Showing 21001 words to 24000 words out of 30722 words

Chapter 8 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

saka layukanta ciki

Cikin yanayin fusata Fatima ta shiga kichin ta dauko wuka , kai tsaye ta fad'a dakin Salma.


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 31&32

Salma tana d'ago kai ta ganta , da sauri ta mike tsaye tana jaa da baya .
Idanun Fatima jajir tamkar wacce ta fita a hayyacinta .
"Wato kin zo gidana , ki hanani farin ciki, kin yi cuta an miki magana, an sa miki jinin mijina,
mahaifiyarshi tana yabonki a gabana, ya sai miki waya , abin da ya rage ki aure shi kooh."
Salma da matukar tashin hankali take ja da baya tana cewa.
"Wallahi Aunty Fatima ba haka bane , babu komai tsakaninmu saii.."
Dakatar da ita tai tana d'aga wukar kamar zata caka mata
"Kafin na yarga biyar , ki kwashe kayanki ki bar wannan gidan , idan baki fita ba wallahi saina
kasheki Salma." Jikin Salma na rawa tai sauri ta zura hijabi, kawai tai waje babu ko takalmi sai
wannan wayar a hannunta.
Tana nishi da ajiyar zuciya ta fito ta tsaya "innalillahi wa innailaihir rajiun. Wannan matar kodai
tana da àljanu, ko takalmi bata bari nasa ba ."
Salma tai maganar tana haki, bakin titi ta nufa , duk ta rame tayi wani irin tsayi, tunanin ta kawai
yanzu ta je ta hau motar Kano
Ringin din waya take ta ji tare da ita , amma ta kasa sanin daga ina ne , sai daga baya ta lura

ashe akwai waya a hannunta, ta dubi fuskar wayar yayin da akai kira biyu babu amsa .
Kafin ta cire fuskar ta kan wayar sai ga wani kiran yana shigowa
Kara wayar tai a kunne kamar mai jin tsoro
"Hello."
Muryar mace taji tana cewa.
"Salma Salma."
Salma ta ce ."Eh ni ce waye."
Babu zato ba tsammani ta ji an ce ."Aunty Hauwa ce Salma kina ina ne ."?
Wani rasss taji a ranta da faduwar gaba "Aunty Hauwa ke ce ."
Kawai ta fashe da kuka
Wani farin ciki Aunty Hauwa taji ya rufeta, ko tsayawa rarrasheta batai ba ta cigaba da cewa.
"Kina ina duk inda kike ki taho Salma na , na dawo ."

Cikin kuka da matukar shauki Salma ta fara mata magana."Ina Bauchi Aunty amma gani nan
yanzu zan taho , sai dai hajjiya Aisha ta siyar da gidan."

Murmushin farin ciki Aunty Hauwa ta sake yi tana cewa.
"Na sani Salma ki hawo mota ki taho idan kin zo zan miki kwatancen sabon gidanmu."

Salma ta share hawaye tana cewa" To Aunty amma babu komai a gurina babu kudi wallahi
yanzu ma daga wani gida aka koroni bani da lafiya."
Ajiyar zuciya Aunty Hauwa tai kana ta ce .
"Tom ki samu wani ya kawoki idan kun zo sai na bashi kudin, idan bai yarda ba kice za a ninka
masa ."

Da sauri Salma ta nufi tasha kamar zata fad'i, sam ta mance ma babu takalmi a kafarta, mutane
kuwa sai kallonta suke , daga taje gurin wannan mai motar sai taje gun wannan, haka ta samu
wani ta ce Gombe zai kaita ita kadai , da kyar ya yadda sai da ta hadashi da Allah da annabi
sannan ya ce ta hau , suka tafi. Matukar shauki da farin ciki take ji kamar tai fiffike ta sauka a Gombe, sam ta mance ma bata da
lafiya, haka suka ringa tafiya har suka fara shiga birnin Gombe


Wajen karfe biyu Aliyuu ya shigo gida , ganin takalmin Salma zube a kofar dakinta, yasa shi
mamakin me yasa bata fito ta ce masa sannu da zuwa ba kamar yadda ta saba
"To ko dai jikin ne."?
Ya tambayi kanshi
"Salma."
Yaji shiru
"Salma."
Fatima ta fito a daki fuskaantar babu annuri
"Na koreta ta tafi inda ta baro, tunda nan dai ba gidan ubanta bane ."
Wani yammm Aliyuu yaji maganar kamar da wasa, ya leka takin nata .

