Showing 6001 words to 9000 words out of 36194 words
Chapter 3 - Ba Kai Nake So Ba Complete Hausa Novel By Fatima Isa Manu.docx
had’a ido, miƙewa tayi tsaye tana cewa. “ Welcome Sir.”
“ To idan ke kina nan ita kuma wancan wacece?.” Ya faɗa a ƙaƙare.
“ Waye kuma Sir?.”
Nuna hanyar ƙofa ya yi yana cewa. “ Me kama dake na gani yanzu fa a waje.”
“ Bani bace ai, ina ga Meerah ka gani.”
“ Ku biyu ke nan?.”
“ Eh.”
Murmushi kawai ya yi yana zama a seat nashi, kafin ya dube ta yana cewa. “ Ke kuma baƙa ita fara, amma daga gani ta fiki iya mutumci da hankali.”
Bata ce komai ba sai murmushin da take yi kawai, cikin ranta kuwa cewa take. ‘ Bata tafka maka rashin mutunci bane, amma ina Meerah ina hankali ai ko haɗuwa basu tabayi ba.’ Katsai mata zancen zucin yayi ta hanyar yin maganar da ya kusa daskarar da ita tsaye.
“ Inaso zan aure ta.”
Zama tayi ba shiri akan seat dinta tana sakin baki ganin yanda yake juyi yana murmushi, kamar wacce bataji me yace ba ta ce. “ Sir me kace?.”
“ Aureeeen ta zanyi…”
“ Wa zaka auya?.” Suka tsinkayi muryansa a bakin ƙofa.
Bayan ta fita daga company bata tsaya ko ina ba sai gidan su Yasmeen wanda yanzu za’a iya kira da gidan su.
Da sallama a bakinta ta shigo, shuru kake ji alamun ba kowa, direct ɗakin Yasmeen ta wuce ta fara rage kayan jikinta.
Bayan ta cire kayan jikinta ne ta ɗaura zani, zama tayi a bakin gadon tana miƙa hannu ta ɗauki maganin da Mansoor ya kawo mata yau da safe, ruwan dake kan bedside ta ɗauka tana balla maganin tasha.
Yamutse fuska ta danyi tana tashi bayan ta ajiye maganin da ruwan, sanin cewa ba kowa a gidan yasa bata saka hijab ba ta fito daga ɗakin dan samowa kanta ruwan zafi.
Kitchen ta shiga tana duba kettle dan ta ɗaura ruwan zafi, fuskarta ɗauke da mamakin ganin kettle din a jone gashi kuma ya tafasa, girgiza kai kawai tayi tana zuwa ta kashe, kana ta ɗauki ruwan tana hamdala an hutar da ita.
Toilet din ɗakinsu ta shiga tana zuba ruwan zafin a bucket, ruwan zafin da zai yi wa mutane kusan uku shi Meerah ta juye zatayi wanka da shi.
“ Wai har yanzu babu wanda ya dawo a cikinsu?.” A cewar Mansoor yana wucewa kitchen.
Turus yaja ya tsaya yana kallon kitchen din da mamaki. “ An kutumar raina min wayo, yanzu waye ya juye ruwan da na kai kusan awa ina jira?.” Ya faɗa a kufule.
Fita yayi yana wucewa parlon dan dubawa ko Mama ne tayi amfani da ruwan, har ɗakinta sai da ya duba amma bai ga kowa ba hakan yasa ya fito ya tsaya a filin gidan yana surutu shi daya.
“ Ai ko aljani ne zaiji tausayi na ya barmun ruwan, gashi kuma yaran nan basa nan balle nace su suka ɗauka.” Duba agogon dake ɗaure a hannun sa yayi yana jan tsiririyar tsaki.
Shuru yayi yana kallon ƙofar ɗakin Yasmeen jin kamar ƙarar ruwa, da sauri ya nufi ɗakin yana aiyana irin rashin mutunci da zai yiwa wacce ta ɗauka masa ruwan.
