Showing 3001 words to 6000 words out of 87052 words

Chapter 2 - MOON Book Complete by Nimcey Sarauta .txt

03 Feb 2025

4283

kiran farko na asuba,bayan ta murje idanunta ta kallesa tare da buɗe jerarrun fararan haƙoranta ta buɗe baki zatai magana yyi saurin sanya hannu ya jawo ta kusa dashi tare Sanya hannu ya rufe mata baki yace "no!! Aƙwai risky a tafiya ta gobe,wasu za suyi tunanin ina da hannun cikin rasuwar ahhalin kawai ka jira i will back you" yana faɗin hakan ya kashe wayar tare da kallon Moon wacce take tsotsar tafin hannunsa har yawo na zuba,ita kowa Moon dake komai ɗaukan sa take na wasa, daɗin da ɗawa yau taga mutumin da bata taɓa gani ba,kasan cewar ko school bata zuwa komai iyayenta ke mata hatta zuwa kasuwa babu wanda yake bari ya san tana tare dashi,yasa da taji tattausan hannun Deen cikin bakinta ta fara tsosa sbd sabo da tayi Dad ɗinta na mata haka, lumshe idanu yayi har lokacin da yaji anyi ASSALATU sannan ya ware idanunsa ya kalleta still hannunsa yana bakinta,cikin ƙasa da murya yace "ciye min hannun to" jin haka yasa ta cire bakinta ba tare kuma da yace komai ba ya nufi hanyar fita,da sauri ta kama hannunsa tare daya fitosa da hannu ya kawo kunnan sa,tsayawa yayi yana kallonta ganin time na shige masa yasa ya durƙosa har ƙasa dai-dai tsayinta,bakinta ta ɗora a kunnansa tace "kul ka gayawa Dad I'm with you,zai ɗauke ni kuma banson i like to stay with you,zaman gida ban so" shuru yyi mata har ya miƙe tsaye ƙara riƙesa tayi tace "Please" kai ya jinjina mata kafin yaja numfashi yace "and you too kada ki fito koda wasa i will be back" juyawa tayi ta ɗauki teddyn ta tare da zama ta fara wasa da teddyn tana faɗin " I am a Muslim child,I will never see him for my money for Thailand for daddy was with my neighbour" Deen na fita ya ƙarasa wajan fanfo yyi alwala ya nufi masallaci,yana zaune har aka idar,bayan anyi sallama wani ya shigo da sauri tare faɗin "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu ake gayamin anje har gida an kashe sabon mai gidance dashi da matarsa,ita kuma yarinyarsa an nemeta an rasa,da sauri Alhaji Murtala aje waya ya miƙe tsaye har yana kusan faɗuwa yace "what maƙocina aka kashe,yasu buhanllah duk a yaushe?" Mutumin yace "wlh jiya da daddare ina ƙwance na dinga jiyo sounds na bindiga da kuma ihun mutane tun daga lokacin kasa ƙarasa bacci nai sbd far gaba,ban ɗaki kam na shiga babu adadi domin gani nake suna gamawa gida ms zasu zo, ya ilahi wannan wacce irin masifa ce,gashi kuma ance babu wanda ya san shi bare a sanar da danginsa yaya za'ai kenan,gadai ƴan sanda cen har sun ƙarasu" Alhaji Murtala aje waya yace "yanzu wanne labari aka samu akan Moon he is my friend domin nine na bashi gidan ya zauna,kasan cewar shi ba mazauni bane" wani yace "Allah sarki bawan Allah mutumin kirki ga halin ƙwarai ai sai muje ai masu suttura kada lokaci ya huce" tashin ƙarar ya bai yana a fuskar Alhaji Murtala aje waya tunanin inda Moon take shine kawai a ransa,ina take waya ɗauke ta itama an kashe ta ko tana raye?shine tarin tambayoyin daya kewa kansa amma babu amsa,gaba ɗaya mutanan cikin masjid ɗin suka fita zuwa gidansu Moon,da kallo kawai Deen ya bisu wanda yake zaune yana riƙe da Kur'ani a hannu,bayan sun fice shima ya miƙe tare da yin waje,kai tsaye cikin gidan da yake gadi ya nufa,ganin babu kowa a compound yasa ya tura kansa zuwa ɗakin,tana ganinsa ta miƙe tsaye tare da ƙara suwa inda yake tsaye tace "sallah zanyi" banza yayi mata ya ƙarasa katifarsa ya ƙwanta sbd sam jiya bai samu yayi bacci ba,yana kwanciya ta zaune a gefensa tace "Dad i want chocolate" ware idanunsa yayi sbd sunan da yaji ta kirasa dashi na Dad,shuru yyi mata da sauri ta mirgina jikinsa tare da kwanciyar a saman cikinsa tace "yunwa na keji Please Dad" idanunsa a lumshe ya tallafo haɓarta tare da ware bakinta ya tura mata ƙaramin ya tsarsa a bakin ta yace "ohyaaa take a sweet...






