Showing 15001 words to 18000 words out of 30540 words
Chapter 6 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf
?ya akai *KUYANGA* Tasami ciki a ina akai hakan meyasa
kukai wannan saken...?
MAMAH ta budi baki ahankali ckn ladabi tace "Ranka yadade Takawa banida laifi ciki
FATUU ma tace "Nima dai banida laifi…
UMMAH ckn jin haushinsu tace "to tunda bakuda laifi ciki saiku gaya masa me laifin naga
alamar dai so kuke kununa masa karara nice da laifi ack
Mai martaba yadaga mata hannu yace "ya isa bana son daga murya domin zcy ta tafasa takeyi
raina abace yake tambaya kawai nayi ba neman jin fitina ba ya akai hakan tafaru agayamin.
MAMAH Tace "Ranka yadade cikin nanfa tun daga turai aka sameshi domin da alamar dashi ta
dawo domin YARIMAN ma da suka tafi dashi can tabaroshi baisaniba ta dawo.
Sarki Abdallah ya furgita da jin wannan maganar yace "TURAI!? ya akai har *KUYANGA* taje
turai batareda sanina ba meyasa yarima yatafi da ita ba,a gayamin ba tabbas FULANI kece da
laifi tunda kinsan da tafiyar tasu kika boyemin kinkuma san halina akan in aka munafurceni a
abu
UMMAH tayi kasa da kanta
Yaci gaba da cewa "To shi yariman ne yayi mata cikin ko wa?
Da sauri tadago tana fadin "ba cikin yarima bane baima san ta taho ba Yace min ta dade bata
gidansa tun zuwanta kasar idonta yabude take bin maza farkan natane yasata ajirgi ta taho
ahalin yanzuma yarima baisan tanada cikiba
Mai Martaba yace "Koma dai menene laifin na yarima ne ko ba cikinsa bane to kune sila
sannan Alhakin yana kanku meyasa Da hankalinki xaki hada mace da namiji suje su zauna
agida daya ba matar saba bakomai ba Alhalin kinsan halayyar d'anKi munada masaniyar yana
bin matan turawan nan acan
Maimartaba yaja ajiyar zuciya yace "Yarima baidauko halin kirki na gidan sarauta ba domin
babu me munin halinsa adangina banyi fasikanci ba banyi shaye shaye ba amma gashi Allah
yajarabceni da yaron dakeyi Allah nagode maka Allah kashirya minshi
UMMAH tahau zubda hawaye tana fadin "Amma dai kasan akwai mahassada na agun baidace
karinga aibunta min Da suna gunba.,
Tsawa yadaka mata "yimin shiru fulani ko ranki yabaci banasan zancen banza wadannan
abokan zaman kine ba mahassadan kiba Kuma ki gaggauta kiran yarima awaya kigaya masa
maza injini yadawo gida
Tahau gyada kai tana goge hawaye
Yace duk sutashi sutafi
Sun mike kenan zasu futa saiga Jakadiya ta shigo da sauri tadurkusa tace "Anzo da babban
batu daga asibitin da aka kwantar da *KUYANGA* Ana bukatar jini ackn gidannan za,a kara
mata domin tana cikin wani hali.
UMMAH taharari Jakadiya
Yayinda FAATU taji wani tausayin *KUYANGAR* Yashigeta tace da jakadiya "Maza Ki kiramin
Ladimo A bangarensa kisanar masa yafito yaje asibitin adebi nasa.…
Mai martaba najin tafadi hakan yai mata magana "akan wane dalili zaki bashi wannan umarnin
Alhalin jiya-jiya yadawo baigama hutawa ba zaki sashi wahala babu nasiyane da baxamu
siyaba.?
FAATU tace "Ranka yadade dazu muna hira dashi yagama fadamin an auna jininsa anga Group
O" ne yace kuma yana son yaga yabaiwa mai bukata domin yasami lada natabbata kuma inyaji
ackn gidannan ne zaije da gaggawa
Mai martaba yagyada kansa yace "To ace masa yabayar din nima na Amince tunda ladan yake
nema.
Jakadiya tace "angama zanje yanzu ko ingaya masa.