Tsayawa yayi yana kallonta ɗaure da towel da wani ƙarami a kanta ta rufe, ko ba’a fada ba yasan daga wanka ta fito.
“ Keee!.” Ya fad’a a dan tsawace.
Ko tsoro babu ta juyo tana kallonsa fuskarta a tsuke.
“ Waya baki izinin ɗaukar min ruwa?.”
Nan ma shuru ta masa tana kallon shi da manyan idanunta.
“ Wai ba magana nake miki ba yarinyar nan, kin wani zubamin na mujiya?.”
Taɓe baki tayi tana juyawa ta zauna a bakin gado.
A fusace ya ƙaraso gurin ta yana cafko hannunta. “ Idan baki sake sakamin wani ruwan ba ki chanja min suna.”
“ Dama ai ban ma san sunanka din ba.” Tayi maganar tana k’ok’arin fusge hannunta daga ruƙon da ya mata.
“ Ohh haba? Dalla Malama tashi ki sake ɗauramin wani ruwan.” Ya kuma faɗa a fusace yana tada ita da ƙarfi.
Harara ta balla masa tana cewa. “ Sai ka barni na saka kaya ai kafin kace na ɗaura maka ruwan.”
“ Da bakisan baki da kaya ba kika ɗaukamin ruwa? Kuma wani jikin za ki sakawa kayan? Ke wuce muje ki sake ɗauramin wani.”
“ Nifah ban iya ba.”
“ Za ki koya muje.”
Turo baki gaba tayi tana wucewa yana binta a baya har zuwa kitchen din.
“ A ina kika ajiye kettle din?.”
“ Yana ɗaki.”
“ Oya je ki ɗauko.” Ya fad’a yana matsa mata dan ta wuce.
Murmushi ta sakar masa tana k’ok’arin wucewa.
“ Wait bari naje na ɗauko.” Da haka ya wuce.
Bata fuska tayi tana magana ita daya. “ Daka bari naje na dauko ai, dani da kettle din duk ba zamu fito ba dan key zan sawa ɗakin.”
“ Shiyasa nace zan ɗauko ai.”
Taji muryansa yana miƙa mata kettle din, hararan shi tayi tana karɓa, ruwa ta zuba tana jonawa.
Kana ta juya ta fita tare da yin magana ƙasa-ƙasa. “ Matar ka ta boni ga bakin hali ga mugunta.”
Da sauri ya juyo yana cewa. “ Kika ce me?.”
Ɗaki ta shige tana saka key.
Ƙwafa yayi yana fita ya koma ɗakinsa.
Dariya Jameel ya yi yana cewa. “ Ita zan aura, ita kadai zan aura, itace wacce na tsaya jira tsawon shekaru.”
Duban Meemah Alyan ya yi yana cewa. “ Dama bayi da lafiya ne ko ciwon shi ne ya tashi?.”
Da sauri Jameel ya iso gurin shi yana kama hannun shi, yana cewa. “ Ga ta da kyau, kwarjini, manyan idanu, ga body, ga shagwaɓa, kai in fact ta hadu Alyan.”
Kallon rashin fahimta ya masa yana cewa. “ Waye wai?.“
“ Annurin zuciyata mana, kai Bobo idan ban auri yarinyar nan ba zan iya mutuwa har lahira.” Ya fad’a yana dafa saitin zuciyarsa tare da sakin murmushi.
Kallon Meemah Alyan ya yi yana son ƙarin bayani.
“ Sir wai akan Mee…” Dakatar da ita Jameel ya yi yana cewa. “ Me na zaƙewa Anutyn mu.”
“ Anuty kuma?.” Tayi maganar tana nuna kanta.
Cigaba da magana Jameel ya yi yana cewa. “ Bobo wacce ta fito daga office ɗinka yanzu fa.”
