Showing 15001 words to 18000 words out of 30722 words

Chapter 6 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

.
"Tom shi ke nan, zan taimaka miki da kyakykyawan zuciya, amma indai kika cutar dani ko

matata bazan yafe miki."
Ya nufi ciki Salma ta bishi suna shiga matarshi tana alwala
"Baby lafiya."
Abin da matar tashi ta ce ke nan tana kallon Salma.
"Fatima ga wannan, ki bata daki idan na dawo zan miki bayani ."
Kana yayi sauri ya juya , kamar yadda ya ce , ta bawa Salma daki, ta fito ta yi alwala tana yin
sallah bacci ya dauketa a gurin .

Wajen karfe 11 na safe Hadiza tana zaune falon Karima tana daura dan kwali ga dukkan alamu
fita zatai domin ga Jakarta nan a gefe .
"Hmm amaryar sultan."
Karima ta fad'a tana kalloonta .
"Aunty Karima da Allah ki bani jan, janbaki nasa."
Inji Hadiza
Karima ta ce .
"Ki je ki dauko mana yana ciki, ki zo ki turan WhatsApp."
Hadiza ta mike da nufin dauko janbaki tana cewa.
"Wayar na jakata ai ki dauka ki tura Aunty."
Karima ta jawo jakar tare da zugeta, kana tasa hannu a ciki

Dasssss dauuu
Abin da Karima taji a zuciyarta, sakamakon cin karo da abu aleda
"Ido da kofato."
Cewar Karima tsoro ya kamata sosai , domin duk a tunanin ta idon mutum ne
Da gudu ta fad'a uwar daki tana cewa.
"Idon mutum a jakarki àljanu Hadiza."
Cikin matukar tsoro
Dariya Hadiza ta sheke da ita tana cewa
"Kai Aunty, wanne irin idon mutum, idon jaki ne fa."

"Me zaki dashi."?
Ba tare da kwanciyar hankali ba ta sake tambaya
Ajiyar zuciya Hadiza tai tare da aje janbakin tana cewa.
"Gaskiya Aunty bana so na fad'a miki, saboda karki fadawa Yaya Adam ya kashe ni."
Karima ta ce .
"Babu abin da zan fad'a masa."

Sannan Hadiza ta fara cewa.
"Tom Aunty kinga akwai wata marubuciya Autar marubuta tom tana son kawon matsala da
rashin cigaba hatta novels dina tana cewa babu kyau wai haram ne , tom shi ne muka je gun
wani malami ni da Umma, za a kuturtar da ita harda makancewa, dan Allah karki fadawa Yaya
Adam."

Ai baki daya Karima mutuwar tsaye tai da jin wannan batu, haka Hadiza tasa mayafi ta fi ce
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, wannan wacce irin zuciya ce da Umma da Hadiza, yanzu mene
laifin wannan marubuciya, innalillahi wa innailaihir rajiun."
Cikin tashin hankali Karima ta zauna a bakin gado tana maganar

Jimm ta yi sosai domin wannan maganar ta girgiza ta matukar gaske , yanzu bata san mene
abin yi ba .

Autar marubuta.


*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 23&24

Bauchi


Karfe 11:20 Salma ta farka a bacci , sannan ta karewa dakin da take ciki kallo, kana ta mike ta
fita tsakar gida, koda ta fita mai gidan da matarshi suna zaune suna ta hira
Salma ta durkusa gabansu tana cewa.
"Ina kwanan ku , kuyi hakuri ."

