Showing 18001 words to 21000 words out of 36194 words

Chapter 7 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx

tsorace ranar kin dillanci, dan Allah ba azzalumin bawansa bane, kuma yanda kakeso na koma bazan taba komawa ba.”

Dariya yayi yana kama hannunta tare da cewa. “ Zo kici abinci dan na samu nawa lunch din anjima, babyn baby.” Ya faɗa yana kashe mata ido daya.

Damtsen hannunsa ta kama tana gantsarawa cizo, da sauri ya sake ta, da gudu ta fice daga ɗakin….

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

11 - 12 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*



*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

*(We stand together)*

🤝🤝🤝🤝

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.11 & 12*

Damtsen hannunsa ta kama tana gantsarawa cizo, da sauri ya sake ta, da gudu ta fice daga ɗakin tana dingishi, abun ka da wacce bata san yanda tsarin gidan ya ke ba, tana fita daga ɗakin ta kalla matakalan da zai kai ka down stairs, juya bayanta ta yi ta ga bai fito ba da sauri take taka stairs bibbiyu har ta sauƙo parlon.

Ƙofan parlon ta nufa da gudu zata buɗe, a rufe taji hakan yasa ta shiga bubbugawa tana kuka tana faɗin. “ Dan Allah wani ya taimake ni.”

Muryansa taji a bayanta yana cewa. “ Babu wanda zai iya taimakon ki.”

A tsorace ta juyo tana kallon shi, takowa yayi izuwa inda take yana cewa. “ Duk inda zaki shiga a faɗin duniyay nan sai na nemo ki, so no need ki nemi hanyay guduwa dan ba samu zakiyi ba, gida kuma zan kai ki amma ba yanzu ba.”

Gaban rigar shi ta cikume tana magana cikin ɗaga murya. “ Wai dan Allah me na maka ne? Me sa kakeso ka deɗanta rayuwata ne.”

Cire hannunta yayi daga gaban rigarsa yana cewa. “ Kay ki soma sabawa da cikume mijinki ba, ba dabi’a me kyau bane.”

“ Nabi dabi’a da gudu dan uban shi, mugu azzalumi kawai Allah ya isa tsakanina da kai, haduwa na da kai bai min komai ba, nayi dana sanin zuwa company ka da neman aiki, da ana komawa baya da na koma na goge wannan babin da duk haka bazata faru ba, mazina…”

“ Ya isa!!!.” Ya daka mata tsawa, da sauri ta ja baya tana kallon yanda idanunsa suka yi ja, har jijiyoyin kansa sai da suka tashi.

Murya a dake cikin tsawa yake cewa. “ Kay ki kuma sake aibanta ni da mugayen kalamai iyin wannan, ni ba tsayanki bane sannan ke ƙanwata ce ta kusan uku, kay ki ga ina miki wasa ki ɗauka ni bani da hankali, ni dabba ne da zan ɗauko mace in yinga kwanciya da ita ba taye da ta zama muhayyama ta ba, ko dan ina kiyan ki da kayuwata sai ki ɗauka hakan ne? ki sake zama kiyi tunani Idiot kawai.” Ya ƙarashe maganar yana nufan upstairs da sauri.

Da ido ta bishi tana zamewa ta zauna a gurin, kamar mutum mutumi haka ta koma, take jikinta yayi wani mugun sanyi taji kunyar da ta rasa gane kanshi yana sauƙar mata.

Ta dade zaune a gurin tana tunanin da ba kai, kafin ta tashi sulum-sulum tana nufan upstairs din, ɗakin farko ta murɗa taji a rufe, ɗaki na biyu taje ta murda taji a buɗe.

Shiga ta yi kanta a sunkuye, yana zaune a kan gujera yana danna laptop amma kallo daya zaka masa ka gane hankalin shi baya kan laptop din kawai dannawa yake.

A bakin ƙofar ta tsaya ta yi shuru, ba tare da ya ganta ba ya ce. “ Ga abinci idan za ki ci.”

Kallon inda basket din yake ta yi, kafin ta dube shi ganin baya kallon ta ne yasa ta nufa gurin tana ɗaukar basket din ta ajiye a ƙasa, ita ma zama ta yi tana ciro food flakes din, spaghetti ne da miyan vegetables yasha nama ga kamshin dake tashi.

Taɓe baki ta yi tana rufewa kana ta miƙe tsaye, duk abunda take yi yana kallonta ta witsiyar ido hakan yasa ya ce. “ Ba za ki ci bane?.”

“ Bana cin alaiyaho.”