“ Wai wa kake faɗa ne?.” Alyan ya yi maganar yana dan boye fargaban shi.
“ Ohh wai ya kake so na faɗa maka ne?.”
“ Sunan ta zaka faɗa min.” A cewar Alyan.
“ Meerah…
09027308227 chart Only
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
5- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
________________________________
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
___________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*P.5*
Cigaba da magana Jameel ya yi yana cewa. “ Bobo wacce ta fito daga office ɗinka yanzu fa.”
“ Wai wa kake faɗa ne?.” Alyan ya yi maganar yana dan boye fargaban shi.
“ Ohh wai ya kake so na faɗa maka ne?.”
“ Sunan ta zaka faɗa min.” A cewar Alyan.
“ Meerah.”
Kallon wawa ya bishi da shi yana jan dogon tsaki tare da cewa. “ Dalla zo ka yakani wani guyi.” Ya ida maganar yana ficewa daga office din.
Kafaɗa Jameel ya ɗaga yana duban Meemah wacce ta saki baki tana kallon su tare da cewa. “ Bari na raka wannan mara R din, wai guyi ana guri yana guyi.” Gyaɗa masa kai tayi tana cewa.” Zan iya tafiya ko?.”
“ Idan kinaso ba, yawwa Anutyn mu yaushe zan fara zuwa hira.” Ya faɗa yana kashe mata ido daya.
“ Babu ruwana a wannan lamarin, kai da Meerah ce.”
Tabe baki yayi yana juyawa ya fita yana waƙa.
# Kar kuga na zake so ne yai min amo#
# Yayi min rukon da bazaiyu na fitta ba#
Duk wanda ya kalla kawai murmushi yake musu, matan kuwa kallon Meerah yake musu har ya isa gurin parking space.
A bangaren Meemah kuwa shuru tayi tana zama ta zuba uban tagumi tana magana ita daya. “ Idan na lura da Sir Jameel son Meerah yake, Yaya Mansoor ma a cikin kwayar idanunsa zaka gane ya kamu da sonta daga shekaran jiya zuwa yau, hmm akwai aiki.” Da haka ta tattare abunda zata ɗauka ta fice daga kamfanin.
“ Mom inason shi zan iya mutu idan ban aure shi ba, ki taimaka ku auramin shi.” Wata ƙyaƙyawar budurwa ta faɗa tana fadawa jikin matar.
“ Ayiriri chass, to kin dade baki mutu ba kuwa.” Tsohuwar da ta fito daga ɗaki ta fada tana gyara zanin jikinta.
Ɗago da kai budurwar ta yi tana cewa. “ Ina ruwanki da rayuwa ta.”
“ Ai kuwa da ruwana har da tsakina, ni da jikana mai bani kudi ya siyamin nama da madarar gora, ai kin ga baza’a masa abunda bazai ji dadi ba.” A faɗar tsohuwar tana mulmula baki alamun tana cin nama.
“ Dama ai bakya so na, kuma nasani kinfi son shi.” Ta sake fashewa da kuka.
Girgiza kai kawai Mom ta yi tana kallon tsohuwar tana cewa. “ Hajiya Mama ina wuni.”
“ Lafiya yar albarka ya hakuri da yaran nan.”
Murmushi Mom kawai tayi tana tashi ta wuce ɗakinta.
Kallon Hajiya Mama Farha ta yi tana cewa. “ Hajiya ki fadamin me kikeso yau zan siyo miki.”
Washe baki Hajiya Mama tayi ta ce. “ Me kuke kiransa wani abu dogo haka dasu nama a ciki ana rufewa da takarda.”
Kashe mata ido daya Farha tayi tana cewa. “ Shawarma ko burger wanne kikeso? Ko duka biyu a siyo miki.”
“ Eh siyomin duka biyun.” Ta fada tana sake washe baki.
“ Angama Hajiya amma fa da sharadi.”
“ Kaji yar banza to me sharadin?.”