Murmushi mijin ya yi , kana ya ce.
"Aa karki damu, Fatima ki dauko mata abinci ta karya ."
Ta mike kamar yadda ya ce .
Ta kawowa Salma doya da kwai sai kunu a cikin kofi
"Na gode ."
Salma ta fad'a bayan ta aje mata a gabanta
"Ammma baiwar Allah kinga jikin ki babu wahala, taya zaki tsinci kanki a haka."
Cewar matar tashi Fatima
"My sweetheart ki bari ta huta mana kina mata wannan maganar ko abinci bata ci ba ."
Ya fad'a wa matarshi
Murmushi Salma tai tana cewa.
"A'a babu damuwa ai , daga Gombe nake , Aunty na ta tafi Dubai jiya , tom shi ne matar gidan
ta koreni , suka ma siyar da gidan , sannan yaronta ya sacewa auntyna waya bayan ya rakata
airport, ya zo ya sani a mota tun dare jiya , ya ce duk inda zani naje ."
"Gashi sai nan da wata biyu zata dawo ,babu inda na sani ."
"Allah sarki."
Ya fad'a yana kallon matarshi
"Tom ni suna na Aliyuu ga matata Fatima."
Salma ta ce .
"Ni suna na Salma."
Fatima ta ta'be baki tana kauda kai
"Zaki zauna damu tsawon wata biyun , idan Allah yasa ta dawo sai ki koma."
Aliyuu ya fad'a , da sauri matarshi Fatima ta kalleshi tana cewa.
"Baby kamar ya wata biyu, daga baka labari baka san gaske take ko karya ba , kawai sai ta
zauna damu."
"Haba Fatima, duk da ba a gane macuci wannan yarinyar ai da gaskiyarta , ki dubeta fa mene
wata biyu, taimako ne kawai ."

Salma kasa tai da kai kawai tai shiru , matar tashi ta mike ta shiga daki.
"Karki damu Salma ki zauna anan ki yi hakuri, kije ki ci abinci."
Ya shige yabi matar tashi, kana Salma tai ajiyar zuciya tare da daukar abincin tai daki ita ma .

Kano

Allah sarki baiwar Allah umman Salma tana zaune ta yi shiru. Tana rike da wata takarda a
hannunta, jin Shigowar Umar yasa ta muskuta tana amsa sallamar da ya yi , tare da tura
wannan takardar karkashinta ,gabanta ya zo ya tsuguna .
"Umma babu wata matsala ko, ko akwai abin da babu."?
Ta murmusa tare da fad'in.
"Allah ya maka albarka Umar, sai dai akwai komai , sai dai kuma Umar tunda Allah yasa kana
aiki , ka yi aure mana, rufin asiri ya samu ai ."

Jin hakan yasa shi jin kunya .

"A'a Umma, ina nan ina jiran Salma inajin tabbas zata dawo."
Umma ta ce .
"A'a Umar, ni yanzu na cire rai da Salma, ka manta da ita kawai, haka ta zabarwa kanta ."
Umar ya ce .
"Tom Umma kinga wannan gidan, zan gyara miki shi asa tayill a gyara dakuna koina in Sha
Allah."
Umma tai murmushi tare da fad'in.
"Tom Umar nagode."

Washe gari

Sokkoto ❤️
Tun jiya da Adam ya dawo daga aiki ya gaza gane kan Karima, sai dai Karima tunda taji zancen
Hadiza duk ta rasa nutsuwa, duk da cewa batasan wannan marubuciya ba , amma abin da taji
za ai mata ya matukar d'aga mata hankali, sai dai aduk tunanin ta babu hanyar da zata iya hana
wannan aika_aika.
Misalin karfe 8 na safiya, Salma harta samu ta karya ta yi wanka , kana shi Aliyuu ma har ya tafi
wajen sana'arshi ta shayi da burodi .
Jimmm ta yi sakamakon yadda taji kanta yana mata ciwo sosai .
"Allah sarki Aunty Hauwa, kona kira bana samu ."
Tai maganar tare da tuna cewa ta ce ."Ta tura mata dubu 30."
Murmushi Salma tai tare da ciro wayarta a caji da nufin shiga opay .
Diffffff
Salma duhu kawai ta gani , tasan da cewa waya ce a hannunta, amma bata iya ganin komai sai
duhu .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun meke faruwa."?
Ta fad'a cikin tashin hankali tare da wurgar da wayar hannunta.
"Aunty."
"Aunty Fatima."
"Auntyyyy."
Salma tana kira cikin tashin hankali, yadda matar aliyuu taji tana kiranta , dah kamar baza ta fito
ba , amma ta fito ta shiga dakin
Ganin idanun Salma a bude yasa tai tsaki tana fad'in.
"Kina ta kirana kamar makauniya lafiya."?
Salma ta daddafa ta mike tsaye tare da fad'in.
"Wallahi Aunty bana ganin komai sai duhu, bana ganin komai wallahi."
Ta fashe da kuka.
"Okay wata yaudarar kika zo msna da ita ke nan, to wallahi kiji tsoron Allah mijina ba kudi
gareshi ba , shayi da burodi ne yake siyarwa."
Fatima ke nan
Cikin sabon tashin hankali Salma ta ce .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."

