Showing 18001 words to 21000 words out of 30540 words

Chapter 7 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf

wayar SAHABI yabarta a bude sunajin tana ring

Saida takusa katsewa kana Sahabin yadaga

Sarkine dakansa yahau masa magana

SAhABI yanutsu awaya jin martabane dakansa

Duk yanda ake ciki dai da mai martaba yazayyane masa kana yakara da koro masa Tambaya

SAHABI yakadu dajin hakan tabbas yasan abin babbane
Nan yagyara zama yafede masa biri hr wutsiya bai rage masa komai ba na abinda yasani duk
domin yaga yafutar da *KUYANGA*

Yarima yaita mamakin SAHABI nayanda yake zayyano bayanai

Da sarki yagamaji yaiwa SAHABI godiya yakashe wayar

Ran sarki yagama baci akan musantawar da Yarima keyi

Yarima yahau sose sosen kai jin Sarki yace masa " kaji abinda abokinka yace anyi hakan?

Yagyada kansa

Sarki yace "Kasan da saninka Inta haihu zan daura muku Aure da ita sannan ayanzu Alhakin
kulawarta yadawo kanta sbd abinda ke jikinta

YARIMA bai yi maganaba

UMMAH Ranta yabaci sosai da jin sannan hukunci

Take Sarki yasallami kowa aka watse

Kwana biyu da faruwar hakan YARIMA yabar gidan batareda Sanin kowaba ckn dare yagudu ko

UMMAH bata saniba

Yahada kayansa yasilale cikin dare yatafi inda yafito

Da labarin yashiga ckn gidan ba karamin tashin hankali mahaifiyarsa tashiga ba Don hartahau
zargin waiko Asiri akai masa dahar yabar gida


Abu kamar da wasa saida yakwana hudu labari ya isa fada

Tabbas Sarki ya guntsi bakin ciki awannan ranar yasan Yarima yanason yakun yatashine kawai
tun aranar yakara tabbatarwa kansa cewar Yarima bai cancanci yaxama sarki ba

Tuni aka hadu kowa da kowa afadar Sarki domin shi yakira taron

Inda yabayyana musu bakin cikin dayake ciki

Yace da *KUYANGA* dafarko inaso kizama me daukar kaddararki haka Allah yatsara miki naso
inga yarima ya aureki domin Asirinki yarufu kedashi dinma

To gashi Allah baiba yanunan ban isaba yawatsan kasa a ido yagudu yabar kasar


Dan haka inaso kikwantar da hankalinki da zarar kinhaihu zan karbi abinda kika Haifa hannu
bibbiyu nayi miki Alqawarin baxaku wulakantaba ke dashi Dan haka wanene kike so ackn
gidananna fadawa ko ckn BAYI xan muku Aure domin inwanke miki zuciya

*KUYANGA* tayi shiru kanta nakasa

Ayayinda MAHBUB dake ckn mutane nesa da ita yadago dakanta yana kallonta gashi dai har
ynzu yana sonta to amma wani Abu ma sukar ransa inya tuna ta yaudareshi duk da azaman
farko da akayi babushi ankawo masa Rahoton cewa Ba da saninta komai yawakamaba
Yarimane ya cuceta
Yana so yafurta kalma abakinsa ya gagara jiyayi mai martaba yayi masa kwarjini bakinsa yayi
masa nauyi

Yaso yafurta shine maaoyinta na asali na gaskiya da akai musu kutse arayuwa aka rushe musu
farin ciki

Allah cikin ikonsa MAHBUB saiya kasa magana Allah yanufi LAMIDO Da maganar data furgita
kowa harni

Hannu LAMIDON ya daga yana fadin "Ranka ya Dade ka Amince min Na Aureta domin inraya
sunnar manzan Allah nakuma shiryi taimaka mata kota halin kaka domin naji zuciyata ta kwanta
da ita....

Kallon kallo UMMAH suka hauyi da Jakadiya hakama MAMAH takalli FAATU yayinda FAATUN
takalli Mai martaba domin jiran Abinda zai yanke akai....



