Showing 3001 words to 6000 words out of 30540 words
Chapter 2 - Kuyanga Book Complete by Nabilancy Love.pdf
ne amma aikinsan zaki huta zakuma kisami hutu da
Aikin gidannan ZEENATU kifa tuna mubayine bayinma kaskantattu wadanda ba,a san inda
iyayanmu sukeba ko suna raye?ko sun mace Allah shiyasani mudai muntsinci kanmune agidan
nan
Dan Allah kikwantar da hankalinki inkinje domin Allah ne yazabeki domin kihuta kedai kiyi
biyayya dama ke me biyayyarce kowa yasani bakida surutu magana bata dame kiba inba sabo
kikayi da mutum ba basawa ba hanawa dan haka ki ajiye soyayyar MAHBUB anan zuwa sanda
zaki dawo kwacigaba
*KUYANGA* Tace "to inma ban ajiyeba yazanyi bayan askiyazo gaban goshi gobe nefa zantafin
dole inyi hkr da komai dama saiyau yabayyana min abinda ke ransa
Zulai tace "hhhmmm keda bakida gano abu da wuri aisaiyau kika ji kika gane amma ai kowa
yagane manufarku tabbas muna muku fatan Alkairi kedashi.
*KUYANGA* Tace "mungode.
Nan *KUYANGA* Tahau shirya kayanta ckn wani Dan akwatin karfe me kyau dashi tana Ninka
kaya tana sakawa tana ayyanota A turai shin ko wane Zama zasuyi insunje……… ???
*muje zuwa fans*
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: *KUYANGA*
*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Dis Page i Dedicated to My Best friend Hauwa,u* *(UMMU ALEESHA wa WALEED)*
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
10-15
Da Sassafe tagama kintsawa misalin Bakwai na safiya Aka aiko kiranta daga Fulani
Tana shiga Sashin Fulanin ta tararta atsaye Yarima na kusa da ita da akwatinsa babba guda
daya da alamar zai dade din domin fam yacika akwatin da duk abinda yasan zai bukata duk da
acan gidan nasa akwai kayansa na sawa
UMMAH Ta daka masa Yaji ta sa anyo masa dambun nama ta soya masa gyada me gishiri duk
abinda tasan dai yana matuqar So ta tanadar masa taxuba masa ckn Akwatin
Yana ganin *KUYANGA* Da akwatin yahau kallonta fuska ba fara,a yace "ke wannan akwatin
irin na mutanen da kumafa? Kina nufin dashi zaki bini? Kinsan kuwa Turai ?Bafa Me dile bace,
maza jeki canzoshi kokuma kitafi ba kaya inmunje xan nasiya miki wasu kawai
UMMAH tayi murmushi tace "Yi mata hakuri Yarima ta canzo kasan sai ahankali kayi mata uzuri
taje ta canzo kayan kokuma inshiga innema mata cikin akwatina na
Yahau girgiza kai yana duba agogon hannunsa
"Barshi UMMAH saura mintina Jirginmu yatashi saima munyi wuta ahanyar zuwa Airport din
don karmu makara
Yakalli *KUYANGA* Yace "ke ajiye kayanki anan muje da najikinki inmunje zansai miki wasu
kiringa sanyawa.
Ckn ladabi tace "to shikenan.
Ta ajiye akwatin karfen nata agefe tabi bayansa UMMAH tana musu Addu,u,a da fatan Alkairi
Wasu bayi maza ne suka kai masa akwatin nasa har ckn mota aka zura a boot *KUYANGA* Ta
shige gidan baya
Motar natafiya zata fuce agidan Sarautar saitaji wani iri aranta tabbas zatayi kewar MAHBUB
yau ranar zata zamo mata ranar bakin ciki tunda ta taso kullum suna tare gashi yau zasuyiwa
juna nisa kamar ance ta dago kanta kuwa tana dagowa takalli bayanta saita hangoshi ta glass
yana dago mata hannu
Ta zura hannunta tahau daga masa itama
Ashe Yarima yana hangosu ta mirro amma baiyi maganaba yai shiru
a Airport kuwa da sukaje Dakyar ta iya daga kafa tahau matattakalar jirgi saida ta rintse idonta
Jirine ma yaso kadata Allah yaso ya kula yai saurin rikota tayo luuu jikinsa yatarota yamannata
ajikinsa yahau da ita ahankali
Yasan arina tunda yasan ba taba hawa tayiba
Koda suka shiga ckn jirgi akusa da juna suka zauna
Kujerarsa na kusa da tata
Idonta akasa bata iya hada ido dashi don kunyar abinda yafaru da kuma biyayya
Yakalleta yadauke kai yana so yai mata magana amma yarasa me zaice mata don baya son
tana jin kunyar nan tasa shikam tana burgeshi amma baya son kunya shi faranse ne wayyayye
Gani yake duk kauyancin nan da zatayi masa bazasu shiryaba domin saiya wayarta kada
tabashi kunya irin nayau
Da aka kawo musu abinsha kin dauka tayi saida yadaka mata tsawa
"Ke Dauki mana meye na kunyar!