WACCE MOON?
WAYE DEEN?
SUWAYE SUKA KASHE IYAYEN MOON?
MENE YASA KOWA YAKE SON YA SAMU MOON A WAJANSA?
WANNE KALLO MOON ZA TAIWA DEEN?


OHHH YAAAAA GUYS DROP YOUR BEAUTIFUL COMMENT AND DAN ALLAH DAN ANNABI IDAN KANA JIN DAƊIN LITTAFIN KAYI SHARE NASA ZUWA WANI GROUPS ƊIN,WANNAN LITTAFIN FREE NE BANA KUƊI BA, IDAN A WATTPAD KA KARANTA KAYI COPY NA LINK ƊIN RASHIN COMMENT ZAI SANYA NA AJJIYE WANNAN LABARIN TABBAS😂






Yana mata kallon mahaifiyarsa wacce da inganta rayuwarsa,bai san cewa duk masifar daya shiga itace sanadi ba,wacce yake tunanin ƙanwarsa ce the save mother and father and wayi gari ta zama matarsa,ya haɗu da ita ya taimaka mata a matsayinta Na ahlil kitab,an wayi gari yaje garin su aka haɗa su ɗaki ɗaya da niyar suyi rayuwar domin hakan shine al'adar garin🙈tashin hankali gashi mazantakarsa mata aiki😟and the end ashe mahaukaciya ta haifeshi waye Wannan? A wanne littafine? Ku nemi book ɗin *Uncle ne* domin jin wannan ƙyataccen labarin aka farashi mai sauƙin 300 masu buƙatar vip inda zanna posting sau biyu kuma su samu littafan dana rubuta na kuɗi irinsu *Sai na aurenta, izzar so, The new emir* zasu biya 600 ta wannan asusun 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616






SARAUTA👑
9/12/21, 5:31 PM - Buhainat�: _⚡MOON ⚡_










_��NIMCYLUV_




ELEGANT ONLINE WTITERS


5-6






FREE book
_*MARUBUTA* masu rubuta littattafan kuɗi wanda suke buƙata ai masu tallah domin su ƙara samun costumer zasu iya nemana domin a tallata masu littafansu cikin sauƙi da kwanciyar hankali🤗_ _*MAKARANTA* wanda suke business kuma suke buƙatar a tallata masu hajarsu suma zasu iya nema ta wannan number 08119237616 zan baza maka tallan business ɗinka zuwa wajaje da dama inda zaka samu costumer siyan ɗaiɗai ko sari 😇_