Duka suka fucedaga Turakar Sarkin
Koda jakadiya tajewa da Lamido wannan magana ta umarnin yaje yabadajini inji mahaifiyarsa
bashiri yahau shiryawa zuwa Asibitin
Direbansa na gidan da aka ware masa yanema yace maza yakaishi Asibitin da suke ganin
likitansu
Zuwansu keda wuya suka tarar ana Auna jinin MAHBUB
Likitan daya gama awon jinin yadawo yatarar dasu duka azaune yace "jinin MAHBUB baiyiba
damar diba shima yana bukata sannan yanada Typhoid
Nan LAMIDO yamike yace da likitan shi aje a debi nasa yanada tabbacin nasa zaiyi tunda
group O ' Ne dashi zai iya baiwa kowa jini
Likitan daya Auna yagani yatabbatar saiyace da LAMIDO "jininka yayi saidai ba leda daya take
bukata ba adebi biyun ba matsala ko adebi daya su sai dayan?
LAMIDO yace "Debi biyun na amince lada nake nema bawani abuba
Take yakwanta aka debi leda biyu
Saida yahuta agadon sannan yafuta daga asibitin ko *KUYANGAR* bai nemi inda takeba don
hankalinsa ba,a gunta yakeba bukatarsa dai ta biya yataimaka mata don baiwaye taba ma.
Koda yakoma gida mahaifiyarsa taringa masa godiya da addu,a gareshi takuma bashi labarin
yarinyar da abinda yafaru da ita
LAMIDO yadade yanajin ciwon abin aransa meyasa akaiwa baiwar Allah haka meyasa don
anga batada gata aka danne mata hakki?
Dayake shi mutum ne mejinkai da tausan bayi sannan gashi da ilimin Addinin domin acan din
dayaje karatu Islamic yakaranta yanada sani sosai
Yadago da kansa ckn Qunar rai yace da Mahaifiyarsa "Amma sam abinda yarima yakeyi baya
kyautawa kodayake UMMAH ta daure masa gindi kuma inada tabbacin shine ma zaiyi cikin
Sharri kawai za.ayi mata
FAATU tace "Muma tunanin mu kenan Amma dai koma meye ai dole asiri zai tonu tunda Inta
futo daga Asibitin zata fadi ko cikin waye kuma Takawa yace agayawa yarima yadawo da
gaggawa
LAMIDO Yace "Insha Allahu saina taimaka mata Da jikina da abin hannuna.
FAATU tayi murmushi tace "Allah yabaka iko D'an Albarka
ACAN asibiti kuwa MAHBUB ne Shida Zulaihat suka kebe yana tambayarta shin abinda yaji
ackn gidan sarki gaskene?
Zulaihat tarintse ido tana futarda kwallah tace "MAHBUB duk abinda kaji gaskiyane Likitocin sun
tabbatar Zeenatu cikine da ita na Daya da satittika wanda yaso ya bare Allah baiyiba rabon dai
ta wahala ne Nayi kuka sosai danaji hakan dama kuma nafara fahimtar hakan kafin rashin lfyr
tata.
MAHBUB yarintse idanuwa yana hawaye kirjinsa zafi yake masa meyasa Zeenatu taci
amanarsa?meyasa Zeenatu tacanza hali? Meyasa tabiyewa sharrin Shaidan da Namiji ta
Amince da wani Alhalin Sunyi Alkawarin Aure ……?