Sakin baki yayi yana kallon ta da mamaki, wai bata cin alaiyaho ikon Allah kafin ya ce. “ Miƙo min ni zanci ai.”

Ɗauka ta yi ta kai mishi tana juyawa ta koma kan gado, hawa tayi tana jan bargo ta rufe har kanta.

“ To me zaki ci?.” Ya tambaye ta.

Mantar da shi ta yi tana sake rufe kan ta me kyau, yasan taji amma sai ya kuma maimaitawa, nan ma mantar dashi ta yi, hakan yasa ya tashi ya ɗauki laptop nashi da basket din ya fice daga ɗakin, tana ji ya saka key.

Buɗe fuskarta ta yi tana kallon ƙofar, tashi ta yi ta nufa gurin window tana kallon tsuntsayen.

*Bayan kwana hudu*

Meemah ce ta shigo part din Mansoor da waya a hannunta tana cewa. “ Yaya Mama tana maka magana.” Ta miƙa masa yana zaune akan three seater.

Waya suka yi da Mama kafin suka yi sallama yana miƙa mata wayanta tare da cewa. “ Ku de idan baku bawa mutum wahala ba, bakwa jin dadi.”

“ Hhh ai haka zaka ɗaure Yaya.”

Hararan wasa ya mata yana cewa. “ Bari na shirya sai muje.”

Waro ido waje ta yi tana cewa. “ Yaya Mama fa bata ce kaje da ni ba.”

“ To sai karki bi umarni na tunda ni nace muje.”

“ Hhh na isa wa zai na siyamin ice cream to.”

“ Oho fa.” Ya faɗa yana shigewa dakinsa, tashi ita kuma tayi tana fita ta koma bangaren su, murmushi ta yi lokacin da ta tuna da Meerah a fili ta ce. “ Allah ya bayyanar dake Love, Allah yasa kina hannu na gari.”

Da Ameen Yasmeen ta amsa mata, murmushi ta mata tana cewa. “ Kin ji wai Yaya ne yace na rakasa unguwa.”

“ Chabb ki ce yau anaji da ke, nifa ranar nan da yayi kyau nace zan rakasa ko a matsayin mai riƙe masa jaka ne amma ya ce wai budurwarsa zata ji haushi, kuma fa bayi da budurwar amma haka inaji ina gani ya hanani zuwa.”

Dariya Meemah ta mata tana cewa. “ Bari na saka abaya akan wannan rigar kawai.” Ta fada tana ciro brown din abaya irin na Meerah sak ta saka.

Yasmeen ce ta ce. “ Sai kika tunamin da Meerah, da irin kayan nan aka ɗauke ta.”

Murmushi ta yi tana kallon abayar tana cewa. “ Har faɗa muka tabayi akan abayar nan, wai nata na saka nace mata nawa fa na saka, sai da ta duba cikin kayanta ta gani kafin ta yarda ba nata na saka ba, kinsan yanda take son abayan nan kuwa.”

“ Allah sarki, Allah ya kubutar da ita.”

“ Ameen.”

Muryan Mansoor suka ji daga waje yana cewa shi fa zai tafi, da sauri Meemah ta fito tana yiwa Yasmeen sallama.

“ Ce miki akayi wai shan ice cream zamu je yi ne?.” Murmushi kawai ta masa, da haka ta shiga ya bude get yana fita da motan.

Suna tafiya suna hira har suka iso wani super market, parking ya yi yana fitowa ita ma ta fito, kallon motan dake wajen yayi yana cewa. “ Mutumin yana nan kenan.”

Ita dai bata ce komai ba, da haka suka jera kwanin burgewa suka nufa cikin super market din.

Gurin kayan sawa na mata suka nufa, kallon ta yayi yana cewa. “ Ki dibi abun da zai miki.” Gyaɗa masa kai ta yi zata juya, karaf suka haɗa ido da shi.

Zuciyansa ne ya tsinke, da sauri ya iso gurin da take zai yi magana ta riga sa cewa. “ Sir ina wuni.”

Muryan ne yaji ba nata ba hakan yasa ya gane cewa yar biyun ta ne, murmushi ya ƙwaƙulo yana daurawa akan fuskan sa tare da cewa. “ Lafiya, ya aikin?.”

Jin tana magana da wani ne yasa Mansoor juyowa, murmushi yayi yana cewa. “ Ai naga motan ka Bobo, nasan kana ciki.”

“ Wato samin ido kake yi?.” Ya faɗa yana bashi hannu suka gaisa.

