Showing 12001 words to 15000 words out of 30540 words

Chapter 5 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf

damuwa kigodewa Allanki.

Yajuya xaitafi kenan tace masa "Dan Allah kada kanuna masa muna tare ina tsoron abinda xai
faru tunda shike da iko da ni da kuma.…


SAHABI yakatseta da Cewa "kwantar da hankalinki nasan kina cikin tsoro kuma kina neman
taimako bazan bari yasan kina guna ba zankoma gidan ma yanzun gun me gadi inja masa
kunne akan kada yagaya masa


Tayi ajiyar zcy tareda kakaro murmushi tace

"To saika dawo.

Yasa kai yafice

Kai tsaye Gidan Abinci ya wuce yasiyo mata me tsadar gaske

Kana yashiga pharmacy yasiya mata magunguna hardana ciwon jiki dana zazzabi da ciwon kan

Sannan yawuce gidan Yarima yai sa,ar kuwa Baidawoba

Yakebe da Me gadin yabayyana masa komai tareda bashi kudi cinhanci

Me gadin musulmine dan kasar cameroon ne yanajin hausa sosai

Yahau gyada kai yace "bazan fadaba insha Allahu domin natausaya mata yarinyar tanada kirki
tun zuwanta nadaina zama da yunwa wannan Yaro bashida kirki sam, baya ganin karama ce
Amma dai kaima kayi taimako Allah yabiyaka.

SAHABI yaji dadi yayi murmushi yace "Amin ngd.suka karayin musabiha yatafi

******
Abangare guda da YARIMA ANwar yadawo gidan bai neme inda takeba ko kusa ko alama
domin cikin fushi yake da ita

Kwana yayi yana tuna yanda takasance atsakaninsu domin ta bashi haushi sosai wato don
yana jin dadi ajikinta shine tasami hanyar rainashi har tana iya musanta masa da sa,insa dashi
lallai dolene yayi maganinta domin bazai zauna da *KUYANGAR* Da bata ganin darajar saba
zai gyara mata zama
Abu daya yake masa yawo akwanyarsa Baiwarta da YANDA take wajen ni,ima tabbas awannan
fage yasan ta ciri tuta ba karya yarinyar tacika mace baitabajin macen daya kusanta yajita zam
-zam kamar taba

Aikoda zaiyi fushi da ita na lokaci kalilan ne bazai iya rabuwa da itaba tunda ya dan daneta yaji
wani abu aransa akanta yazaune masa kamar super glu aransa

Yakwana yana tuno Dadin dayaji ajikin *KUYANGA*


Da Gari yawaye sai yashirya zaifuta gidan wani abokinsa zasu je wani shoping har ya futa kuma
yai tunanin yacancanta yaganota tunda baiji motsin taba ko batada lafiya

Yana kuma son dai yaganta domin shap dinta na burgeshi da cikar kirjinta



Yana shiga abin mamaki baiganta ba baikuma ji motsinta a toilet ba har lekawa yayi

Saiyaja yatsaya a tsakiyar dakin yana tambayar kansa "to shin ina wannan yarinyar taje ne?

Yai sauri yafuta yaleka kicin namma bata nan

Yazaga bayan gidan shine har lambu yagama zagayensa yana neme nemensa amma shiru ba
bayaninta balle ma wata alamar ko tana gidan

Nan kuma jikinsa yafara sanyi kada dai guduwa tayi? Yatambayi kansa

Gabansa yafadi alokaci guda

Domin yasan inhar ta gudu ba iya kai kanta gida xatayiba tunda batada kudin jirgi balle wata
hanya agarin da xata iya guduwa gida

Yatafi da saurinsa yatambayi me gadi yace masa shin ko yaga fitowar Zeenatun?

Me gadin yahau girgixa kai yana nuna tu,ajjibinsa azahiri yana fadin "bangantaba tun jiya
rabona da insata a ido

Yarima yace "azamanka nayau aget kamatsa na awa nawa ko minti nawa?

Me gadi yahau sosa keya yace

"Eh to dayake dai yau natashi da bacewar ciki inata shiga toilet shiyasa bana ce ko sau nawa
ma nabar get ba kuma nakan dade kafin nadawo.


Yarima yadafe kai yace "Shikenan ta gudu! Nashiga uku.


Me gadi yazabura yace "ta gudu? Zeenatun innalillahi wa innailaihirrajiun.


