Showing 3001 words to 6000 words out of 30722 words

Chapter 2 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

jigatar da tai da irin abin da take ji yasa bata iya magana sai
kokarin magana da hannu tana nuna tabar ta a gurin ta tafi.
"Salma bazan barki anan gurin ba , ki karfafa gwiwarki Allah zai taimaka mana."
Tai maganar tare da kokarin cicci'bata a bayanta .
"Timm."
Salma taji ta fado kasa , da sauri ta juyo ta durkusa gabanta

Tana juyota ta ga ko motsi bata yi
"Salmaaa."
Ta fada cikin murya mai kara da kuka
"Salma."
"Haba dan Allah, innalillahi wa innailaihir rajiun."
Salma ta fad'a tana jijjigata


Kuka ta kifa tana yi sosai ita ma kamar ranta zai fita a wannan lokacin
Ba karamin tashin hankali Salma ta shiga ba ganinta a wannan yanayi , haka rana ta fara
fitowa mai zafi ta fara dukanta .

Yadda taji matukar yunwa da kasala yasa ta mike tsaye domin tafiya gaba ko Allah zai had'a ta
da wata halittar
Ta juyo ta kalli Salma dake kwance matsayin gawa ta rushe da kuka tana cewa.
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, ki yafe mini Salma, wallahi kafafuna basa daukata nima , da
saina dauke gawarki a wannan wajen."

"Ki yafe mini , ki yi hakuri."

Ta juya cikin tashin hankali na kuka tana d'ingishi ta fara tafiya tana juyowa tana kallon gawarta
.

Autar marubuta
07040805269
WhatsApp only

*MARUBUCIYA* ✍️

Na
Autar marubuta


____________________________________________


Page 5&6

Haka Salma ta cigaba da tafiya cikin matukar wahala da tsoron wannan dajin , tana tafiya tana
duban hanya tana juyo bayanta, har tai nisa sosai ta dena ganin gawar Salma, lokacin da taji
matukar yunwa ne yasa ta sake fad'a wa cikin wani dajin, sai dai babu wata itaciya da ta gani
wacce ake ci , sai wata bishiyar goruba , d'anya shakaf , ganin ta yi mata tsayi yasa ta zauna
kasan bishiyar tana tunanin daga nan ina zata je , babu zato taji abu yana bin bayanta, da sauri

tasa hannu ta kamoshi cikin tsoro tana yar'bar dashi .
A million ta mike tasa gudu ganin koren mucijin data kamo da hannunta, ta sake danna kanta
cikin dajin .


Anan kuwa tunda garin Allah ya waye Umman Salma bata fito ba , sakamakon yadda kanta
yake mata ciwo tun daren jiya.
Sai dai har yanzu bata ji motsin Salma ba, saboda Salma ta saba kullum tana fitowa tayi shara,
koda kuwa zata koma bacci. Wannan tunanin yasa Umman nata dauriya tana fitowa waje , ta
tura dakin Salma yana budewa ta ga babu alamun motsinta , ban daki ta leka nan ma babu
labarinta. "To ina Salma ta shiga ne ."? Take tambayar kanta
A lokacin Umma taji gabanta ya fadi tare da tunanin tabbas sam bata ji motsin Salma ba ,
hakan yasa ta nufi dakin malam Aminu, karo taci da Umar
Ya durkusa har kasa yana gashsheta. "Ko ka aiki Salma ne ."
Jin Umma ta ce dashi haka ya sa shi fad'in.
"A'a yanzu ma na bude gidan , don yau da asuba duk bamu je masallaci ba." Ya karasa
maganar yana nuna mata mukullin da kwad'o
Ajiyar zuciya tai tana cewa."To ina ta shiga haka ."
Jin wannan kananun maganganu ne ya sa Malam Aminu fitowa,
"Wai me ake yi ne ? Me ke faruwa."?
Umma ta maida masa da cewa. "Salma ce ba a gani bafa Malam."
"Kamar ya ba a ga Salma ba , ku sake dubawa dai ."
Ya fad'a cikin mamaki
Umma ta sake sauke ajiyar zuciya tana cewa."To babu dai inda ban duba ba ."
Malam Aminu yasa kai cikin gidan ya nufi dakin Salma, suma suka bi bayanshi .
Ido suka tsurawa dakin kamar suna duban wani abu
Wani akwati dake kasa malam yasa hannu yana bude cikinsa, ganin hijabai a ninke guda uku
yasa shi cewa.
"Ina sauran kayan nata ? Ko daman su ke nan."?
Umma da Umar suka leko suna duban kayan .
"Haba dai kayan Salma ai duk basa nan." Cewar Umma
Malam Aminu ya ce .
"To tabbas kuwa Salma ba a gida ta kwana ba ."
"Kira babanka muji ko taje can ."
Umar dajin haka ya zaro wayar a aljihunansa yana danna kira ga Alaji Yusuf, kira guda ya yi,
mamansu Karima ta miko masa wayar .
"Salamu alaikum Umar." Bayan Alaji ya d'aga wayar
"Baba ina kwana, an tashi lafiya."?
Alaji ya ce ."Lafiya alhamdulillah har kun taho ne ."?
Jin wannan maganar yasa Umar ya fara yin jimm kafin ya ce .
"Baba bata zo bane ."?
Alaji ya ce ."kamar ya ta taho ne ."

