Showing 9001 words to 12000 words out of 30722 words

Chapter 4 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

dora sai ta tsaya cak
Tana kallon electric din.
Tunanin da take , ta ya ne zata kunnata , tana ganin irinta ne kawai a cikin films.


Ba zato taji an rike mata hannu tare da damke rigarta ta baya .
"Innalillahi."
Ta fad'a cikin tashin hankali da juyawa baya
"Kaii ne ."?

Ta cewa Anas
Wata shegiyar dariya ya yi yana cewa.
"Tom wa kike tunani ni ne ."

"Sake ni ."
Yaki sakinta

"Wallahi zan maka ihu ."
Ta sake fad'a
Wata dariya ya sheke da ita tare da cewa.
"Tom ai nan gidanmu ne , daga ni sai ke sai mommy."
"Kawai malama ki cire wannan rigar." Ya fad'a yana dora hannunsa a bayanta.
Bige hannunsa tai da nata tana jin tsoro jikinta na rawa
"Dan Allah ka yi hakuri."
Jin hakan yasa ya fincike hannun rigar Salma sai ji take
Feshhh
Rigar ta yage
Daidai karfinta ta wurgar dashi tasa gudu , ya mike da gudu ya bi bayanta .
Da sauri Salma Allah ya bata sa a ta shige dakinta ta kulle ,
Ta dafe kirjinta dake bugun dubu dubu , jikinta na rawa da durkusa kasa .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun.
Wannan wacce irin masifa ce."?
Ta tambaya kanta cikin tashin hankali.

"Ki bude kofar nan , ki bude kofar nan ."
Taji muryarshi yana magana a kofar dakin , wani tsoron ne ya sake rufeta
Shiru tai masa kawai tana ta kakkarwa
"Shi ke nan, kere na yawo zabo na yawo ai ."
Jin hakan ya tambatar mata da ya tafi , sakamakon taji sautin takunsa .

Kuka Salma ta fashe dashi tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."



Haka ta zauna a dakin nan ko bacci bata iya yi ba , ga yunwa tana ji har saida Aunty Hauwa ta
dawo .
Koda Aunty Hauwa ta dawo bata fita falo ba , kawai dai ta bude kofar dakinta sannan ta cire
wannan rigar."
"Assalamualaikum Salma."
Ta shigo rike da jakar aikinta a hannu
Murmushi Salma tai mata mai cike da matukar kewa kafin ta ce .
"Sannu da zuwa Aunty."

Aunty Hauwa ta zauna gefen gado tana cewa.
"Ya baki da lafiya ne Salma,na ga idonki ya yi ja ."

Murmushi na yake Salma ta kuma yi kana ta ce .
"Lafiya lau Aunty babu abin dake damuna."

Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya tare da zuge wannan jaka tana cewa.
"Tom ai shi ke nan."

Waya ta zaro Hot 30i sabuwa a cikin gidanta tare da SMS din Glo da MTN
Sannan ta mikawa Salma
Wani dassss Salma taji a zuciyarta tasa hannun ta karba kamar mai jin tsoro.
Kafin ta ce komai Aunty Hauwa ta sake zaro wata bakar laptop karama ta sake mika mata
"Salma wannan naki ne ki yi amfani dasu saboda rubutun ki ."

Wasu hawaye ne suka zubowa Salma lokaci guda
Domin bata taba tsammanin irin wannan ba .
Cikin kuka ta ce .
"Bansan ta ya zan gode miki ba Aunty, Allah ya saka da gidan aljanna, Allah ya jikan iyaye ,
Allah yasa baki abin da kike nema , wallahi Aunty..."

Aunty Hauwa ta dakatar da ita da cewa.
"Na gode Salma, ki gode Allah, ammma ki yi shiru ki dena wannan kukan ."

Salma ta share hawaye tana sake kallon irin wannan kaya da suke hannunta .
Sannan Aunty Hauwa ta sake fad'in.
"In Sha Allah zuwa dare zan nuna miki yadda zaki rubutu a laptop din , ki yi saving, ki yi share."

"Sannan anjuma zamu je ai miki register na SMS."

Salma ta girgiza kai alamun tom domin ta kasa magana
Tana gama magana ta mike , ta sake kallon Salma tana cewa.
"Salma ki maida hankali kinji, sannan akwai wani marubuci Sir Abubakar Sadiq, shugaban
kungiyar Lafazi writer's Association, zan had'a ki dashi , domin shiga kungiyar zai taimaka miki."

"Too Aunty."
Abin da ta iya fad'a ke nan, sai Aunty Hauwa ta fita .

Allah sarki Umman Salma addu'a ta rike gashi ta fara dangana da rashin Salma, domin a yanzu
haka tana zaune tana sauraran redio


Hadiza ce kwance a tsakar gida tana danna waya .

