Showing 6001 words to 9000 words out of 48065 words

Chapter 3 - ZUCIYATACE HAUSA BOOKS COMPELET BY ESHAAT SMILER.txt

23 Jan 2025

3923




Bayan *ZUBEE* takawo masa abinci ta'ajiye sai zata tafi cikin daure fuska yace waike wace irin yarinya ce?


Da sauri Ammi ta kallesa tace "a ah metayi kuma? Itama *ZUBEEN* kallesa tayi ciki jin haushin kalaman sa tace ni" bansan abu da nayi saba?.,


tsaki yai mtsww yace toh " dama taya za'ai kisan" abunda ki kayin, tunda ke baki da tunanin sani yin komai sai shirme,


Dalla gafa malama" kije kikawo Mani ruwan wanke- hannun da kuma drink mai sanyi,


Juyawa tayi ta nufi fridge tana gun-guni, yayinda da Ammi tace kidauko masa favourite drink dinsa, *"ZUBEE* tace toh"
Dariya yayi yace my Ammi hada shi ki kata nadar Mani?


tace ba dole naba tunda nasan my young pilot dina yacika tsanda dayawa


yai murmushi yace Allah my Ammi idan ba food dinki naciba sam bana jin dadi kowani irin,idan fa naje tafiya nike nan faman cin abinci gwangwani,
Shiyasa kullum nake Addu'a Allah ya barni dake Ammi na


Ta girgiza Kai tareda cewa kayya "ai shi Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, koba mutuwa akwai rabuwa ta aure,
Don haka abunda nake so dakai shine kafara koyon cin abin guri wasu.


"Adai-dai lokacin Da *ZUBEE'* tadawo hannun ta dauke da faranti jug ne da cup tareda wata yar karamar roba me danfadi ruwane aciki Na wanke hannun,


agaban sa ta'ajiye hannun sa yasa Cikin roban yana wanke wa,


Ammi ta kalli *ZUBEE* tace "ai kaganta'nan bata son yin aiki, idan nace tazo mu shiga kicin sai tace ita karatu zatayi.


Harara ya watsa ma *ZUBEE* aran sa yace karatun iskanci ba,
afili kuma yace Laziness girl" kawai my Ammi kifada ma yarinyan gwara ta tsaya ta koyi girki don ni wallahi bazan Lamunta da cin abinci masu "aiki ba "a toh"


Murmushi Ammi tayi tareda cewa "ai yanzu kam dole ta tsaya ta koya tunda " aure zatai,


Yace oho indai bata koya ba wannan kuma laluran tane", dai-dai lokacin da yakai lomar sakwara bakinsa,
yacin abinci yana santi Ammi yai masa dariya har yagama,


Yace Alhamdullah tareda kallon agogon parlor 10:30Ap, yamike tsaye yace my Ammi Zan tafi Na kwanta sai 1:30pm
Zan tashi tace toh" sai kafito.


Koda *SEERAJ* ya shiga daki ya isko miss call dayawa a wayar sa, best friend dinsa yafa kira wato *SAGEER*,


*SAGEER ALEEYU NASKO* shine asalin sunan Amma friends suna kiransa da S A NASKO, Alh Aleeyu nasko shine mahaifinsa shima ya kasance hamshakin Dan kasuwa ne yanada shaguna dayawa Na saida kayan provisions anan Minna cikin kasuwar gwadabe,


Alh Aleeyu shima gidansa anan cikin tunga yake saidai akwai tazara tsakanin gidan su Sageer danasu *SEERAJ*
Alh Aleeyu nasko
matarsa daya Haj Hadiza da ya'ya uku namiji daya *SAGEER* shine babba sannan Hassana Da Hussaina


*SEERAJ* da *SAGEER* tare sukai primary da Secondary sun shakuda juna sosai duk dai halinsu"


Yasha ban-ban kasan cewar *SAGEER* irin samarin nan ne masu shegen Neman matan tsiya, sabani *SEERAJ* da ko" budurwar bai tabayi ba


Bayan sun gama Secondary school dinsu sai shi *SEERAJ* yatafi Jordan, shikum Sageer yaci gabada kula Da taimakawa baban sa da kasuwacin sa.


