Showing 27001 words to 30000 words out of 30540 words
Chapter 10 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf
irin LAMIDO sai antona
Toooí ½í¹„í ½í¸³fans *KUYANGA* me kuka fuskanta ne a Heart din KUYANGA
To kodai ta kamu ne ???
Muje zuwa
[8/8, 8:11 PM] Ummi Tandama: í ½í³¿ *KUYANGA...* í ½í³¿
*_í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœí ¼í¿» ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv* í ½í²˜
(Auntyn S&S)
90-95
FAATU ce A zaune aturakar mai martaba bayan yagama cin abinci yadubeta yace "Kince
kinada magana inajinki meke tafe dake akwai damuwane?
Ta gyara zama tace "Dama maganar LAMIDO ne Naga tunda har anyi sadakar arbain din jaririn
Zeenatu nace to me zai hana atsaida ranar Auransu da LAMIDON ba tunda har ya amince
kuma naga kamar yafara sonta
Murmushi Sarki yayi yace "To babu komai sai a tsaida Wata daya mai zuwa sai adaura Auran
nasu bamusan me Allah ya ajiyeba kuma Inaso aranar da za,a daura Auran ayi bikin dorashi
Kan karagar mulki natsufa yakamata nayi murabus nadorashi akai duk abinda nakeyi wanda
yakamata yake kaina zai iya sannan ya cancanta don haka zansa ayi shela agari kowa yasanda
wannan rana
FAATU tace "To amma Takawa kana ganin wannan abun dakayi bazai kawo rabuwar kai
atsakaninsa da Dan,uwansa yarima ba mahaifiyar safa ta kudurci dantane zai zama sarki
natabbata zataji ba dadi koma tayi bore
Sarki yace "Nike da iko da komai daga kan mutan gari da bayi da ku kanku iyalaina da dukuma
Sarautar kanta Dan haka babu me canzamin zabin da nayiwa Garina
Ckn biyayya FAATU tace " angama ranka ya Dade Allah yaja kwana yakara lfy
Yace "Amin Fatima. Inkin futa kituromin LAMIDO
tace "To.
Bayan futarta tazarce Dakin MAMAH domin takai mata wannan batu sbd duk abinda take ciki
saita sanarta kuma bata zartar da komai saida izininta
Jakadiya na zaune kusa da MAMAH tana mata hira
Shigowar FAATU yasa ta tsahirta tareda gaisata
FAATU ta amsa tareda zama kusada MAMAH
Ta zayyanewa MAMAH komai na abinda Mai martaba yatsara na bikin LAMIDO da
*KUYANGA* Da kuma bikin nada LAMIDO Sarki da za,ayi
Jakadiya na qunsa tafuce da rawar jiki ta nufi dakin UMMAH Donkai mata Rahoto
UMMAH taga shigowar Jakadiya hankali atashe
Ranta yai matuqar baci dajin wannan kalami daga bakin Jakadiya kamar ta Dora hannu aka
tayi kuka taji
Inama tana da damar da zata hana wannan Nadi
Jakadiya tace "Kibar komai ahannuna domin nima bazanso adora Lamido INA gani ba zanso
ace Yarima ne zaizama sarkinmu
UMMAH ta gyada kanta tana fadin "Nagode jakadiya nasan ke me qaunata CE
Jakadiya taxo futa adakin kenan sukai kicibus da Yarima shima yashigo dakin UMMAH
Kallon kallo sukaiwa juna ko gaidashi Jakadiya ba tayiba kowa aransa akwai abinda yake
ayyanawa akansu
Yaxauna akan kushin yana fadin "UMMAH naxo gaya mikine zantafi turai nan da kwana biyu
nagaji da zama agarinnan babu masu sona
Tace "Kamar yaya babu masu sonka baya gamu nida mahaifinka
Yace "Hhhmmm adane kike sona amma ayanzu kam dagake har TAKAWA babu me kaunata
kinrabani da gudan jinina kinkuma ki sanyawa Takawa ya yafemin yafaina fushi dani
Tace "YARIMA kai kake janyo komai gashi yanzuma zaka tafi kuma kasan bason tafiyarka
yakeyiba Danhaka tafiyarka daidai take da karin wani laifin kanka sannan kuma abinda nayi
daidaine agunmu nidakai domin inhar Yaron ya girma xai iya tasowa ackn wani yanaya na
mugayen halayya ko kuma muzama abin kwatance
Inaso kacireshi aranka kafuskanci abinda ke shirin Kasantomu na Nadin Sarauta da mai
martaba zaiyi akan kaninka LAMIDO
Yarima ya gyara zama da firgici akan fuskarsa yace "Da gaske UMMAH yanzu haka Takawa
zaimini SBD yabakanta min rai. Tabbas saina dauki mataki sosai akai
Waye ya kawo miki wannan labarin?