To muma fans da writers sai mubi layi afada domin jiran tacewar Sarki Abdallah


‍♀‍♂‍❤‍‍‍‍‍‍‍‍

Muje zuwa
[8/1, 3:17 PM] Ummi Tandama: *KUYANGA...*




*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)



60-65



AFIRGICE *KUYANGA* ta dago dakanta takai kallonta ga LAMIDO daya furta wannan kalami
wanda azatonto ko karya kunnenta yajiye mata saitaga da gasken ne jin Abinda Mai martaba
yace

"LAMIDO da gaske zaka Aureta? Har zuciyarka ka Amince?

LAMIDO da fuskarsa ke cike da Murmushi da Annuri yace "Na Amince har ckn raina babu wasa
ko yaudara zan Auri *KUYANGA ZEENATU* ko domin inga asirin gidannam bai buduba kuma
don itama inrufa mata Asirin Amma inhar kaida mahaifiyata kun Amince

Mai martaba yayi murmushi yace "Nidai na amince nakuma yi farin ciki kafitarni kunya domin
banzamo me kyamatar talaka ba ko bawa na duk daya muke mu dasu gun ubangiji Saidai ko
mahaifiyarka xamuso muji ta bakinta domin bata hakkinta.

FAATU tayi murmushi tace "Tunda har ka amince TAKAWA ainima dole in amince akullum Allah
nakewa Godiya akan yanda mukai dace da samun D'a nagari wanda akullum burinsa shine
yaga ya kyautata mana ya kuma bi sahun masu bin tafarkin ubangiji burinsa akullum yasami
lada arayuwarsa kaga dole muzamo masu bashi goyon baya Allah yasa hakan yazamo Alkairi
arayuwarsa

*"AMINNNN*"

Kaf Al,ummar gurin suka furta banda mutum biyu

MAHBUB da xcyrsa ta cika da kishi

Da kuma UMMAH da hakan bai mata dadiba

Mai martaba yadubi *KUYANGA* yace mata "Dazarar kin haihu za,a daura muku Aure da
LAMIDO kigodewa Allah sannan duk abinda kika haifa mace ko namiji zamu karba da hannu
bibbiyu Zansoshi kamar yadda nake son iyalaina tunda jinina ne za.a bashi kulawa sosai
bakuma nafatan yataso cikin tsangwama ko bayan raina dan hakan ki Kizama me mika
lamuranki ga Allah

*KUYANGA* Ta ckn ladabi ta Amsa tana godiya

Sarki yadubi LAMIDO yace "Asakamakon Wannan farantawar da kaimin ina me yi maka Albishir
da cewa kaine zaka haye kan karagar Sarauta idan nayi murabus nan ba da dadewa ba
Halayanka sunnuna kaine zaka iya rike masarautar nan ko bayan raina kacancnta babu haufi
kaine adalin Mutumin da akullum ake nunamin amafarki wanda zai zamo sarkin garinnan
Kadauko halayen kwarai na iyaye da kakanninmu kwarai ina godiya da Allah daya bani kai
amatsayin D'a

Yadubi Tarin jama.ar da suka cika fadar maza da mata na gidan yaci gaba dacewa "Inaso
kusheda daga yau LAMIDO Shine wanda zaizama jagoranku nan bada dadewa ba LAMIDO
shine xai xama sarkin gobe da yardar Allah.

Take Gurin yahautsine da sowa da murna fadawa Suka hau Kabbara

Bayi mata tsoffin da manyan suka gau guda

Yayinda MAMAH ta rafka guda tareda cewa sarki "TAKAWA Allah Yaja da ranka muna taya
LAMIDO murna kuma muna tayashi yin Godiya da wannan kyauta

Maimartaba yagyada kai yana murmushi

Dayake anyi tsit ana sauraren maganr MAMAH

Saijin kukan UMMAH Akayi ta dora hannu aka tana fadin "Shikenan burinku yacika kun raba
D'ana da gidan ubansa kunyi kutunguilar da D'anku zai zama sarki kuma walh baku isaba

Sarki yadaka mata tsawa

Amaimakon tayi shiru saita mike tana fadin "walh baza,a dakeni ahanani kukaba. Tafuce fuuu
tana kukan bakin ciki


LAMIDON da kansa yanuna godiyarsa ga sarki

Maimartaba yahau shafa kan LAMIDON yana fadin "Kacancnci hakan LAMIDO fatana
harkullum Abinda kayi min na Farantawa to ubangiji Allah yafaranta maka kaima