Ta ke ce da wani kuka sai ga wasu hawaye zirrrr
Sai a lokacin fatima ta matsa kusa da ita , kana tasa hannu a fuskar ta , don tabbatar da bata
gani .
"Innalillahi tom garin ya kika dena gani Salma, dama kina irin wannan ne , ko kina da àljanu."?
Da mamaki Fatima tai maganar tana jahh da baya ,
Fi ce wa tai tare da daukar wayarta, kai tsaye ta kira mijinta, dake shima dan albarka ne ko minti
10 bai bata ba , sai gashi ya zo
Tsakar gida ya samesu dake Fatima ta riko hannunta sun fito
"Me ke faruwa haka ne ? Da gaske bata gani."?
Da rudewa ya ke maganar
"Wallahi kuwa, ina daki take kirana."
Fatima ta ba shi amsa

Aliyuu ya juya ya juyo da matukar mamaki .
"To ai gara mu tafi asubiti, tun kafin lamarin ya yi tsamari ."
Haka suka wu ce suka tafi asubiti, aiko suna isa likitan ido ya zo ya duba Salma.
"Dactor ya ake ciki to ."?
Likitan ya kalli Aliyuu yana ba shi amsa da fad'in. "A'a karka damu ba babbar matsala ba ce ,
muna warware irin wannan da dama , dan haka in sha Allah zata sami lafiya, sai dai akwai
kudade sosai da zaku cire , domin magunguna idan ta kama harda aiki ma ."
Ajiyar zuciya Aliyuu ya yi yana kallon Salma "Tom shi ke nan likita."
"Yaya Aliyuu akwai dubu 30 cikin account dina , sannan a gida ina da laptop, a siyar tare da
wayata ."
Matukar tausayin Salma ne ya sake rufe Aliyuu, sai da wasu hawaye su ga gangaro masa ,
yasa hannu ya share .
"Tabb sannu wai kuka kake yi nan , idan bani da lafiya ko irin wannan baka mini."
Cewar Fatima
Da fuskar tausayi ya kalleta " Haba Fatima ki dubi halin da take ciki ."

Ya koma ya kalli Salma dake cikin damuwa da hawaye ya ce .
"Ki yi hakuri Salma, ni ba mutum ba ne mai kudi, banda haka bazan siyar da laptop da wayarki
ba , sai na siyar na hada da nawa zan samu damar ....."
Bai kai aya ba Salma ta katse shi .
"Na sani , ko baka ce ba , babu yadda zan da wannan kaddarar ."
Ta cigaba da kuka ,da sauri Aliyuu ya fice cikin wani yanayi .

Fatima ce ta zauna wajen Salma har wajen magariba , tunda Aliyuu ya fita bai dawo ba sai a
wannan lokacin
"Wai sai yanzu zaka dawo haba , ka barmu da yunwa babu kudi ."
Abin da Fatima ta fara tarar shi dashi ke nan
Wani bacin rai yaji ya turnike masa zuciya, kawai shiru ya yi , ya kalli Salma da fad'in.
"Ya jikin naki Salma."?
"Da sauki ."