Saida kusan kullum *SEERAJ* da *SAGEER* suna Waya wannan kenan.


"Ahankali yakai wayar akun'nan sa ciki salon zolaya yace ya "aikai yine *NAMAMAJO*?
(sunan dayake kirana dashi kenan wani lokaci)


Daga can bangaren *SAGEER* Yace S A saurdauna kaifa iskancin ka yawane dashi me, tsoron mata kawai *SEERAJ* yai dariya tareda cewa "eh nadaiji, *SAGEER* yace kaidai kasani, halan yaushe kadawo? *SEERAJ* yace dazun kasan ni Na kawo Alhazai nan yace af hakane fa "ai naman ta ne wallahi,
Sundan taba fira sannan sukai sallama akan sai sun hadu anjima.


*****//****\\*****
Washe gari da misalin 8:00Am Cikin shirin su Na zuwa islamiyya, kamar yadda suka sabo *SAJEEDAH* ita da Sajeed..

Yau *SAJEEDAH* bata dauki Qur'ani ba saida kananan littafai su hadisi da ahalari,


kasan cewar yau tashi da menstrual pain yanzu hakama tanajin maranta yanai mata ciwo kadan-kadan,


yauma harza su tafi sai Sajeed yace su tsaya su sha kunu,
Hararan sa tayi Cikin jin haushi abunda yake masu kwana biyun nan ,


Cikin takaici tace Sajeed wai mene ne haka ne ka keyi? ashe dama ba sai mundawa muke karyawa ba?..


Amma yanzu sai kace dole sai mun tsaya munkarya sannan mutafi
toh" ni yau bazan tsaya ba, kum...


Inna ce ta katse tada cewa toh" kar kitsaya din kiyi ta tafiya shi" idan ya gama zaya iske ki kinji KO "?


dagajin yadda Inna tayi magara tasan ranta yabaci, toh" itama tadai tafadi hakane kawai Amma sam bazata iya tafiya tabar Sajeed ba,


Don haka dole ta" tsaya suka sha kunu sannan suka fito,
suna Cikin tafiya tace kasan Allah idan gobe kace sai mun tsaya shan kunu KO?..


toh"Saina tafi kuma daga ranan babu ruwana dakai'tunda so kake kullum mudinga makaranta,


Kallifa wani,kojajjan "agogon fata dake daure a hannun ta taduba, Wanda *"SADEEQAH* ce' tabata kwancen sa,
kagani KO" yanzu har 8:30Am abunda ake zuwa 8:00Ap


Amma shine sai 8:30Ap zamu tafi kuma duk Kai kesa muna yin latti tayi kwaf,


Cikin marairaice fuska Sajeed yace Aunty *JEEDAH* nabari kinji?


tace oho "indai baka bari ba toh"bazan karayi maka magana ba ta karashe managan,
adai-dai lokacin da suke kokari shiga wani lungu.


Jitayi an'bugeta da Dan karfi har saida littafan hannun ta suka zube kasa da Sauri tadaga Kai Cikin jin haushi tace....?