Tasa hannu ahankali tadauki lemon taja ta rike takasa budewa
Yana kallonta tagefe taki budewa kanta akas!
Saida yashanye kana yakalleta yace "kawo inbude miki.
Ta mika masa ahankali
Yabude mata na gongwanine me gas
Taringasha ahankali kusan awa guda kafin tagama
Anyi rabin tafiya Tafara bacci takwanto da kanta kan hannun kujera yatsura mata idanu yana
kallon kyakykyawar fuskarta da dan bakinta yaji kamar yakai hannunsa yashafata saidai yana
gudun kada tafarka
Can bacci yai mata dadi saiga kanta ajikinsa
Yarasa yazaiyi da ita saboda mutane nakusa dasu suna kallonsu
Haka yabasar bai motsaba gudun kada ta farka takasa komawa
*******
Koda suka Sauka a England Kaitsaye suka hau mota ta haya har gidansa
Tamfatsetsen gidane da maimartaba yasiya don kawai insunzo karatu suzo suzauna ackn sa
Daki guda mekyau da tsari yakaita yace mata nanne inda zata ringa kwana
Dayake kayan jikinta riga da zanine tasanya hijabinta hannunta rike da carbi
Tazauna zagwade abakin gado tana so tayi sallah gashi bata san yazatayiba nafarko bata san
inane gabas ba gashi Bandakin yawuce tunaninta batasan yanda zata sarrafa ruwa yazubo ba
gashi ba agogo adakin
Data gaji da zama saita futo falon domin tambayarsa
Ta dade afalon azaune bayanan yana ciki tajiyoshi yafito daga wanka
Tananan zaune harya kintsa yafito
Yakalleta yace "Ya kika baro dakin kika dawo nananan Qalau ko?
Tace "Dama, Alwala zanyi inyi Sallah to bansan yazanyi ruwa yaxubo ba kuma bansan ina zan
kalla ba gashi lokaci nakeson gani
Ya koma ciki yadauko mata agogon bango yadawo yace mata "Taho muje.
Ta biyoshi abaya har dakin da yace natane
Suna shiga ya ajiye mata agogon Akan mirro me lado ladone xata gane shi
Yashige bandakin yana kiranta
Tabi bayansa yaringa nuna mata yanda zata kunna komai takashe ckn Sauki
Da yanda zatayi wanka da shaya dakuma yanda intayi kashi zatayi fuloshin da duk abinda
yasan dai zai gagareta
Saida ya tabbatar tagane komai kana suka dawo dakin yanuna mata Gabas sannan yace mata
inta idar ta jirashi xaije yasiyo musu abinci yadawo
Kafin yadawo kuwa tagama komai don har wanka itama ta sallo ta maida kayan jikinta taxauna
ta takure agado tana jiransa don yunwa takeji
Daya dawo yashigo yakawo mata abincin na take away sannan yabata wata ledar kaya yace
"Ga kayan sawa nan kala biyar na Siyo miki kafin nakaro miki wasu gaba
Takarba da biyayya tana godiya
Daya fita yabarta tacinye abincin tas tana santi kunnanta kamar yacire
Tayi mamakin ma data iya cin wannan kalar abinci domin a ido dai yaburgeta dama gashi abaka
ma gwanin dadi bata taba ganin irinsa ko a hoto ba
Ta wanko hannun tasha ruwa sannan tazo ga Ledar ta zaxxage kayan tana daddagasu daya
bayan daya tana mamaki da yatsina fuska domin kayan basuyi mataba
Asalima tayi tsammanin ko canzan leda sukayi da wani domin kayan bana sawar "yar musulmi
bane
Itakam ko da kudi bazata taba sasu ba rigunan "yan bigil suke kanana wanda in an saka zasu
damewa mutum jiki
Ga Wanduna pensil ga "yan gajerun wanduna sai siket masu roba iya cinya da riguna marasa
hannun harda bes tashan iska kayan sunyi kyau
Ga masu sawa Amma
Ta maidasu cikin ledarsu tana mamakin wannan kaya ai baxata taba iya sasuba haba aiko
batada kunya wannan kayan sai a gidan mijinta yaushe
Sai bayan wasu awanni yashigo mata don ganin ko qalau take
Yana zuwa yaga kayan akusa da ita yahau tambayarta
"Baki bude kayan bane?nakine fa nasiyo mk yakamata kigwada ma ingani don inga wanda
sukafi miki daidai sbd xankoma siya miki irinsu nan gaba.