Sai dai ga komai nata nan , hakan yasa bai yarda ba
Ganin bai yarda ba ya sake fusata Fatima tana cewa.
"To wallahi na koreta babu ko takalmi, shegiya matsiyaciya , harda wani sai mata waya , daga
nan kuma ka ce zaka aureta ko."

Da sauri Aliyuu ya juyo tare da mamaki sosai. "Wai dan Allah da gaske kin koreta, baki da
hankali ne Fatima, mene ta tsare miki."
Yayo kanta da jajayen idanu kamar zai daketa

"Saboda ba gidan ubanta bane, ba kuma na mijinta ba ."

Jin zancen shirmen dake fitowa daga bakin Fatima ya sake bakanta masa rai .
Ganin karya 'bata lokaci yasa ya fice da gudu, neman Salma ya shiga yi lungu da sako ko Allah
zaisa ya ganta , haka har yaje tasha yana ta tambaya, nan ya samu wasu suke tabbatar masa
ta hau mota zuwa Gombe kuma tun dazu ne, yanzu baza ta gaza zuwa ba .
Bakin ciki da takaici ne ya turnike masa zuciya, cikin kasala ya nufi gidan mahaifiyarshi
Baba Laure tana zaune gama cin abincinta ke nan ya samu guri ya zauna bayan sun gaisa . "To
ko jikin Salman ne , mene yake faruwa."?
Ta tambaya domin ta ganshi a wannan yanayi.
Sai da ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya fara cewa. "Wallahi Baba shigata gida ke nan yanzu,
wai Fatima ta kori Salma tsabar rashin mutunci."

"Aliyuu ban gane me kake magana ba , dazu fa na baro gidan , kamar ya ta koreta me tai mata
."?
Cewar Baba Laure da ita ma labarin bai mata dadin ji ba

Aliyuu cikin yanayin rashin walwala ya ce ."Baba gaske nake miki, yanzu ma daga Tasha nake ,
an ce mini ta hau motar Gombe, yanzu ma taje."

Baba ta rike haba tana cewa."Innalillahi wa innailaihir rajiun meke damun Fatima, wannan
wanne irin rashin hankali ne , yanzu ya za ai."?
Aliyuu ya maida mata da cewa.
"Babu yadda za ai kuwa Baba , domin ni ko number Salma bani dashi ."

Baba ta girgiza kai.
"Wannan matar taka ko 'yar banza wallahi, an yi shasha sha."
Aliyuu ya zame ya kwanta bisa wannan tabarma



Anan kuwa Salma da driver suna tsaye suna jiran ganin ta inda Aunty Hauwa zata bullo
Wata mota Salma ta ga ta nufosu blue mai bakaken murfi .
"Motar Aunty Hauwa ba blue ba ce ."

Cewar Salma tana sake hangawa

Bayan motar ta tsaya ko gilashi ba a bude ba , kawai aka bude kofar motar .
Da gudu Salma ta nufi Aunty Hauwa ta rumgumeta da matukar kewa da farin cikin yadda ta
ganta , amma tun da farin Aunty Hauwa abin data fara lura dashi Salma ta rame sosai babu ko
takalmi kuma a kafarta.
Driver da ya kawo Salma ya yi murmushi yana cewa. "Kai ai dah raina wannan yarinyar nake ,
ashe yar masu kudi ce . Bari naje a sallame ni ."