Aha


Muje Zuwa


Yanzu za'afara










Don haka




kubiyoni



A




馃挊ZUCIYATA CE馃挊





Tareda





Alkalamin





鉁�





馃挊LUFHAT CE馃挊
[8:30AM, 2/20/2018] 鈥�+234 902 288 0912鈥�: 馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊
馃挊
馃挊ZUCIYATA CE馃挊
_Based on true life Story
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊馃洬馃挊
馃挊馃洬馃挊
馃挊


(Labarin Sarkakkiyar Soyayya)


4鈨�


WRITEN BY


馃挊AMEENAT UMAR FARUQ馃挊
OR
馃挊(MEENAT)馃挊


This page dedicated to All members of pen writers association do yours know what? Hmmm wallahi ina matukar kaunar *KU IRIN SO MUCH LOVE din NAN fa I LOVE YOURS ALL ONCE AGAIN Ana TARE* 馃挊馃拫馃拫馃拫馃挊




----------------------------------------
*_庐PEN:WRITERS ASSOCIATION_*


*_PEN THE STRONGEST WEAPON_*
----------------------------------------




*_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be writers_*






鉁嶐煆�






"Kasa cewa komai tayi' saka makon idon da suka hada dashi, hakan ne yasa taji kirjinta ya buga da karfi don, haka da sauri ta sunkuyar Da kanta kasa yayinda gabanta yaci gaba faduwa, "aranta take fadi innalillahi shikuma wannan mutumin wani irin magic ke Cikin idanun sa?.. Na shiga uku ni *SAJEEDAH*.


*SEERAJ* kenan shima jiyayi kirjinsa ya bugawa gawani abuda yaji yazi yarci jikinsa a lokaci guda, Wanda tunda yake baitaba jin irinsa gawata "diya mace ba sai wannan.


Yana "sanye da kayan sports black da ratsin white suna da tambarin adidas, Riga mai dogon hannu da wando dogo, kansa da hula facing cap wacce batayi nasarar rufe masa lallausan gashin kansa ba, itama hular tanada tambarin adidas saidai yamai da gaban hular ta baya.


"A lokacin daya suka tsugun'na don kwasar litattafain da suka zube akasa,
Saida kashhh basu" Kai ga daukar litattafan ba suka yin wani lafiyayyan karon,
dayasa KO" wannen su" rike goshi sa saboda zafin da sukaji,
*SAJEEDAH* tace washhhhhh! shikuma *SEERAJ* yace Auchhhhh!


Sajeed dayake tsaye gefe yana kallon su
Dariya yake ganin yadda suka rike goshi,
cikin tsokana yace Sorry Aunty jeedah
Banza tayi dashi tareda sun kuyawa kasa ta kwashi litattafan ta.


Dama *SEERAJ* yasaba duk ranan Asabar da lahadi, idan yai sallar asuba sai yadan taba karatun Qur'an, toh" kuma bayan yagama sai sufita jogging shida *SAGEER*.


idan suka gama jogging sai kowa yanufi gida Kamar yanzu ma sun gama ne zaya tafi gida sai sukai karo da *SAJEEDAH,*


*SEERAJ* ya kalli Sajeed cikin wasa yace "Oho abun injustice ne ko wato Aunty ka kawai zaka cewa sorry
So"what of me?..
Dariya Sajeed yai yace toh" Sorry Sir , murmushi Seeraj yai tareda mika masa hannun yace thanks my name is *SEERAJ* and u?


Shima hannun Ya mika masa tareda cewa my name is Sajeed Abubakar Sadeeq,
Murmushi Seeraj yai yace gud Sajeed Will you be my friend? Sajeed
Yace yes I will,


*SEERAJ* yace yauwa kaga as from today you're my best friend KO?.. Sajeed yai murmushi tareda cewa yessssss,
*SEERAJ* yace my friend ya sunan Aunty ka?..