Wattpad Nimcyluv










Girgiza masa kayi tayi ba tare data ƙara magana ba tayi lamo a jikinsa,turo da yatsan daya sa mata a baki tayi,kafun ta kallesa taga ya rufe idanunsa yana bacci,hannunta tasa ta shafi sajensa tace "laaaa Dad kaima kana da irin na Dad na" shuru yayi mata bawai dan baya jinta ba,lips ɗinsa ta taɓa ta ƙara faɗin "Dad kaima kana shan sweet ne" kafin ta ƙara faɗin wani abun aka fara bugun ƙofar ƙaramin ɗakin nasa,da sauri ya miƙe tsaye tare da ɗaukan Moon ya sanyata a bayan ƙofa, buɗe ƙofar yayi ganin Alhaji tsaye yasa yayi shuru yana kallonsa kafin yace "mrng Alhaji" Alhaji yace "mrng too ba zaka fito ai jana'izar da kai bane?" Ƙasa yayi da kansa sbd kallon da yaga Alhajin nayi masa gaba ɗaya ya manta cewa gashin kansa a kunce yake,cikin basarwa yace "eh,ban jin daɗi ne" jinjina kai Alhaji yayi alamar gamsuwa kafin ya juya ya nufi cikin motarsa yayi waje,yana zuwa ya fito daga motar ya karasa wajan jami'in jana'izar da za'ai,gaba aka shimfiɗesu su uku har yanzu jini bai bar zuba daga cikin ko wannan su ba, addu'ar da ake yi a cikin sallar jana'iza Liman ɗin ya fara.
"اللهم اغ�ر لله وارحمه،وعاع� عنه،وأكرم نزاله،ووسع مدخله،واغسله بالماء والثج والبرد،ونقه من الطايا كما نقيت الصوب الأبيض من الدنس،وأبدله دآرآ خير من داره،وأهلا خيرآ من زوجه وأدخله الجنة،وأعذه من عذاب القبر وعذاب النار."
_(Ya Allah ka yi masa gafara,ka jiƙansa,ka amintar da shi daga bala'i ka yi masa rangwame,kuma ka girmama liyafarsa,ka yalwata mashigarsa (kabarinsa), kuma ka wanke laifukansa kamar yadda ka ke tsaftace farar tura daga dauɗa, kuma ka musanya masa gidan da ya fi gidansa alheri,da mutanen gida da suka fi mutanen gidansa alheri,da mata matar da ta fi matarsa alheri (da mijin daya fi mijinta alheri) kuma ga shigar da shi /ita aljanna,ka tserar ta da shi /ita daga azabar kabari da azabar wuta)_






Ana kammala jana'izar aka miƙa su zuwa gidansu na gsy,bayan an dawo Alhaji yana zaune a saman danning yana breakfast gefensa Farouk da Yasmin sai matarsa Hajja khadu suna kiranta da Ummi ta kallesa tace "wannan lamarin yana bani mamaki,ace an kashe kowa na gidan amma a rasa inda ƙaramar yarinya take,wannan wacce irin rayuwace yanzu wa yasan halin da yarinyar take ciki, Allah yana gani da za'a ga rinyar nan nice zan riƙe ta,Alhaji anya ba wanda suka aikata wannan abin bane suka ɗauke ta ba?" Ta faɗa tana ɗaukan tea tare da kaiwa bakinta Farouk yace "Ummi ko ajiya naga yarinyar ta tsallako titi hannunta riƙe da ice cream,sosai nai mmki sbd ban taɓa tunanin aƙwai wata ƙaramar yarinya ba a cikin gidan" Ummi tace "Nima sau ɗaya na taɓa ganinta,kamar dai basa barinta fita tunda ko compound na gidan da wahala ka ganta ciki" sai lokacin Yasmin tace "to Ummi ko dai ɓoyeta suke?" Kai Alhaji ya ɗaga ya kalli autar tasa kafin ya miƙe yace "Auta me zai sanya a ɓoye ƴar ne? Kawai da bata da cikakkiyar lafiya shiyasa ko da wanne lokaci a kuma ko ina ciwonta na iya tashi"yana faɗin hakan yay shuru da bakinsa ya nufi part ɗinsa, cikin ƙasa da murya Farouk yace "Ummi meke damunta?" Miƙewa Ummi tayi tace "Ni tayaya zan sanan wannan lamari Allah dai ya bai yana ta,ko kuma ya kaita hannu na gari, Allah sarki ƙyakkyawar yarinya da ita"