Umar ya mikawa malam Aminu wayar yana cewa."Baba kai masa bayani."
"Wanne irin bayani mene ke faruwa ne." Alaji Yusuf ya fad'a yayin da baban Salma ya kara
wayar a kunne .
"Dama Salma ce ba a gani ba , kuma ga dukkan alamu bama ta kwana a gida ba ." Ya fad'a
masa haka kai tsaye
"Wannan wacce irin magana ce, to ina taje ku sake dubawa dai." Alaji yana gama magana ya
kashe wayar
"Alaji meke faruwa kuma." Cewar matarshi
"Wai Salma ce , ba a gani ba tun jiya." Ya karasa maganar yana mikewa tsaye
Cikin mamaki mamansu Karima ta ce ."Innalillahi garin ya kuma."
Alaji ya ce .
"Ai yanzu zanje taraunin wannan wanne irin magana ne."
Jingum-jingum su Umma sukai, domin duk inda suke tunanin samun Salma babu labari.
Lokacin da dabara ta zo wa Umar ya kira number zainab
A spiker yasa wayar tana ta shiga amma ba a dauka ba , tana katsewa ya sake kira .
A bacci Zainab kiran ya tasheta , ta jawo wayar tana dauka .
"Su Salma an sami wayar Yaya Umar ke nan."
Jin haka yasa Umar murmushi yana kallon su Baba.
"A'a Zainab ni ne ba Salma ba ce ."
"Ahu Yaya Ina kwana." Ya amsa da fad'in."lafiya lau Zainab ko Salma tazo nan ."
Taji gabanta ya ce rasss
Sai da tai shiru kana ta ce ."Salma kuma bata zo ba , lafiya kuwa."?
Umar ya ce ."Lafiya lau, dama tun jiya ne ba a ganta ba ."
Cikin tashin hankali Zainab ta ce ."Innalillahi amma jiya da dare ta zo gidanmu ta kawon Littafin
Hadisina , harda jaka a hannunta na ce ina zata ta ce gidan Aunty Murja."
Malam Aminu da Umma suka kalli juna.
Sannan Umar ya ce .
"Tom shi ke nan bari na kira Aunty Murjan." Ya gintse wayar .
Duk Zainab taji ta nemi wannan baccin ta rasa , cikin matukar mamaki ta mike ta zauna, kallon
Littafin da Salma ta kawo mata a daren jiya tai, cikin mamaki tasa hannu tana dauko Littafin

Sun sake shiga matukar tashin hankali sosai yayin da suka kira Aunty Murjan wato kanwar
umman Salma, domin ta tabbatar musu rabonta da Salma za ai wata biyu zuwa uku, hankalin
su ya sake matukar tashi tsaye a wannan yanayi


Da sauri Husna ta shigo daki tana tashin Karima "Aunty Karima ki tashi , ga baba can ya fita ,
Salma ce ta bata tun jiya ."
Zumbur Karima ta mike tana cewa."Mee wacce Salma."
Husna ta ce ."Nima yanzu mommy take sanar mini." Sukai jugum- jugum.