Tace "JAKADIYA CE
yace "shikenan.
Yafuta yanufi Dakinsa yadebo kudi masu yawa aljihunsa yafito yanufi sashin da Jakadiya take
Cikin ikon Allah Yatararta Ita kadai kuwa
Tanaganinsa gabanta yafadi ganin irin kallon da yayi mata dazu tana ganin ko akwai manufarsa
ta hakan
Yakalleta ba fara,a afuskarsa ya mika mata kudi ahannunsa yace "Karbi wannan !
Jiki na tsuma ta karba
Tace "na menene wannan?
Yace "Nakine aiki zansaki
Tace '"aikin meye hakan? Wannan uban kudi yafi karfina
Yace "Yanda kika zama makisiya shine nakeso ki kashemin wani nima
Ta zabura "Baxan iya ba walh
Yadaka mata tsawa "zaki iya !! Waishinma kinji kowaye?
Tace "waxan kashe?
Kaitsaye yace mata "LAMIDO!!
taji dirar Kalmar akunnenta tadira gefe tana miko masa kudin "karbi kudinka bazan iya kashe
LAMIDO ba ka kaiwa wadanda sukai maka aiki akan MAHBUB suyi walh bazan iyaba
Yadaka mata harara yace "babu Wanda zansa yayi saike don haka kisani k'in yinki yana daidai
da tonuwar asirinki
Yana gama fadin haka yajuya yabar ta tsaye atsorace take da wannan lamari ina ita ina iya
kashe LAMIDO to yanzu yazatayi gashi tana bukatar kudin sbd yawansu yakai ace tagina kanta
da rayuwarta na wasu shekaru toshin yanzu Yaya zatayi ? Rana zafi inuwa Quna!!
Mafita ce tazo mata arai gara taraba kudin biyu taje tasami Fadawan da taga yasa su kashe
MAHBUB tabasu sutayata aikin
******
Abin Duniya yadami Yarima gashi da gasken Gaske Mai martaba yajuya masa baya ko
gaisuwarsa baya amsa masa don hakan ma ya qudiri niyyar kawar da LAMIDO domin yazamo
dolen sarki yanad'ashi agaba yakuma Auri *KUYANGA*
Shawara ya yanke natafiya Turai tun agobe domin in aka kashe LAMIDO kada adora zargi
akansa gara ayi bayanan
Da safiyar Lahadi ya daga ko sallama da Mahaifinsa baije yayiba yabarwa UMMAH sallahun
tagaya masa
Itako dama ranta baiso ba
Da kuwa taje ga sarki tagaya masa ko uffan baice mataba shiru yayi mata dole tabar maganar
yariman ta tafi
Amma ta qudurci yin aikin Asiri atsakaninsu domin janyo soyayyar yariman azuciyar sarkin
Yarima Yana dira akasar waje Allah yahadashi da wata bakar fata Ta nuna tana muradinsa
azahiri bama tasan shidin Dan sarki bane saida taga alamomi a Dan zaman da sukayi na
mintina a Airport
Hindu "Yar Minister ce a jahar Kaduna mahaifinta me kudine sananne Alh Khalid Baffanyo
"Yar boko ce gata da jijji da kai da dagawa Amma yau sai Allah ya damketa duk yanda take
wulakanta samari a garinsu sai gashi ayau Allah yasa mata Soyayyar Saurayin da batasan
asalin saba tashi guda
Dayake yariman ma na mamajo ne tuni ya afka cikin sonta shima taringa kanainaya da kissa
don yasota takuma yi sa,a
Har rakiyarta yanema gidansa takuma bishi
Saidataje gidansa ta tabbatar shidin Dan babban gidane ta gane dawa take tare Domin
tafahimci da alamar Dan gatane kamar yadda take yar gatan babanta
Saida suka kadaita sannan yahau tambayarta meya kawota England ?
