Showing 21001 words to 24000 words out of 30540 words
Chapter 8 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf
yanzu babban yayana shine sarkin garinmu kasan da haka
Babbar masarautace datafi wannan munada mata kyawawa yan boko wayayyu sai wacce
kazaba babu me kinka walh kanada cikar da namiji kaidin gwarzone me tattare da mazan taka
gaka kyakkyawa kafi LAMIDO kyau da kwarjini Meye naka na damuwa da Baiwa Alhalin kafi
karfinta shi din dayace abashi ita ya Aura kabarsu dama da ita yadace
Yarima yakyabe fuska yace " UMMAH bazaki ganebane
Tace "tayakuwa zangane kaki amsar batuna
Dayaga da Gaske takeyi baxata sakkoba saiya rushe mata da kuka yasan lagontane bata son
damuwarsa balle ganin hawayensa
Nan take kuwa ta rude tace masa yayi shiru zata duba lamarin yaje zuwa gobe kafin tasan
abinyi
Yana Fita ta aika aka nemo mata jakadiya
Jakadiya na zuwa tagurfana gabanta
" gaisuwa nakeyi Uwar dakina barka da warhaka gani ckn ladabi mezan miki ?nasan bukatace
babba tasa kk kirani
UMMAH tagyada kai tace "tabbas kuwa jakadiya domin Yarima yaxo min da banzan zance wai
yanzu shi *KUYANGA* yakeso kuma ya amince da cikin jikinta nasane
Jakadiya tadafe kirji tace " wannan Abu bai Dadin jiba kamar Wanda akai masa surkulle
UMMAH TACE "Maza kije kishirya kije min gurin GOGAL matsafiya kice inaso acire masa son
yarinyar ckn kwana daya
Da sauri jakadiya tace " angama uwar dakina.
UMMAH takawo kudi tabata jakadiya tafuce da sauri
Amma kafin ta tafi gurin matsafiyar tasu dake bayan gari saida tafaki ido tashige Sashin
MAMAH Takai musu Gulmar wai ga Yarima can yarikicewa Mahaifiyarsa waishikam yanzun
*KUYANGA* Yakeso kuma ya amince cikin jikinta nasane
FAATU DA MAMAH sunyi mamakin wannan Abu sunkuma Daukeshi arainin hankali yariman
yazo dashi sunsan kuma TAKAWA bazai daukaba
Yo muma ba dauka zamuyi ba
Muje zuwa
[8/3, 11:13 AM] Ummi Tandama: *KUYANGA*
*_KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
*wannan shafin Sadaukarwace ga Binta kabir Auntyn Yasmin Mrs ibrahim R/k quarters*
Kawata inayinki Ina godiya da tayani posting a grps
70-75
JAKADIYA tana isa cikin Dajin tayita shiga cikin Ko tsoro babu atare da ita haka har tazo
gindin wani tsauni ta haye daf !daf!!daf!!! Ta nufi wata babbar bishiyar Kuka dake kan katon
Dutsen
Tana isa ga bishiyar saita cire takalmanta ta tsaya gaban bishiyar tana fadin "Gafaranku dai
manya da kanana na fadar GOGAL ga jaririya tazo tazo Neman taimako da cin Albarkaci ayi
min iso gurin Hakima mandiya shugabar matsafa
Wani kuka taji yana tashi na muryoyin yara daga ckn bishiyar taitaji harna tsahon minti talatin
can kuma taji shiru sai kuma ga amsa kuwwar Babbar murya tana fadin
" SANNUNKI DA ZUWA HATSABIBIYAR JAKADIYA GAMANDI ME HADA WANDA TASO
Jakadiya ta hadiyi yawu domin kirarin nan bai mataba tasaba yi matashi
,"Barkanki da isowa GOGAL
Cewar Jakadiya
GOGAL da ba,a ganinta saijin muryarta ta jikin bishiyar tace da jakadiya
"NAji zuwanki angayamin tunkina afarkon daji nasan meke tafe Uwar Dakinki ta aikoki akan
Acirewa D'anta son da yakewa *KUYANGA* Daga zuciyar sa ko?
Jakadiya tace " E kwarai hakan yake.