LAMIDO ya amsa da "Amin, Aminn


Saida Sarki yabada umarnin tafiya sannan kowa yatashi yayi nasa guri


Jakadiya har sashin FAATU tabisu tana Rangada guda

Tareda fara yi masa kirari na sarakai

Saida tafaranta musu rai
Da kalamanta garesu masu dadin saurare sannan tafuta


Jakadiya
Tana barin Bangaren FAATU ta wuce sashin UMMAH Domin tayata Jimami da Alhini tunda tafi
kowa sanin yanda UMMAH take da burin taga Yariman yazamo sarki

Ta tarar UMMAH tana waya da Yarima tana bashi labarin komai daya faru sannan Tabashi ixinin

akan yadawo Gida maza maza akwai abinda take shirya masa akai


Yarima ya amsa da to zaidawo nanda kwana uku ko
biyu

Kai UMMAH ta hada da guiwa tareda dayin shiru na minti Talatin

Jakadiya na gefe taa jiran tafara kawo gulma da soki burutsin karya Data saba donta sami fada
agun Fulanin

UMMAH tadago takalleta tace mata

"Jakadiya jeki kya dawo anjima ayanzu baxan iya maganaba ina ckn wani hali banda lokacin
zanta wata magana kibari nahutawa bakin cikin dana dauko afada

Sum sum jakadiya ta tashi tafuce guiwa asage


Itako *KUYANGA* Kwana tayi ba ci basha Sai dakyar Akwana na biyu da Yin abun sannan
Zulaihat data matsa mata taci abinci kadan duk tasaka damuwa ackn ranta

Zulaihat tace mata "walh kigodewa Allah ma ayanzu ji nake dama nice ke kuma nasan bani
kadai ke wannan tunanin ackn bayin gidan nanba domin kin xama "yar baiwa tunda gashi Allah
yakusa "yantaki

Zaki zamo matar sarki Surukar Sarki.……

"Uwar Shege ko Shegiya kuma ba.

Cewar Zeenatun tana matsar kwallah

Zulaihat tace "kibar fadin hakan domin inma shegene ko shegiya duk kafin yafito duniya ne ko
tafito duniya domin Kinji ta bakin Sarki yakarba kuma za,a bashi kulawa zai zamo tamkar d'a ko
"ya me "yanci to balle LAMIDO natare dake kinyi matsayin da bakowacce zata iya takashiba
ackn mu *KUYANGIN* Gidan kema kinsan hakan
Zeenatu tace "hhhmmm ke kike ta wannan tunanin ni tunani na yatafi ga masoyina MAHBUN
tausayinsa nakeji yanzu shikenan ……

Zulaihat ta daga mata hannu "saurara niarki dameni da xancensa domin banga yayi hobbasa
yanuna soyayyar da yake mikiba agun dan da,a ce sonda yake miki har zucine da kafin
LAMIDO yace wani abu akai tuni shizaice

Dan Allah kicireshi aranki tunda yanzu bake kadai bace ba,bafa ason me ciki da shiga damuwa
balle kuma abinda zaki haifa me matsayine agidan

Zeeatu tace "Zulaihat da alama bakisan radadin soyayya a zuciba Ni LAMIDO baya gabana
Mulkin gidannan baya gabana ko arzikinsu kawai Matsayina nake tunawa ayanzu


Zulaihat tace "ke nifa Allah nagodewa da bai nufi MAHBUB da magana akan kiba agun
natabbata da tuni LAMIDO baice komai b.……

Sallamar Wata yar matashiyar yarinya ce cikin bayi tashigo dakin nasu takatseta tashigo musu
da ladabi tagaidasu

Zulaihat tace "Laminde ya akai akwai wani abune?

Laminde tace "Ustaz ne yace Zeenatu taje yana waje.

Da sauri Zeenatun tace mata "kije maza kice masa ina zuwa

Ta xira hijab tabi bayan Laminde data futa da mintina uku

Yau ya canxa gurin tsayuwa can gefen hanya yaja tunga yatsaya yana jiranta

Tun daga nesa yakura mata idanu yana kallonta tayi haske fuskarta taxamo yar kuyas tayi kyau
saidaita rame

Takasara gareshi da sallama tagaidashi

Ya amsa yana kallon yana fadin "ZEENAH ina sonki amma dole inbarki, yanzu kinmin nisa kinfi
karfina.……

takatseshi dacewa "kadaina fadin haka komai nufin Allah ne matar mutum kabarinsa saikaga
muna tamune Allah na nasa zai iya kuma canza lamarin aduk sanda yaso bamu zataba kaifa
malamine kasan hakan kazama me tawakkali mana kana fa da Sani....