Muje zuwa fans
[7/30, 2:25 PM] Ummi Tandama: *KUYANGA...*
*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
50-55
Jakadiya ce Zaune agaban UMMAH tagama kawo mata tsegumin Matan Sarki wai da alamar
sun hade mata kai sunaso asirinta yatonu agidan abata mata d'a
UMMAH ta furzar da iska abakinta kana tace "jakadiya nadade da sanin abinda suke ciki
nasan basa sona dani da yarima Kuma walh sainayi maganinsu agidan nan daya bayan daya
cikinsu
Jakadiya tace " nibakomai nakeji ba sai *KUYANGA* Kada tacewa sarki cikin na Yarima ne
domin zata iya k'ak'aba masa don tagaji abin arxiki na gdn Sarauta
UMMAH ta quta kana tace "zankuwayi maganinta domin nagama yanke shawarar abinda
zansaka kiyi mata Wanda inhar kikayi zanbaki makudan kudi da zinare da gida agefen gari ckn
gidajen Yarima
Jakadiya tahau murmushi tace " fadi ko meye kikeso inyi zanyishi uwar dakina "yr sarki jikar
sarki me babban daki uwar gidan Sarki Fulani uwar Yarima Wanda zaihaye karaga da yardar
Allah
UMMAH tayi murmushi najin Dadin kambamawa tace " So nake dazarar ansallamo
*KUYANGA* daga asibiti yazamo tadawo karkashin kulawarki koda ace ta fadi ckn Yarima ne
ko bama nashin bane yazama tana tare dake kullum zansa ta dawo dakinki inyaso kafin ta
haihu kisa mata guba a abinci ko kishaqeta da filo ta mutu kawai
Zabura jakadiya tayi kana tace "Ranki ya Dade bazai yiyu akasheta da gaggawa ba za.a
fassara mu kokuma azo ayi nadama gara dai inta haihu inbi dare inkashe abinda ta Haifa
UMMAH tayi murmushi tace " Dakyau jakadiya kinada hangen nesa tabbas zama dake akwai
riba hakan ma da kika tsara yayi don haka kizama ckn shiri
Koda jakadiya ta futa daga dakin UMMAH saita nufi Dakin MAMAH domin kai mata tsegumin
UMMAN tayi sa,a kuwa ta tarar da FAATU atare da MAMAHn suna hira
Jakadiya takai gaisuwa garesu kana ta xauna gefe bakinta na motsawa irin na munafukai
sunso tsegumin
MAMAH tace "ya akai jakadiya akwai wani abun ne?
Jakadiya tahau shafa hab'a tana fadin 'Dama wani Abu najiyo dayake damuna tunda naji
nakasa fada muku
FAATU tace 'ikon Allah mene wannan Abu fadi muji shi
Jakadiya tayi kasa da murya tace " Ranki ya Dade Gimbiya FAATU zancen ma dai akan d'an
kine domin FULANI tananan tana hakon tayi masa mugun Abu domin kada yagaji sarautar
mahaifinsa kada ma yaji yanaso aransa sannan inada tabbacin Yarima ne yayiwa *KUYANGA*
cikin nan amma naga tanaso adanne mata hakkinta don haka yakamata kuyi wani Abu akai
MAMAH Da FAATU suka kama baki suna mamaki domin kuwa basu zataba duk da sun Dora
zarginsu akai
MAMAH tace "lallai jakadiya mungode munyarda ke me kaunarmuce don haka munbaki izini
akan kiringa bibiyar lamarin don kar hakanta yacimma ruwa
Jakadiya tace " Angama ranki ya Dade Amaryar Sarki Dangwale shalele agun maimartaba
Uwar Lamido me jiran gado
Koda jakadiya tafuta sai FAATU tacewa MAMAH "Nifa shiyasa bantabajin inason LAMIDO
yahau kankaragar nan ba in maimartaba yayi murabus haka shima LAMIDON bashida ra,ayi
Sam mulkin baya gabansa balle yadorawa ransa
MAAMAH tace " to duk da hakan dai saiki tashi tsaye kiringa addu.a ba dare ba rana kirage
bacci kigayawa Allah akan yakawo muku agaji kada aje a cutar miki dashi
Nan dai MAMAH tayita bata addu,o,in na kariya domin sunfurgita da zancen da sukaji abakin
Jakadiya
**********
A can Asibiti kuwa anbaiwa *KUYANGA* kulawa daidai gwargwado harta samu kanta
Zulaihat CE agunta kafin arubuta musu sallama
Domin sai data kwana daya a asibitin kana aka bata sallama
Suka dawo gida Zulai ita ta gaya mata duk abinda yafaru da ita tunda a sume aka debeta xuwa
asibiti batasan me akai mata ba tundaga Karin jini da daukar jininta aka auna aka gano tanada
shigar cikin
Hannu ta Dora aka taringa kuka tana fadin "Nashiga uku na cuci kaina da tun farko na aminta
dakai ban bujire makaba.biyayya batayimin ranaba wayyo Rayuwata ta gurbata Allah kadauki
Raina kona hu.... Zulaihat tayi saurin toshe mata baki
" kada kice haka Zeenatu Allah yajarabceki da hakan babu tsimi babu dabara sannan Ni bana
zarginki sai tausayinki
"Inke bakya zargina Zulaihat MAHBUB fa ? Nasan kome zance baxai yardaba Allah ne kadai
zaifutar ni ko a gidannan.
