Showing 1 words to 3000 words out of 30540 words

Chapter 1 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf

[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA...* 📿




*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*Nabilancy Luv* 💘
(Auntyn S&S)



1-5


Sarki Abdallah Adalin Sarki ne mutum me kamala da Son talakawansa Wanda yake da mata
Uku sai yara biyu matarsa ta farko uwar gidan itace Hauwa,u Anace mata *UMMAH*

Mebi mata itace Saratu *MAMAH* sai ta Uku amaryar sarki itace Fatima Amma *FATU* akece
mata


UMMAH macece me tsananin kishin gaske Tanada gadara da iko ita din yar gidan Sarautace
tana buga ikonta agidan sarki domin sarki Abdallah yanaji da ita don haka take buga sha,aninta
ackn gidan kowa shakkarta yakeyi tundaga fadawa,Bayi maxa da Kuyangin gidan da duk
wanda ke cin gidan har kishiyoyinta D'anta Daya jal Yarima Anwar Wanda aka shagwaba shi da
Gata Awaje yayi karatunsa Tundaga Sakandare har tagaba da Sakandaren wanda ba karamar
tabarbarewar tarbiyya zamansa acan yaja masa ba don tun daya gama karatunsa yaki dawowa
Yasamu guri xan babu kwaba babu harara

Har saida labarin abinda yakeyi yadawo kunnan me martaba yai masa aike takakkiya aka taho
dashi

Yayi masa fada sosai har kurari yaimasa yace inhar baidaina ba zai yi masa Aure ackn dangi
zai laluba yadaura masa Aure da koma wacece

Aikin Anwar acan neman matan banza turawan nan sun sassanshi haka abokan banza yake
mu,amula dasu basu da aikin komai saibin club club ana lolewa da mata anashan Giya ana
raye raye

Amma yafi Ronce da wata baturiya data nace masa mesuna RIHANNA wacce duk
wulakancinsa takan shanye Abu daya yasa yake d'anshan mintinta tasan takan iya kulawa da
d'a namiji duk luggar yaudara da iya Romance ta kware

Inda tayi musu zarra kenan gata da kishin tsiya tasha zane mata masu kawo masa hari Amma
ahakan yake yakiceta yaje yashana da wacce yakeso danma tana shakkarsa da bazata bari
yasakeba

Anwar yanada isa da jinkai jinsa yake tamkar sarkin wani zubin to kullum azuciyarsa yana jin
kome zaiyi babu wanda ya isa yakawo masa cikas tunda shi din dan sarkine me jiran gado

Mahaifiyarsa ke kara sakawa yaji izxa aransa akullum takan nusarsa cewar shine sarkin gobe
duk da shi bawani son yazama sarki yakeyiba tunda yasan inya zama sarki dole yazauna guri
guda kuma yabar duk abinda yakeyi knn.

Sarki Abdallah akullum cikin bakin cikin Abinda dansa Anwar yakeyi yakeji aransa wanda
yarasa yadda zaiyi dashi don yakintsu tunda shine babban dansa wanda wataran dole shine
sarki agarin

Yasan da cewar Mahaifiyarsa ke xugashi tunda yahaneshi da zaman turai tace abarshi yahuta
acan kafin wani lokaci bata son abinda zai bata masa rai

Sauran matan Sarki su idone nasu domin ta tsakiya MAMAH bata taba haihuwa ba itako
Amaryar sarki FATU ta haifi Danta namiji tsiransu shekara biyar da Anwar yaron sunansa
LAMIDO

Ummah bata kaunar FATU da D'anta sbd Fatun bata dade da zuwa gidanba ta samu ciki

Ko MAMAH data rigata xuwa bata qullaci fatun ba domin MAMAH macece me tawakkali duniya
bata dametaba

Kowane d'a daga cikinsu tadaukeshi tamkar ita ta haifeshi

Amma tun tasowarsu da suka girma sai tafi kaunar Lamido domin shi yarone me hankali
magana ma bata dameshiba a Nigeria yayi karatunsa

Lokacin daya isa shiga jami,a alokacin Sarki yaso turashi Turai shima Amma sai FATU taki
amincewa sbd a ganinnta xaman turai ga yaro ba uwa ba uba na bata yaro da canza masa
halinsa mekyau zuwa mara kyau tunda shima Anwar dayaje ba haka yakeba ada daga baya

yakoyo wasu dabi'un

Sarki bai bata rai akn hknba domin takawo masa kwararan hujjojinta akan rashin son zuwan
nata Turai yakuma gamsu

