Showing 1 words to 3000 words out of 30722 words

Chapter 1 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

*MARUBUCIYA*✍️
Na
Autar Marubuta
_________________________________________
Bismillahir rahmanir Rahim.
Da sunan Allah mai rahma mai jin kai,
Zan fara wannan labari mai suna MARUBUCIYA✍️
Wanda na sadaukar da wannan labarin ga marubuta....



Gageren labari ne , kuma kagaggene daga alkalamin Fatima Abdallah kano
(Autar marubuta ✍️)


Bayan dogon lokacin dana dauka banyi typing ba yanzu na dawo, sai dai inajin alkalamin nawa
yana da'kirewa

Tooo Allah ya bamu sa'ar duniya da lahira ✌️☺️





*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________

_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>


Ku yi mini subscribe Something big is coming....�
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g



Page 1&2



"A hankali yake shafa jikinta yana wani irin murmushi, lokaci guda ya fara cewa gaskiya baby...".

Salma ce ta mike zuwa gaban 'yan aji ta fisge littafin a hannun wata budurwa dake karanta
littafin a gaban yan ajin .

Kowa ido ya zuba mata ganin yadda take huci , amma babu wanda ya iya cewa komai , sai
wata budurwa sa'arta wacce ita ce marubuciyar labarin.


"Ke Salma dallah bama san hauka mene haka wai."?
Cikin fusata tai maganar

Wacce aka kira da Salma ba tare da annuri ba ta kalli mai maganar tana cewa .
"Haba dan Allah Hadiza, wannan wanne irin littafi ne , to wallahi abin ya isa haka , wannan ai
iskanci ne da rashin mutunci, kuma a cikin islamiyya, to wallahi zan sanarwa da malam Auwal ."


Cikin fuskar rashin mutunci Hadiza ta mike ta Sha gaban Salma ta fisge littafin tana cewa .
"Aikin banza , ai ni na dade da sanin bakin cikin da kike mini , saboda kinga ba a karanta
littattafan ki ."

Murmushi Salma tayi ba tare da taso ba , kana ta ce .
"Allah sarki ."
Kawai ta koma gurin zamanta kusa da wata aminiyarta zainab ta zauna.

"Aikin banza aikin wofi , hassada ta yi wa mutum yawa."
Hadiza ta karasa maganar tana neman gurin zama .

Zainab ce ta kalli Salma tana cewa.
"Salma shi yasa baba yake hanaki rubutu saboda marubutan batsa da sukai yawa, suke bata
muku suna , tunaninsa abin da kike yi ke nan."

Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa.
"Wallahi haka ne Zainab, ni kuma gaskiya ina da buri a cikin duniyar marubuta, sai dai baba
yana bani matsala."


Tana karasa maganar sukaji karar kararrawa alamar an tashi , hakan yasa kowa ya mike tare
da jakarshi a hannu wasu a kafad'a.

"Zainab ki sauri dan Allah muje ki bani hadisin nan , kin san malam Naziru idan ban masa aikin
nan ba , bazai barni ba ."

Salma tai maganar yayin da suke fita daga get din makaranta.
"Haka ne wlh ai ba shi da kirki ,mi sauri kan a kira magari ba ."

Suka fara tafiya cikin sauri , kamar yadda Zainab ta bukata.
"Allah ya kawo mu lokacin da zaki waya Salma, kodan ki zo online ki ga irin littattafan da Hadiza
take yi na marasa mutunci, ni wlh bama na iya karantawa."

Salma ta ce .
"Hmm!."
"Ai ki bari kawai Yaya Umar yana son sai min waya kwanan nan ."
Ta karasa maganar tana tuntu'be da wani dutse kamar zata fadi .


Dariya Zainab tai tana cewa.
"Ai kodan soyayyar shi yasai miki."

Salma ta ta'be baki tana cewa.
"Wacce soyayya kuma bayan muna gida daya."
Ta karasa tare da jefa mata harara .

Hadiza cikin fushi sosai tabar islamiyya suka nufi gida ita da kawarta Ruma .


"Ai wallahi Ruma na tsani Salma,bana san ta wlh , munafuka ce ta karshe bana kaunarta ."

Ruma tai murmushi tare da cewa .
"Haka ne , ammma ki dena damuwa da ita mudai a cigaba da rubuta mana littattafai muna more
duniya, idan badan haka ba ai wani abin ba sani zami ba , tunda dai ko a islamiyya ba a Mana

filla filla 'baro 'baro yadda zamu gane , sai dai aita damun mu da wani wankan wajibi wankan
tsarki ."