Tace aranta "Aiki game k'areka.
Afili tace "kayi hkr nagansu baxan iya Sawa bane sunyi kanana dayawa.
Yahade rai baya son kauyanci da Raini fa
Yace "akan wane dalili tokisani nanba gida bane baxakiyi kauyan cinnan nakiba dolene kisaka
su don awannan garin baruwan wani da wata dankin saka bame kallonki balle yaga laifinki
kuma bazaki taba samini wadannan riga da zanin naku nagargajiya ba dan haka maza kisaka
su ingani nabaki minti biyar ina jiranki afalo
Yana gama fadin hakan yajuya yafuce
Wani qululun bakin cikine yatsaye axcyr *KUYANGA* TABBAS tun daga yau tafara nadamar
xuwa Turai lallai inko haka zata ringa shigar kayan arna gara bataxoba Gara kuma taita zama
dana jikinta
Tasaka kayan agaba tana kallonsu data kalli agogo taga saura minti biyu lokacin daya bata
yacika saitayi saurin tashi ta janyo ledar taciro wata riga me karamin hannu tacire ta jikinta
tasaka dakyar
Sannan ta sille zanin tasaka wani dogon wando
Bata iya cire dankwalin kayan ba tabarshi akan nata don kada yaga gashinta
Takalli kanta a madubi
Ai dasauri ta rintse idonta tana fadin "innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Yanzu haka xanje gaban namiji?yanzu haka zanje gareshi yagannin nashig uku yau naga
takaina meye mafita ………………?
*Fans kugaya mata mafita*
*Auntyn Sayyada da Shahida ce*
[7/23, 10:28 AM] Ummi Tandama: *KUYANGA...*
*_KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*Dis Page i dedicated to my lovely Sister *NABILA RABI'U LADY* a writer of *BANI BANE*
Always i solute you my Namesake. oh my Lord! bless her and help her everythings
*Nabilancy Luv*
(Auntyn S&S)
15-20
*KUYANGA* Tak'ara kallon kanta a madubi taga agaskiya bazata iya futa gaban Yarima
ahakaba ai taxama mara kunya kenan inhar yaganta ahakan..."bashi yabaki umarni daki sakaba
" bashi yakawo miki don ki sakaba? Wata zuciyarta tace mata
Azancen gaskiya kayan sun mata kyau domin wandon yamatseta tsam !dam! Yafito mata da
shap sosai abin gwanin burgewa dai
Ga rigar ta kamata tamkar ajikinta aka kirkireta dama ita ba ma,abociyar saka bra ba saiga
nonuwa tsaye tsar ! Me sifar kan tasa ga nipple nan tsir ya nuna kansa
Ita kanta abin bai mata tsari ba balle kyangani domin sifarta tafito tamkar komai awaje yake
To yata iya inhar taki futa taje gun nasa zaizamo hakan tamkar ta bujirewa maganar sane
sannan umarni yabata ba zab'i ba
Kuma ita din akan bin umarninsa take zaune sannan babu musu ko k'iwa atsakaninsu akullum
ita din baiwa ce makaskanciya agunsa *KUYANGA* me hidimta masa
Ta tuno kalaman mahaifiyarsa da take ce mata "DUK ABINDA YA UMARCEKI DAKIYI KIYI
MASA DONKI FARANTA MASA KECE MEYI MASA KOMAI ME KULA DA KOMAI NASA
Saikuma ta tuno da kalaman masoyinta MAHBUB da yake ce mata "KADA KIBARI
AZALINCEKI KADA KIBARI ACUCEKI SBD KINA AMATSAYIN BAIWA KADA KIYI ABINDA BAI
DACEBA ACKN BIYAYYA.