MAMAH ma bataga laifin taba domin tasan komai kuma kansu ahade yake su biyun

Sautari UMMAH takance wai sun hade mata kai

Sukuwa shakkarta da sukeyine yasa basa shiga Sabgarta

******

Tun Dawowar da Anwar yayi Nigeria kusan wata biyar yaji yagaji da zaman atakure yake baya
futa club balle korawa da neman mata sbd babu dama duk inda yayi ido akansa suke inma yayi
awajen gari Sarki zai iyaji azo ace yabatawa gidan suna shiyasa yafison yafita away

Rihanna tayi ta damunsa akan inhar bai dawo Turai ba zata hado kayanta ta biyoshi ta nemi
inda yake

Hankalinsa yadaga dan yasan zata iya shiko yasan inhar tazo kashinsa yagama bushewa ackn
gidan

Ba shiri yahau hada kayan dazai tafi dasu domin yai mata Alqawarin zaitaho cikin Satin domin
ma kwana biyu yabata zaitafin

Da tunanin yanda zaishawo kan Sarki yabarshi yatafin yashiga cikin gidan Bangaren
Mahaifiyarsa domin yafara kai mata zancen su samo mafita tukun


Yana tafe afarfajiyar gidan yana tafiyar Jinkai da wani shankamshi da Rangaji ackn Shigar
Alfarma ta sarauta

Bayi maza Da kuyangu mata nata aiyuka suna wuceshi tareda durkusawa suna kai gaisuwarsu
ga Yarima sarkin gobe

Wata *KUYANGA* Yakurawa idanu dayaga tanata sharar gurin ajiye dawakai kanta ba dankwali
dan gyalen data yane kanta ya xame bata saniba

Farace shar gata da hips ga nashanu suncika mata kirji

Ta dago zata bar gurin yakwalla mata kira

Aguje takaraso gareshi da biyayya ta durkusa tana gaidashi

Yakara kallonta na sakanni kana yace ckn shanqamshi "me kikeyi acan?

Da rawar murya tace "ina..,ina yin..,Shara nakeyi...

Yace "Dama Sharar gurin Dawakai nakune mata kona Bayi Maza?

Tayi kasa da kai tace ckn rage murya "Allah yataimaki Yarima tuba nakeyi ba aikina bane
MAHBUB nake tayawa yatafi wani uzurin.

Yace "MAHBUB!wanene kuma *MAHBUB?*

Tahau kame kame tazaci ko laifi tayi

Tace "Abokin shawaratane tamu tazo daya.shima yana tayani Aiki shiyasa nake tayashi

Ayanda take maganar yabashi Sha,awa bakinta me kama da anzana heart yatsurawa idanu
yaga tana motsashi ahankali

Koda tayi shiru shima shirun yayi yana kallonta kawai

Wani abu yaringa ayyanawa aransa

Dataji shi shiru saita dago kanta dasauri tayi tsammanin yatafine saitaga ashe yana gun

Tayi saurin yin kas da kanta don gudun kada suhada idanu

Yace mata "meye sunanki?

Tace " sunana *KUYANGA* !!

Yace "ke Sunanki nace zaki fadamin na gaskiy KUYANGA ba suna bane aguna wannan kalmar
larabcine abangaren hausa kuma ace Baiwa.

Tace "Sunana *ZEENATU*

Ya gyada kai kawai yawuceta yana kara ayyana abubuwa ackn ransa

Koda yashiga cikin Dakin Mahaifiyar tasa tararta yayi hadimanta na mata hidima daga me
matsa mata kafa ana mata tausa sai meyi mata furfita saikuma masu bare mata ayaba tana
karba tanaci

Yana shiga hadiman suka miko tasu gaisuwar xuwa gareshi

Ya amsa da ka

Ta nuna musu kofa tareda alamun sufuta subasu guri

Saida suka futa kana yagyara zama yace "UMMAH Barkanki da warhaka

Tayi murmushi " Yawwa barkanka Abin faharina yarima Mejiran gado sarkin gobe da yardar
Allah.