Tace masa tazo Hutu ne gun kawunta Wanda shiya riketa alokacin datayi karatunta acan
Takuma gaya masa asalinta da matsayin data taka na aiki domin tana aiki da Ministry of Health
itace Director asashen kula da Asibitocin Shiyyar Su
Ya jinjina kai yace " Ina sonki zaki Aureni?
Da zakuwa tace "Kwarai kuwa inhar da Gaske kake na amince maka amma kada ka yaudareni
bani da dadi
Yayi dariya yace " nima ba Dadin gareniba.
Tayi dariya kawai
Aranar ta tayashi kwana agidan sunyi romance amma basu zarta nan ba don ya ayyana aransa
ita zai aura takwanta masa
Aranar sun tsaida magana zaizo nanda sati biyu Kaduna yagaida iyayanta zai kuma tura
magabatansa
Tunda suka tsaida magana da Hindu shikenan soyayya ta dinke atsakaninsu akullum suna tare
awaya ba dare ba rana
Shaquwa sukai sosai in basuji muryar juna ba basajin dadi
Tana daga Kaduna amma kowa nata yasan da Fara soyayyarta da yarima
Iyayanta harsun San da sunansa domin ta gaya musu tuni
Dama ita kadai suka Haifa itace shalele sunaji da ita basa son bacin ranta
Yarima yakasa sakat tuni yahado kayansa sai Nigeria
Amaimakon yadiro Kano saiya zarce Kaduna
Kai tsaye yabi kwatancen d tayi masa
Ta aika da mota aka daukoshi aka kaishi gidan
Yaji Dadin tarbar da tayi masa da yan gidan
Yai mamakin ganin shankwamen gidansu kamar gidan Gwamna ga tarin motoci kamar ana
saidasu
Akaita kawo masa gaisuwa ma,aikatan gidan aka cika gabansa da kayan ciye ciye
A main falour aka saukeshi
Mahaifiyarta taje takuma yaba da zabin diyar tata
Saida yajira mahaifinta Alh baffanyo yadawo suka gaisa ckn mutunci
Dayake mutumne wayyaye tuni yace yabashi ita yakuma bashi sati yaturo magabatansa
Yarima yai na,am
Sunyi soyayya kafin yatafi da yamma yai mata sallama yabi jirgi yataho Kano
Yaringajin kamar karsu rabu tamkar Wanda tayi masa asiri yaringaji
Ransa Dari qal yasami Matar Aure yasan yanzu dole maimartaba zai sauko inyaji zaiyi Aure
Muje zuwa fans
[8/12, 10:51 AM] Ummi Tandama: í ½í³¿ *KUYANGA* í ½í³¿
*_í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœí ¼í¿» ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*HAPPY SALLAH*
Eidâ -Mubarak to all the muslims all around the world. May Allah SWT grant us the ability to make
the most of this years.
*Nabilancy Luv* í ½í²˜
(Auntyn S&S)
95-100
Da Isar yarima gida kai tsaye gun mahaifiyarsa ya nufa
Tayi mamakin zuwansa bai sanar mata ba
Yana murmushi yace "UMMAH dawowar gaggawace tasameni adalilin Matar Aure dana gamu
da ita
UMMAH da mamaki tace " Matar Aure kuma yarima ?a INA?