“ Na isa na sawa Mama’s Boy ido, ai sai a ɗaure ni.”

“ Tsaf ma kuwa.” Ya faɗa yana dariya, wanda yasa dimple nashi duka biyu lotsewa.

“ Me ya kawo ka nan.”

“ Uhm wata nazowa siyayya fa.”

Kallon bangane ba Mansoor ya masa, gira ya ɗaga masa yana cewa. “ Abun da kaji shi na ce.”

Dariya yayi yana cewa. “ Ai ina son ƙarin bayani ne.”

“ Babu abunda zaka ji kuwa.”

Meemah ce tayi murmushi tana cewa. “ Yaya bari naje na fara.”

Gyaɗa mata kai yayi yana kama hannun Alyan.

“ Please duk abunda kika ɗauka ya zama bibbiyu kuma iyi daya.”

Mansoor ne ya ce. “ Komai fa Bobo, komai fa.”

Hararan shi yayi yana cewa. “ Komai ina nufin komai har da abun ku na cikin nan.” Da sauri Meemah ta tafi tana cewa to.

Dariya Mansoor ya masa, shi kuma ya harare shi yana cewa. “ Ba kai dan iska ba, ai gwaya na fayyace maka komai.”

“ Ai nasan halinka ne.”

Waje suka samu suna zama, Mansoor ya ce.” Bobo wa ka samu ne?.”

Dan sosa keya yayi yana tari, murmushi kawai Mansoor yayi yana cewa. “ Ba gaskiya zaka fada ba gwara kawai kayi shuru.”

“ Ni nace maka.”

“ Bobo tun muna yara fa muke tare, so babu halinkan da ban sani ba yanzu,,, ni ba wannan bama dama inaso na ganka ne.”

Gyara zama yayi yana cewa. “ Gani ai yanzu.”

Numfashi Mansoor ya sauke yana cewa. “ Akan case din twins din Meemah ne wato Meerah.”

Da sauri zuciyan Alyan ya tsinke, cikin dakewa ya ce. “ Uhm me tayi.”

“ Kasan ta bata last 4 days.”

“ Inna’illahi a garin ya?.”

“ Daga fita fa wai zata siya biscuit shi kenan ba ita ba labarin ta.”

“ Allah sarki, In Sha Allah tana hannun na gari.”

“ To Allah ya sa.”

Da sauri ya ce. “ Ameen.” Cigaba da magana Mansoor ya yi yana cewa. “ To yanzu dama inaso ka yiwa IG magana ne ko zasu ɗauki maganar da serious.”

“ To zan masa.” Alyan ya faɗa, cikin ransa kuwa cewa yake ‘ Ai ni ne IG din’.

“ Kasan Jameel da yaji labari kuka yazo yake min.” Mansoor ya faɗa yana dariya, dan shi har yanzu dariyar Jameel yake.

“ Ai Jameel da hauka 5 & 6 ne, ni cewa nayi zamu kaisa gurin ka da Eyshey ai.”

“ Yawwa ranar fa Eysher ta kira ni, wai ta ganka da mace.”

Da sauri ya ce. “ Subhanallah, A’uzubillahi minal shaidanin rajim wai yaushe Eyshey ta koma magulmaciya.”

Dariya Mansoor ya masa yana cewa. “ Wai na maka faɗa ka mayar da ƴar mutane gidan su, wai ta same ta ma ba lafiya, ni kuma lokacin muna jimamin rashin Meerah sai ban ɗauki maganar serious ba, and by the way nasan halinka.”

Shi dai bai ce komai ba sai idon da yake bin Mansoor da shi.

Meemah ce ta fito da abun saka kaya a ciki, ko wanne ta cika dam da kaya.

Miƙewa suka yi a tare suna isa gurin ta, murmushi ta musu tana cewa. “ Na gama kuma ko wanne iri daya ne.”

Murmushi Alyan ya sakar mata yana cewa. “ Har da su sleeping dress kin diba?.”

“ Eh na ma fi saka su.”

“ Ok.”

Gurin da ake biya suka nufa, akayi calculating Alyan ya bata Atm dinsa aka cire kudin.

A leda aka zuba masu aikin suka tattara suka nufa mota da shi, suma suka fito Meemah na masa godiya.

“ Bobo sai mun hadu kuma, dan Allah ka ɗauki zancen chan serious.”

“ Ai baka da matsala Man, za kaji feedback.” Da haka kowa ya shiga motansa, su sukayi hanyar unguwar Dosa, shi kuma yayi hanyar unguwar Rimi.