Umman ta ce ta fito daga daki cikin masifa tana cewa.
"Wai ke babu inda zaki iya zuwa ne , kullum kina gida yau juma'a ma babu inda zaki."

Hadiza ta ce .
"Haba umma to ina zani , islamiyya dai yau babu ai."

Tana rufe baki wani yaro ya shigo yana cewa.
"Assalamualaikum, wai Hadiza ta zo in ji wani a cikin mota ."
Hadiza suka had'a ido da mahaifiyarta

Bayan korafin rashin ganin page 5 &6 da page 7&8 tom zan sashi a channel kadai.

Autar marubuta
07040805269


*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>


Ku yi mini subscribe Something big is coming....�

https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar Marubuta
_______________________________________
Page 15&16

"Tom ka ce tana zuwa."
Ummanta ta bawa yaron amsa , sannan ya fice
"Tashi ki je ."
Cewar Ummanta
Hadiza babu musu ta tashi da sauri ta fara shiryawa, wata abayarta tasa ruwan toka , sannan ta
baza turare aka fita .

Cikin taku mai kyau ta fita waje ta hangi wani dogon saurayi fari kalar hutu, ya jingina jikin bakar
motarshi yana danna waya .
Kamar kamshin turaren Hadiza ne ya dakeshi, ya juyo yana kallonta tare da cire gilashi.

Ganin taki karasowa inda yake , hakan yasa ya taka cikin taku na girma ya tsaya a gabanta .
"Assalamualaiki ma 'a bociyar kyau da kasaita."
Ya fad'a yana murmushi

Murmushi tai kamar baza ta amsa ba, sannan ta amsa .
Kana ya cigaba da cewa.
"Suna na Sultan yaron gidan Alaji Babawo."

Da sauri Hadiza ta sake kallo hadadden saurayin cikin mamaki .....
"Tom sannu da zuwa."
Cikin kunya da durkusar da kai ta fad'a.

"Wato Hadiza ina yawan ganinki zaki tafi islamiyya, da nai tambaya ake sanar mini ai baku
dad'e da dawowa nan ba ."
Hadiza ta ce .
"Haka ne , amma dan Allah mene ya kawoka saboda Umma ta sani aiki a ciki."

Murmushi ya yi yana rausaya kai , kana ya ce .
"Tom babu damuwa Hadiza, idan kin amince zan dawo wani lokacin."

Ta ce .
"Babu damuwa."

Da gudu ta shige gida tana tsalle , ita ma Umma dake jiran shigowarta ta fara tambaya.

"Ya akai mene ya faru ."?....

Tun asuba da Salma ta tashi bata koma ba , saboda irin tarin shauki da farin cikin da take ciki .

Wayarta ta dauka tare da yiwa Sir Sadiq Abubakar magana.
Nan suka gaisa ta gabatar masa da kanta, nan take ya fahimci wacce Aunty Hauwa tai masa
magana akan ta ne .
Ta yi matukar farin cikin yadda shima ya karfafa mata gwiwa da yabon kokarinta sosai.
Haka ta cike form din shiga wannan kungiyar ta Lafazi writer's Association, kana ya sata cikin
muhimman group na marubuta, ciki kuwa harda Bakandamiya reading club.


Ta samu kanta cikin matukar farin ciki sosai a wannan yanayi
Hakan yasa babu 'bata lokaci ta fara rubuta littafin ta na farko mai suna "FATIMA DA ZARAH."

Lokacin da take tunanin sunanta Salma Aminu Waziri , tai tunanin kawowa kanta matsala,
hakan yasa ta canza sunanta zuwa Autar marubuta

Haka har gari ya fara wayewa , Aunty Hauwa ta fara shirin fita , sai hankalin Salma ya tashi
kuma , ganin cewa Anas yana nan kuma baza ta iya sanarwa da Aunty Hauwa wannan lamarin
ba .
Hakan yasa bayan ta tafi , Salma ta rufe dakinta ta cigaba da abin dake gabanta .

Bayan wasu kwanaki......

Anan kuwa Masha Allah biki ya yi biki , Amarya Karima saidai mu ce Allah san ya alheri ya
kawo na yan baya , lokacin da aka zo tafiya da Amarya su Husna an sha kuka , hatta shima
Umar ya yi wannan kuka sakamakon yadda yake yawan tunanin Salma babu labarinta .

Bayan wani lokaci.
Hadiza ce kwance kamar kullm , sai dai a wannan lokacin tana bangaren Karima.
Datarta a kunne ta ga sako ya shigo daga cikin group dinta .
"Dan Allah Fatima da zarah daga page 5 zuwa inda aka tsaya."
Bayan ta karanta sakon tai shiru tare da tunanin ina tasan wannan Littafin Fatima da zarah.
Karima ce ta shigo ta katse ta da fad'in.
"Hadiza kin bar karamar wayarki dakin Mama ana ta kira ."

