Showing 6001 words to 9000 words out of 30722 words
Chapter 3 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf
a wuyanta .
"Ke lafiya kike tsaye anan kina kuka ."?
Tambayar data fara jefawa Salma ke nan
"Wallahi ina bukatar taimako, tun daga Kano nake , yan fashi suka tare mu , sun kashe koya ,
muna ta gudu cikin Daji yanzu wani tsoho yake tabbatar mini a Gombe nake yanzu, babu
wanda na sani ."
Ta karasa maganar da kuka
Matashiyar ta kalli Salma sama da kasa , ta kuma gamsu da jawabinta , hakan yasa tai jimm na
wani lokaci kafin ta ce .
"Allah sarki.
Ki yi hakuri."
"Shigo ciki ."
Ba tare da Salma tai tunanin wanne irin hannu zata fad'a ba kawai ta shige cikin motar
Matar ta rufe glass din , suka tafi .
Ganin halin da Salma take ciki yasa matar murmushi tare da kara gudun na'urar sanyaya motar.
"Nagode Allah ya saka da alheri."
Salma ta kalli matashiyar ta fad'a cikin girmamawa
"Mene ne sunanki ."?
Matashiyar ta tambaya tare da karyawa da shiga zuwa wani titi da ya rabu biyu .
"Suna na Salma."
Matashiyar bata kuma cewa komai ba , kawai ta cigaba da tuki .
Wani titi ta sake shiga wanda kana iya gano wasu manya-manyan gidaje na masu kudi .
Nan tai tare da shiga wani lungu ta nufi wani babban gida launin toka .
Tana karasawa mai gadi ya bude mata babban bakin get din , kana ta shige .
Sannan tai burgi , ta fito ta budewa Salma kofa .
Salma ta fito tana kallon wannan katafaren gida tun kafin ta shiga ciki .
"Taho."
Matashiyar ta fad'a tare dasa kai ciki
Suna shiga falon , wata farar mata ce mai kimanin shekaru 47
Zaune tana cin abinci.
"Assalamualaikum."
Tai sallama
Matar bata amsa ba , hakan bai hana matashiyar zama a daya daga cikin kujerun alfarmar ba
Salma kamar mai jin tsoro ta karaso ta zauna a kasa
"Ina wuni hajjiya."?
Ta gaida wannan matar
A lokacin ta d'ago cikin isa tana cewa.
"Lfy lau, wannan kuma daga ina."?
Matashiyar kawai tai ajiyar zuciya tare da warware rolling din dake kanta .
Bayan Umman Salma ta idar da sallah, tai addu'a kamar yadda ta saba , sai dai kwana biyun
nan tana yawan kuka , shima haka malam Aminu yana cikin damuwa Sosai, sai dai suna ta
addu'a.
Hadiza ce ta ke sauraran voice din da Ruma ta aiko mata bayan ta gama saurara ta maida
mata da cewa .
"Allah sarki kawata, wallahi nima bansan zamu tashi ba ,kawai abin ne ya zo ."
Sannan ta tura mata ,Ruma da kamar jira take a aiko tai saurin budewa tare da maido da amsa
.
"To ai shikenan kawata, Allah ya sa haka ne yafi alheri, sai dai gaskiya ina kewarki sosai ,
sannan kuma in baki labari mutuniyarki Salma an nemeta an rasa wlh , ta gudu saboda kanin
babanta ya hanata rubutu."
Bayan Hadiza ta gama saurara, ita ma ta maida mata da fad'in.
"Waii Ruma gaske ko karya , tab , dama ina ita ina had'a kanta dani to Allah ya kyauta."
Tana tura mata , ta bude group dinta domin yin reply
Wani sako ta gani wata mai irin sunata tana cewa.
"Muna godiya Aunty Hadiza, gaskiya wannan labarin akwai citta."
Ba tare data bata amsa ba ta sake karanta wani sako dake kasanshi .
"Mun gode, muna jiran update na yau dan Allah ,gaskiya Najif ba shi da hankali gaban kowa ya
fad'a wa matarshi daga aure."
Ita ma bata bata amsa ba , ta fito daga group din kana ta bude wani sako wanda number babu
suna .
"Wallahi kiji tsoron Allah, kina koyawa yara iskancin banza da sunan novels, Allah yana ganinki ,
ko mutuwa kikai wannan abin bazai goge ba , kin rubuta wallahi ki tuba ."