Sokkoto birnin shehu �

Su Hadiza sun sauka lafiya lau, yanzu da Adam ya shirya fita aiki yake cewa."Mama yaushe
zaku tafi ne , kinsan an kusa kawo kaya, ya kamata ace kuna Kano."
Umman Hadiza ta kalli dan nata tana fad'in."Adam ka jini da kunnen Basira, baka ganin mun
debo duk kayanmu ne , tom mun dawo nan , mun dawo nan , idan kuma baza ka iya rike mu
bane sai naji ."
Adam ya ce ."A'a Umma shi ke nan, ni zan tafi wajen aiki." Ya musu sallama ya tafi ransa babu
dadi .

Haka Umman Hadiza ta samu daki ta zuba kayanta, sakamakon gidan 'dan ta ne Adam da suke
zaune da mahaifiyar baban Adam, lokacin da Allah yayiwa baban Adam rasuwa ta koma Kano
tai aure, bayan mahaifin Hadiza shima ya rasu shi ne ta dawo sokkoto, ta ce bazata kuma aure
ba , tunda dai duk wanda ta aura sai Allah yayi masa rasuwa.


Salma kuwa anan ba a cewa komai, domin ta matukar jigata da gajiya da tafiya saidai har
yanzu bata iya hangen komai a inda take . Komai nata ta zubar kafafunta kuwa sun kunbura
tsabar gudu da irin abubuwan da take takawa a hanya
Wani rami ta hango cike da ruwa, sai dai gurin ya cika da ciyayi da kananun ramuka da kayoyi,
yadda taji tana bukatar amfanuwa da wannan ruwan yasa ta fara takawa a hankali tana shiga
cikin ramin .
Kafin ta karasa ciki, ta fara jin wani kuka mai karfi yana ziyara a kumnenta , amma ta duba
koina da ina babu abin data iya gani , dawo da kanta da zatai zuwa cikin wannna ramin ta ga
wani bakin abu a cikin ruwan idanu jajaye yana dilalo yawu yana kallon ta .
Firgita tai da ganin wannan halitta da bata ta'ba gani ba , hakan yasa ta fito da gudu tana canza
hanya , shima binta yayi a guje yana kuka tana neman cizanta .
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, la ila ha illallahu , innalillahi, Allah ya Allah." Abin da Salma ke
nan ta ringa fad'a tana gudu kamar zata fadi
Tsalle ya yi. Ya kamo mata riga , ta fincike ta sake sa giya tana ihu .
Ya dade yana binta suna cin wannan uban gudun , duk abin ya yazo bakinta fada take tana
addu'a,
Kamar irin yadda mutum yake yin gudu yana duban bayanshi haka Salma take, sai wannan
halittaar ganinta yake kara bata tsoro.
Shiru Salma taji babu kukun wannan dabba , tana juyawa kuwa babu ita babu alamun ta, nan
take jikinta ya fara rawa yana 'bari , domin tabbas a tunanin ta wannan ba komai bane bace
àljani koda kuwa wacce irin dabba ce , cikin wannna yanayi ta cigaba da tafiya, tafiyar na harde
mata kamar zata fadi, tari ne ya biyota tana kokarin amai , ta kai kasa tana zubar da wani irin
koren ruwa daga bakinta , lokaci guda kuma tsoron wannan abin yana ranta , ta mike tana
d'ingishi domin barin gurin kafin wannan abin ya dawo .