Ya matsa kusa yana wata far'a
Hawaye har sun kawowa Salma, ta kalli wannan driver tana cewa."Aunty ga wanda ya kawoni ,
duk cewa suke baza su zo wata Gombe ba , shi ne ya taimaka mini . "

Jin haka yasa ya yake hakora
"Allah sarki, mun gode bawan Allah."
Cewar Aunty Hauwa tana zura kai a mota , kudi ta ciro kimanin dubu 30 ta mika masa, cikin
murna yasa hannu ya karba ya gamsu shimm ya yi godiya.

Hakan yasa Salma suka shige mota suka fara tafiya.
Rufe idanu tai tana wata nannauyar ajiyar zuciya, yadda tai kewar sanyin motar Aunty Hauwa
yasa ta tuna farkon haduwarsu, har lumshe ido take tana jin cewa tabbas duk kan wahalar ta ta
kare .
Aunty Hauwa kamar tasan tunanin da take , ta kalleta tana murmushi kafin ta ce ..
"Salma wayata aka sace mini sam ban kula ba , har saida muka je Dubai , ki gafarta mini."

Jin hakan yasa Salma ta bude idanunta.
"Aunty na sani , domin kuwa Anas shi ne wanda ya sace miki waya bayan ya rakoki, har gida ya
zo da ita , sannan suka koreni suka siyar da gidan ."

Aunty Hauwa ta sha kwana , sannan ta kalli Salma tare da maida hankali zuwa tukinta tana
cewa. "Daman Anas ne ya sace mini waya , lallai yaron nan , ai yanzu zancen da nake miki
hajjiya Aisha tana cann an kulleta, domin tunda na dawo na shigar da ita kara, dukkan duniyar
mahaifina ta dawo gurina ."
Jin hakan ya sa ran Salma sanyi , ta sake furzar da iska
Wani gida Aunty Hauwa tai parking motarta bai kai wancen girma ba , amma yafi wancen kyau
sosai da kayan more rayuwa, gidan a bude yake suka sa kafa suka shiga .



MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta

________________________________________
Page 33&34

Suna shiga ciki , sabuwar yar aikin Aunty Hauwa dake zaune falo tana kallo, ta sake rissinawa
tana cewa. "Sannu da zuwa Aunty."
Aunty Hauwa ta kalleta tare da zama a kujera tana cewa."yawwa sannu Farida, fatan kin
dorawa Salma ruwan wankan da nace ."
Cikin girmamawa Faridan ta ce ."Na dora Aunty, har abinci ma an gama ."

Ta ce "yawwa."
Salma tai murmushi sannan ta nemi guri ta zauna , yayin da Farida take shigewa ciki . Ajiyar
zuciya mai zafi Salma ta sauke ."Aunty wannan gidan ya yi kyau sosai." Ta fad'a tana duban
koina
Aunty Hauwa ita ma ta murmusa tare da fad'in."Tom Salma kije ki fara wanka , ki ci abinci sai
kiyi sallah."

"Tom Aunty."
Salma ta fad'a tana bin hanyar da Farida tabi , ba tare da tasan ina ne a cikin gidan ba , bayan
Salma tai wanka , ta saka wata atamfar Aunty Hauwa, sannan ta fito falo ta saka sallaya ta fara
sallah, daidai lokacin data idar da wannan sallar, ita kuma Aunty ta gama cin abinci

Shiru Salma tai tayi zuruu , hakan yasa Aunty cewa. "Salma ga abinci nan." Ta nuna mata kular
dake gefe tare da ruwa da lemo
"Gaskiya kin rame sosai Salma." Saida Salma tai murmushi ta ce . "Ai Aunty nayi kiba ma ,
nasan yanzu Yaya Aliyuu hankalinshi yana tashe shi da Baba Laure."

"Su waye su , baki fad'a musu zaki dawo bane , sannan ina babbar wayarki , kullum ina kiranki
Salma, ammma shiru , kuma ke baki neme ni ba ."
Aunty Hauwa tai magana cikin damuwa, zama Salma ta gyara kana ta ce ."Hmmm Aunty ke
nan, na yi zatan mutuwa zan wallahi, ashe zamu sake haduwa."

Aunty Hauwa tai dariya tana cewa. "Salma wai mene ya kai ki Bauchi to."?