Ummi ta faɗa tana miƙewa tsaye tare da kiran sunan mai aikinta Hanne,Hanne na zuwa tace "gani Hajiya" Ummi tace "yawwa Hanne ɗauki warmer ɗin nan ki miƙa wa mai gadi nasa breakfast ɗin" cikin girmamawa Hanne ta amsa tare da fice daga cikin gida...
Yana ƙwance Moon na jikinsa sai ya mutsa masa gefen fuskarsa take,fuska ta kwaɓe tace "Dad i want eat food,ina jin yunwa"sai a lokacin ya ware idanunsa wanda suka ɗan janye kaɗan yace "kee shuru" cikin muryar kuka tace "Please Dad" baya ya juya mata ba tare da yace mata komai ba,baki ta buɗe zata magana yayi saurin rufe mata bakin,a lokacin kuma aka fara buga ƙofar ɗakin miƙewa yayi tare da tura Moon bayan ƙofa,jerarrun hqranta ta buɗe tare da ɗaga hannunta ta girgiza alamar ba zatai magana ba..
Buɗe ƙofar yayi yaga Hanne tsaye hannunta riƙe da warmer, bai ce mata komai ba sai data gama kallonsa tace "abin karyawa" amsa yayi tare da juyawa da sauri tace "bawan Allah yaya mu kaji da wannan tashin hankalin ɗaya samemu yau" cikin ƙasa da Murya yace "Allahamdulillah" tace "wanann rashin imani dame yayi kama,OHHH! ni Hanne yanzu har ƴar yarinyar nan ba'a gani ba,kaii duniya ina zaki damu ko me ya tare masu ohhhu..,ai ɗazo Alhaji ya dawo daga jana'izar wai har aka saka su makwancin su jini na zuba..,Ni kam nace wanne irin harbi akai masu?" Tunda ta fara magana yake kallonta ba tare daya tan kata,ta buɗe baki zatai wata maganar yayi saurin juyawa ya barta tsaye baki a buɗe.
Wajan gate ta nufa tare da leƙawa ta wata ƙofa ta hangi gidansu Moon tace "Allahu akbar,yanzu duk girman gidan nan babu kowa,yooo duniya kenan kana zaune da kowa lfy baka san me ƙullatarka a zcy ba,mutum zcyarsa fari fattt amma ta wani tirrrr kada kasu kaga baƙin dake cikinta sbd mugun abu,yanzu wannan gidan kayan daɗi na nan kala kala kuma iri-iri karama bonvita da obalti suji lbr,ko ina marainiyar Allah tayi ohhhhu,amma dole zan bincika idan na tabbatar da abinda nake tunani babu shakka zan bata taimako wanda zai zame mata kariya irin na har abada ɗin nan"jin motsi a bayanta yasa ta juya da sauri dan ganin wanene,tsaye taga Farouk sanye da riga da wando na baƙin yadin boyal sai ƙamshi yake,ganin yana kallon ɗakin Deen yasa itama ta kalli direction ɗin da yake kallo itama, ɗauke kansa kawai yayi ya nufi wajan motarsa yabar gidan gaba ɗaya ba tare da yyiwa Deen magana ba,itama Laure juyawa ta nufi cikin gida..
Ajjiyar zcy Deen ya sauke bayan yaga Farouk ya fice daga cikin gidan, ƙaramin ribbon ya ɗauka ya naɗe gashin kansa dashi kafin ya juya ya nufi inda ya ajjiye warmer ɗin breakfast ɗin,zama yayi ya ɗan lumshe idanunsa, Moon dake zaune hannunta riƙe da teddy tace "Dad" kallonta yayi na wasu seconds kana ya ɗauke idanunsa a kanta ya zama can gefe yace "eat" Moon ta kalli warmer ɗin kana tace "Dady nane yazo ko, Dad kace masa bana nan sai na daɗe wajanka zan koma"still ƙansa yana ƙasa bai ce mata komai ba,shuru ne ya biyo baya kafin ta miƙe ta zauna daf dashi tace "Dad mene jana'iza?" Ɗan waro idanunsa yayi cike da mmki kafin ya ɗaga kai ya kalleta nan ma shuru yayi mata bai kula ta ba,marai-raice fuska tayi tace "wata rana na taɓa ji Daddy yace yaje jana'iza,amma ni ban son ai masa jana'iza" nan ma kallonta yayi kana ya ɗauke idanunsa yaci gaba da latsa babbar wayarsa mai ƙirar iphone 12 max pro, murmushi tayi masa har sai da beauty points ɗinta suka loma tace "kasan me yasa nace haka..?" tsaki yaja kafin yace "talkative..! Shut up" yana faɗin hakan yayi ƙasa da murya cikin nutsuwa yace"Ututu oma" (good morning) shuru yayi yana sauraran abinda ake faɗa masa,kafin yaja idanunsa ya lumshe idanunsa ya sauke ajjiyar zcy yace "owk" yana faɗin hakan ya kashe wayar,kana ya kunna data wayarsa ya shiga I.G yana shiga messages ɗin Nana khadii wajan biyar suka shigo cikin wayarsa wani lalataccen murmushi gefen baki yayi kafin ya fara karanta messages ɗin kamar haka.