“ Za ki saka shi ya aure ni.”
“ Bobo wato Beb din nan ta hadu sosai, kallo daya na mata na kamu da mahaukacin kaunar ta, mace iya mace ga hankali, ga nutsuwa komai ta had’a, Bobo muna haduwa fa ta sakar min murmushi wanda zuciyata ta harba da harsashi mai zafi har ya yi sanadiyar bula zuciyar.”
Ba shiri Alyan ya juyo yana zuba masa sexy eyes nasa, fuska babu ko annuri yake bin Jameel da kallo, kafin ya ce. “ Zaka iya sauƙa ka tafi okay, don’t try to disturb me.” Ya fad’a a dan d’aga murya.
“ Bobo sorry nayi shuru amma anjima zaka rakani hira gurin ta ko?.”
“ God forbid.”
Shuru Jameel ya yi yana kallon shi cike da mamaki, tun da suka tashi tare komai da Jameel yace yana so shi Alyan zai ce yake so dan kar su samu matsala, hakan yasa suka yi karatu daya amma a nan ra’ayi ya babban ta, in da Alyan ya ce shi waƙa zai yi shi kuma Jameel yace engineer zai yi, ganin hankalin su zai rabu ne yasa Dad yace su gina company kuma hankalinsu ya zama rabi da kwata yana chan,,, haka kuwa akayi amma bai hana Alyan zama mawaki ba shi kuma Jameel engineer.
Har suka isa babu wanda ya kuma yin magana a cikinsu.
*ALYAN MUSIC STUDIO*
Shi ne sunan dake manne a katafaran studio, bud’e musu k’ofa bodyguard na shi suka yi, kafin suka fito a tare suna tunkaran ciki.
Zaune suke a parlon suna dan taba hira, Mansoor ne ya shigo fuska a tamke yana kallon su, shuru kowa ya yi suna sauraran me zai ce.
“ A cikin ku waye take da baƙo?.”
Kallon junan su suka yi da mamaki, a dan tsawace ya kuma cewa. “ Magana fa nake yi kun mai dani mahaukaci.”
Da sauri Meemah ta ce. “ Nikam Yaya babu wanda muka yi dashi zai zo, amma bansan ko Yasmeen da Meerah ba.” Ta fada tana kallon su.
“ A’a Yaya ni ma banyi da kowa zai zo ba.” A cewar Yasmeen tana kallon Meerah.
Zuba mata ido yayi yana jiran yaji me zata ce.
“ Sai dai ko muje na duba, wata kila nayi da mutum zai zo na manta.” Ta ida maganar tana tashi tsaye.
“ Kee!!!.” Ya daka mata tsawa wanda yasa ta toshe kunnen ta da sauri tana runtse ido, bama ita kadai ba har su Yasmeen sai da suka dan tsorata.
“ Ni za ki nunawa fallin zamani? Ki fito fili kice kina tara samari mana, useless get lost dalla.”
Da gudu ta fita daga parlon tana wucewa daki ta dauko himar dinta, idanunta fal hawaye ta fita daga gidan.
Yana tsaye a jikin motarsa ya juya mata baya yana danna waya, cike da haushi ta iso gurin shi ko sallama babu ta fara masifa.
“ Waye kai da zakazo ka addabi rayuwata? Tukun nan ma gurin wa kazo ne?.”
Bai jiyo ba ya ce. “ Guyin ki nazo.”
“ Gurina ka sanni ne malam? Irin kune mazan da basa rike girman su ai, suna tafiya girman na tafiya, kana gardi da kai zaka zo gurina kamin me?.”
Runtse ido yayi yana cije baki, cigaba da magana ta yi. “ Malam dan Allah ka tafi ka bar nan gurin.”
“ I said guyin ki nazo!!!.” Ya fada da dan karfi.
Shuru ta yi tana tunanin mai muryan, matsowa dab da shi ta yi tana k’ok’arin lekan shi.