Ta bashi amsa
"Tom kin ga yanzu haka na hado dubu dari biyu Salma, sannan SMS dinki suna kasa ."
"Dan haka bari naje gun likita ."
"Wai dan Allah mene ne na wannan barin jikin, na ce maka yunwa nake ji , ammma sai ta
wannan yarinyar kake yi ."
Yaji wani abu ya tokare masa makogaronsa, ya fita babu cewa komai
"Wallahi bari Baba ta dawo daga katsina ,zaku had'u."
Abin da Fatima ta fad'a ke nan tana kallon Salma da harara


Autar marubuta
07040805269


*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 25&26

Bayan Aliyuu ya kai wannan kudin , likita ya rubuta musu wani magani suka siyo , ya ce a diga
cikin idon nata , haka dai har kwana uku babu wani canji duk da irin magunguna da Salma take
sha , hakan yasa likitan ya musu transfer zuwa babban asubitin da ake duba marasa lafiyar ido

, domin yi wa Salma aiki .

Aliyuu ya matukar rame sosai , ko dan irin abin da matarshi ke yi masa , domin tana tunanin a
karshe tabbas zai ce yana son Salma, har yakai ya aureta, wannan lamarin take gudu yasa take
yin abin da take

Kimanin kwana 3 Aunty Hauwa tana jaraba kiran wayar Salma, amma shiru ,domin ta samu ta
maida komai nata bayan tasai waya a Dubai, Allah yasa komai tana aje shi a email kamar
yadda ta koyawa Salma.
Bayan yayan baban ta ya tabbatar mata hajjiya Aisha ta tashi ta siyar da gida , kana ta kori
Salma kamar yadda Suwaiba take sanar dashi.
Hankalin Aunty Hauwa ya matukar tashi sosai, har shugaban kungiyar Lafazi tai wa magana
amma ya ce shima number Salma bata tafiya, online ma babu labarinta.

Washe gari da safe jigum Aliyuu ya yi , domin an shigar da Salma ana mata aiki yaso ya sanar
da mahaifiyarshi wannan lamarin , sai dai tana cann wani kyauye a katsina nertwork ma babu ,
idan taje ta yi wata biyu ko 4 kafin ta dawo .
Allah dai ya baki lafiya Salma
Yana zaune sai ga Dactor din ya fito, shigarsa da fitowarshi bai ci ace ya yi wannan aiki ba ,
hakan yasa da tsoro Aliyuu ya mike tsaye.
"Dactor meke faruwa."?
"Biyoni office."
Abin da ya ce ke nan, bayan Aliyuu yabi bayanshi suka shiga office suka zauna.
"Likita me yake faruwa dan Allah."?
Kafin ya fara bashi amsa , ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in.
"Ammm Malam Aliyuu, zan maido maka da kudadenka ,saboda wannan yarinyar ciwonta bana
asubiti bane , hakan yasa ban yi mata aiki ba ma."
"Likita kamar ya kuma." Da damuwa Aliyuu ya tambaya
"Eh kamar dai shafar àljanu ne , saboda a halin da ake ciki yanzu, hannayenta duk biyun, sun
tsaya cak , basa aiki ."

"Tom ashawarce a koma gida a yi magani saboda duk asubitin da zaku je , Tom zasu ci kudin
ku ne kawai."