Jakadiya taci gaba da cewa "Hakan data tsara nikuma incanza salon abun yazamo amaimakon
ancire masa son yarinyar saidai ma akara masa don ya axabtu sosai
Yakasa sakat yashiga damuwa akanta sakamakon yanda yasaka yarinyar adamuwa
Wata bunsurar dariya aka sheke da ita dg jikin bishiyar kukar
Daga can kuma akace da jakadiya " ko baki fadaba hakan za,ayi domin Baxan iya cire wannan
soyayyar dake ransaba na duba naga ajiyar Allah ce ban isa in girgizata ba Dan haka zankara
da Dora aikinki da kika bukata domin nima ayaune zanrama abinda YARIMA yataba yiwa
Jikana yafita rangadi suka hadu ahanya YARIMA yabuge minshi da doki yafadi ko kulaminshi
YARIMA baiyiba harya suma agun
Jakadiya tahau gyada kanta
Tana mamakin jin wannan labari na GOGAL duk da tasan zai aikata din
Jakadiya tahau godiya tareda ajiye kudin da uwar dakinta tabata agindin bishiyar ta mike da
niyyar tafiya
Sai taji ana mata magana da muryar tsohuwa ta jikin bishiyar
"Kema kibi lamuranki na gidan nan a sannu domin a irin zaqewar da kikeyi wataran zaki girbi
kashinki ahannu domin akwai abinda zaki aikata zaija miki babban aiki da kuma danasani
HAHAHAHA
Aka rufe da katuwar dariya
Jakadiya na kyarma tace " Ataimaka agayamin ko mene wannan Abu da zaijamin danasani
don inkiyaye
Dariyar dai akaci gaba dayi mata babu wani Karin bayani
Tana kallo kudin data ajiye yabace sundauke
Difff! Taji anmata tasan bakuma xasu karace mata kanxil ba shiyasa ta tafi da baya kamar
yadda ta saba
*******
Yarima Yana kwance akan makeken Gadonsa yanata juyi yakasa controlling din kansa akan
soyayyar *KUYANGA* Da take azabtar dashi arai
Hotonta ke masa gixo alokacin dayake kanta a time din suna Turai
Tabbas Yanda takeda tarin baiwa bazai iya barin taba saiyayi yanda yayi ya mallaketa baxai
taba barin LAMIDO ya Aure taba
Can kuma saiya mike da sauri ayau saiya ganta kota halin kakane koda zai karya billensa
yashiga ckn gidan bayin bazaiji wani Abu aransaba Sontane yaja
Yazira kaya ajikinsa dama dagashi sai gajeran wando da singilet
Yafito farfajiyar gidan yatsaya yana karewa kowa dake wucewa kallo duk Wanda zai wuce ta
kusa dashi saiya kawo masa gaisuwa
Da ka kawai yake amsawa
Sarkin gida ya hango agurin ajiyar dokuna yana baiwa wani farin doki da LAMIDO kefuta dashi
abinci
Matsawa yayi kusa da Sarkin gidan tareda kwalla masa kira
Da sauri yabar abinda yakeyi yataho gurin Yariman
Ya mika gaisuwa tareda tsayawa ckn ladabi agefen yarima yanajiran abinda zaice masa
Yarima yace "Sarkin gida Inaso kaje ka kiramin *KUYANGA* Zeenatu
Sarkin gida yace " Tana tareda MAHBUB acan bayan Gamji da suka saba zama
Yarima yadaka masa tsawa yace "To intana tareda wani bazatazo ba ko Yaya?shi wanin
yafinine ?mijin tane ko waye dinta?