"Kuma ke mene naki na damuwa Hadiza, ke fa Hadiza RM sunanki , ita kuma Salma Aminu, a
suna ma naki yafi dadi bare littafi."

Sannan Hadiza ta samu tai murmushi


Har yanzu Salma bata samu ta isa gida ba , sakamakon tana tsaye kofar gidansu Zainab tana
jiran fitowarta ta kawo mata Littafin Hadisi

A lokacin wani farin gaye kirar yaran hutu ya tsaya gaban Salma yana cewa .
" 'yan mata adon gari , kwana biyu."
Wani takaici Salma taji ya rike mata zuciya, ta kalleshi tana cewa.
"Lfy lau. Ammma dan Allah bakajin kiran sallah ake ka tafi inda ya dace ."

Farin saurayin me suna Kalifa ya ce .
"Haba Salma, bafa na samun damar ganiinki , kuma kinsan irin san da nake miki."


Lokacin Zainab ta fito rike da wannan littafin ta mikawa Salma, kana Salma tai godiya Zainab ta
ce mata "Saida safe."
Sannan ta shige ba tare da ta ce da wannan gayen komai ba .

Salma ma ta juya ta nufi hanyar gida.


Baban Salma ne da yayanshi Yusuf, dawowarsu daga masallaci ke nan
Yayan nashi yake cewa.
"Har yanzu Salma wai bata dawo ba ."
Yake tambayar Yaya Umar da shima shigowarshi ke nan.


Ansa ya ba shi tare da cewa .
"Eh baba ammma nasan tana hanya ."

Sallama Salma tai tana shigowa cikin gidan ta na hada ido da yayan babanta taji gabanta ya
fadi.....



Bayan Hadiza ta isa kofar gidansu ta hangi wata vabbar mota cike da kaya a ciki , hakan yasa

ta karasa da sauri cikin mamaki , mahaifiyarta dake ganawa da mai motar ta fara tambaya.

"Mama me yake faruwa ne Ina zamu haka ."?

"Shiga mota kawai Hadiza, babu lokaci yau sai kwanan sokkoto mun bar kano domin bamu da
kowa ."

"Mama wannan wanne irin tashi ne haka fisabidillahi, sai ka ce ana korarmu na shiga uku."

Mahaifiyarta kawai ta shige gaban motar , yayin da shima driver ya shige , ganin babu yadda
Hadiza zata yi , ta kama motar ta shiga kusa da mahaifiyarta cikin bakin ciki.
Sannan driver yaja mota cike da kaya suka tafi .


Tunda Salma ta shigo ta durkusa gabansu tana ta kuka , sakamakon irin maganganu da Alaji
Yusuf yake yi .


Malam Aminu ba shi da kowa sai wannan yayan nashi Alaji Yusuf, suna zaune lfy sosai , sai dai
Alaji Yusuf yafi mlm Aminu rufin asiri domin har yaje ya zama Alaji.


Irin girmamawa da malam Aminu yake da ita , hakan yasa yake daukar duk maganar yayan
nashi Alaji Yusuf, hakan yasa ma Umar ya zo ya zauna gurin malam Aminu har ya kammala
karatunsa , yadda yaji dadin zama da kuma yadda yake son Salma yasa har yau bai koma gida
ba .

Kuma Salma take sharba sosai , sai dai mahaifiyarta babu yadda zata yi ne , ammma bata san
wannan hali na Alaji Yusuf.


"Tom ai ba lefinki ba ne , domin tuntuni nake cewa ka bani yarinyar nan ta dawo gidana da
zama, duk ga sa anninta nan su Karima da Husna , ammma kaki ."

Cikin fusata da fada Alaji Yusuf ya cigaba da cewa "To in Sha Allah komai ya kare , gobe ki
shirya kayanki tsaf Umar ya kawo ki."

Kuka Salma ta sake rushewa dashi tana kallon mahaifiyarta.
Babanta malam Aminu shi ne ya ce .
"To mene abin kuka kuma, kin san cewa bama san wannan rubutun da kike yi , karya da
gaskiya da shedanci , ammma bakya ji ."

Umar ne da ransa ba ya masa dadi ya kallah kanin babanshi yana fad'in .
"Baba wallahi wannan abin da Salma take bafa abin sabo bane ko ...".

Kafin ya karasa maganar babanshi ya dakatar dashi da cewa .
"Baki daya Umar nawa kake da har kasan duniya, mu muka ga ga jiya muka ga yau , duk
iskancin da ake a fim kala kala su waye ke rubutawa in ba marubuta ba , to bazai yiyu yarinya
ta zo tana jaa mana zagi ba ."
"Wanne irin iskanci ne basa yi duk aita lalata tarbiya."
Ya sake kallon malam Aminu yana cewa."Wai har da marubutan matan aure, tsabar isgili to
rubutu dai Salma ba a wannan zuri'ar tamu ba ."