Bayan Hadiza ta gama karantawa kawai tai blocking din ta .
Salma ce kwance kan kujera , bayan ta yi wanka da ruwan zafi , aka bata wani riga mara nauyi
ta Sanya
Sannan likitan da aka kira ya sanya mata ruwa , tare da rubuta mata magunguna , kana ya tafi .
"Har yanzu bansan sunanki ba ."
Salma tai maganar tare da kallon ta
Murmushi tai tare da rike hannun Salma tana cewa.
"Suna na Hauwa'u, kuma ni yar jarida ce , sannan 'yar gata ce ni kafin iyayena da mijina su rasu
, yau watanni 4 da kwanaki da rasuwarsu , sakamakon hadarin mota ."
Hawaye suka gangaro mata
Salma ta share mata hawayen tare da fad'in.
"Ki yi hakuri Aunty, Allah ya musu rahma."
Aunty Hauwa tai murmushi tare da cewa.
"To salmana ki kwantar da hankali nan gidanku ne , na samu kawa, sannan waccen matar da
kika ganta .
Sunan ta hajjiya Aisha matar mahaifina ."
Kafin ta karasa maganar wani saurayi ya bankado labulai kana yasa ido yana kallonta .
"A'a Aunty Hauwa wannan babyn fa ."
Ya nufo da nufin ta'ba Salma
Tsawa Aunty Hauwa tasa masa tare da cewa.
"Baka da hankali ne Anas, mene haka ."?
Jin haka yasa shi cewa .
"Ai shi ke nan."
Ya wuce sama yana tafiyar yan shaye-shaye.
Hankalin Salma ya matukar tashi ganin wannan yanayi , hakan ya sa ta kalli aunty Hauwa tana
cewa.
"Aunty wa ye wannan kuma ."?
"Ki kwantar da hankalinki , wannan yaron hajjiya Aisha ne , amma ba babanmu daya ba , kusan
anan gidan ya girma."
Salma tai ajiyar zuciya
Lokacin Aunty Hauwa ta mike da cewa .
"Ina Suwaiba ne , ko har ta tafi."
Salma ta bata amsa da cewa.
"Ai tunda ta gama girki ta tafi."
Ta ce .
"Okay."....
Umar ne cikin daki har ya kwanta, rike yake da wayarshi yana kallon hoton Salma, baisan
lokacin da hawaye suka zubo masa ba
Ya share su tare da sake sa ido cikin hoton yana cewa.
"Haba Salma, yaushe zaki dawo?
Kin barni cikin kunar zuciya da kewar ki, rayuwa bata mini dadi Salma."
Ya aje maganar yana rumgume wayar yana kuka .
Wayyyo masu karatu a jona da wannan page
Sai mun had'u a wani.
07040805269
WhatsApp only
Ku yi mini subscribe Something big is coming....
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️
Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️
A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...
*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>
Ku yi mini subscribe Something big is coming....
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 11&12
Misalin karfe 11 na safe , Adam har ya iso Kano, domin a halin da ake ciki yanzu yana zaune a
falo, sun gaisa da Alaji da kowa da kowa .
Sai dai abincin da Karima ta aji ye masa , bai fara ci ba , kawai ruwa ya iya sha .
"Assalamualaikum."
Karima ta shigo da sallama, harara ta jefa masa tana cewa.
"Wai dan Allah ka ci abinci."
Murmushi Adam ya yi yana cewa.
"To ta ya zanci abinci, kin kawo mini kuma kin fita , tare zaki zo mu ci ."
Murmushi ita ma Karima tai masa tana cewa.
"Haba , sai ka ce a novel."
"Hhhhh ."
Adam ya yi dariya , sannan ya ce .
"Novels ko, ki ce kina karantawa ke ma ko kina rubutawa."
"A'a, wane ni , rubuta novels ai sai 'yan baiwa , fasihai marubuta."
Adam ya ce .
"Tom kema ai 'yar baiwa ce Sosai, kuma a gurare da dama ."
"Kin ga kanwata Hadiza ma marubuciya ce ."
Zunburo baki Karima ta yi kana ta ce .
"Ammma baka ta'ba fad'a min ba ."
"Tom ni dai gaskiya ka bani number ta."
Adam ya bude baki cikin mamaki yana cewa.
"To mene na sauri , naga dai kin kusa komawa kusa da ita , kuma bake za a ba number ta ba ,
ita za a ba taki ."
Ya gyara zama yana cigaba da cewa.