Jin wannan tambayar yasa Salma ta fara bata labari , tun daga ranar data sa kafa ta tafi Dubai,
har zuwa wannan ranar
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, Salma makancewa fa kika ce." Aunty Hauwa bayan ta saurari
duk labarin abin da ta ce ke nan.

"Hmmm Aunty ke nan, harda kuturta ma kuwa."

Girgiza kai Aunty tai kafin ta ce .
"Abin mamaki tom wane ne zai miki sihiri Salma, gaskiya su Baba Laure sun yi kokari, in sha

Allah zamu kai musu ziyara da zarar aiki ya ragarmin."
Ta sake muskutawa tana cewa. "Ikon Allah Salma, gaskiya kina shan wahalar rayuwa, amma in
sha Allah yanzu ta kare , ko yaushe na kira wayarki a kashe , Allah sarki."

Salma ta sunkuyar da kai kasa tana murmushi
"Tom ki ci abinci Salma ni yanzu zan fita wani aiki, duk abin da kike bukata ki yi wa Farida
magana." Ta karasa maganar tana mikewa tsaye
Salma ta ce .
"To Aunty a dawo lafiya."
Har ta kai kofar falon sai ta juyo tana cewa.
"Idan na dawo kuma da dare ,zamu je shopping daga nan sai ki siyo waya da laptop din ki ."
Jin dadin hakan yasa Salma ta washe baki tana cewa.
"Na gode Aunty a dawo lafiya."
Sannan ta fice ta tafi

Ajiyar zuciya Salma tai mai matukar girma, sannan ta jawo wannan abincin ta fara ci .

Bayan kwana biyu
Alhamdulillah Salma dai sai farin ciki, a halin yanzu tana zaune dakinta tana danna laptop, har
an yi kiba an yi kyau .

Aunty Hauwa ce ta shigo ta zauna, hakan yasa ta aje duk abin da take yi tana fuskantar Aunty
da cewa.
"Aunty lafiya. Naga jikin ki duk a mace ."
Aunty Hauwa tai murmushi tana fad'in. "Kai Salma baki ga daidai ba , daman ina so na sanar
dake akwai wani babban shago dana siya, tom akwai abaya a ciki , atamfofi da sauran duk
kayan mata , to Salma babban shago ne , akwai ma'aikata , ina so gobe ki shirya muje , domin
zan mallaka miki shi ."

"Me kika ce Aunty."?
Cewar Salma
Aunty Hauwa tai murmushi tare da mikewa tsaye tana cewa. "Ai kinji duk me na fad'a, kuma
bana son godiya." Tana gama maganar ta fi ce

Ai Salma ji take kamar ba ita ba ce , irin wannan babban magana, tom sai dai mu ce Allah ya
tabbatar da alheri, aiko washe gari da safe , suka shirya suka tafi wannan babban shago , aka
nunawa Salma komai , sannan Aunty ta wuce office



Anan kuwa Hadiza ce a online.
Bude datarta ke nan ta ga sabon update na cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta

Yadda ta ga ana posting dinshi a koina take mamakin yadda wannan abin ya faru .
Kai tsaye ta nufi Facebook shafin Autar marubuta
"Alhamdulillah masoyana na dawo , cikin ikon ubangiji bayan doguwar jinya , na yi kewar ku
sosai."
Abin da ta gani ke nan, kwana daya da rubutawa
Hankalin ta ne ya tashi ganin wannan lamarin, like dubu biyar akai wa wannan Post na Salma,
banda comments marasa adadi , zazzafar ajiyar zuciya tai , tana cewa."Kutumar u..."
Cikin mamaki take sanar da mahaifiyarta, yayin da Umma take tambayar ya za ai , Hadiza ta ce
abar mata komai a hannunta

