Showing 3001 words to 6000 words out of 36194 words

Chapter 2 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx

/>
“ Ƴar nan karki min rashin kunya, ko baki gane ni bane.” A cewar mutumin yana ɗaga murya.

Kallon up and down ta masa tana cewa. “ Ba Malam Zubairu bane mai gida.”

“ Ashe kin gane ni.”

“ Sosai kuwa, yau kuma da wani rashin mutuncin ka dawo.” Ta yi maganar tana duban gardawan dake gefen shi tsaye su huɗu.

Jin shuru har yanzu Meerah bata shigo ba ya sa Meemah tashi ta saka hijab sannan ta fito. Ganin mai gidan hayan da suke ciki ne ya sa Meemah cewa. “ Baba lafiya dai ko.”

“ Zuwa nayi ku fita min daga gida na.”

A kiɗime Meemah ke cewa.” Baba me muka yi kuma? Ka rufa mana asiri dan Allah.”

“ Idan ba za ku fita salin alin ba, zan saka gardawan nan su fitar da ku ta ƙarfin tsiya.”

Ɗurkusawa ƙasa Meemah ta yi tana cewa. “ Ka rufa mana asiri dan Allah, ina zamu je da yamman nan idan ka kore mu.”

“ Wannan kuma ku kuka jiyo, kai dalla shiga ku ciro duk kayan dake gidan.” A cewar Zubairu yana nuna gardawan da suke tsaye.

Bangaje Meemah suka yi suka nufa cikin gidan, murmushi Meerah ta yi tana cewa. “ Me na kuka kuma Sis.”

“ Meerah koran mu fa akayi daga gidan, ina zamu je ki ke tunani.” Cikin kuka Meemah ke faɗan hakan.

Goge mata hawayen fuskarta ta yi tana cewa. “ Kar ki damu, ko kin manta Allah ne gatan mu.”

“ Amma Meerah ai…” Saurin rufe mata baki ta yi tana girgiza mata kai.

Matsawa gefe suka yi, aka fara wurgo musu da kayan su waje, duk mutanen da zasu wuce sai sun bada hakurin akan a bar su zuwa gobe, amma Malam Zubairu ya rufe ido ya ce ba’a gidan shi zasu kwana ba.

Sai da aka gama cire kayan su tas a gidan, aka dasa ƙwaɗo a ƙofar, kowa ya watse gurin ya rage su biyu, ga shi lokacin ana kiran sallan isha.

Ganin yanda Meerah ke rawan sanyi ne ya sa Meemah tashi da wuri ta ɗauko bargon su, rufe mata jikinta ta yi tana cewa. “ Ina ki ka saka inhelan ki.”

Cije labba ta yi tana cewa. “ Yana handbag dina.”

Ɗauko mata ta yi tana saka mata a baki, a hankali ta ja tana ɗaura kanta a kafaɗar Meemah.

Sun dade a zaune a gurin kafin Meerah ta tashi tana cewa. “ Kin ga dare yana yi, kizo mu nemi inda zamu kwanta zuwa gobe, kinsan akwai barayi da ƴan shaye-shaye.”

“ To Meerah ina zamu je?.”

Murmushi ta yi tana kama ta, kana ta ce. “ Muje school mu ƙwana, mu ɗiɓe kayan sawan mu da wani abun buƙatar mu muje, kinga dama katifar ba namu bane shi ya sa bai fito mana da shi ba, iya kayan mu kawai ya watso mana.” Sai kuma ta dafe kanta tana cewa. “ Wallahi na gaji da surutun nan.”

“ Sorry.” A cewar Meemah, kafin suka shiga tattare kayakin su, mai adaidaita sahu suka tara, suka zuba kayakin su a ciki kafin suka hau.

Ƙwatance Meemah ta masa inda zai kai su, wato unguwar Dosa, a ƙofar wani gida suka tsaya, ta ciro dari uku ta basa, ya ciro musu kayakin su kafin yaja machine nasa ya bar gurin.

Kallon juna suka yi kafin Meemah ta ce. “ Mu ajiye kayan mu sai mu wuce hostel mu ƙwana.”

Gyaɗa kai kawai Meerah ta yi saboda ciwon kan da ya ke damunta, surutun da tata yi ne ya saka mata ciwon kai.

Tattare kayan suka yi suna dosan cikin gidan da sallama.

Wata budurwa ce ta fito daga ɗaki tana amsa sallaman nasu, turus taja ta tsaya tana kallon su da mamaki, kafin ta iso gurin su tana cewa. “ Me ya faru na ganku haka?.”