To yanzu ina za.aje aganta wata sani a kasar nan?

Yarima yaharareshi yace "koma wata sani ko bata sanin ba ai kana da hannu aciki tunda kana
wasa da aikinka baka rufe gidan yadda yakamata.

Yajuya yabar Megadi da atsaye saroro


Aifa aranar yarima yarasa tsugum yanata Faman xaryar gun jami,an tsaron garin yana basu
bayanin B'atan *KUYANGA* waiko Allah zaisa aganta ahanya


Kwana biyu sukai suna checking akanta amma shiru dole yahakura yakira gida yana tambayar
mahaifiyarsa

Koda UMMAH taji abinda yake faruwa daga bakinsa ta kidime tahau yi masa fada

"Yarima kodai akwai abinda kake matane?ko takura mata kayi da ayyuka da fadanka?


Yarima yace "To UMMAH inma nayi mata fadan saita gudu? Banida ikon dazan matane?kawai
dai yawon bude ido nakejin ta tafi tunda idonta yabude dama bakiga yanda take shigar kananan
kayaba tana son tafuta gari nahanata ashe dai xata shammaceni tagudu


Jin Hakan yasa UMMAH ta yarda tahau fada tana cewa "to ai da ba guduwa yakamata tayiba
saita fada maka maza take bukata saika dawo da ita gida ayi mata Aure yanzu kaga hakan ai
sharri zata jawo maka ace kai ka koreta ko cutarta kakeyi yasa ta gudu gani da mahassada
ackn gida (kishiyoyi)

Kuma dole kasan TAKAWA zaiyi fada amma kabarni dashi zansan mezan fada masa

Yarima yahau godiya yanajin dadi aransa


******
Akwana na ukunta agidan SAHABI bizarta ta samu itadashi

Suka kamo hanyar dawowa Nigeria

Dayake tasaki jikinta dashi tunda taga ba cutarta xaiyiba sai suketa hirarsu ajirgi tana ta masa
godiya da nuna masa farin cikinta azahiri

Shikam bakomai yake ce mata ba sai "nikam bazan daina gaya miki ina sonkiba kirike alkawari

Ta lumshe idanunta tabbas inda wanda zataso to abayan SAHABI yake amma ina yau data nufi
kasarta ji take wata kaunar MAHBUB ta dawo mata sabuwa

Dayaga tashiga tunani saiyace mata "Zeenatu kada fa kisawa kanki damuwa kicire komai aranki
domin ni da Aure nake sonki kuma bazan ringa miki kallon abinda yarima yai miki ba kimance
da komai yadda nima zanmanta da komai haka kuma kija bakinki kiyi tsit kada kifadawa kowa
abinda yasa kika dawo ko abinda yarima ke miki kimarki zata ragu agun mutane sannan za,aita
yawo da maganar agidan.

Tagyada kanta tagamsu itanma ai zataso asirinta yarufu domin kada masoyinta yaji bazaiji
dadiba sannan ga "yan uwanta KUYANGU abin xai iya zama abin surutu ayi mata wani kallo


Da dare suka diro kasar Nigeria bayan Ishsha'i

Har gidan sarki Abdallah yarima yadauki shatar mota aka kaisu amma shi bai bari anganshiba

Ita kadai aka sauke akodar gidan sarki aka tafi dashi zuwa hotel din dazai kama yakwana ingari
yawaye ya wuce Daura garinsu

Kafin su rabu tun amota yabata waya karama kirar Tecno domin yace yana son yaringa jin
muryarta akoyaushe sannan in tanada Damuwa ta sanar masa zai mata maganin damuwar


Tabbas SAHABI yagama mata komai

Shigarta gidan tun daga kofa aka fara mamakin dawowarta tunda ansan da Ita da yarima suka

tafi kuma basuda labarin dawowar yariman

Kai tsaye bangarensu ta zarce bata bari kowa yagabta ba

Adakinsu mutum biyune basuyi bacci ba Zulaihat idonta biyu kawarta

Da zulaihat taganta kirji ta dafe tana fadin "wa nk gani kamar Zeenatu? Dama yau kuna tafe
amma banji sanarwar ackn gidan ba

*KUYANGA* Tazauna tana fadin "wash !barni na huta tukunna zulaihat saiki watson tambayar

Zulaihat ta janyo jakar da Zeenatun tashigo da ita takaya tace "lallai kyan tafiya dawowa ina
yariman ko batare kuka dawo ba?