ta rintse idanu tana kwalla tana fadin "MAHBUB kayi hkr gashi anfara, zankuma karya maka
doka Zanyi biyayya ga abinda bai daceba zanbi umarnin uban dakina.
Tana gama fadin hakan tafuce gurinsa
Yana zaune afalon yadora kafa daya kan daya yana latsa waya
Tun daga nesa yakura mata idanu itako kanta na kasa
Saida ta isa dab dashi tadago kanta taga ashe shid'in ita yake kallo saiTaji wata kunya ta
mamayeta
Yai saurin kawar da ganinsa daga kanta yace "Very nice sunyi mk kayan daga yau sune Kayan
sawarki kada nakara ganinki da zani domin nanba kauye bane ina mu,amula da wayayyu
bazanso suga dawa nake tareba inhar ba kin kile ba tunda duk bakon danayi saikinzo kinyi
masa hidima
Ta gyada kai kawai
Yace "oya muje kicin na nunnuna miki kayan amfanin da zaki ringayi akullum.
Ya wuce gaba tabi bayansa ad'arare
Yaringa nuna mata abubuwa komai har gas yanuna mata yanda zatayi amfani dashi domin
acan gidan sarauta Manyan bayi ke girki ba yaransuba
Balle su iya komai su k'ananan Bayi saisun kai munzalin Aure ake fara Trenasu
Saida yaga ta kwashe akwanyarta na wasu abubuwan kana yace suje su zaga gidan domin can
ma akwai abinda zai nunnuna matan
Tana gaba yana bayanta yana karewa mazaunanta kallo
Yawu yake had'iya kawai domin yasha Mamaki aransa yarinyar ta da ita amma komai yaji
Yakaita gurin shukoki don yace ita yakeso taringa basu ruwa kana yakaita gaiding nanma yace
hurumin tane
Cai !! ashe zaki wahala *KUYANGA*
Yakaita yanunata ga mai gadinsa domin su san juna sosai tunda ita zata dawo girkin gidan zata
ringa bashi shima
Au ainaxaci gadinma ita zatayi
Kwanan *KUYANGA* Biyar agidan takwashe komai akwakwalwarta ta iya kunna gas tayi masa
sassaukan girki takan mikawa me gadi intayi
Girkinsa bai wuce indomie Cuscus da suyar dankali da doya da kwai sai sauran abubuwan da
basuda nauyi masu Saukin yi
D'an wahala shiyasa bakada k'iba
iyakarta dakinta in yana falo bata yarda tafito inba abinci zata kai masaba shima a kunyace take
zuwa sbd kare mata kallo yakeyi duk kayan kuma data sanya saiya furta cewar sun mata kyau
Magana me tsayi bata hada su to me zatace masa ? Bayaga ina kwana ina wuni sai tambayar
wani abun kuma
*******
Cikin Sati biyu yazamto tafara sabo da komai hatta kayan datake sawa matsatstsu yazame
mata jiki tasaba dasu tunda yakaro mata wasu yakawo mata dayawa
Tun tana kunya inta sakasu harta daina
Yakawo mata manshawa masu kyau da man wanke kai da sabulai nagyaran fata dai
Tana tsafta sosai tana gyara kanta dayake tanada tsahon gashi da cika saidai kullum yasha
gyara ko tayi masa manyan kalba ta bazo jelar kalbar baya aiko takanyi balain kyau dama ga
fuska kamar ba india sosai kyanta yanata bayyana don hutu yanata shigarta ba koina take zuwa
ba kullum bacci daga dakinta sai kicin sai falo
Sai intafuta kaiwa me gadi abinci ko aikin farfajiya
Zaman gidan yafara damunta to amma bayanda zatayi tunda baice tazo tafuta wajenba
aibaxata iya futa batare da izinin saba
Yakan futa tun dare sai tsakar dare yadawo tarasa wane aikine haka kamar na barayi
Hhhh bakisan club yake zuwa ba kenan to zauna wataran zaki sani
wata ranar Lahadi tana Daki akwance tayi rub daciki tanata tunanin masoyinta MAHBUB Tasan
akoina yake yanzun hakan yananan da kewarta
Kawai taji yashigo mata ba sallama
Ta tashi da sauri tace "Sannu dashigowa akwai abinda kake bukatane?