Sai da ta jigata sosai ba kadan ba, ta fara tafiya tana jan kafa .

Autar marubuta

*MARUBUCIYA* ✍️

Na
Autar marubuta
____________________________________________
Page 7&8



Lokacin da Alaji Yusuf ya karaso, babu wani labari dai na Salma, nan suka zauna suna tunanin
mafita da yadda za a bullowa lamarin.
"Da dai an sanar da 'yan sanda ko."? Inji Umma
Alaji Yusuf ya ce ."Yanzu yarinyar nan bana tunanin 'bata tayi ko sace ta akai , to mu sanar da
yan sanda mu ce musu me ."
Malam Aminu ya ce ."Haka ne ."
Umma ta sake fad'in."Sanin gaibu ai sai Allah duk bamu da tabbacin meke faruwa da Salma ko
."
A lokacin Zainab ta rado sallama tana turo kai , ganinsu jigum wasu a tsaye yasa taji duk ta
sake shiga yanayi, haka ta gashshesu, suka amsa

Sannan Zainab ta kalli Umar tana miki masa wannan Littafi na hadisi tana cewa.
"Yaya Umar naga wani rubutu a ciki Salma ce tayi ."
Jin haka yasa duk suka 'kagu dajin abin dake faruwa
"Mene a ciki karanto shi." Inji Alaji Yusuf
Yayin da Umar ke kokarin budewa , page din karshe da yake da rarar gun rubutu ya nufa kamar
yadda Zainab tai masa nuni.
Yana bude gurin ya kallesu sannan ya fara karanta rubutun a zuciyarshi
Alaji Yusuf ne ya sake fad'in."Karanto mana Umar."
Umar cikin rashin jin dadi ya sake sa ido kan rubutun da akai da pencil.
"Zainab idan kin ga wannan rubutun ki kaiwa Yaya Umar, domin ni daga nan bansan inda zan
nufa ba , saboda babansu Karima zai mai dani gidanshi, saboda baya so na cigaba da rubutu."
"Ina mai basu hakuri, na yanke wannan hukuncin ne domin cikar burina na zama marubuciya,
Ina son rubutu kamar raina, kuma Ina San iyayena fiye da komai, amma zama gidansu Karima
zai zama tarnaki ga burina, a yi hakuri a yafeni, kar kuma a neme ni domin nayi nisa daku ."
Daga karshe aka zana wata fuska tana kuka
Umar ya d'ago yana kallonsu
"Habawa habaawa, wannan shi ne abin da Salma zatai mana, mene ne mutane zasu ce
innalillahi wa innailaihir rajiun." Inji Alaji Yusuf cikin matukar mamaki
Umma kawai kai ta durkusar ta fara kuka

Malam Aminu Kam yayi shiru yana mamakin ikon Allah.

Alaji Yusuf ne ya kuma fad'in."Wannan yarinyar ta lalata tarihin gidanmu , yanzu dai ta rantse
sai ta yi wannan rubutun."

Malam Aminu ya ce .
"Tom yanzu me ne abin yi ."?
Umar ya yi shiru yana sake kallon wannan rubutun.
Cikin kuka Umma ta ce ."Ga shi nan yanzu Salma tabar gida mene aibun abin da take yi , Allah
ne yasan sanda zanga Salma."
"Allah ya bayyana ki Salma, Allah ya kareki a duk inda kike." Ta sake fashewa da kuka
Alaji Yusuf ya ce ."Allah ya kyauta amma wannan yarinyar tayi rashin hankali ke taya kika samu
wannan rubutun nata ." Ya nuna Zainab
Zainab ta ce .
"Jiya da muka taso daga islamiyya na bata, saboda zatai Assignment, kuma a jiyan ta dawon
dashi, saida Yaya Umar ya kirani dana duba na gani ."

Alaji ya girgiza kai , haka duk jikinsu yayi sanyi babu wanda yaji dadin wannan abin, Alaji Yusuf
ya koma gida.
Aiko yana isa gida duk suna zaune a falo suna jiranshi domin ya dawo suji inda aka kwana.