Hakan yasa ta tashi ta nufi cann , ita ma Karima wayarta ta dauka kai tsaye ta nufi WhatsApp,
sakon kanwar ta Husna ta bude kana ta kunna voice din.
"Haba Aunty, to a gaida Yaya Adam din, kar dai garin karanta novels aje a kona masa girki.
Kuma Aunty har yau ina ta jira baki turan Littafin kanwar Yaya Adam din ba ."

Iya kar voice din ke nan .

Karima tai murmushi tare da maida mata da cewa.
"Ke yarinyar nan wallahi ki kiyaye ni ,wato wayar mommy kike dauka,kinga idan baba ya gano ki
babu ruwana, sannan kuma rabu da littattafan Hadiza duk ba dadi na fita a channel da group
din ta ma, akwai wata sabuwar marubuciya Autar marubuta zan turo miki link din group din ta."
Tana gama voice din ta tura mata, ganin Husna bata online yasa Karima kashe data


Duk su Aunty Hauwa suna falo, ana ta hira , Salma indai ba Aunty Hauwa bace ta dawo samm
bata sakin jiki kamar haka .

"Gaskiya Salma kina kokari sosai wannan Littafin da kike rubuta wa Allah ya kara Basira."
Hajjiya Aisha ta ce .
"Amin summa Amin."

Anas yayi murmushi, Salma ta kauda kai ko kallonshi batai ba
"Aunty Hauwa gobe shekarar Umma 5 da rasuwa."
Cewar Anas
Aunty Hauwa ta ce .
"Haka ne ,ya akai baka manta ba , ai na zata ni ka dai nake lissafin."

Kafin ya kuma cewa komai Salma ta ce .
"Wa ce Umman."?
Anas ya bata amsa da fad'in.
"Mahaifiyar Aunty Hauwa ke nan , mutuniyar kirki."
Jin hakan yasa ta kalli hajjiya Aisha
"Dama ba tare suka rasu da su Daddy ba ."?

Salma ta tambayi Aunty Hauwa
"A'a ba tare bane Salma, su Baba da mijina ko shekara basi ba , sun yi accident ne ."

Ta karasa maganar tana kuka

"Haba Hauwa'u ki yi hakuri mana , ai addu'a ita ce komai." Cewar hajjiya Aisha

Salma ta ce .
"Haka ne, dan Allah Aunty ki yi hakuri Allah ya kara haske a kabarinsu ."..



Umman Salma ce zaune tana sauraran redio, kwana biyu kamar yadda take jin wata tasha da
Salma ke saurara ita take saurara tunda Salma tabar gida.
Domin ana karanta littattafan Hausa kala kala na marubuta da dama , har akan gayyato wasu
daga cikin marubutan, a dai dai wannan lokacin Malam Aminu ya shigo yana daddafa bango

Umar ya rikeshi .
Da sauri ta tashi tana fad'in.
"Innalillahi Umar lafiya."?

Umar ya maida mata da fad'in.
"Wallahi Umma faduwa ya yi."
Ta sake fad'in.
"Subahanallahi." Ta fara kokarin kawo tabarma



"Mun gode Autar marubuta Allah ya kara Basira da daukaka."

"Gaskiya Fatima da zarah wannan Littafin ya yi Allah yasa a gama lafiya."

"Ikon Allah Fatima da zarah muna jiran cigaba, Allah ya sa afi haka."

Irin yadda Salma take karanta comments ke nan abin yana faranta mata sosai .

"Gaskiya Umma na samu kudi a wannan Littafin."
Cewar Hadiza
"Dubu 29 fa yanxu haka,kuma ba a gama siye ba nasan."
Karima dake yankan alaiyahu tai murmushi
"Tom ai ina miki addu'a Hadiza."
Cewar Ummanta

Ajiyar zuciya dai Karima tai cikin zuciyarta tana cewa.
"Allah ya shirya."

Wani dassss Salma taji a ranta ganin update din wani Littafi mai suna "Aure dadi ."
A cikin group din ta
Na
Hadiza RM
Abin data gani ke nan , zuciyarta taji tana mata zafi ganin irin yadda Hadiza ta sake kwarewa a
shashanci da rubuta batsa babu ko kunya ko tsoron Allah.


Goge posting din tai tare da rubuta, "duk wacce ta sake turo irin wannan zan cire ta."

Kana ta fito daga group din tana mamaki. Cikin ikon Allah ta kammala Fatima da zarah harta
fara wani Littafi mai suna .
"HIJIRA."