Yace "Duk na susuce Zeenatu ayanxune akwanakin nan biyu da faruwar lamarin naji kaunarki
ta karu araina tamkar ana kara rura wutarta ma

Kokinsan YARIMA yadawo Gida adaren jiya labarin yakarade gidan nan. Sarki ko kallonsa
baiyiba haryanzu yayi fushi dashi kuma duk akan ne "yar baiwa

Duk da gabanta yafadi jin ya ambaci sunan yarima sai bata nunaba a fuska ta dake tareda

kawar da maganar ma tace masa

"Ko awane hali nake bazan manta dakaiba bakuma zan daina son kaba kaine kadai wanda
naso a afarko da karshe ackn Duniyar nan ……


Adaidai lokacin da *KUYANGA* Ke furtawa MAHBUB wannan daddad'an kalma ar daidai
lokacinne Allah yakawo yarima yazo xai girfta ta gun yahangosu yabiyo ta jikin katangar da
suke tsaye kunnansa yadebo masa wannan kalami da muryarta yawatso akunnansa

Yaja da sauri yatsaya baya so su ganshi domin dan ita kawai yabiyo ta gurin

Rintse idanunsa yayi wani abu yaji yana masa yawo akirjinsa

Tabbas yau yakara aminta da zargin dayake mata na soyayya da MAHBUB duk da ta taba
tabbatar masa amma kalaminta na yau yakara bashi haske

Ya dafe kansa domin Wani hali yashiga Akanta yadawo adalilinta tun daya hada kayansa yabr
kasr yakoma turai yakas sakat Allah yajarabceahi da azababbiyar kaunarta dayaji batun da
mahaifiyarsa ta gaya masa na LAMIDO zai Aureta bakaramin tashin hankali yashiga ba
domin yasan shirinsa yagama baci
Nemanta yakeyi ido arufe ruwa ajallo Donsu keb'e yanuna mata nadamarsa ya amshi cikin nasa
domin ta yarda dashi yakuma roki alfarmar tarakashi gun Sarki Ta tayashi neman yafiya
Yasan ita din me hkr ce da biyayya bazaisha wahalar taba

Waishin ma tawace hanyar zaisamu hakan? Anya bai makaro ba kuwa hhhhhh fans kufito ku
gaya masa ���




Muje zuwa
[8/2, 5:04 PM] Ummi Tandama: *KUYANGA..*




*KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION*
{United We Stand and succeed;Our Ambition is to entertain & motivate the mind of reader's}

*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)


*KAFIN AYI NISA KAI TSAYE INA MIKO GAISUWA DA GODIYA GA D'AUKACIN "YAN CIKIN
GIDAN NABILA'S ONLY 4 STARS WRITERS MA,ABOTA KARANTA KUYANGA MUSAMMAN
MASU COMMENT*





65-70


A SANYAYE Yarima yajuya da baya don gara yakoma kada wani cikinsu yaganshi su rainashi

Yakoma sashen mahaifiyarsa ya tararta tana Safa da marwa atsakar dakinta tana buga
hannunta daya cikin daya tana kwafa da alamar har yanzun ranta abace yake tana kuma ckn
halin damuwa

Tana ganinsa tahau fadin "Ya Akai yarima kasame tane?


Yazauna akan kushin yana fadin "Bansami ganawa da itaba UMMAH natarta ne da wani
Kazamin bawa da take so..,UMMAH Takatse shi da sauri

"Au dama ackn gidan nanma akwai wanda take soyayya dashi ? Ashe haka tazama yarinyar to
da alama ma cikin agida tayishi kenan

Yarima yadago da sauri yadubi mahaifiyarsa da jajayen ido yace "A,a UMMAH tunjiya Dana
dawo nagaya miki cewar Wannan cikin fa nawa ne kada ki kakabawa wani makaskanci mana
jini na karba.... " Dakata!

Ta dakatar dashi da daga murya ranta abace

"Wai bazaka daina kiran cikin jikin *KUYANGA* da sunan mallakin kaba,walh inkai ka karba to
ni ban karb'aba domin bazan yarda da shege ace shine jikanaba jikanma ajikin baiwa Allah
yakiyaye dama ajikin wata baturiyar ne ko " yar sarauta da sauki

Yarima yace " Amma ai u UMMAH shi .mahaifina
yakarba ballantana ke da kike mace kikafi sona.