Jiki a sanyaye Meemah ke cewa. “ Ya kore mu daga gidan ne.”

“ Inna’illahi wa’inna illahi raji’un, me kuka masa da zai kore ku?.” A cewar budurwar.

“ Yesmeen bamu san me muka yi ba, haka kawai ya kore mu ko notice babu.” Meemah ta faɗa kamar zata yi kuka.

Rungume ta Yasmeen ta yi tare da cewa. “ Kar ki damu ƙawata Allah yana tare da ku a ko da yaushe.” Kana ta ɗago tana duban Meerah da ta dafa kanta dake sara mata, ƙarɓan kayan hannunta din ta yi tana cewa. “ Ku shigo ciki, Mama suna nan.”

Da haka suka nufa cikin parlon bayan sun ajiye kayakin su a ɗakin Yasmeen.

09027308227 chart only

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

3- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*



*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

________________________________

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

‎Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP

___________________________________

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

____________________________________

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

*(We stand together)*

🤝🤝🤝

___________________________________

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.3*

Da haka suka nufa cikin parlon bayan sun ajiye kayakin su a ɗakin Yasmeen.

Gaishe da Mahaifiyarta suka yi suna gaishe da Yayanta Mansoor, kafin suka samu guri suka zauna, nan Meemah ta basu labarin abunda ya faru, da koran su da ya yi daga gidan.

Sosai suka tausaya musu, cikin taushin murya Mansoor da tun da suka shigo idanunsa ke kansu ya ce. “ Nikam waye ce acikin ku Meerah din?.” Ya ida maganar yana bin su da ido.

Murmushi Meemah ta yi yayin da Meerah ta faki idon Mama tana wurga masa harara.

Ai tun kafin a bashi amsa ya ce. “ Wancan mai katon kai din ne Meerah, daga ganin irin kallon da ta mun.”

Dariya Yasmeen ta yi tana cewa. “ Kai Yaya har kaga kallon da ta maka?.”

“ Ke dai bari ni naga abunda aka min.” Ya yi maganar yana danna waya.

Mama ce ta dube su tana cewa. “ Sai mu zauna da ku a nan har kuyi aure ko?.” Ta fad’a tana faɗaɗa murmushinta.

Ba shiri suka ɗago ido suna kallon ta fuskarsu ɗauke da mamaki, dan ko kaɗan basu zaton hakan ba, cike da farin ciki Meemah ke cewa. “ Mun gode sosai Mama Allah ya saka.”

“ Me na godewa kuma, bana son shirme fa, yara ai na kowa ne, baka san baiwar da Allah ya yi wa kowa ba, saboda haka kar ka raina mutum ko kaƙi taimaka masa.”

Jinjina kai suka yi Meerah na buɗan baki cikin rashin son magana irin nata ta ce. “ Mun gode Mama.”

“ Ai badan ke aka taimakawa ba, da iyayin naki, wani wai Mama mun gode.” A cewar Mansoor yana ƙwaiƙwayan muryan ta.

Dariya Meemah da Yasmeen suka yi, ita kuma ta haɗa rai tana jefa masa harara ta ƙasa, ai kuwa karaf suka had’a ido, cike da mamaki yake cewa. “ Wai ni ki ke harara ƴar nan? Ka duba fa yarinya karama da rashin kunya.” Yana nunata ya ke maganar.

Mama ce ta harare shi tana cewa. “ Wai kai Mansoor ina ruwanka da yarinyar nan? Karka takurawa yarinya mana.”

Taɓe baki ya yi yana tashi zai fita ya ce. “ Ai muna gidan da ita sai na koya mata tarbiya.”

Harara tabi bayansa da shi har ya fita daga parlon, kafin ta dube Yasmeen tana cewa. “ Dan Allah wanka nake son yi.”

Da sauri Mama ta ce. “ Akwai ruwa a hitter, maza tashi ki haɗa mata na lura bata jin dadin jikinta.”

Tashi Yasmeen ta yi tana fita daga parlon Meerah na mara mata baya.

Kana Mama ta dube Meemah tana cewa. “ Meerah ba lafiya ne?.”

Fuskarta ne ya koma na damuwa, cikin yanayin rashin walwala take cewa. “ Ɗazu ne da sanyi ya buge ta asmanta ya tashi, ta shaka Inhela ma amma nasan zuwa anjima sai ya dame ta, kuma yanzu tana cewa zata yi wanka sanyi zai sake shigar ta ne.”