Zulaihat tace " Waye yayi miki cikin?
*KUYANGA* Tace "wakuwa zaimin inba Yarima ba cikin sane bantaba sanin wani namiji ba
inba shiba harta dole yakemin....nan tahau baiwa zulaihat labarin yanda rayuwarta ta gudana a
Turai tareda Yarima bata rage mata komai ba har taimakonta Da SAHABI yayi
Zulaihat tashare hawayen tausayin zeenatu tace " Zeenatu Yarima yacuce ki domin ayanda
nafuskanci MAHBUB yaji ciwon abun yakuma zaci ko kinyi cikinne abisa sonki har kuka yayi
yace yayi nadamar fara kaunarki yace kincuceshi yayi kuka sosai a asibiti
Kuka takara fashewa dashi jin yanda MAHBUB yadauki lamarin
Shikenan tafaru ta kare tasan ko a agidan bakowa zai yarda ba sai Wanda yasan halayyar
Yariman
Zulaihat ita tayi ta dannarta tana bata baki Dan kwantar mata da zcy
Kwana tayi kuka duk tafuta hayyacinta ta rame
Ko futa dainawa tayi saidai Zulaihat ta karbo mata abincinta in an gama abangaren nasu
dayake dakinsu daya da zulaihat din
Tayi zaton ko MAHBUB zaizo yadubata amma saitajishi shiru na wasu kwanaki baizoba
Sannan takara tabbatarwa lallai yadau zafi da ita
Sati Daya da maganar cikin da *KUYANGA* Tazo dashi daga turai YARIMA yadawo
Magana ta yada ko ina na cikin gidan sarki
Wasu suna yarda na yarimane wasu kuma suna ganin bazai zama nashiba tunda ance yawonta
take da maza dataje turan
KARSHEN TIKA TIKI TIK!!
Dawowar yYarima yasa kowa agidan yashiga murna domin ansan tunda yadawo kasar za,a
samo matsaya akan cikin *KUYANGA*
Tana Zaune adaki tana tunanin data sabayi Zulaihat ta shigo da Sauri tace mata
"Zeenatu yi sauri kidauko hijabi muje an aiko sanarwa daga Fada Sarki nabukatarki agun
Yarima yana can fadar da Kaf Ahalin Gidan za,ayi Zubeben kwarya...
Gabantane yafadi tareda dafe kirji take hawaye suka hau zarya akuncinta
Zulaihat tajata jiki tace mata "daina kuka kwantar da hankalinki me gaskiya yana tare da Allah
Abinda kika Sani shi zaki fada kada kiji tsoro kada kuma kirage komai
*KUYANGA* Tahau gyada kanta taredajin karfin guiwa ajikinta
Zulaihat tace " muje inrakaki fadar......
♀♀❤❤❤ fans kutaho rakiya mana
Duk masoyin *KUYANGA* kada yasake abarshi abaya ataho arakata Fadar *SARKI
ABDALLAH*
MUJE ZUWA FANS
[7/31, 11:29 AM] Ummi Tandama: *KUYANGA...*
*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
55-60
CARBI ne ahannun *KUYANGA* datake ja ackn burmemen hijabin dayake jikinta Addua kawai
takeyi Akan Allah yabata Nasara yashige mata gaba yakuma dorata akan maimartaba
Gaban tane yafadi ganin yanda fada ta cika da ahalin gidan daga matansa da yaransa YARIMA
da LAMIDO da kuma fadawa da Galadima da sauran masu mukaman gidan Bayi ne kawai
basa gurin
Kowa ita yake kallo itako kanta akasa tasami guri anesa dasu tazauna Zulaihat ma ta xauna
kusa da ita
Maimartaba yana ganin shigowarta yayi Gyaran murya ganin tazauna nesa da mutane duk aka
nutsu ana kallonsa
Yace " *KUYANGA ZEENATU* Ke muke jira kuma adalilinki muka taru anan Dan haka kidawo
tsakiyar mutane kizauna domin ki amsa tambayoyi daga bakina
Tayi saurin tashi tabi umarni takoma tsakiyarsu inda fadawa suka bata guri akusa da Yarima
dayake kusada Sarki LAMIDO na gefen yariman Wanda tunshigowar *KUYANGA* Yazuba mata
idanu yana kare mata kallo
Bayan ta zauna Mai martaba yawatso mata tambayar data rikita mata kwanya
"Dawa kike tarayyar fasikanci a kasar waje ???