"Idan tare muka dawo zaki ganmu atarene?

Zulaihat Tahau murmushi tana fadin "inafa kawai dai tambayace

*KUYANGA* tace '"to batni nahuta tukunna sannan kibani labari akan MAHBUB dina.

Zulaihat tayi dariya tace "MAHBUB dinki yananan qalau.

"To masha Allahu.


******
Gari na wayewa aka aiko kiran *KUYANGA* labari yakaiwa UMMAH anga Zeenatu ta dawo gdn
da daddare


Saida UMMAH ta tabbatar da lallai Zeenatun ce tunda tazo da gaggawa kiran tadurkusa
agabanta

UMMAH tace "Meya dawo dake Gida yarima baisaniba?

Gaban *KUYANGA* Yafadi take dabara tazo mata

"Fita nayi don ganin gari shine na bace har wasu suka tsinceni suka tambayeni inda nake
nikuma namanta inda zance musu bansan kwatancen mazaunin yarima shiyasa dasukace zasu
dawo dani Nigeria ban musa musuba


UMMAH nagama ji tace "kodai yawon iskanci kika tafi Allah yakamaki aka dawo dake gidan?.

Da sauri tahau girgixa kai tana hawaye tabudi baki tace "walh ba haka bane waccen maganar
danayi ce gaskiya.


UMMAH Tace ta tashi tabata guri tayiwa kanta rayuwar jin dadi wasu ma nema suke

Tana futa UMMAH takira Yarima tagaya masa komai

Yarima yasha mamakin dahar ta iya dawowa ita kadai yacewa UMMAN yana tunanin akwai
wanda yataimaka mata ta gudo zaiyi bincike

UMMAH Tace "nidai kawai kadawo Yarima domin nafi son zamanka akusa da mahaifinka don
inyana ganinka akusa dashi zaifi shakuwa dakai sannan Hakan ne zaisa sarauta ta dawo
hannunka ta sauki tunda wancen Sahoramin yatafi Sudan karatu bazai dawo yanzuba

Yarima yace "Nima bana jin Zandawo Yanzun UMMAH saikamar nanda wata guda.

Tace "To kayi kokarin kadawo awata gudan kada ka kara fa.

Yace "angama UMMAH Na baxan karaba.

Sukai sallama

Saida Labari yakai kunnan sarki wai *KUYANGA*

Dasuka tafi Turai da Yarima ta gudo itakadai

Mamaki ya ishi sarki domin baisan anyi tafiya da mace ba da bazai bariba balle har ya yarda
yabar yarima yatafi da mace

Aranar yasaka UMMAH agaba yace ban kanki in aske

Yaita mata fada harsaida tayi hawaye

Tana fadin "Ayi hkr Takawa ai anrigada anyi kure dahar aka tafi ba.a gaya makanba baza.a
karaba


Ita kuwa *KUYANGA* tasake ackn "yan'uwanta Bayi bata nuna wata damuwa ba ko Wani abun

Haka suma basu gano komai ba saima yabon canxawarta dasuke tayi wai tayi kyau fatarta tayi
kyau acan

Shiko MAHBUB kallonta yai tayi yana fara,a dajin dadi yana fadin '" kincanza dayawa Zeenah
kinyi matuqar kyau fatarki sai sheki takeyi lallai kin huta acan kinbarmu ckn aikin wahal


Inafa Hutu tambayemu kasha labarin komai �


tayi fari 🙄 tace kaima ka kara kyau anya kayi kewata kamar yadda nayi taka kuwa?

Yace "sosai kuwa ko nan gurin damuke xama zaishedi hakan dafatan dai soyayyata batayi gibi
ba tananan yanda nasanta da yawa?

Gibi kai�� Amma injini ita cewa tayi

"Saima karuwa tayi ai aduk inda nake dana tafi ina tare da sonka da kaunarka

Yace "naji dadi soaai.