“ Sir kai ne?.”
Juyowa ya yi suna fuskantar juna, fuskan sa ba yabo ba fallasa yake kallon ta.
Hade rai ta yi tana kama kugu. “ Me ya kawo ka?.”
“ We need to talk.”
Hararan shi tayi tana cewa. “ Yawwa tun da kazo barima na fada maka cewa na daina zuwa aiki daga yau.”
“ Damuwayki ce, ni yanzu magana nakeso muyi.”
“ Baza’a yin ba.” Tana gama fada ta juya zata shige cikin gidan.
Fuzgo hannunta ya yi da karfi wanda yasa ta juyo ba shiri tana k’ok’arin fadi ya rungume ta, a dai-dai lokacin ne kuma Mansoor ya fito shi da su Meemaah…
Ayi comments da likes dayawa sai na kara yawan typing 😒✌️
*SIGN BY SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
6- *💅BA KAI NAKE SO BA💅*
_The story is all about love, romantic, sacrifice, heartbreak and destiny_
*STORY & WRITTEN*
*BY*
*FATIMA ISA MANU💐*
*( DR TEEMAH)🦋🕊*
*SAHIBAR JAJIRTATTU✍🏼*
________________________________
Masu neman littafin *BA KAI NAKE SO BA* daga farko tare da sauran littafina zaku iya following channel ɗi na dan samu👇https://whatsapp.com/channel/0029Vaf6CpQDuMRYD1FMD92T
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/IKUcfCN5rPQ9o0CaBtB2qP
___________________________________
*https://www.facebook.com/61556643936657/posts/122103978398221464/?substory_index=1596987511055341&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
(J.W.A)
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan ƙasaitacciyar baiwa su sauya tunanin al'umma cikin sauƙi_.✏️*
____________________________________
*DIAMOND 💎 STAR ⭐*
*LADIES🧝♀️🧝♀️🧝♀️*
*(We stand together)*
🤝🤝🤝
___________________________________
*GARGADI*
Wannan littafin ƙagaggen labari ne, ban yarda wani ko wata ya sauya min shi ba ta kowace siga, sannan kuma ban amince a dauramin shi a youtube ba tare da izini na ba.
*BISMILLAHI RAHAMANIN RAHIM 🙏💫*
*P.6*
Fuzgo hannunta ya yi da ƙarfi wanda ya sa ta juyo ba shiri tana k’ok’arin faɗi ya rungume ta, a dai-dai lokacin ne kuma Mansoor ya fito shi da su Meemaah.
Waro ido suka yi, kusan a tare Yasmeen da Meemah suka kira sunan ta. “ Meerah!!!.”
Da sauri ta fuzge jikinta daga ruƙon da ya mata tana juyowa a razane, dai dai nan kuma nepa suka kawo wuta.
“ Bani na rike shi ba, shi…. shi ne fa..”
“ Alyan?!!.” Mansoor ya kira sunan shi da mamaki.
Sai yanzu kusan za’a ce yasan da mutane a gurin, kallon Mansoor din yayi yana cewa. “ Man dama ƙannen ka ne?.”
“ Me ya kawo ka nan?.”
“ Magana za muyi da ita.”
“ Kasan ta ne dama?.”
“ Man ya kana min wani iyin tambaya fa, and by the way idan nazo ƙofan gidan ku ai basai ka tambaye ni ba.”
“ Yeah, but ya nagan ku a had….” Mai da idanunsa yayi kan su yana nuna musu hanyar gida.
“ Ku wuce ku tafi ciki.”
Bata fuska Meerah ta yi tana kau da kai gefe tare da cewa. “ Ni bazan shiga gidan ba, ba zaiyu ana min tsawa ba ana zagina ba.”
“ Ni kike faɗawa haka?.” A cewar Mansoor.
“ Man bamu gama magana ma da ita ba, da ka bayta idan muka kayasa sai ta shiga