana Amina Junaid ya ga Marigayi Alhaji Junaid dala, sannan kanwa ga Most richest Man ina Kaduna Alyan Junaid Dala.”
Saurin kallon ta Meerah tayi zuciyarta na harba tara tara, nan taga kamannin su sak a fuskarta, muryanta har rawa ya fara gurin furta. “ Wani Alyan din?.”
“ Naga yana yin ki ya chanja da damuwa ne ko akwai wani abu ne?.”
Girgiza mata kai tayi tana kallon ta.
“ Alyan dai daya, dan nasan shine most popular a garin kaduna.”
Gyara natsuwar ta tayi tana cewa. “ Amma ya akayi bansan shi ba.”
Kallon kin raina min hankali Laylerh ta mata tana hade rai. “ Ni zaki cewa baki san Alyan ba, yanda sunan shi yayi tsaura a garin nan shine baki san shi ba.”
Tabe baki Meerah ta yi tana furta. “ Ban san shi ba nikam.”
Wayanta ta ciro daga cikin handbag din ta ta kunna ta shiga photos, photon da sukayi tare ta nuna mata tana cewa. “ Baki san shi ba?.”
Kallon kurilla take yiwa photon dan ko a mafarki ta tashi zata gane shi, saurin dauke idanunta tayi daga kan wayan tana tabe baki, murmushi Laylerh ta mata tana ta fara waka neman magana. “ Ta kamu na gane ta kamu, taga kyakyawa ta kamu sosai.”
“ Waye wai ya kamun ne?.”
“ Ni fa ban kira suna ba madam waka kawai nake.”
“ Ok.”
Hango Meemah tayi da Yasmeen da alama ita suke dubawa, hannu ta daga musu kafin duka karaso gurin nasu, kallon Laylerh Meemah tayi tana cewa. “ Kamar nasan fuskar nan?.”
Murmushi ta mata tare da cewa. “ Maybe za ki sani ko ta dalilin Yayana.”
“ Ayya ya school to?.”
“ Alhamdulillah.” Ta furta tana kallon Yasmeen. “ Yasmeen har an gama lecture din?.”
“ An gama ai kin ki shiga.”
“ Lecturer din ne kwata-kwata bai iya ba, yana yi yana face majina ina zan iya.”
Dariya suka yi dukan su. “ Allah fa haushi yake bani kawai.”
“ Lallai ai kuwa gwara ki dage dan ba haka ba kina cikin masu CO wannan karan.” Cewar Yasmeen.
“ Allah ma ya kiyaye.”
Suka hada baki gurin furta. “ Ameen.”
“ Zamu iya tafiya ai ko?.” Cewar Meerah tana tashi.
“ In-law wani unguwa za kuje?.”
“ Dukan mu ai gidan mu daya.” Cewar Yasmeen.
“ Haba, ai dama nace zan zowa Yasmeen tun da Oga baya kasar.”
Da sauri Meerah ta ce. “ Kina da aure ne?.”
Dariya ta mata tana cewa. “ Wanda na nuna miki shine ai mijin ko kina kishi ne?.” Ta fada tana daga mata gira.
“ Kai haba dai kishi kuma shi a suwa, wannan ne zanyi kishi akai.” Ta fada tana yin gaba, biyo bayanta suka yi Laylerh sai neman tsokana take wai jini yaja ta kaysa da yayanta, ita dai ko magana bata kuma yi mata ba.
Tafiya sosai suka yi kafin suka iso bakin get din Makarantar suna dan taba hira, Yasmeen ce ta ce. “ Yau babu mota ne Laylerh?.”
“ Yaya yace wai idan baza’a kai ni ba to bazan yi tuki ba, shiyasa naga gwara na rin ga hawa Napep kawai.”
Ita dai Meerah bin ta da ido kawai take, tana jin yanda take yaba yayan nata da kuma yanda take tsoron shi, tabe baki tayi tana jin haushin kowa.
Napep suka tara Laylerh ta hau suma suka tara wani suka tafi gida.
“ Kin ga yanda yake shishige