Tashi Mama ta yi tana cewa. “ To bari mu tokare tun kafin dare ya yi.” Da haka ta fita daga parlon tana kiran Mansoor a waya.

Biyo bayan ta Meemah ta yi tana wucewa ɗakin da suke.

Tana shiga taga Yasmeen zaune a bakin gado tana danne-danne a waya, zama itama ta yi tana ciro wayanta ta fara dannawa.

Suna haka Meerah ta fito tana attishawa tare da rawan sanyi tana jawo numfashinta da kyar, tashi Meemah ta yi da sauri tana rike ta, zaunar da ita suka yi a bakin gadon suna rufe ta da bargo.

Kafin Yasmeen ta yi waje dan kiran Mama.

A tare suka shigo da Mansoor wanda Mama ta kira shi ya zo ya duba Meerah, da sallama ya shigo bayan su Mama sun fara shiga, amsawa suka yi ya ƙaraso gurin gadon.

Ta rufe jikinta da bargo sai karkarwa take yi, ganin ya tsaya yana kallon ta ne yasa Mama cewa. “ Kai duba ta zaka yi fa bawai cewa aka yi kazo kana kallon ta ba.”

Saurin kafsewa ya yi tare da cewa.” Mama ina nazartan yanayin ta ne.” Kafin ya fita daga ɗakin, bai daɗe ba ya dawo hannun shi ɗauke da wani ƙaramin ket.

Matsa masa suka yi ya zauna a bakin gadon yana ciro allura, bayan ya had’a komai ya tashi yana duban su Yasmeen ya ce. “ Kuzo ku rike ta.”

Mama ce ta ce. “ Me na rike ta kuma sai kace wacce zata gudu.” Kafin ta zo tana jan bargon da Meerah ta rufu dashi daga fuska, idanunta a rufe suke kuruf sai nishin da take fitarwa da sauri-sauri.

Hannu ya kai bayanta yana k’ok’arin mata alluran, duk da tana jin ciwon hakan bai hana ta buge hannunsa ba daga jikinta.

Rike hannun ya yi tsam yana soka mata alluran ba tare da ya ɗaga bargon da ta rufu da shi ba.

Kuka ta fashe da shi tana magana ƙasa-ƙasa. “ Allah ya isa mugu kawai.”

Dariya Yasmeen ta yi tana duban Mansoor wanda ya yi suman tsaye yana kallon Meerah, kafin ya girgiza kai yana tattare kayan shi ya fice daga ɗakin.

WASHE GARI

Karfe bakwai ya musu a company, tana zuwa PA ta bud’e mata office din.

Duk da yanda jikinta yake mata ba dadi, hakan bai hanata yin aikin ba, before 8 o’clock ta gyara office din ta yi mopping ta gama komai ta koma ta zauna a seat din da suke gefe.

Bakinsa ɗauke da sallama ya shigo office din, yana aiyana kalan rashin mutuncin da zai mata idan bata zo ba.

Tura ƙofar ya yi yana juyowa, idanunsa ne suka sauƙa akan ta, cike da mamaki yake kallon ta, dan bai taɓa tunanin zata zo ba.

Hade rai ya yi yana kau da kansa ya nufa gurin seat ya zauna, ajiye jakar hannunsa ya yi yana ciro laptop daga cikin jakar, kana ya buɗe yana fara dannawa.

Muryanta can ƙasa irin na marasa lafiya ta ce. “ Good morning Sir.”

Ɗagowa ya yi ya dube ta, kafin ya cigaba da aiki bai kula ta ba.

Sun dade a haka babu wanda ya yiwa wani magana, sai bata fuska Meerah take tana cika tana batsewa, chan da zaman ya isheta ta miƙe tsaye zuwa gurin shi tana cewa. “ Malam zan iya tafiya? Naga na gama maka aiki ai.”

Ɗago da kansa ya yi yana ganin yanda ta tsaya masa akai kamar wacce take binshi bashi, kafin ya bud’e baki a hankali yana cewa. “ Malama haka ake yin aiki?.”

Harara ta watsa masa ta ƙasar ido, kana ta kama kugu tana cewa. “ Wani aiki ne ban maka ba?.”

“ Where is my coffee?.” Ya ida faɗar hakan yana zuba mata sexy eyes na shi.

Da sauri ta kau da kai tana cewa. “ Bansan inda yake ba.”

“ Ok.”

Juyawa ta yi ta nufa hanyar fita kamar zata faɗi, a gadarance yake cewa. “ Kuɗin ki ne zai yi kuka, so if u like go….