Durkusar da kai Aliyuu ya yi , bayan likitan ya karfafa masa gwiwa ya tashi ya koma wajen
Salma.
Yana shiga tana zaune hawaye sai kwarara suke a idonta , ya dubi hannayenta
Yatsunta duk guda goman wasu sun lankwashe kamar zasu karye, wasu kuma suna tsaye cakk
, baki ya rike sakamakon wani kuka da ya ke ce masa , jin hakan ya tabbatar wa da Salma ya
shigo inda take .
"Allah yana jaraftar bayinsa ta duk inda ya so , ki yi hakuri Salma irin taki kaddarrar ke nan, gida
zamu koma zamu nemi mai magani ."
Cikin kuka kamar mace Aliyuu yake mata wannan maganar

Bayan su karasa gida, Fatima tana zaune ta kara wayarta a kunne tana sauraran wani Littafi
Sallama Aliyuu ya yi , amma bata ko kulasu ba , yarinyar data rako Salma ya nuna mata dakin
Salma ta shige da ita , kana ta fito ta tafi , Aliyuu yana ciro naira 50 yana bata .
"Yanzu rashin mutuncin ki yakai haka Fatima, mu shigo ko kallo bamu isheki ba."
Duk da ya yi wannan maganar ko a jikinta, volume din Littafin ta karo .
"Fatima da zarah kashi na 57 , mai sauraro mun tsaya daidai gunn." Hannu yasa ya zaro wayar
ya wurgar da ita saida ta rabe gida biyu .
Wani gigitaccen kuka Salma ta fashe dashi sakamakon yadda taji Fatima tana sauraran Littafin
ta , amma gata cikin gidanta ba tare da tasan ita ba ce .

Irin rayuwar da Salma suka ringa yi ke nan cikin wannna gidan har kimanin wata biyu, sai
Fatima ta gadama zata taimaka wa Salma da wulakanci, Aliyuu yasha danko mata masu aiki
domin su kula da Salma, amma basa zama , saboda Aliyuu ba ya iya biyansu

Karfe 11 na dare Aliyuu ya rufe shago ya dawo, bayan ya yi wanka ta kawo masa abinci.
Ba tare da ya bude abincin ba ya kalli Fatima da cewa.
"Ina kika je dazu , na aike ki gidan Baba ne."
Ajiyar zuciya tai kana ta ce .
"Tom naga dai Baba ta dawo jiya,lefi ne dan naje ña gashsheta , ta ce kuma karka fita koina ka
jirata da safe tana zuwa."

Ya mike ya shige daki yana cewa."Dauke abincin ki."
Gombe state Akko local government
Yayan baban Aunty Hauwa ne shida matarshi har wajen 11:29 sai hira suke matar tashi ce take
cewa.
"Tom ni ai ban yi mamaki ba , dan hajjiya Aisha ta yi haka ."
Mijin na ta ya ce
"Hmm tom ai ke abin da baki sani ba ,duk wannan baya damun Hauwa'u, wannan yarinyar
Salma da ba a san ina take ba , shi ne babban tashin hankalin Hauwa'u, ta ce mini kullum saita
kira number ta ko Allah zaisa a samu , wani karin abin ma ta ce ba yanzu zata dawo ba , sai
nan da wata 4, wani aikin ya kuma bullo musu ."
Matar tashi ta ce
"Allah sarki Hauwa, Allah dai ya bayyana yarinyar ko hankalinta ya kwanta."
Ya ce .
"Amin ."
Washe gari da safe misalin karfe 8, bayan Aliyuu ya yi wanka ya tsaya jiran mahaifiyarshi.
Ba zato yaji sallamar ta a kunnuwansa , da firgice ya mike ya fice yana amsa sallamar yana
cewa.
"Sannu da zuwa Baba."
Baba da idanunta taji kwalli , irin mutanen nan ne da suka ga yau suka ga jiya , idanunta a bude
.

"Ki shigo ciki baba.".
Aliyuu ya fad'a yayin da Fatima ke fitowa
"Ba zama nazo ba Aliyuu, ina son yanzu ka kori yarinyar daka kawo gidanka take tsiyata ka ,
kake ramewa , dube ka ."
Ta nunashi da hannunta jajir yasha kunshin tsofaffi
Dogon numfashi Aliyuu yaja yana cewa.
"Baba ki yi hakuri mana , wallahi duk abin da Fatima ta zo ta fad'a miki ba gaskiya bane ."
"To mene ne gaskiya, me yasa kai baka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login