Sajeed yace Aunty *JEEDAH* cikin mamaki *SEERAJ* yace Jeedah Kuma?.. Sajeed Yadaga Kai alamar "eh, yace mean? Yace Aunty *"SAJEEDAH,*
"Oho I understand so you Aunty is deaf KO?.. Sajeed idanu ya zaro alamar tsoro Da sauri yace a ah bafa kurma bace,


*SEERAJ* yace toh" idan ba kurma bace" meyasa batayi magana ba?.. sannan Kuma ita batace Mani Sorry ba,


Sajeed dariya yai yace *YAH SEERAJ* toh" aikai ne ka buge Aunty Jeedah don haka Kaine zaka cema ta Sorry,
Seeraj yace "au haka ne? Sajeed yace "eh


itakam *SAJEEDAH* mamakin Sajeed take, har tana fadi aranta amma dai yaron nan gabine ji yadda yaketa zuba surutu Da mutumin" da bai taba ganisa ba sai yau,


Amma dayake Shi' Sarkin surutu ne hada wani fada masa sunan mu, saboda yaji dadin asirce mu dawan nan magical eye's din'nasa, tai kwaf tareda cewa sokon yaro kawai.


Cikin slow motion *SEERAJ* ya juya wurin *SAJEEDAH* Ya zuba mata lumsasun idanun sa datace suna dauke da magic,


Kallon ta yake Ciki wani irin yanayi soyake ta juyo ta kallesa KO" yasake jin irin abin dayaji dazu saboda yanayin yaimasa dadi zaiso yaitaji irinsa,
saidai kashhhh takasa kallon nasa asalima Sajeed take kallon,


Ganin bata"da ninyar kallon sa" yasa yadauki hannuwan sa" duk biyu, yakama kun'nu wansa tareda yin muryar yara yace Soweeeey Aunty *JEEDAH* pls forgive me,
Shikam Sajeed dariya yake sosai
ita kam *SAJEEDAH* da sauri tajuyo saka makon jinda tayi yakirata Aunty,


"aiko karaf suka hada idanu yayinda suka tsaya cif suna" kallon kwayar idanun junansu, tamkar suna neman wani Abu aciki, sunkai kusan 5mint suna kallon juna,
*SAJEEDAH* ce tayi sauri dauke kanta shikam *SEERAJ* ba haka yasoba,


"itakam *SAJEEDAH* wani irin kasala kwayar idanu sa suka saukar mata ajikinta"
A hankali yasake tsura mata idanu sa" tareda cewa pls am so sorry,


Batare data kalle "saba saidai cikin rawar murya tace no badamuwa, Sajeed last go we getting late Sajeed yace toh.


Shikam *SEERAJ* mutuwar tsaye yayi saka makon jin zazzakar muryar *SAJEEDAH*, Sajeed ne ya girgiza masa" hannu tareda cewa bye bye my best friend mun tafi,


Da sauri *SEERAJ* yadawo hayyacin sa yace" eh! me kace? dariya Sajeed yai yace mun tafi, *SEERAJ* yace shikenan?.. Sajeed yadaga Kai alamar "eh, yace OK " bye bye sai kundawo yayinda yabi bayan *"SAJEEDAH* da kallo, itakam tuni tayi gaba domin gaba daya ta matsu da subar guri, saboda yadda taji kafa fuwanta suna Neman kada ita" kasa,


Yana tsaye yana kallon "su har saida "suka shige wani lungu,sannan yasauke nauyayyan ajiyar zuciya a hankali yajuya jiki bakwari yatafi,


Itakam *SAJEEDAH* suna shiga lungun ta tsaya tareda dukawa, tana maida numfashi sai kace wadda tayi gudun kilo mita 100,


A hankali ta daga kai tana hararan Sajeed Wanda ya tsura mata" idanu yana kallon ta, cikin jin haushisa tace dalla meye haka sai wani kallo Na kake" sai kace baka san'ni ba, kai tsaya madai tukun'na "a ina kasan wancan mutumin ne?
Yace "a ah ni bansan shiba sai yau,


Kai ta girgiza tace baka sanshi" ba Amma dayake "kaidin parrot ne Sarkin surutu,


shine kasaki baki kana tazuba surutu da "mutumin daka fara gani yau" ko?
kwaf tayi, tareda sake cewa Allah Sajeed surutun ka is too much wlh, Ya Dan turo baki tareda cewa sorry Aunty *JEEDAH"*
Hararan sa tayi tareda cewa "eh da'anyi magana sai kace wai sorry,
dalla gafara ni wuce mutafi tasashi gaba suka tafi.