Ahankali tace " Bakowa,
Yace "To waye yayi miki ciki?
Hawaye na zuba a idonta tace " cikin jikina bana kowa bane illah na YARIMA!
fadawa suka hau salati
Yayinda Sarki ya rintse idanu jin yasami jika Dan gaba da fatiha a ckn gida
Suko matan kirji suka dafe alamun mamaki
Yarima kuwa fuskar sace ta nuna bacin rai tsababa ji yake tamkar yashaqeta ta mutu akan
wannan tonon sililin datayi masa
LAMIDO kuwa girgiza kai kawai yk yi na al,ajab sannan yana mamakin yayan nasa da wannan
hali
UMMAH mahaifiyar Yarima Ta dakawa *KUYANGA* Tsawa "karya takeyi munafuka saikin nemo
Wanda yayi miki inma ackn turawan da kika barosu kika gudo
Sarki ne yatsawatar mata akan tayi shiru
Yajuya kan Yarima yace masa " YARIMA ya abin yake? kanada tabbacin naka ne ko ba
nakaba?
Yarima yaji sassanyar Tambaya sai yahau gyada kai yana fadin "Ranka ya Dade bansan da
maganar ba baninayi mata cikiba
Sarki yace " to wanene?
Yarima yayi shiru
Jin yayi masa shiru yasa yaci gaba da tambayarsa
"Sau nawa kataba Kusantar ta?
Nan ma yayi shiru kansa akasa yahau fidda xufa
Ganin haka sarki yace " tun anan alamu sun nuna cikin kane Dan haka bazaka wulakanta
Rayuwar yarinya kaci riba ita ta wulakantaba Dolene ka Aureta....
"bazai yiyuba!
Cewar UMMAH tafada ranta abace
" don ci baya sai D'ana ya Auri KUYANGA gaskiya da sake
Mai marmataba yanunata da yatsa "kishiga taitayinki Fulani idan Dan kine nima nawane nama
fiki iko dashi danhaka magana dole abita in anason zaman lfy dani
YARIMA yadukar dakansa yana magana ahankali " Ina Neman Alfarma ayimin rai walh bana
sonta akwai wacce nakeso mun mayi alkawarin yin Aure atsakaninmu ayimin kowanne irin
hukunci amma banda wannan
Galadima yayi Gyaran murya yace "kwantar da hankalinka Yarima Munanan ma baza.ai hakaba
kaidai katsaya da gaskiyarka inhar bakai kayi cikin nan ba Ai jini zai nuna dazarar ta haihu za
a auna jininka da abinda ta haifan agani
Galadima yadubi *KUYANGA* duk don yakamata da laifi sbd yana goyon bayan Yarima yace
mata
" Ke Wanene shaidarki akan wannan lamari?
Tadago dakai ahankali tana tace "SAHABI shine Shaidata domin shine yadawo dani daga kasar
waje
YARIMA yazaro idanu yana mamakin lafazinta wato Ashe SAHABI munafukin Sane?
Galadima yace mata " wanene kuma SAHABI?
Tace "Abokin Yarima tun acan yasan wasu abubuwan
Nan tahau bada labari tiryan tiryan Har takai karshe tana fidda kwalla a idonta
Kowa agun yaji labarin KUYANGA me taba zuciya Wanda masu tausayi agun harda hawayensu
irinsu MAMAH da FAATU
Haka LAMIDO yacika da tausayinta zufa taringaa karyo masa agoshi yana gogewa
Sarki yakalli Yarima daya sunkui dakai alamun rashin gaskiya yace masa "Maza kira SAHABI
awayarka kasaka handsfree kowa
Jiki asanyaye yakira