Yayi murmushi yace "Uwata maganin kukana yauma gani gabanki nakawo kukana nasan banda
matsala tabangarenki zaki sharen hawaye Mai martaba kawai nakeji


Tace "fadi ko meyeshi zanmaka zankuma saka ayi maka

Yace "Ummah inaso inkoma Turai nagaji da zaman Nigeria niba aiki nake futaba kusan kullum
nake gida bana motsa jiki kewa ta dameni kitaimakamin kisa baki me martaba yabarni intafi.


Tayi murmushi "Angama Yarima yaushe kake son katafin?

Yace "Jibi nashirya tafiyar

Tace "Jibi jibin nan? Amma baiyi kusaba kuwa nikaina bason kayi nesa dani nakeba gashi kaida
akeso kahaye karaga wataran yaxa,ayi aga baka xama abaka.

Yace "kada kidamu da Wannan Ummah na wataran ai dole inxauna din nidai yanzu kiyimin
kokari intafi

Tace "kada kadamu kamar katafi kagama zanyiwa TAKAWA maganar ayau.


Yayi murmushi yace "Yawwa nagode Ummah saidai kuma.……

yai shiru yana sosa keya

Tace "ehe!fadi mana yakai shiru kafadi komeye in akwai bazai gagara ba zanmaka.

Yace ckn rage murya "Saidai naga wata yarinya awaje ackn KUYANGU zanso mutafi da ita
tayimin Rakiya domin ta hidimta mini acan.

Murmushi tayi tace "bakada wannan matsalar kowannensu akarkashinka suke kanada ikon
kowanne bawa agidannan ko kuyangu dan haka kasa aranka kamar ka tafi da ita kagama
yatake yarinyar?

Take yahau kwatantata

Tagano ko wa yake nufi domin KUYANGA Zeenatu tafi kaf kuyangun gidan Nutsuwa dakyawun
yanayi tanada kyau nagani afurta

Jin mahaifiyar tasa ta Amince masa yasa yaita xuba mata godiya


Shiyasa yake matuqar son mahaifiyar tasa baitaba neman abu ta bangarenta yarasaba tana
son akullum tafaranta masa bata son laifinsa

Koda yafuto farfajiyar gidan baza ido yaitayi ko zai sake ganinta

Amma baiyi sa.ar ganin kome kamartaba


Tsaki yaja Aransa yace "to meye nawa nadamuwa da son ganinta Alhalin ita zata zamo gadon
baccina ita xata xamo jin dadina ita zata zamo komai nawa sai yadda nayi da ita..……



_Tabdijan muje zuwa_
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA....* 📿





*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*Nabilancy Luv*💘

(Auntyn S&S)




5-10


mai Martaba Sarki Abdallah yayi shiru bayan gama jin Bayanan da Ummah Tazo masa dashi
natafiyar Anwar Turai

Yakalleta yana murmushi yace "Naga alamar yaronnan inmuka ta tashi bazai gyara halin saba
Nikam bana sonsa da zaman wajen nan nafisonsa akusa damu domin Aure nake so yayi tunda
yakai munzalin Aure ko Lamido yanzun ya isa Aure barantana shi

Ummah tace " Aure ai nufin Allah ne baisamu wacce tayi masa bane shiyasa saimu tayashi da
Addu,a kada mutakura masa Tunda can din yafi jindadi gara kabarshin yaje aidebe kewa
yakeso yayi

"Kina baiwa yaronnan gudummawa naga alamar bakya son yagyaru shiyasa kike daure masa
gindi

Ta dafe kirji tacanza fuska

"Kamar yaya? Nikam walh babu wani daure masa gindi danakeyi kawai bana son yashiga
takurane da damuwa Tunda shi bayaro bane da hankalinsa ai ko yana nesa damu bazai lalace
ba shiriya fa ta Allah ce Addu.a kawai yadace muringa binsa dashi.

Mai martaba yace "Amma dai kinsan bazaki hada halinsa dana Lamido bako? Lamido yafishi
nutsuwa da hankali harma biyayya da ace Lamidon ne babba dana more....

Ta katseshi tana kuka "Kawai dai kace kafison Lamido akan shi nikam walh banajin Dadi sai
inga kamar kana nunan banbancine kuma komai lalacewar Yarima ai dai shine babba kuma
dole shizai zama sarki acan gaba....