馃挊馃挊馃洬馃挊馃挊


Shikam *SEERAJ* koda ya isa gida toilet kawai yashiga yasakar wa kansa" shawa, yadan jima sannan yafito daure da towel gaban dressing mirror ya" tsaya, ya Dan Shafa mai sannan yafeshe jikinsa da kalolin body spring masu kamshi,


Sannan yasa wata jallabiya bayan yasa sai ya kalli agogon dakin yanuna masa 9:15Am , sai naga kawai yafada saman faffadan gadonsa mai dauke da lallausan katifa da bedsheet, jinai yace bismillahi tareda rufe ido.


_a ah kai su captain *SEERAJ* za'adan matsene(bacci) to barina jamaka kofa to atashi Lafiya._




Washhhh! wayyo! Inna marata ciwo wayyo! Inna inajin kamar marata zata fashe, *SAJEEDAH* kenan sai juyi take ta tafamanyi tareda murkususu akan wata yar yalo yalon katifa, wacce basuda maraba da tabarma saboda tsabar latsewarta,


Inna dake zaune kusa da "yarta ta sai sannu take tafaman zuba mata, Ciki tausayi tace oh! Allah yarabaki da wanna ciwon Mara sannu,


yanzu kam takasa magana saidai Kai kawai take gyada wa saboda tsabar Azabar ciwo, Sajeed ma Ciki tausayi yar'uwarsa yace Sannu Aunty jeedah, Bari nasake dubawa KO "baba yadawo sai Na karbi kudi nasiyo maki magani KO? Kai tadaga masa" alamar "eh,


Da sauri yamike zaya fita saiga baban ya shigo da sallama Innata amsa sallamar,


yayinda Sajeed yace baba sannu da dawowa tareda karban ledan hannun sa, baba yace yau sannu Sajeedu, mikawa innar taku ledan dankaline nadan siyo mana sai adan dafa mana ya Kai karshen maganar dayin dariya,


Allah sarki Malam Abubakar talaka ne shi Amma Kuma yanada wadatar zuci, mutum neshi" Wanda yadogara da Allah da kuma kansa" haka zalika bai taba tunanin rokon wani wai yate maka masaba kasan cewar sa mai karamin karfi,


akoda yaushe burin sa yawadata iyalinsa da abunda Allah ya yahore masa,
gashi mutun'ne dayasan hakkin mako'ci duk abunda zaiyi inda Wanda yashefi mako'cisa yasani ne toh' zai Sanar masa.


Ciki tsananin kulawa yace "a ah *SAJEEDATU* meke faruwa ne?.. dai- dai lokacin da ya zauna akujera yar tsugune,


Inna tace wlh yau ta" tashi Da ciwon Mara ne ga shinan, tundazu dasuka dawo islamiyya take faman shan wahala, Baba yace Ashhhsha! sannu sannu *SAJEEDATU* toh" tasha magani kuwa?. Inna tace "a a bata shaba saboda naira gomace nake da'ita" Kuma naira ashirin ne ake siyar da maganin,


Da sauri Baba yatura hannunsa aljihun gaban rigarsa, tareda cewa toh" Sajeedu zoka siyo mata "ai inada sauran chanji anan, yaciro naira talali yamika wa Sajeed naira ashirin,


Sajeed ya karba tareda Dan bata fuska , (saboda yasan Ogan Chidinma bayada mutunci da ragowa) Baba yace yaya Kuma? Yace Baba shi "Oga chidinma sai yaita masifa wai bana naira ashirin waiya nadai bani ne kawai,


Baba ya mika masa sauran naira goman tareda cewa toh" gashi kace yai hakuri yabaka Na naira talatin din, Sajeed ya karba tareda cewa toh" da gudu yafita.




