Showing 30001 words to 30540 words out of 30540 words
Chapter 11 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf
ance abinda ta Haifa yarasu
Yarima yace " Eh, Sunkusa Aure da LAMIDO...
SAHABI yakatseshi da sauri "ya akai hakan dama soyayya sukeyi?
Nan yarima yazayyane masa komai
SAHABI yace " Gud ammafa naji dadi LAMIDO yaburgeni Allah yasanya Alheri
Yarima baikulaba yai masa sallama
Acan kasan ransa soyayyar Zeenatu na nan baxai mantawa
******
Anata shirye shiryen biki akowane bangaren
Shi yarima agidansa na cikin gari zai zauna baiyda ra,ayin zama acikin gidansu wai kada
atakura masa shida amaryarsa
Shiko LAMIDO sashi guda aka gyara masa agidan me dauke da dakuna agidan gidan yasha
gyara babbane dama ba kowa ciki
Aka zuba komai na alfarma agidan
Lefe yazo daga Dubai akwatuna goma Sha biyu cike fal da kaya tsadaddu
Komai dozinne ciki koina acikin gidan da wajen gidan zancen kayan lefensa akeyi domin
sunhadu sunburge kowa
Saida aka kaiwa takawa yagani yace sunyi yasa albarka kana mata suka hadu suka dauka
bayan Su MAMAH DA FAATU sun gani aka kaiwa KUYANGA
Tsoffinsu sunsaka albarka sunyaba Angyagije Zeenatu anfiddata kunya dukda sunsan arina
Shiko Yarima karya yahada ackn kayan duk don ace nashi sunfi na LAMIDO
Harda key din mota yasaka akan lefen mahaifiyarsa ta saka takardun gida duk akan lefen
gudummawarta duk don mutane suga na LAMIDO lami ne sannan su burge mutan Kaduna
Amarya anata rawar kai anatashan magungunan karin Ni,IMA da tsukewa sbd gurin anshigeshi
Tun fara karatunta a Abroad tayi soyayya da wani Anwar yamaisheta tamkar mata ta amince
masa daga baya ya yaudareta yana gama karatu yakoma kasarsu yamance da ita
Shiyasa data hadu da yarima takasa ta tsare saida taga natsaida lokacin Aure sannan
hankalinta yakwanta
Duk kashe kudin da akai alefenta baisa sunyi rawar jiki ko an yababa tunda su ba farin shigar
komai bane ita kanta motocinta biyu na hawa tanada gidaje kuma
Aiko dai yan kawo kaya suka koma jiki asanyaye danma anbasu tukuici me tsoka
Rana bata karya saidai uwar diya taji kunya
Allah yakawomu wannan rana
Ranar Asabar takama ranar daurin Auren da nadin sarautar
Ancika agdn sarki anata kade kade da bushe Bushe da algaita LAMIDO yasha kwalliyar
sarakai
Yayinda yarima yai tashi ta angwaye daidai misali ba yabo ba fallasa yasha tsadaddiyar shadda
babbar Riga d yar ciki
Saida akayi nadi LAMIDO yazama sarki sannan aka daura auransa da KUYANGA kana akayi
shagulgula sannan wasu suka dunguma da angoma Yarima suka tafi daurin Aurensa Kaduna
Andauro Aure antaho da Amarya a ranar domin sai dare suka iso aka ajiyeta a gidansa dake
GRA
Itako KUYANGA data tashi daga wannan suna daga yau ta tare ackn gidan sarkin A gidan
mijinta LAMIDO daya zamo sarki ayau
To fans saimu Tara a page din gaba *GIMBIYA ZEENATU* Cigaban KUYANGA
Wanda zakuji badaqala da cakwakiya ackn Wanda nake muku zaton yafi wannan Dan haka
kada kubari abaku labari
Taku har kullum Auntyn Sayyada da Shahida