Yaja yatsaya yaruke murkar kofa yace "kitaso maza kidafa abinci ga bakina nan zuwa gidannan
"yan Nigeriane amma anan suke karatu Abokina ne sosai Shi d'in Jinin Sarautane kitsaya
kinitsu kiyi abinci me dadi bawai bamuda inda zamu ciyo bane akwai hotels kawai dai yafison
abincin gidane nasan sa sarai
Ckn ladabi kai akasa tace "to angama.
Yajuya yafuta yana karewa "yar shimin dake jikinta kallo wanda agaban rigar aka rubuta *HOT
KISS!* Da manyan Harufa
adaidai lokacin da bak'in nasa sukazo adaidai lokacin Allah yabata sa,a tagama komai
Har juice ta hada na mango da Banana da kayan fruit dai
dayake yakawo komai yasaka afurji
Itako akwai basirar iya yin komai wani abunma ba koya tayiba datayi nazari aranta tsaf zata
hada
*Tab kaga KUYANGA "YAR Baiwa* ho Allah yabamu yataki zeenatu
Tayi musu sallama falon yarimane sai bak'in su biyu kawai kallo suke suna hira
Bakin suka bita da kallo
Ta dire akan table tareda durkusawa tagaidasu
Yarima yana kallon yanda suketa kallonta
Saida takoma ciki Yarima yakaiwa nakusa dashi duka yana fadin "kai SAHABI kashiga
hankalinka wannan kallo haka na miyene?
Wanda aka kira da SAHABIN yakyalkyale da dariya yace "yo mutumina ai abu nagani kamar
Zinare agidanka tabbas inhar zai dauku saina daukeshi.
Yarima yasake kai masa bugu
"dan ubanka wannan ba kalar taku bace kafi karfinta *KUYANGA* Ce fa da ita nataho ita
tadabance ackn BAYIN ma
SAHABI yace "kai anya kuwa zanyarda da batunka ace wannan *KUYANGA* CE tabbas ackn
kuyangun ma ta dabance kaga halitta fa ga kyau ga cikar halitta Ga kuma………
Yarima yarufe masa baki yana fadin "basaika karasaba abar maganar akoma wata wannan
munwuce ajinta.
SAHABI YACE "kaga yarima kabarni nikam wannan tayimin ta furgitani dayawa domin ko ackn
KUYANGIN gidanmu bantaba ganin mekyau irinta ba
ASHRAF da sukazo tare ya bushe da dariya yace "Kai SAHABI kadai tafi dayawane Plz cool
your mine kada kafara ma you are handsome and gentle fa karike girmanka dai.
Yarima yace "yama fara mana nikam dai bazan yardaba badani a wannan abin kunyarba domin
yafi karfin ajinta shima yasani
SAHABI YACE "Kai! yarima bangane bafa kodai dama kaine aciki.?
Yarima yaja wani mugun tsaki yace "Allah yakiyaye niko mezan da wannan kamanta nine? ko a
mata cikakku ba kowacce nake kulawa ba balle ackn Bayin gidanmu haba Abokina Me Yarima
irina zaiyi da *KUYANGA*
Yahau bude abincin Duk Dan abar maganar yana fadin "Kufara cin abinci tukunna dai.
Anyi haka da kwana guda yacimmata har daki yace mata "Ke Daga yau inhar kinjini da baki
kidaina Saka kananun kayan dana kawo miki
Tace "to, amma babu wasu dazansaka sai wanda mukazo dasu kuma sun tsufa
Yace