Ya mike tsaye tare da sake kallon Salma yana cewa
"Gobe babu fashi Ina sauran ku ."
Ya nad'e malum malum ya fice , mahaifiyarta na cewa "A sauka lfy Allah yasa haka ne yafi
alheri."
Salma ta sake bushewa da kuka .

07040805269
WhatsApp only
Autar marubuta ✍️


MARUBUCIYA
Na
Autar marubuta
________________________________________

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so

Dangin dalas...

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>


Ku yi mini subscribe Something big is coming....�
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g


Page 3&4

Bayan Alaji Yusuf ya tafi Salma ta mike ta shige daki ta cigaba da kuka , duk yadda Umar yayi
domin ya rarrasheta taki , domin tasan idan ta koma gidan Alaji Yusuf burinta na zama
marubuciya tabbas sai dai mafarki.

Haka tai ta kuka tana sunbatu kala-kala har akai kiran sallar isha'i
Ko abinci bata iya ci ba ta shige daki ta rufe , mahaifiyarta abin yana damunta sai dai babu
yadda zata yi , domin komai wuya tafi son Salma a kusa da ita .


Anan cikin gidan Alaji Yusuf kuwa .
Karima ce zaune sai had'a gumi take rike da waya a hannu , da gudu Husna ta shigo tana
cewa.
"Wallahi Aunty Karima ga babana ."

A firgice ta aje wayar tare da tula mata kaya tana dariya
"Kaiiiiiiiiiiii Husna wallahi littafin nan abin tausayi, gaskiya marubuta suna kokari, ai wallahi
komai nacin baba yau saina gama karanta shi ."
Dariya suka sake fashewa da ita , sannan suka fita tare domin yi wa baban nasu sannu da
zuwa.


Salma kamar hankalinta ya fita ta yanke wannan d'anyen hukunci na barin gida , kayanta ta
tattara ta zuba a wata karamar bakko , sannan ta fara sanya ido, mahaifiyarta harta kwanta ,
shima Umar haka sai dai duk basi bacci ba , kuma ba a rufe gida ba sakamakon malam Aminu
bai shigo ba .

A hankali ta dauko wannan bakko ta jawo dakin , daidai sanda ta hangi mahaifiyarta na kwance
ta ji kuka ya sake rufeta , haka tai sauri ta wuce ta kofar dakin Umar ta fita waje tana kuka , tana
kuka zuciyarta na sa'ka mata tana shirin yin babban kuskure, wannan ba shi ne hanyar cikin
burinta ba , ammma wata zuciyar na fad'a mata aka sin haka , hakan yasa kawai tai gaba ta nufi
tasha tana kuka .
Babu jimawa mlm Aminu ya dawo , aiko babu wata -wata ya rufe gida .

Cikin tasha take tafiya tana kuka tana waige -waige
"Salma Ina zuwa lafiya kuwa."?
Da firgice ta juya don ganin me magana
Kalifa ne saurayinta
"Ina zaki , ke da bakya fitowa da dare."

Salma ta share hawaye tana cewa.
"Kalifa ka rantan dubu biyar in sha Allah zan biyaka ."

Dariya Kalifa ya yi yana cewa.
"Haba sweetheart, ai kinfi karfin rance a guri na , kina da kyau da hankali."

"Zan baki dubu 10 Salma, amma idan kina so ."
"Ina so mana."
Ta fada cikin kuka
"Tom ki dena kuka ki zo muje dakina minti biyar zaki a can zan baki dubu 10."

Wani abu Salma taji ya tokare mata zuciya dajin wannan batu daga bakin Kalifa , ashe tabbas
gaskiya ake fada a kanshi ya lalata yan mata da yawa .
Abin da yazo kanta ke nan.

Ba tare da ta ce Komai ba kawai ta juya zata tafi.
Jawo mata hijabi ya yi yana cewa.
"Haba Salma karki wasa da damarki ."

Juyowa tai cikin sabon bakin ciki da takaici ta falla masa mari , bata san lokacin data d'uro wata
ashar ba tare da cewa.
"Wallahi zan maka ihu anan gurin banza jahili mahaukaci wawa dabba ."