_na riga na faÉ—awa iyaye na, kuma sun amince_
Hannu yasa yaja gefenmu ya ƙara ware manyan idanunsa.
_Na jika shuru_
Messages É—inta na huÉ—u ya duba.
_Allah yasa ba aikin ka fasayi dani ba_
Cikin sauri sauri ya rubuta mata "ok gobe ki sameni a *Nnamdi Azikiwe International Airport* by 10:30, za kiga wani sanye da blue ɗin sweater You can follow him" yana gama typing ɗin yayi send kana ya kashe data na wayar,wani danne danne yayi wajan 5seconds ya kashe wayar gaba ɗaya ya ajjiye ta a ƙasa pillow, Moon da yunwa ya fara cinta tayi shuru tana kallonsa kamar mai nazartar wani abu a wajansa,sai kuma tace "Dad zan sha tea" ɗago kai yayi da sauri sbd gaba ɗaya ya manta da ita a ɗakin,inda Allah ya taimake sa ba wani abu yace ba,komai a rubuce yayi shi,dan sosai ya fahimci shegen surutun da take dashi, haɗe fuska yyi sai kuma yaja warmer ɗin ya buɗe,wajan part huɗu ne cikin warmer ɗin kafin yasa hannu ya buɗe part ɗin farko soyayyan dankalin turawa ne wanda yasha ƙwai, ɗaya part ɗin ya buɗe yaga soyayyiyar doya,fito dasu yayi tare tura mata gabanta yace "ohhyaa ci" kamar jira take tai bisimillah ta fara cin dankali sai da ta cinye tass sannan sannan ta ture doyan tace "Dad water" fesar da numfashi ya ɗauki hularsa ya saka a kansa tare da tura duka gashinsa ciki,ya fita zuwa waje,wajan 10minutes ya dawo hannunsa riƙe da gorar ruwa mai sanyi da mara sanyi sai kuma chocolate,yana shigowa Alhaji na fitowa daga cikin gida zai fita,kallon Deen yayi yace "chocolate kamar yaro" cije lips yayi ba tare kuma da yace komai ba ya buɗe ɗakin ya shiga,tana zaune riƙe da wayarsa a kunanta da sauri ya amshe wayar,kallonsa Moon tayi tace "ance ka kai babyn wai" hannu yasa ya rankwashi tsakiyar kanta yace "kika ƙara taɓa wayar saina harbeki stupid"Baki ta buɗe zatai kuka yayi sauri jawo ta jikinsa ya rungome haɗe dasa hannu ya toshe mata bakin,da idanu kawai Alhaji yabi Deen da kallo kafin yayi murmushi ya shige cikin motarsa,shuru yayi mata yana jin yadda take tauna hannunsa da haƙoranta yay mata banza, buɗe idanunsa yayi sbd horn ɗin da yaji a nayi janye jikinsa yayi ya nufi waje,motar Alhaji ya gani a gaban gate da nutsuwar da ta gama zama a jikinsa ya buɗe gate ɗin ba tare da kalli motar ba yaja baya,shima Alhajin baiko kalli inda yake ba ya fice daga cikin gidan.
Da yamma wajan ƙarfe biyar Deen na zaune saman benci a gefen gate bayan ya lallaɓa Moon tayi bacci sbd kukan Mummy da Daddy data fara.
Daga can gefen yaji ana faɗin " yallaɓai C.P (commissioner of police) bawai ina tunani bane,a'a ina son na tabbatar maka yarinyar nan aƙwai wanda suka ɗauke ta bawai kasheta akai ba,zuwanka shine zai ƙara tabbatar maka" shuru yayi na wani lokaci kafin yace "ok yallaɓai C.P ina gdy sosai saika zo ɗin" yana faɗin hakan ya shige cikin gidansa ba tare daya kalli Deen dake zaune ba..
Misalin ƙarfe 11 na dare gidan yayi shuru ba kajin kukan komai saina gyare dake ta faman kuka "tsut tsut tsut" wata babbar akwati Deen ya buɗe ya kallin Moon dake bacci ta rungome teddynta hannunta riƙe da chocolate wani shu'umin murmushi yyi kafin a hankali ya ɗauke ta cak ya ya sakata cikin akwatin da sauri ta buɗe idanunsa sbd zafin da taji,kallonsa tayi shima ya kalleta tana ƙoƙarin kiran sunansa yayi saurin dannata cikin akwatin tare da zuge zip ɗin...