Yakatseta dacewa "Saurara Fulani kinsan dacewa Adalin Sarki me kamun kai shike cancanta
da yin sarauta akowace masarauta dan haka dole sai inyarima yakasance da hakan sannan zai
mulki garin nan inko bai canzaba to Al,umma bazasu soshiba Tunda ko a yanzun sunfara farga
da banbancin halayyarsu
Tace "To walh koma meye Nikam Bazan taba barin Wani bayan Yarima ya mulki garinnan ba
inba shiba dan haka koma meye za,a yi masa shine dai gaba

Yadaga mata hannu "ya isa meye na tada hankali da kuka indai wannan maganar mulki ce
Allah ketsara komai bamu zamu tsara ba tafiya turai kuma Yaje yaita tafiya Nadaina hanashi
tunda bakya so inhana din duk randa yagaji da zuwa yadaina Amma kusan da sani zanbashi
mata nan ba dadewa ba Har zatayi magana kuma saita fasa tunda bazata ari bakin yariman ba tasan halinsa sarai
shima bazai so Auran hadiba.

Ta mike tafuce batareda ta gaya masa cewar da "yar rakiya zai tafiba wannan tafiyar tasan
Sarkin bazai bariba

*****
Ana gobe zai tafin Ummah tasa aka kira mata *KUYANGA*

Koda tazo ckn biyayya ta durkusa gabanta tana jiran umarni domin tayi tsammanin aiki aka
kirata tayi

Ummah tace mata "Kuyanga Zeenatu ko?

Ta daga kai sama

"To kifara shiri daga yau gobe zaku tafi turai keda yarima zakijene domin kiringa hidimta masa
komai nashi kece basai yace ba indai aikin wahalane kada kibari yayi Har sai ranar da yaga
damar dawowa zaku dawo tashi kije.



*KUYANGA* Tace "Angama Ranki yadade.

Ta mike tafuce daga dakin fulanin

Koda takoma sashinsu zama tayi a inda suke zama da MAHBUB Ta zabga tagumi tashiga
tunanin wai itace zataje turai tabdijan lallai zataji dadin Rayuwa zata canza tawaye tunda
tashigo gidan sarki tun tana karama bata taba futa wajen gari ba sai gashi abin farin ciki zata
keta hazo
TO ABIN BAKIN CIKIN FA? wata xuciyar ta tambayeta tare dayi mata tunin abinda zatajeyi turai
dakuma tuni da wanda zataje din

Take fuskarta tacanza daga walwala zuwa Damuwa

Zuciyarta tahau bugawa to shin wane irin zama zasuyi Alhalin halinsa bame kyau bane?ance
yana shan giya ance yana neman mata zance ya yadu agidan dan dai ana boyewane kada aji
abakin mutum a hukuntashi.

Jitayi antabata afurgice tadago kanta saitaga ashe MAHBUB ne abokinta abokin sha,awararta

Takalleshi kawai yau babu dariyar datakeyi masa

Yazauna kusa da ita yafahimci akwai damuwa yau kenan

Yacire mata tagumin da tayi yace " *ZEENAH*! Haka yake ce mata


Takalleshi akaro na biyu tasunkui dakai

Yace mata "meya faru naganki ckn damuwa anyi miki wani abin ne bayan nabarki anan din?

Ta dago ahankali tace "Bayan barinka nan gurin aka aiko kirana daga Fulani

Koda naje kiran saitake gayamin wai infara shiri gobe Yarima zaiyi koma Turai dani xai tafi
domin hidimta masa da koma kuma inmun tafi ba ranar dawowa harsai inyagaji yadawo
dankansa

MAHBUB yadafe kirjinsa tareda Rintse idanu yana kiran sunan Allah

Tabbas yashiga tashin hankali domin ayau yashiga halin dabai taba shiga ba arayuwarsa tunda
yazo duniya


Yana bude idonsa kwalla nabiyo baya yace mata "ZEENAH tafiyarki Turai tana daidai da tafiyar
farin cikina nackn gidannan Domin kece me deban kewa akoyaushe kuma ke nake kallo nake
jin dadi koda ina ckn jin Yunwa ke nake kallo naji nakoshi kinsan da cewa Nadade ina son.....