Kawai ta dauki kayanta tai gaba
Koda taje tasha bata san inda zata ba , kuka ta tsaya kawai tana yi , zuciyar ta na saka mata ta
koma gida

"Sister ina zaki ."?
Wata yarinya da bata wuce sa'ar ta ba ta tsaya gaban ta tare da wani saurayi tana tambaya,

Salma tai shiru kafin ta ce .
"Unguwa zani ."
Ta fada kamar tanajin tsoro .
"Ki dena kuka komai tsanani yana tare da sauki ki yi hakuri."
"Ki zo ga mota yanzu zata tashi zaria zamu ."

Salma ta bi bayansu ta shige motar , ba tare da tunanin babu Wanda ta sani a zaria ba .
Bayan sun zazzauna mota ta cika ta fara tafiya Salma ta cigaba da kuka tana shashsheka .

Hakan yasa wannan matashiyar ta kalli wannan kyakykyawan saurayi da suke matukar kama
da juna , murmushi ya yi mata kawai , hakan yasa ta dora hannu jikin Salma tana cewa
"Sister."
Salma ta d'ago cikin hawaye
"Ki yi hakuri dan Allah."

Murmushi Salma tai tare da share hawaye tana cewa.
"Na gode mene sunanki ."
Ita ma tai murmushi tare da fad'in ."Suna na Salma, ga yanana can Yaya Umar."

Salma bata san lokacin da tai dariya ba tana cewa.
"Abin mamaki, nima suna na Salma kuma ina da Yaya Umar."

Ta karasa maganar tana kallon wancen Umar din .


Murmushi d'ayar Salman tai tana cewa.
"Masha Allah, mu zamu tafi zaria ne , saboda munzo ziyara nan kuma ga shi mun yi dare."

Salma ta ce .
"Uhmm Allah ya sauke mu lafiya ."

Sauran mutanen motar sun yi shiru kowa da abin da yake sakawa a ransa, babu gida gaba
babu baya , sawu na motoci da mutane duk ya dauke a wannan hanya .

Lokacin driver yaji mutum ya fado gaban motarsa , wanda kowa Saida ya firgita , yana shirin
tsayawa, wani mutum ya ce .
"Karka tsaya wallahi hanyar nan bata da kyau."
Driver ya ce .
"Innalillahi mutum ne fa na kad'e ."
Yayi sauri ya fito , kowa hankalinshi ya tashi , mutumin da ya kade jikinsa duk jini yana cewa.
"Kai sauri kaja motarka ku tafi , yan bindiga dadi ne suka biyo ni , kai sauri kaja motar ku bar
nan ."

Cikin rudewa driver ya ce .
"Taso mu tafi bama barka anan ba ."
Yana zuwa kusa dashi sai karar bindiga suka ji ta koina

Sai ihu da salati , mutane suka fito daga motar sai gudu
Sun yi wa driver da wannan mutumin kaca-kaca da harbi
Salma da gudu suka nufi wata hanya su biyar cikin tashin hankali suna gudu .
Sai ji sukai a bude wuta a ta wajen su juyawar da Salma zatai taga duk an zubar da su kasa ,
sai ita kadai a tsaye
Ta fashe da kuka ganin yadda wannan Salman take rike da gawar yayanta Umar an fasa masa
kai .

Yan bindigar ne suka sake biyosu suna harbi , da kyar Salma Aminu ta rarrashi Salma ta taso
tabar gawar yayanta Umar agun suka cigaba da gudu suna faduwa suna kuka

Gudu suke sosai basu san inda suke sa kafarsu ba , daji ne ga duhu


Haka har asuba tai musu a wannan gurin ,jikin dayar Salma duk yayi rauni haka ta fadi a
wannan wajen .

Babu gida gaba babu gida baya , kurgurmin daji ne sai bishiyu , hakan yasa Salma ta tsaya
gurin dayar Salman tana kokarin tashinta zaune .
Bayan ta tasheta ta jingina ta jikin wata bishiya tana wani irin nishi tana cewa.
"Mun yi tafiya Sosai sister, daga nan babu inda zan kara , sai dai nasan mun tserewa wannan
yan bindigar mun yi musu nisa."

Tana yi tana wani irin nishi idanunta sun yi jaaa
Salma kawai ta fashe da kuka mai matukar gwanin ban tausayi.
'Dayar Salman ta cigaba da cewa .
"Sister Allah yana tare da ke , ammma ni mutuwa zan yi a wannan gurin , sun kashe Yaya Umar
a gabana , sun kashe mutane da yawa, Allah ya hada mu a aljanna."

Cikin tashin hankali da sabon kuka Salma Aminu ta fara cewa.
"A'a Salma, ba mutuwa zaki ba , bazan barki anan gurin ba , mu karasa gaba ko zamu samu
wani rafi mai ruwa , zaki dawo daidai."

Kawai shiru Salman tai domin irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login