Dayake wayar da yarima yabata Boyeta tayi sam bazata bari MAHBUB yagani ba balle yayi
mata fassara gara Zulaihat ta nuna mata amma tace kada tafada wa kowa

Zulaihat hartana tsokanart dacewa "Toko dai SAHABIN nan zaki Aurane komai kice SAHABI
mudai kada kiyi mana sakiyar daba ruwa


*KUYANGA* tace "Banga abinda zaisa nabar MAHBUB ba kima bar wannan maganar SAHABI
abokin shawara ne abokan taka ce atsakaninmu


Dariya kawai Zulaihat tayi tare dajan bakinta tayi gum

*****
Watan *KUYANGA* D'aya da dawowa yanayinta yacanxa domin wani laulayi taringayi ga yawan
Zazzabin dare Da ciwon Ciki da bacci da kasala da kwadayi da take yawan yi

Zulaihat itace tajikinta ita tasan matsalarta na rashin lfyr saita samo mata magunguna taita bata
na gargajiya tana jikawa tana bata tana sha

Kwana biyu tayi akwance MAHBUB yatada hankalinsa ganin ciwo yaki lafawa Kullum cikin
Aikawa da Rubutu yake

Aranar data gama shanye jikon da Zulaihat tayi mata aranar tayita malelekuwa atsakar daki
mararta na ciwo kamar ta mutu

Tana ihu tana kiran sunan Allah

Jini ne yaringa xuba ajikinta ta kasanta me yawa

Zulaihat ta tsorata ainun

Da gudu tagayowa manyansu tsoffin Bayin gidan

Da sukazo kanta sukaga ikon Allah abin yafi karfinsu sai suka baxama cikin gidan gun matan
Sarki aka gayo musu


Mamah ta tsakiya da Amaryar Sarki Faatu mahaifiyar Lamido sune suka fara zuwa gunta kafin
UMMAH Tazo

Likitansu na ckn gidan aka kira macece *DOCTOR HALIMA WASAI*

da kayan aikinta tazo taxaci abin karamine

Saida tazo taganta tace musu ai bari zatayi da alamar cikine da ita maza atafi da ita asibiti don
inya bare ayo mata wankin cikin


Hankalin kowa na gidan yatashi ba,a bari sarki yajiba

UMMAH taringa fadin "shegiyar yarinya Me sifar munafukai ashe abinda tayo akasar ta gudo
kenan lallai asirinki yatonu Yarima bashida Alhaki shiyasa baima saniba ta munafurceshi.


MAMAH tace "ai irin wannan ba,a aibunta mutum kuma bamu tabbatar ba likitanma zato takeyi
dan haka muyi mata fatan Alkairi tunda D'a nakowane


UMMAH ta harari MAMAH dama haushinta takeji ganin ta rungumi FAATU sunhade mata kai

UMMAH ta watsowa MAMAH magana me zafi dan taji haushi tace "TO IN D'A NAKOWANE
WANI MA YAYI D'AN MANA NAZACI TUN ZUWANKI GIDANNAN KATON KASHI KAWAI
KIKEYI KOKIN TABA YIN BARIN MA?

MAMAH jarumar mace me tawakkali tayi murmushi tace "Bantabayi ba Amma nagodewa Allah
yabani Taqwa da Sanin yakamta kuma ina dada gode masa nasn kuma bai manta daniba, na
tabbatar kuma inhar yabani agaba inda yawan rai xanfiki iya yiwa yara tarbiyya....FAATU ce taja
hannun MAMAH tana fadin "kibar maganar haka kiyi shiru ga mutane fa bayinku agun
baikamata ba.


MAMAH da FAATU suka bar gurin

Ita UMMAH Data gwaba me zafi aka mayar mata tafi MAMAHn jin xafin maganar ma

Yawwa ai gara hakan dama inbaki yafadi son rai aibaisan me za,a mayar masa ba.


*Muje zuwa dai Auntyn Sayyadah da Shahidah*


��🤣😀�����☺�
[7/28, 9:09 PM] Ummi Tandama: 📿 *KUYANGA* 📿






*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*WANNAN PAGE DIN SADAUKARWA CE GA KAWATA TAKAINA REAL UMMEEY ZEEY
Marubuciyar "YAMMATA ALKAIRIN ALLAH YAKAI INDA KIKE INA FANS DINA KUNEMI BUK
DIN "YAMMATA KADA KUBARI ABAKU LABARI*




*Nabilancy Luv* 💘

(Auntyn S&S)





45-50


ACAN Asibiti Likitoci sunata iya bakin kokarinsu domin Suga jinin dake zuba daga jikinta
yatsaya don tafuta ahayyacinta

Saida Allah yataimaka jinin yatsaya kana sukai mata allurar bacci sannan aka nemi "yan uwanta
domin suzo adebi jininsu akara mata


Likitocin kansu sunyi zaton cikin dake jikinta yazube to ajiyar Allah baifita ba sai wuya datasha