A hanya sai da ya tsaya ya sayi kayan ciye ciye, kafin ya isa gidan, ko da ya shigo a parlon ya bar su kayan yana nufan ɗakin da leda a hannun shi.

Saka key yayi yana buɗewa kafin ya shiga da sallama a bakinsa.

Tana kwance a ƙasa da tayi sallan azahar ta kwanta, isowa gurinta yayi yana ajiye ledan kafin ya saka hannun yana ɗaukar ta ya mayar da ita kan gadon.

Buɗe idanunta tayi tana zuba masa, kallon junansu sukeyi kusan second’s ashirin, matso da fuskan shi yayi nata har numfashin su yana haɗuwa.

Bakinsa ya zura cikin nata yana lalubo harshen ta ya shiga sucking, runtse ido tayi tana amsar sakon da yake kai mata, hannunsa ya ɗaura kan bob’s din yana murzawa.

Saurin ture shi ta fara tana k’ok’arin tashi, amma ya hana ta tashi saboda ya sakar mata nauyin shi duka.

Kuka ta fashe masa tana ture shi, barin ta yayi yana komawa gefe.

“ Ni ka mayar dani gida dan Allah, banason wannan rayuwar.”

“ Shuu banason kukan ki.” Ya faɗa yana tashi ya zauna, jawo ta jikinsa yayi yana cewa. “ Zan mayay dake amma sai kin kwantay da hankalin ki, kinyi jiki kafin zaki koma.”

“ A yanda kake min din ne zanyi jiki? Ka ɗauke ni tamkar baiwa wacce bata da inci.” Tayi maganar tana k’ok’arin janye jikinta daga nashi.

Lumshe ido kawai yayi, kafin ya tashi yana ɗaukar ta kamar wata baby ya daura ta a kafadarsa, cilli ta fara da kafan yana son sauƙa, ɗaukar ledan yayi yana fita daga ɗakin.

Down stairs ya sauƙo yana dire ta akan two seater, turo baki gaba tayi tana kallon lodin kayan dake ledan.

Zama yayi yana ajiye ledan hannun shi tare da cewa. “ Ga shi a nan kam bazaki yasa abun ci ba.”

Ɗaukan ledan tayi tana budewa. “ Roasted fish ne, sai su chocolate da ice cream.” Murmushi ta sakar tana zaman cin abinci.

Ture kifin tayi a gefe tana ɗaukar ice cream, sha kawai take tana buɗe wani, sai da ta shanye roba biyu manya kafin ta ɗauki wani chocolate 🍫 tana fara ci.

Duk abunda take yi yana kallon ta ta kasar ido, murmushi kawai yayi har ta gama ciye-ciyen ta, kafin ta ce. “ Na gama.”

Buɗe ido yayi yana gyara zama, kana ya ce. “ Ga kayakin ki, iyi daya ne da twins naki.”

Da sauri ta tashi ta isowa gurin shi, nan da nan hawaye ya cika mata ido. “ Me ka mata, Wallahi idan ka cutar min da ƴar uwata kamar yanda ka cutar dani sai na kashe ka.”

Da mamaki yake kallon ta, ‘ kaji yayinya da karfin hali’ ya faɗa a zuciyarsa, kafin ya ce. “ Ni din mugu ne?.”

“ Ai kai a mugayen ka samu result…

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

13 - 14 *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*



*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

*(We stand together)*

🤝🤝🤝🤝

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.13 & 14*

Da mamaki ya ke kallon ta, ‘ kaji yayinya da ƙarfin hali’ ya faɗa a zuciyarsa, kafin ya ce. “ Ni ɗin mugu ne?.”

“ Ai kai a mugayen ka samu result ko ince certificate.”

Yi yayi baiji mai ta ce ba, ya chanza maganar da cewa. “ Je ki gwaɗa ko zasu miki.”

“ Bazan saka ba.”

“ Ok ki ciyemin nawa in yaso sai kiyi yawo a haka.”

“ Shi ma bazan yi ba.”

Tashi tsaye yayi yana ɗaukar ta cak, ya nufa upstairs da ita a kafaɗarsa, hakori tasa tana gantsara masa cizo, ba tare da ya ce komai ba ya buɗe ɗakin yana shiga ya saka key.

Sauƙe ta yayi yana nufan bathroom ya shiga, ita kuma ta zauna a kan sopa tana hura hanci, wanka yayi yana fitowa ɗaure da towel, saurin kau da kanta tayi tana miƙewa tsaye.

Matsowa dab da ita yayi har suna shaƙar numfashin juna, matsawa tazo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login