Sarkin gida yahau fadin " kayi hkr ba nufina kenan ba sanar maka nayi dai bata gida agarceni
bari aje can akirata
Yatafi da sauri inda yasan zaisametan
Yarima yahau cizar yatsa jin wai tana can tareda MAHBUB tabbas dole yadau mataki akan
wannan Bawan dazai kawo masa tsaiko
Yananan har lokacin da Sarkin gida yadawo tareda ita tana biye dashi sanye take da
zurmemen hijab harkasa
Yaringa kare mata kallo na yanda take tafiya anutse kanta akasa
Gabantane yake faduwa domin batasan dame yazo mataba
Tana ZUWA gareshi tagaidashi tareda tsayawa gefe kanta akasa
Yana murmushi yace
"Zeenatu dago kai kikalleni gani agabanki da kokon barata
Nazo Neman yafiyar kine
Akan laifin dana aikata miki nayi nadama nakuma karbi cikin jikinki domin tabbas D'ana ne ko
"yata zaki Haifa jininane inason abuna ki kwantar da hankalinki kisaki kowa ki kamani domin
rufuwar asirinki
Ta dago da sauri takalleshi ido cikin ido ayau Allah yadauke mata shakkarsa tace masa " Ai
asirina yagama rufuwa atun lokacin daka budeshi Allah yanufi Dan uwanka da rufeshi kuma
abinda yaimin bazan taba mantawa dashiba bakuma zankishiba na aminta shi zan
Aura....dasauri yakatseta
"Kina nufin kice Kinason LAMIDO?
Ta girgiza kanta
" zan Auri LAMIDO sbd halaccinsa agareni da muhimmancinsa aguna da gun abinda zan Haifa
sannan bazan bijireba INA ganin kima da daraja ta me martaba amma SO d'aya tak!
MAHBUB nabaiwa shi
Kamar ta watsa masa wuta amakoshi yaji jinta Ambaci MAHBUB take so
Tabbas Zeenatu tacanxa yaushe tayi baki haka yaushe tasan tagaya masa magana tsararo
babu taunawa tabbas babu musu MAHBUB ne zai kintsa mata komai akansa tunda suna tare
yasan gunsa ta taho kuma saiyayi maganinsa
Yadubeta duba na tsanaki yace "Nayi alqawarin saina raba zuciyarki da soyayyar bawa Mara
amfani
Tace " agunkane baida amfani amma aguna yana da amfani
Tana gama fadin haka tajuya tatafi abinta
Ayanxu ji take komai zata iya gaya masa tunda yazubda mutuncinsa agunta
Yadade tsaye yana kallonta harta qule zancenta na masa yawo azuci kamar tadaba masa wuqa
haka yaji tabbas ayau ba sai gobe zaiyi maganin MAHBUB shine sila nakomai datayi masa
ayau
Kafin yabar gurin saida ya yanke shawarar abinda zaiyiwa MAHBUB
wasu fadawa Yasamu guda biyu dasuke girmamashi ya yafito su suka taho da sauri suna
zuwa yace musu
"Wani aiki zanbaku me tattare da hatsari amma zaku samu abin alheri me tsoka
Sukai farat sukace " indai zamu samu matsayi agunka da kuma abin duniya kowane irine
zamuyi
Yarima yaji dadi yagyara tsaiwa yace "nasan zaku iya daganinku anga jarumai Wani bawa
nakeso kukashe adaren yau...
Yayi shiru yana so yaga wane action zasuyi ko zasu firgita saiyaga sabanin hakan ko gezau
basuyiba da alamun zasu iya abinda yafi hakanma dama da ganinsu tantiraine
Yaci gaba dafadin " dazarar kunkasheshi zanbaku gida ackn gari zanbaku kudi har naira Miliyan
daya duk kuraba amma kuxama masu sirri so nake dasafe atashi da kukan mutuwarsa
Sukace atare "angama ranka yadade.
Yace " kutafi kujira zuwa dare da zaku aikata hakan saikunyi natabbatar zanbaku abinda na
alqawarta muku
Sukace "to shikenan Ranka yadade.
Suka tafi shima yajuya yashige ciki
Itama Jakadiya dataji komai akan kunnenta tajuya koma inda tafuto tana gyada kai mamakin
abin fal ranta lallai Yarima yazama Takaddari acikin gidan Sarki......