Yayi shiru yana goge kwallar datake gudu akuncinsa

Yakalleta ido da ido yace "ZEENAH bantaba gaya miki Sirrin zuciyata ba saiyau, yauma dole ce
zata saka domin naga zakiyi nisa dani Walh ZEENAH zaman da nake dake bana abokantaka
bace Na SO Ne zallah dan Allah kisoni koda bazamui Aure ba kice kema kina sona ko naringa
tuno kalmar inajin Dadi
*KUYANGA* Taji wani yarrr!ajikinta taringajin shigar wani abu tundaga tafin kafarta har zuwa
kwanyarta tabbas Tafahimci wannan abun dayake shigarta bakomai bane illah Son MAHBUB
ada itakam tadaukeshi aboki amini amma ayau saitaji yanayin yajuye mata da So

Tabbas tana sonsa itama bayama data tuno zasuyiwa juna nisa saitaji xcyrta ta karye hawayen
da basu zubo ba saigashi sunxubo ganin nasa ma sunzubo din

Tace ahankali " MAHBUB meyasa baka gaya min tuntuniba meyasa kaboye sai yau da muka
makarowa juna zaka fada yanzu gashi zanyi maka nisa

Yace "Duk nisan da zakiyi indai kina sona to tamkar muna tare ne kedai kitaimaka ki furta min
ko naji dadi.

Takalleshi tayi murmushi tasadda kanta akasa tace

"INA SONKA MAHBUB."!

yai ajiyar zuciya tareda yin hamdala ga Allah yace "nagode naji dadi ki rikemin Alkawari ki rike
amana kikuma kula inkun tafi bamu da ikon kanmu ZEENATU akarkashin ikon Sarki da
Matansa da "YA"YANSA muke bamu isa muyi musu da Umarninsu ba sai yadda sukayi damu
amma kada kiyi biyayya da aikin zalinci kada kisake acuceki kikasance me addu,a aduk inda
kike kikuma zamo me kamun kai aduk inda kika tsinci kanki domin kada ayi miki cutar da zata
karya miki Lagon Rayuwarki.

Taja ajiyar zuciyar Zuciyar xuciya tace "Naji na amince nakuma gode da Shawararka ya
masoyina .

.

Ya mike yace mata "maza tashi kije kifara shiri indare yayi kizo muhadu anan dan muyi sallamar
karshe

Tayi murmushi tace " sallamar karshe kamar wanda xan mutu inmunje can

Yayi murmushi yace " ba haka nake nufiba, nasan wataqila da sassafe zaku tafi kinga ai zaifi
kyau mukadaita mu dade tare mukara yin wata hirar soyayyar ko?

Tagyada kai tana dariya

Ya daga mata gira tareda kanne ido yana kallonta

Harya tafi yabar gun bata daina kallon saba tabbas MAHBUB yahadu rashin gata ne da yanayi
yasa cikar kamalarsa bata fito ba harsai ankura ido ake hanga atattare dashi

Ta girgiza kai kawai takara gaba tabar gun tayi dakinsu

Tana shiga Taga Aminiyarta ZULAI

Zulaihat tace "Hhhmmm inata nemanki ai saikuma nahangoki acan lambun soyayya.

*KUYANGA* Tayi dariya tareda dukan kafadar Zulai tace "harkin sakawa gurin zaman namu
lambun soyayya lallai Zulaihat ke "yar sa ido ce.

"Ba wani sa,ido gaskiyace ba lambun soyayyar bane?

"Eh bashi bane, to ai ba soyayyar akeba.

Cewar *KUYANGA* Tana dariya

Zulaihat tace "kifadawa keya yarinya kowa yafahimceku ingaya miki duk wanda yaga yanda
kuke tabbas zaigano ckn mintina batareda yasha wuya ba.

"Hhhmmm to inma soyayyar akeyi saime? Ko bamu daceba.

Zulai takama baki tace "ho! Ni na isa ince baku daceba aji haushina to walh bari kiji kundace da
MAHBUB tamkar danjunanku akayoku ina kuma Son tarayyarku.

Zama *KUYANGA* Tayi kusa da ita tace " Zulai gobe zanketa hazo fa.

Da sauri Zulaihat takalleta da alamar tambaya tace "hazo kuma?kamar yaya?

Nan Ta zayyano mata komai nagame da Rakiyar da Zatai wa Yarima Turai

Zulaihat tace "wayyo Allah na inama ni aka zaba.

*KUYANGA* Tace "tabdijan !kenan har wani son tarayya kike yi da Yarima?mutumin dakowa
yasan halinsa marasa kyau. To walh ni ckn bakin ciki nake ahalin yanzu da har aka zabeni

Zulai tace "Dan dai zakiyiwa MAHBUB nisa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login