Anan kuwa gama cirewa Malam Aminu karin jini ke nan.
Matarshi dake zaune cikin damuwa ya kallah yana cewa.
"Yau baki kunna redion taki ba ."
Murmushi tai kafin ta ce .
"Hmm Malam ke nan, ai bana takura ma ba kana bacci ma Alaji Yusuf ya zo , ya ce zai dawo ."

Umar ne ya shigo yana dariya yana bude hakora gaban baban nashi ya zauna yana cewa.
"Baba yanzu aka aikon da sako a waya , wannan aikin na company da nake nema an dauke ni
."
Ya koma ya kalli Umma cikin farin ciki.
"Alhamdulillah , Alhamdulillah Umar Allah mun gode maka."
Umman Salma ta fad'a
Cikin karfin hali Malam Aminu ya nuna farin cikin sa matukar gaske , tare da yiwa Umar tarin
nasihohi da fatan alheri, sannan Umar ya shirya domin tafiya gidansu Dawaki, da wannan
babban zance mai dadi .

Autar marubuta

https://chat.whatsapp.com/G3YMYAHnKG4DiU7ZeuwDGk
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_

<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>


Ku yi mini subscribe Something big is coming....�
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 17&18



Salma sai dai mu ce Alhamdulillah, domin tana da tarin mabiya da suke karanta Littafin ta, wani
abin farin cikin da ya sake samunta shi ne , yadda masu YouTube suka sai Littafin nata akai
audio dinsa, nan ne sunanta ya sake bunkasa domin ba karamin hikima da tunani aka zuwa a
wannan Littafin mai suna Fatima da zarah ba , duk da cewa ta fara rubuta wani Littafin.
Aunty Hauwa tana tsaye cikin falo tana amsa waya, domin tana waya ne da yayan babanta,
tana sanar dashi tafiyar da zatai zuwa Dubai .
Bayan ta gama ta dawo cikinsu hajjiya Aisha ta zauna, ta kalli Anas da fad'in.
"Tom tafiya ta zo ."
Salma da sam batasan da tafiyar ba ta kalleta tare da tambaya.
"Aunty wacce irin tafiya."?
Cikin damuwa ta tambaya
Da annuri a tare da ita ta ce.
"Daga wajen aiki ne Salma, zamu je Dubai wata biyu kawai zami ."

Ajiyar zuciya Salma tai kafin ta sake fad'in.
"Yaushe Aunty har wata biyu."?

"Eh Salma wata biyu zami , sauran sati daya mu tafi , amma ai ga mommy karki damu."
Ta nuna hajjiya Aisha

Hajjiya Aisha tai wa Salma murmushi tare da fad'in.
"Karki damu Salma, ai an zama daya , sai dai mi mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya."

Ajiyar zuciya mai zafi Salma ta sake saukewa tana kallon Anas.
"Tab Aunty ni zaki bari a wannan gidan, wallahi akwai matsala."

Tai maganar cikin zuciyarta

Aunty Hauwa ce ta sake fad'in.
"Kuma ina dawowa zamu je Kano, wajen yayan baban naki.".

Salma tai murmushi mai cike da damuwa tare da cewa.
"Tom Aunty."
Tunani Salma ta sake lulukawa ciki tana hango irin damuwar da zata shiga a wannan gidan idan
babu Aunty Hauwa.


Jikin Malam Aminu ya yi tsanani sosai, domin jiya ma a asubiti suka kwana, sai dai mu ce Allah
ya bada lafiya

Su Aunty Hauwa suna cikin cigaba da hirarsu, aka fara kiran wayarta .
Ganin kanin babanta ne yasa ta tashi ta shige dakinta.
"Assalamualaikum Baba."
Abin da Aunty Hauwa ta ce ke nan bayan d'aga wayar
Daga can bangaren yayan baban nata ya ce .
"Wa'alaikumus salam Hauwa'u, muna waya na tafi wani uzurin ."

Da girmamawa ta ce .
"A'a babu komai Baba."

Jin hakan yasa ya cigaba da cewa.
"Tom wannan shi ne , da hajjiya Aisha zata bayar da kadarorin mahaifinki tuni ta bayar, to amma
babu niyyar haka, dan haka kotu zamu kaita ."

Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai tare da cewa.
"Baba bawai bana so a tayar da maganar bane, ammma hajjiya Aisha duk ta canza wallahi
kwana biyu, a yi hakuri idan na dawo daga Dubai sai a yi maganar, yi hakuri Baba."


Kamar bai ji dadin maganar ba ya ce .
"To ai shi ke nan Salma, ina yin wannan ne kawai a matsayinki na amana a guri na , tunda haka
kika ce Allah ya dawo dake lafiya."
Ta amsa masa da"Amin babana."
Sannan sukai sallama ta kashe wayar


Yayan baban nata yana kashe wayar ya kalli matarshi dake gefe ya ce .
"Allah sa mu dace , Allah raba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login