To fans mujira zuwa safe muga ikon Allah mukasa mutsare mujira
Auntyn Sayyada da Shahida CE
[8/4, 11:18 AM] Ummi Tandama: *KUYANGA...*
*_KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
75-80
Kwana Jakadiya tayi tana Tunanin abinda kunnenta yajiye mata akan Abinda YARIMA yasa
ayiwa MAHBUB tabbas indai suka aikata hakan Sai ta tona asirinsu
Da gaggawa wata zuciyar ta kwabeta
"Ke kinsan ko abinda kk fada?yariman zaki tonawa asiri toki tabbatar indai kika fada sunanki
matacciya kema kokuma korarriya a gidan Sarki domin yarima da mahaifiyarsa babarinki
zasuyiba
Ta tuno yanda mahaifiyarsa keji dashi da sangartashi da gudun Bacin ransa
Ta tuno rashin mutuncin Yariman
Sannan ta tuno Yanda za.aita bibiyarta ana Neman cikakkiyar sheda daga gareta dazarar ta
tona asiri domin dolene saita kawo shaida inko bata kawoba za,a hukunta akuma koreta agidan
dama UMMAH ce ta daukaketa agidan
Dataga jan bakinta tayi shiru yafiye mata alkairi saitaja komai tasa agefe Dan yafiye mata
kwanciyar hankali
********
Tashin hankali Wanda ba,asa masa rana domin abangaren bayi suntashi dashi
*KUYANGA* Da zulaihat suna kwance da Sassafe ihun da suka ringa jiyowa da koke koke
agidan shiya tashesu afurgice
Zulaihat tace da ita " munshiga uku wannan ihun kuwa na lafiyane.
*KUYANGA* Tace "Ba lafiyaba gaskiya tashi muleko
Suna futowa bakin kofarsu sai suka hango dandazon mutane Asashin maza
Suntaru gefensu kuma mata ne tsoffi da yaran mata sunata kuka
Zulaihat ta yafito wata yarinya Laminde da batafi shekara gomaba yar Aiken Uztaz MAHBUB
Laminde tana goge hawaye ta iso garesu
Zulaihat tace mata " Ke laminde meyake faruwa agidanne?
Cikin kuka laminde tace "Tashi kawai akayi akaga wai UZTAZ ya mutu kuma ance kasheshi
akayi da fullo....
" me!? Afirgice *KUYANGA* ta riketa tana tambayarta "waye yakashemin MAHBUB wayyo
nashiga uku in Zeenatu
Ta Dora hannu aka tana kuka
Zulaihat da jikinta yayi sanyi takamo Zeenatu ajikinta tana fadin
" kada kidaga hankalinki muje mutabbatar dai
Tajata suka karasa gurin tsoffin
Lantana wata sa,arsu ta matso da sauri garesu tana kuka tana fadin "shikenan Ankashe uztaz
Ya mutu ancucemu munyi rashin mallam
Zulaihat ta kara yadda sai kuka itama
Wata tsohuwa Iya Sha,awa mutuniyar Kirki tana son *KUYANGAR* ta maso da sauri gunsu ta
janyo *KUYANGA* da taketa rufza kuka hannu aka tace mata " yi shiru Zeenatu kiyi masa
addu,a Wanda kuma duk yayi wannan Abun Allah yatoni asirinsa
Zulaihat tace "wai iya me akayi masane?
Iya sha,awa tace " antashi dai anganshi yana kwance ayashe akasan katifarsa ga filo akan
fuskarsa
Awuyansa da alamar shaqeshi akayi yajigata ma kafin sukasheshin ba,a gano kosuwaye suka
aikataba
Kuka sosai suka ringayi dagama jin wannan mummunan labarin
Kaf kafatanin gidan sarki sun shiga tu,ajjibun abun
Banda wadanda suka aikata da yarima
Itako jakadiya ackn bakin ciki ta wuni
Gashidai tasan kosu waye amma badamar bayyanawa tana tsoro
Taji mutuwar MAHBUB sosai har kuka tayi itama
Yo muma munji mutuwarsa fans kutaho muje gaisuwa gidan sarki
Matan Sarki kaf sun halacci bangaren Bayi domin yi musu gaisuwa Mai martaba yazo gun
ansallaci mamaci amma sai yakoma fada akaci gaba da karbar gaisuwa acan
Suma bangaren bayi mata a bangaren Tsoffin gidan suka taru ake zaman makokin
*KUYANGA* Tafi kowa agun damuwa domin jiyan sun Dade tare suna hira me dadi yana bata
shawara na yanda zata zauna da rayuwarta tayi kyau inta Auri LAMIDO
sosai yaita kwantar mata da hankali yana gaya mata irin son da yake mata
Ko zuwa kiran da yariman yai mata suna taren shiya takura mata saida taje ajiyan
Kwana tayi baci basha saida iya sha,awa ta takura mata
Sai aranar sadakar ukun MAHBUB sannan LAMIDO yazo bangaren Bayi ya aika tazo domin
yai mata gaisuwa
Ta iso cikin hijab har kasa kanta akasa
Tagaidashi ckn sanyin murya
Idonsa akan fuskarta yana murmushi ya amsa tareda yi mata gaisuwa
Ta amsa tana yi masa godiya
Yace "Allah yajikansa yabaku hakuri da juriyar rashinsa
Ta dago da kanta takalleshi tace " Amin ngd
Yana murmushi yace "bakomai yiwa Kaine bari nakoma.