Iya Yabi wata tsohuwa cikin wadanda suka kawota tace musu su taimaka su karasa fitar da
cikin ba Aurene da itaba Abin kunya taja musu

Dr Halima tace mata

"Gaskiya bama zubda ciki domin inmunyi hakan tamkar munyiwa ubangiji shishshigine domin
bamusan nufinsa dayasa tasamu cikin ba alokacin da bai dace tasamu ba

Iya tace "Amma dai da kuntaimaka sbd idan labarin yaje kunnan sarki baxataji ta dadiba dan
korarta ma zaiyi agidan kuma gashi bamusan cikin wayeba gata marainiya


Dr halima tace "koma dai meye ne iya saidai kuyi hkr mufa bama Abotion a asibitinnan sannan
kusani wannan ciki bame futa bane inhar kuma kukayi kokarin yi masa dole to tabbas zaku iya
rasa ranta awajen zubarwa

Iya Yabi ta tsorata matuqa gaya jiki na rawa tace "to abar maganar Allah yabata lfy yarufa Asiri


Acan gida Da labarin neman jini yazowa kowa sai akaita nokewa MAHBUB kuwa da rawar jiki
yanufi asibitin sbd yabada jininsa ga masoyiyarsa

Shi atunaninsa ko wata lalaurar ce tadaban take wahalar da ita

*********

Dayake aranar LAMIDO yadawo yanufi daga SUDAN yagama karatunsa wanda yayi na
shekara 5

Rangadi suka futa shida maimartaba domin Sarki yana son LAMIDO kwarai. can bayan gari
yajashi wai suyi hirar yaushe gamo anitse kada atakura musu

LAMIDO yaji dadin wannan zaman da mahaifin nasa domin sunsa hira tun da sukazo wajen sha
daya nasafe sai yamma suka fara haramar komawa gida dayake dirar sassafe yayi Nigeriyar


Jakadiya tana gaban UMMAH tana fadin "Ranki yadade naje cikin azama fada domin insanarwa
sarki labarin irin abin kunyar da *KUYANGA* ta hada mana ayau sainatarar bayanan natambayi
Dogari wai yafuta shida LAMIDO dakuma fadawa Rangadi


Lallai nayarda Sarki yana son LAMIDO domin namanta rabon dana ganshi yafuta ran gadi balle
bai taba zuwa da YARIMA ba anya kuwa ranki yadade ba asiri Matar can tayiwa Sarki da
Yarima ba kuwa?


UMMAH ta hau gyada kai ckn takaici tana fadin "Ai walh jakadiya matar can burinta ackn gidan
nan baxai taba cikaba domin D'ana shine sarkin gobe da yardar Allah kuma Duk me binsa Da
sharri sai nayi maganinsa muxuba mugani



Har dare da Sarki yadawo shida LAMIDO labari baije kunnan saba

Sai da Sassafe Jakadiya ta bazama taje takai gaisuwa tagurfana agabansa don takware a
munafurci da gulma

Saida tagama banbadan cinta dayi masa kirari kana ta zayyano masa komai duk abinda tasani
daya faru

Sarki yayi Shiru kirjinsa na dukan uku uku dan fargaba

Yanzu cikin KUYANGUNsa akaiwa 1 ciki?me hankalin ciki da yasanta farin sani sbd yawan
Ayyukanta ackn gidanba da ladabinta

Yadafe kai yai tsahon minti biyar ahakan kana yadago ya kalli jakadiya yace

"maza kije ki kira min matan gidannan su ukun

Su UMMAH Da FAATU Da MAMAH yake nufi

Dakin fulani tafara isa tagaya mata kana tawuce dakin MAMAH

Bayan tasanarta kiran sarki saita wuce Dakin FAATU Tana shiga ta tararta da LAMIDO Suna
hira tadurkusa takai gaisuwarta garesu kana ta isar da sako tafuta

Koda suka hadu gaban Sarki UMMAH tafisu faduwar gaba sbd tasan kaf dinsu itace me laifi
tunda itace silar samuwar cikin *KUYANGA* dan dabata turata kasar wajeba da yarimanba da
batasa samuba


Bayan Shiru na wasu mintina Sarki yayi gyaran murya kana yakallesu d'aya bayan d'aya yace
"Kunada masaniyar Abinda yake faruwa agidannan?

Suka hau gyada kai

Yace "to ya akai har hakan tafaru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login