Tace "Dan babanka yakarba be dameniba domin yakarbane da wata manufa aransa tunda
bayason azageshi bakuma yaso Dan daza,a haifa yatashi yarasa madafa amma nasan ba har
zuci yakarba

" kidaina fadar haka UMMAH.

"Saina fada din kaida bakasan inda yake mk ciwo ba baka ma damu da kyautar kujerar sarauta
da Aka baiwa LAMIDO ba

Yarima yace "Ni wannan kam baya gabana fatana dai ayanzu *KUYANGA* zeenatu ta Amince
da abinda nazo dashi sbd Allah yajabceni da kaunarta UMMAH kitaimaka kiyi wani Abun walh
sonta nakeyi sosai har cikin raina

UMMAH ta maka masa wata harara tace "Shima LAMIDOn daya Amsa yana sonta zai Auretan
nasan badan Allah yayiba a to.

Yarima ya shiga tunani

Kai Yadafe don kan nasa ke bugawa dolene yasamo mafita akan MAHBUB Domin irin kalamin
dayaji tana watsa masa na soyayya tabbas su yake muradin yaji wataran tagaya masa

Toshin ta wace hanyar? Ta Yaya?

Yakasa samo amsar tambayar domin kansa yakulle Dole saiya nutsu

UMMAH bacin ran abinda Yarima yaxo mata dashi baisa tasami nutsuwa ckn rantaba tabbas
dolene tasami mafita akai rana zafi inuwa quna knn domin wannan shine ana wata ga wata can
Hukuncin da sarki ya yanke nabaiwa LAMIDO sarauta nacinta arai saigashi Yarima yazo mata
da wani batu wai yana son *KUYANGA* to tawace hanyar ma zaisameta Alhalin LAMIDO
yakarba kowa yashaida hakan lokaci kawai ake jira

Yarima yadago dakansa yaga mahaifiyarsa ta hada kai da guiwa
.yasauko kasa Yakama kafafunta yana fadin

"UMMAH kitaimaka mini kije ga mai martaba kinemamin yafiya sannan kifada masa batuna na
karbar cikin *KUYANGA* da zanyi kice nayi nadama sharrin shaidanne inasonta yadaina fushi
dani

Wani dunqulelen abune yatsayewa UMMAH a maqoshi na takaici da bakin ciki

Taki jinin jin Kalmar nan dayake furtawa na son *KUYANGA* dayake fada mata yanayi domin ita
ji takeyi tana kara tsanarta ma tunda itace tazamo silar rushewar Burinta ayau,tayi nadamar
amincewa da tayi tun farko daya yatafi da ita kasar waje tasan da bata yarda sun tafin ba da

tuni hakan bata faruba tunda gashi akan Yariman yak'ita yaki cikin ne LAMIDO yashirya
manaqisa yakarba don abashi sarauta kuma anbashin kamar yadda sukeso kuma bazata taba
bari suji Dadin yin mulkinba indai daranta saita zame musu masifa a ckn gidan

Wannan tunanin tane

UMMAH dai taga Yarima da Gaske yakeyi domin shirin kuka yake mata akan bukatarsa

Dabara ce tafado mata tace masa "kwantar da hankalinka shalele zansan abinyi agun Takawa

Yace " to agun ZEENATUN fa?


Tahade rai

Yamarairaice mata Taga dai da Gaske ne lamarin nasa saitahau tunanin anya kuwa ba Wani
abun akaiwa D'an nataba mutumin dayaqi Abu futuk kuma cikin "yan kwanaki saiya haukace
akai

Lamarin Allah nefa UMMAH �Allah yakara inji fans �


Takama hannayensa itama ckn marairaita tace masa "YARIMA kai D'ane D'an fari abin so aduk
wani gidan sarauta baikamata ka lanjare a son BAIWA ba kafi karfin Auren *KUYANGA* ajinka
da kimarka da izzarka na Dan sarki zai ragu inhar ka Auri *KUYANGA* inaso kayi hakuri kabarta
ni dakaina zansamo maka ko ackn gidan sarautar mune akwai mata masu kyau adangina
mahaifina kafin ya mutu yayi sarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login