Yakawo kudi masu yawa yamika mata
" gashi kibada Sadaka
Takarba tana fadin "Allah yakarba.
Tajuya ta tafi tana zancen zuci " wato shi wannan nafahimci yana matuqar son yaga ya aikata
aikin lada.
Tayi murmushi "yanada hali me kyau ga yawan fara,a
*KUYANGA* kodai kin yaba ne...??
*********
Sai ranar sadakar bakwai Yarima yazo mata shikuma Gaisuwa
Fuskarta babu annuri tafuto gurinsa tagaidashi tayi shiru agefe guda kanta akasa
Yace mata " nasan kina cikin damuwa na rashin masoyi to amma yakamata ace kinsa hkr
aranki domin Allah yafimu sonsa shiyasa yakarbi kayansa
Tayi masa banza don ba burgeta kalaminsa yayiba
Yaci gaba da fadin "duk kinrame Zeenatu Saikace Wanda mijinta yarasu
Bata dago takalleshiba balle tabashi amsa
Dayaga batada niyyar magana saiyayi mata sallama yatafi kawai yanajin farin ciki aransa
Yasan gaba dole zata soshi inta zama mallakinsa domin Saiya kauda LAMIDO shima inyaso
ahakura abashi ita don bazai juri yaga tazama mallakin waniba alhalin ayanzu yana mata
mugun so
Bayan wata biyar Cikin *KUYANGA* yana wata Takwas alokacin Yarima yazo mata da Kudi wai
tayi sayayya na kayan jarirai
Taso taki karba saikuma taga dacewar karbar dazatayi domin Allah ma take godewa da har
Ya karkato da hankalin yariman kan cikin tunda wasu sunshiga zarginta afarko tunda yariman
yace bacikinsa bane ake tunanin cikin wani ne
YARIMA yazo da Sati biyu *KUYANGA* ta haihu ta haifo D'anta Zankadede kyakykyawa Wanda
tsananin kyansa yasa aketa zuzutashi agidan tamkar balarabe
Saidai kuma yadauko wasu abubuwan na yarima afuskarsa kamar kwayar idonsa da habarsa
sannan wani ikon Allah saiga cindo ahannunsa na hagu
Haka yarima yanada wannan cindo ahannun hagu
Wannan shiya kara tabbatarwa Al,ummar gidan lallai wannan yaro mallakin Yariman jinin sane
ba haufi
Mai martaba ya Dade yana kallon Yaron
Yatabbatar da wasu abubuwan na yarima ajikin Yaron saiyaga tamkar yarima yana Yaro
Wata kaunar yaronce taringa shigar Sarki yaji inama tahanyar sunna aka haifoshi
Koda yakebe shikadai kuka yaringayi waiyau shine da jikan dayazo bata hanyar Aureba yarima
yacuceshi yabata masa suna
Yarima baidauko halinsa ba baiyi shashanci ba yana saurayi Komai nasa da nutsuwa da
kamun kai yayishi harsaida yayi Aure yasan mace to amma gashi Allah yajarabceshi da
abubuwan tir agidansa
Munjajanta maka Sarki Abdallah
Abin arxiki FAATU da MAMAH suka hada sosai na kayan jariri aka kaiwa *KUYANGA*
Jakadiya tabazama ta gayowa UMMAH
Fulani tahau gyada kai tana fadin "munafukai nagama ganosu sunayine badan Allah ba saidon
Neman suna da kuma Neman duniya agun Sarki
Kinaji ko Jakadiya nima zanhada kayan inbaki kikai badan Allah zanyiba saidan wadancan
munafukan Dan