😱😱😱tab ɗin team Moon how far..?


_afuwan da jina shuru da kukai na shiga busy na biki amma Allhamdulillah mun kammala cikin farin ciki da kwanciyar hankali🥰abu na biyu na faɗa muku duk bayan ƙwana biyu zanna posting sbd ina book ɗin Uncle ne kuma na kuɗi ne nake ending na book 1 duk mai buƙatar siya sai yyimin mgn 08119237616_


*Tabbas idan ba'a comments da share zan ajjiye book ɗin,ko kuma ya koma na kuɗi tunda kunfi gane haka😂😂*








SARAUTA👑
9/12/21, 5:31 PM - Buhainat�: I just published "7-8" of my story "Human Trafficking {Moon}". https://www.wattpad.com/1086128791?utm_source=android&utm_medium=com.gbwhatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=nimcyluv&wp_originator=HWs2b%2Bs2bzLWu%2BP%2BVHHypwMwGUASLNTABtwfEJPshvvzPupfINv9%2BIi%2By9F5EaIBEJdYGKNvnydG7rmdM5yYhwKPb7Mg32qzhWOMVmZS%2FFQ0%2BWkrrIOWEn6A8jr%2BqFs9








_� MOON ⚡_






_�� NIMCYLUV_




ELEGANT ONLINE WTITERS


7-8






_*MASARAUTAR MU.. MASARAUTAR MU* SHIN KUN TA�A JIN MASARAUTA MAI CIKE DA RUƊANI? SHIN KUNA SON KU SAN AL'ADUN NA CIKIN MASARAUTA? KUNA SON SUWAYE SUKE GADON SARAUTA? KUNA SON KUNJI YADDA KO WANNE MUTUM NA CIKIN GIDAN SARAUTA YAKE ƘWAƊAYIN KUJERAR MULKI? TO KU MATSO JA DAMA TA SAMEKU *SHARARIYYAR MARUBUCIYAR NAN MAI TA ƘAMA DA AL'ƘALAMINTA WACCE TAYI FICE A CIKIN JERIN MARUBUTA WATI FATIMA ZAHRA* TA SHIRYA TSAF DOMIN KAWO MAKU WANNAN ƘASAITACCEN LABARIN,ABIN MAMAKI LITTAFIN ZAKU SAMESA A ƘYAUTA BA TARE DAKO SISINKU BA, BURIN MARUBUCIYAR SHINE KOWA TA AMFANA DA TA TA KALLAR BAIWAR🌚INA KIRA GA DUK MASOYA NIMCYLUV SARAUTA NA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login