Sai juyi *SEERAJ* yake yi kan gado yakasa run tsawa dasunan yin bacci, saka makon matsananci tunani *"SAJEEDAH* daya addabi *ZUCIYAR* sa"


"A hankali ya zuro santala-santalan kafa funsa"kasa tareda mikewa tsaye, gaban mirror yaje yadauki wayar sa me line din MTN yazura aljihu Saboda yana espeting call, yazura takal mansa"sannan yafita.


Tafiya yake' cikin nutsuwa yana cikin tafiya, sai kawai yaji yatsinci kansa" dasan bin hanyar dasuka hadu dazu dasu *"SAJEEDAH,*


Saboda haka kawai sai yafara bin hanyar, ya tafiya yana Dan waige- waige kamar mene man wani abun, yadan yi nisa da yafita sai ya hangi "Sajeed yana Ko Karin shiga wani shogo,


Wani irin Sanyine ya ziyarci *ZUCIYAR* *SEERAJ, DOMIN YANZU KAM YA TABBATAR DACEWA ZUCIYAR SA TAKAMU DA KAUNAR "SAJEEDAH Da kuma SAN SAKE GANIN TA'* saboda haka Da sauri ya kwala ma Sajeed kira.


Sajeed ya juyo dan yaga "wanene yake kiransa, Wanda yagani ne yasashi sakin murmushi tareda cewa Lah My friend Kai ne?..


Shima *SEERAJ* murmushi yayi yace "eh nine me zaka siya a wannan shop din? bata fuska Sajeed yai yace magani Zan siya wa Aunty *"JEEDAH,*


Da sauri *SEERAJ* yace meyasa "meta? Sajeed yace cikinta' ne yake mata" ciwo sosai, Da sauri *SEERAJ* yace sosai fa kace ? yace "eh kuma tanata" kuka shine "baba yace nazo nasiya mata" magani, yakara sa maganar fuska sa cike da tausayi yar' uwarsa".


Shikam *SEERAJ* jiyayi kirjinsa na bugawa, 'ahankali yace toh" muje ka siya, Sajeed yace toh".


Allah sarki Sajeed yaukam da kwarin gwiwar sa"yashiga kyamis din Oga Chidinma, ganin cewa yau yariko kudi dayawa har naira talatin,


Shikam oga Chidinma yana gani Sajeed sai ya daure fuska,
(dayake bayada mutunci balle ragowa) yace kazo KO?..


dariya Sajeed yayi adai-dai lokaci daya yaciro kudin, daga gaban aljihun riga ya mika masa" yace "eh Oga "Chidinma kabani maganin ciwon Ciki irin wannan din'nan,


Harara Oga Chidinma ya watsa wa Sajeed tareda fara yimasa masifa cikin harshan Hausa,


(dayake ya" naji Hausa kamar jakin kano) yana cewa bana fada maka"kar kasake zuwa da naira ashirin ba?..


Amma dayake kai bakajin magana, shine yauma kasake zuwa dashi, sabada kaga Ina baka KO"?toh" yau bazan baka,


Dauri Sajeed yace Lah! Oga "Chidinma yaufa naira talatin, nakawo kagani KO? yafada tareda nuna masa kudi,


Cikin masifa Oga Chidinma yace toh" bazan siyar ba fita mun a shago,


Sajeed yace pls Oga Chidinma kabani maganin, kaga "Aunty *JEEDAH* ta can tana kuka Saboda Ciki ta yana mata ciwo sosai.


Oga Chidinma yace Oho "lna ruwana "ta mutu man.. maganar ta tsaya saboda,


Wani uban tsawa da *SEERAJ* yadaka masa", Wanda yake tsaye tundazu "abakin kyamis din yana saura ranan duk abida ke faruwa,
Ciki bacin rai yace....?






Aha




Muje Zuwa



Kubiyoni


A


馃挊ZUCIYATA CE馃挊




Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login