Jiki a sanyaye Alaji ya shiga gidan, domin yana tunanin silarsa ne Salma tai wannan aika aika .
"Alaji an ganta kuwa."?
Tambayar da mamansu Karima ta fara masa ke nan, zama yayi kan kujera yana cewa."Allah ya
kyauta."
"Ta ya za a ganta ta gudu harda wasika ta ajiye."
Husna da Karima suka kalli juna

"Wai Alaji meke faruwa, sai kace za ai mata auren dole." Cewar ummansu Karima

Alaji Yusuf ya jingina jikin kujera yana cewa."Saboda mun hanata rubutu, mun hanata rubutun
banza dana wofi shi yasa."
Sannan Alaji ya kalli Karima yana cewa.
"Ke Karima karki kuskure wannan zancen ya fita dangin mijin da zaki aura . Saboda Salma ta
gama zubar mana da mutunci, idan kuwa kika sake kika saki baki zancen ya fita, to ina tabbatar
miki kin samu abin Gori wajen dangin miji."
Karima ta sauke kai kasa
Umma ta ce ."To ubangiji Allah ya bayyana ta."
Alaji ya tashi ya shige ciki
Husna da lamarin ke dukanta ta ce ."Amma Aunty Salma ta yi rashin hankali wallahi."
Karima tai ajiyar zuciya tana girgiza kai .

Umman Salma ta matukar shiga wani yanayi, sai dai kawai Allah ya bayyana mana Salma



Salma tafiya tayi tafiya, tamkar Mahaukaciya ta koma , lokacin data fara hango bakin titi da
giftawar abin hawa yasa ta dau damarar kaiwa wajen , tafiya ta fara yi sosai, abin da ya bata
mamaki tana tafiya amma kamar bata yi , domin akwai gonaki sosai kafin ta kai ga bakin titi.
Haka har yamma ta kawo kai rana ta kusa faduwa, sannan ta isa wata gona ,daga wannan
gonar sai titi.
Saidai babu kowa gurin banda wani tsoho da ya tula Kara kan kekensa.
Ganin yana shirin hawa ya tafi Salma ta nufi gunshi da sauri tana d'ingishi tana cewa."Baba.
Baba."

Jin haka yasa tsohon dakatawa bayan yana shirin hawa.
Kallon Salma ya yi yana cewa."Ke yarinya yanzu ai babu aikin gona sai kuma gobe ."
"Gobe ki zo ."

Salma ta sake matsawa kusa da shi tana cewa."Baba ba aiki na zo ba , wai dan Allah nan
wanne gari ne ."?

Dattijon ya sake kallon Salma da fad'in.
"Yarinyar baki san inda kike bane , ai nan Gombe ke nan ."

Wani dasss taji a ranta dajin irin amsar da ya bata .
"Gombe kuma ." Ta maimaita cikin mamaki tana duban garin.

Autar marubuta


*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah

Mahaukacin so
Dangin dalas...

*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 9&10



Haka wannan tsohon yaja kekensa ya tafi, tun Salma na hango shi , har ta dena ganinshi.
Ga magariba ta kawo kai, lokacin da ya tabbatar mata tana Jahar Gombe ta sake shi ga tashin
hankali, kafadunta sun kunbura duk ciwuka a jikinsu .

Kuka ta fashe dashi ta kara matsawa bakin titi tana tare abin hawa , amma babu wanda yake
tsayawa, domin wasu ma suna mata kallon Mahaukaciya ne .

A daidai wannan lokacin ne wata farar mota ta tsaya gaban Salma, sai dai bata iya ganin waye
ciki , saboda bakin gilashi dake rufe .

A hankali akai kasa da gilas din motar
Salma cikin hawaye take kallon mai motar .
Wata farar matashiya ce mai kimanin shekaru 28
Sanye da abaya da rolling din mayafi, sai wani card dake sa'kale

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login