Karima kuwa kullum tana sauraran Littafin Fatima da zarah da ake yi a gidan redio, Littafi ne
mai yawan gaske , domin kuwa har yau ba a kammala ba , wayarta ta lalace hakan yasa
Karima bata WhatsApp, sai idan an karbo daga wajen gyara
Sunan Autar marubuta ya yi shura sosai, hatta a masana'antar kannywood saboda irin fina finai
da take rubutawa, sai dai ana kawo mata gayyata sosai daga gidajen television domin hira da
ita , sai dai Salma bata amsar wannan bukata, ta ce akwai lokaci
Sir Sadiq Abubakar yana matukar farin cikin yadda Salma take tare dasu har yanzu, ita ma
Aunty Hauwa ba karamin alfahari take da Salma ba, sai dai duk yadda zatai alfahari da ita, to
Salma tana ninka wannan adadin tana alfahari da Aunty Hauwa

Tana cikin falonta, gefe aje da shayi, tana rubuta wani fim , Aunty Hauwa ce ta kwala mata kira
tana daga falo , hakan yasa Salma tashi ta nufi falon, zama ta yi tana cewa.
"Aunty meke faruwa."

Aunty Hauwa ta ce .
"Gaskiya Salma na yi mamaki sosai, ki dubi adadin ribar da kika samu 2 millionaire Salma, cikin
kankanin lokaci, Allah yayi wa rayuwar ki albarka, sai dai daga yau duk abin da aka samu kar
naji labarin, domin sirrin ki ne ."

Dariya Salma tai tana cewa. "Kai Aunty."
Ita ma dariya ta yi tana cewa.
"Sannan kuma an kirani daga gidan redion Kano Salma, akwai abokin aikina a can , ya ce kuma
sun nemi hira dake , amma baki amince ba , tom dan Allah Salma ki amince ."

Saida tai ajiyar zuciya mai zafi, sannan ta ce .
"To Aunty, ai duk abin da kika ce mini wajibi na aikata, kinfi karfin wannan, su ne mutanen farko
dazan fara hira dasu ."

Aunty Hauwa ta ce .
"Yawwa kanwata , Allah ya kara Basira da lafiya da nisan kwana, sannan kuma tare zamu je
kanon , daga nan zamu biya gidan yayan baban nan naki ."
"Saboda nima zan yi kwana uku bana aiki a lokacin."

"Tom Aunty."
"Amma Aunty ina so daga nan zamu je Bauchi, domin ganin su Inna, ina so na saiwa Yaya
Aliyuu mota."

Murmushi Aunty Hauwa tai tana cewa.
"To Salma rigima, banda abinki ai ni Baba Laure ya kama ki yiwa wani abin. Ammma tunda
haka ne , akwai tsohuwar motata, sai a bashi , ita kuwa Baba Laure zuwa hajjin bana ki shirya
zuwa da ita ." Ta karasa maganar tana dariya
Ita ma dariya sosai Salma tai , kafin ta ce ."Tom shi ke nan Auntyna. Allah ya saka da alheri na
gode ."
Aunty Hauwa ta ce ."Babu komai ai Salma, mahaifina yabar mini dukiya mai yawa, zan yi
amfani da ita domin gina lahirarsu da tawa. Sannan kuma yau zan bada akai motar Kano, idan
munje sai a dauka danke baki iya mota ba ."

Tai dariya tana cewa."Aunty banda gori ."
bayan Salma ta koma daki , ta tsaya ta yi jimmm
Cikin zuciyarta take cewa.
"Tabbas lokaci ya yi dazan fadawa Aunty Hauwa gaskiya koni wace ce, domin na gaji da
yaudarar ta, Allah yasa ta fahimce ni ."
Taji wasu hawaye

Karima da Adam ne suke karyawa, farin ciki ya ishi Karima, domin kuwa jiya da dare bayan ya
dawo ya taho mata da wayarta, sannan yake tabbatar mata yanzu idan ya fita zai sa a sako
mata data

"Wai kuwa kin karbo dinkin ki Karima, bukin nan fa sauran kwana biyu."
Cikin shagwababbabbiyar murya Karima ta ce da mijin nata "Ni ban karbo ba , kai ne zaka anso
mini."

Ya kalleta da cewa.
"Ni kuma , ina ni ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login