Anjima zan sake yin wani update, dan wannan yayi kadan.

09027308227 chart only

*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

4- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*

_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny_

*STORY & WRITTEN*

*BY*

*FATIMA ISA MANU💐*

*( DR TEEMAH)🦋🕊*



*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*

________________________________

Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T

Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP

___________________________________

*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️

(J.W.A)

_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*

____________________________________

*DIAMOND 💎 STAR ⭐*

*LADIES🧝‍♀️🧝‍♀️🧝‍♀️*

*(We stand together)*

🤝🤝🤝

___________________________________

*GARGADI*

Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.

*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*

*P.4*

Juyawa ta yi ta nufa hanyar fita kamar zata faɗi, a gadarance yake cewa. “ Kudin ki ne zai yi kuka, so if u like go.”

Tunawa da maganar da Meemah ta faɗa mata tayi, da sauri ta ce. “ Dan Allah ka taimaka muna buƙatar kudin ne, tun da na gama maka aiki ka barni na tafi bani da lafiya ne.” Ta faɗa cikin sanyin murya da yanayin rashin jin dadi a tattare da ita.

Wani shu’umin murmushi ya saki wanda idan baka lura ba, ba za ka taɓa tunanin ya yi ba.

Janyo wani ƙaramin takarda ya yi ba tare da ya dube ta ba, ya yi rubutu yana ɗagowa ya dube ta tare da cewa. “ Uhm.”

Ba tabi ta kansa ba, dan yau kawai magana take saboda ba za ta iya wani faɗa ba tsabar ciwon dake damun ta, takowa ta yi zuwa gabansa ta sa hannu ta karba takardan.

Buɗewa ta yi tana kallon, da mamaki akan fuskarta ta dube sa da sauri tana cewa. “ 100k ?.” Sai ta kuma duba takardan ta sake dagowa ta dube shi tare da cewa. “ Me zanyi da shi?.”

“ Kiyi sadaka da shi idan kin ga dama.” Ya faɗa yana danna laptop din gaban shi.

Haɗe rai ta yi tana murguda masa baki, kana ta kuma cewa. “ Thanks.”

“ Da ki ka gama muyguda min baki kenan?.”

Shuru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Cigaba da magana ya yi ba tare daya gan ta ba. “ Office din accounter za kije ya baki kudin, and buy medicine for ur health, and before u go make sure u bring some tea for me.”

Gyaɗa masa kai ta yi ta juya zata fita. “ Ga kitchen fa Madam.” Ya nuna mata wani ƙaramin ƙofa da idan baka lura ba zaka ce wani toilet ne.

Ajiyar zuciya ta sauƙe kafin ta juya ta nufa kitchen din, babu wani kayan tarkace a ciki daga gas sai tukunya da kayan shayi da kwalin indomie.

Sauri-sauri ta yi ta haɗa masa tea din duk da irin hajijiyar da yake k’ok’arin dibar ta, tana gamawa ta fito hannunta rike da tray ta ajiye masa a kan table, kana ta jiyo zata masa magana suka haɗa ido.

Murmushi ya sakar mata yana cewa. “ You can go.” Ya faɗa yana nuna mata hanyar fita.

Chan ƙasa-ƙasa ta ce. “ Thanks.” Tare da juyawa ta fice daga office din tana rufe ƙofa.

Da harara PA ta rakata tana jan dogon tsaki, ba shiri Meerah ta juyo tana zuba mata lulu eyes din ta wanda hakan yasa PA yin shuru tana cigaba da aikin ta.

Ƙwafa ta yi tana juyawa ta fice, duk da bata jin dadin jikinta taso ace PA ta kuma tanka mata dan sai taga mai tsaya mata a garin nan.

Tana tafiya tana harare harare ba tare da ta ankara ba ta bangaje mutum, saurin dafa goshin ta ta yi tana ɗagowa ta kalle shi.

“ Kina tafiya bakya lura da hanya.” Taji sauƙar muryansa a kunnen ta.

“ Ai ba laifi na bane, kai ma kana tafiya baka ganin hanya ne ai.” Ta mayar masa da amsa tana wucewa ta gefe.

Sakin baki ya yi yana kallon ta har ta bacewa ganin sa, Jijjiga kai kawai ya yi ya nufa office nashi; yana buɗewa ya ganta zaune tana daddanna laptop, da mamaki ya juya yana kallon hanyar da Meerah ta bi kafin ya juyo yana kallon Meemah.

Dago ido tayi da zummar kallon waye ne, karaf suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login