Yagyara zama yazayyane mata komai
Tahau gyada kai tana jin farin ciki aranta domin jin yarinyar yar masu dashine kuma hakan yayi
mata arai tafiso shima yariman yayi Aure kamar yadda LAMIDO zaiyi domin Aure yana karawa
mutum martaba da kima a idon Al,umma abin tinkahon tane ace tayi suruka Yar babban gida
ba "yar Bayi ba dama
Tasawa abin albarka tareda karfafa masa guiwa " na amince maka kayi Aure adaidai wannan
lokaci Yarima domin makiya suji kunyar abinda ake shirin maka tunda nasan duk don abakanta
maka aka shiryi Auren su balle anga kafito da maitarka karara ka watsar dasu zuwa gaba
mushirya kutunguila akansu inhar Aka nada LAMIDO sarautar domin baxamu barsuba
Ya gyada kai yace "Nima akwai shirin Dana shirya akan LAMIDON, UMMAH saidai zan ajiye
komai agefe sai bayan nayi Auren tukunna amma kiyi kokari Takawa ya karbi abin da
muhimmanci ahada ayi tareda na LAMIDON domin iyayan yarinyar da Gaske suke asatinnan
zasu Zuba idon ganina
UMMAH tace " kada kaji komai Aure fa kamar anyi Angama
******
Koda UMMAH tajewa da Mai martaba wannan zance Murna ma yayi domin yasan yin Auren
Yariman kamar wata hanyace zatazo masa ta shiriya don haka saiya nuna amincewarsa da
gaggawa tareda tsayar mata da maganar zai tura aje akai kudin Aure tareda tsaida musu rana
daidai Dana LAMIDO
Taji dadi tayi masa godiya takoma yiwa Yariman Albishir
Da farin ciki yakwana jin antsaida masa ranar Aure sati uku masu zuwa
Yaiwa Amarya Hindu albishir
Ai ihu taringayi Dan dadi da farin cikin data tsinci kanta aciki
Tuni ta gayawa iyayanta tamkar suma sungaji da itan saigashi suma suna murnar
Ackn Satin kuwa Mai martaba ya Aiko batun nan Aure
Galadima ne da Liman Amintattun Sarki sukaje kai kudin Aure Dubu Dari biyar
Da kwatance suka sami gidan domin mahaifin Hindu fitaccene babu Wanda baisan Gidan
Minista ba a A T/wada Kaduna
Anbasu an amince musu nanda sati ukun Dayake kanin mahaifinsa ne da Yayan mahaifin nata
da Amininsa suka karbesu agidan Ministan
Anbasu tukuici me tsoka tareda karramawa domin da tsaraba aka rakosu da zasu koma
Kaji da cake da lemuka da turarika da shaddoji haka aka zubasu a but din motarsu
Koda suka koma suka rattabasa sarki abinda suka gano cewar iyayan yarintafa Sunada
mutumci da Halin girma
Sarki yaji dadi yasawa abin Albarka
Zancen Auren yarima da LAMIDO yazagaya gari anata irgen kwanakin dasuka rage sbd irin
shagulgulan da aka shiryi yi sbd nad'in da za,aiwa LAMIDO na zama sarki da zaiyi
Lefe ma yarima A England yatafi yahado
Shiko LAMIDO dayaje gun *KUYANGA* tambayarta yayi
"Gimbiya!
Takalleshi da murmushi kan fuskarta tana murza zoben hannunta da MAHBUB yabata kafin
yarasu
Tace ahankali
" Harna zama gimbiyar ?ai naga Gimbiya Matar Sarkice wacce yakeso kuma
Yayi murmushi dama shidin ma,abocin murmushine yace "Zeenatu kenan ai kamar kinzamane
Tunda saura kwanaki daga lokacin da Aka daura mana Aure nima naxama Sarki Kema kinzama
Gimbiya tunda aranar za,ai Nadi
Ta gyada kai tanajin annashuwa aranta da kuma sonshi ackn zcyrta
Shima hakan yakeji aransa agame da itan
Yakatse shirun nata dacewa " Awace kasa kikeso ahado miki lefe?
Takama baki "Ni na isa? Wacece ni tab ahado anan
Yasha mur! Yace " keko kika isa kuma ke me matsayice da kima don haka daga yau kidaina
ma daukar kanki maqasqanciya agidannan domin kintashi daga *KUYANGA* kindawo
*GIMBIYA ZEENATU*
Tayi murmushi ita kanta sunan yayi mata dadi
Yaci gaba da fadin"kinaji ko zamuje Sudan ko Dubai inhado miki komai acan nida Abokina
Safwan tare mukai karatu dashi acan mahaifinsa ne liman na gidannan tare TAKAWA ya biya
mana zaizo kugaisa
Takawa yana sonki Zeenatu ki godewa Allah jarabtar da Allah yayi mk arayuwa tazame miki riba
da ci gaba domin ayau yakirani yakaramin kudi akan Wanda yabamu na siyayya nida yarima
yace ke tadabance inyi miki siyayya mekyau
Yakarasa maganar yana kallon kyakykyawar fuskarta yana murmushi
Itama murmushin takeyi tana fadin "Naji dadi nagode ayiwa takawa godiya
Yace " To ni zankoma
Tayi masa yar rakiya da baifi taku biyar ba ta koma tana waigensa
LAMIDO ya burgeta tabbas yanada aji ga iya magana da kalami duk macen dayace yanaso
dole ta amsa domin shi din abin sone
Tana shiga Daki tafada akan gado tana fara,a
Zulaihat tabita da kallo tana fadin "Yarinya tashiga kogin soyayya tafito
Dafatan kinyo iyo kinkamo kifi?
*KUYANGA* tayi murmushi tareda tashi tazauna tana fadin "Zulaihat kifaye ma nakamo ba
kifiba tabbas LAMIDO yatafi dani kamar yadda nima natafi dashi
Allah nake godewa da yabani wannan baiwar ta zama matarsa gashi Yace Takawa yana sona
yakara masa kudi akan Wanda yabasu da yarima na soyayyar lefe
Mahaifiyarsa kawai nakeji bansaniba ko itama tana sona kamar yadda Sarkin ke sona?
Zulaihat tace "Hhhhmm Zeenatu kenan aike abar soce itama banajin zataki sonki tunda ta tako
har gidannan tazo miki barka da gaisuwa Dan haka kigodewa Allah kawai
" Allah nagode maka.cewar *KUYANGA*
Zulaihat tace "Ga magunguna can inji Iya Sha,awa tace kada kiyi sake da kowanne masu
kyaune akwai nasha da nono dakuma nasha da Zuma anjima zata kawo miki na tsugunno
*KUYANGA* takama baki " oh maganin mata kuma tun yanzun?
Zulaihat tace "Eh aishine daidai hakan kinga abin xaifi kamaki Sosai
" Hhhmmm Allah dai yasa ba daci
Zulaita tace "koma me gareshi haka zakisha tunda kinsan Halin tsoffin nan insuka bada Abu
ba,ashaba fada zasuyi suce suna mana gata muna gocewa
*KUYANGA* Tayi murmushi tadauki magungunan tafara hada wa xatasha
******
Yarima yadauki wayarsa yalalubo nambar abokinsa SAHABI da suka Dade basuyi wayaba
Acan bangaren SAHABI yana ganin kiran Yariman yayi murmushi yadaga yana fadin" Dama
kana da nambata kamance dani
Yarima yace "inada ita mana fushi nayi dakai na abinda kayimin amma yanzu na huce Dan
haka Ina gayyatarka Aurena karshen wata
SAHABI yayi murmushi yace " Allah yasanya Alkairi nima Auren zanyi nanda sati mezuwa kafin
nakama
Yarima yace "Shegen kaya wato banda nakira bazanjiba kenan ?lallai na yarda karikeni aranka
SAHABI
SAHABI yace " ba haka bane yarima Aurenne ba Wanda nakeso ba Hadani akai da yarinyar
diyar kanin mahaifina ce ita ke sona
Dariya yarima yabushe masa yace "sunmin daidai walh domin insun kyaleka " yar talakawa
zaka dauko musu banza me sakaran ra,ayi
Sahabi yace "kai " yar INA zaka aura?
Yarima yabashi labarin Hindu da yanda suka hadu a Airport a England
SAHABI yace "Hhhmmm to bagiringirin ba dai tayi mai
Yarima yace " oho dai nafika tunda ni Auran Soyayya zamuyi
"Nima bawai kinta nakeba tunda yar 'uwa tace
Ina Zeenatu naji