"Wato naji haushin dawowarsu Umma, naso sun yi zamansu a nan ."
Karima ta sake murmushi tare da fad'in.
"Nifa ka fara cin abinci sai sanyi yake yi."..
Ya ce .
"To masoyiya."
Tai murmushi a karo na ba adadi
Aunty Hauwa ce tai saurin fitowa harabar gida
Kana ta doshi kusa da wani mutum dogo yasha malum-malum
"Haba Baba ai daka iso ciki , amma ka tsaya anan."
Babban mutum din ya yi murmushi yana cewa.
"Haba Hauwa'u, ai ba saina shigo ba , sauri nake yi ma , saboda mun zo daurin aure garin naku
ne , na ce bari na shigo naga 'yata."
Aunty Hauwa tai murmushi tare da fad'in.
"Allah sarki Baba ,yasu momy dasu Khalid."?
Ya maida mata da cewa.
"Suna nan alhamdulillah Hauwa'u, ya kuma hakuri da zama da hajjiya Aisha."?
Murmushi Aunty Hauwa ta fara yi , sannan ta ce .
"Baba ke nan."
Hakan yasa ya sake cewa.
"Tomm Hauwa'u , hajjiya Aisha ta gama takaba, kuma kema kin fita harkin cigaba da aiki ."
"To maganar gaskiya a matsayina na mahaifinki , bazan sa ido wannan muguwar matar ku
cigaba da zama ba , duk abin da Alaji ya bari naki ne ,kuma zaman ta ya kare anan , tunda ba
mutunci ta sani ba ."
Aunty Hauwa ta durkusar da kai kasa ta ce .
"Haka ne Baba ,sai dai akwai kadarorin Daddyna da yawa a gunta , ammma bana son a tayar
da wannan maganar , sai na dawo daidai, domin har yanzu wannan mutuwar tana dawo mini
sabuwa."
Ganin yadda kulla ke kokarin zubo mata ya sa shi cewa .
"Shi ke nan Hauwa'u, babu komai a cigaba da hakuri."
"Ni zan koma yanzu, domin an kusa daura auren .Ina abokiyar taki Salma."?
Aunty Hauwa ta ce .
"Tana ciki , ai har gida zamu zo ne ."
Ya ce .
"Tom shi ke nan, Allah ya kawo ku Hauwa."
Sannan ya fita , Aunty Hauwa tai ajiyar zuciya sannan ta koma ciki
Allah sarki Umma duk tabi ta rame, rashin Salma yana matukar dukanta
Tana zaune tsakar gida malam Aminu ya fito daga daki.
"Malam sannu da fitowa."
Ya ce ."yawwa sannu da gida , sai dai ya kamata ki cire damuwa a ranki , domin da ikon Allah
Salma zata dawo ."
Umma ta ce.
"Tom malam idan zata dawo sai yaushe, wa ne yasan a wanne hali take yanzu, ai dole abin ya
dame ni ."
Ta sake kallon mlm Aminu tana cewa.
"Tom malam ko zamu koma wajen malam Sharif mai almajirai ne ."
Malam Aminu ya yi ajiyar zuciya tare da fad'in.
"Karki manta , malamai suna ta addu'a, in Sha Allah Salma zata bayyana kawai ki cigaba da
addu'a ke ma ."
"Sannan ya kamata kije gidansu Umar, an kawo kayan Karima."
Yana rufe baki Murja kanwar umman Salma ta rado sallama
Aunty Hauwa ce zaune cikin dakinta tana yin waya .
Salma ce ta shigo da sallama, kana ta zauna a kasa
Aunty Hauwa ta cigaba da wayarta tana cewa.
"To director in sha Allah ma London zasu tura mu , domin zamu fi jin dadi."
"Tom shi ke nan sai na jika ."
Sannan ta aje wayar tana murmushi da kallon Salma.
"Ina kwana Aunty."?
"Lafiya lau Salma ya jikin naki."?
Salma ta ce .
"Alhamdulillah naji sauki Aunty."
Sannan Aunty Hauwa ta ce
"Kina bacci dazu yayan babana ya zo yana tambayar ki ya zo daga Akko local government
daurin aure."
Salma ta ce .
"Allah sarki har ya sanni ."?
Aunty Hauwa tai dariya ta ce .
"Eh mana , mahaifiyarsu daya da babana ."
Salma tai murmushi
Hakan yasa cewa da Aunty Hauwa.
"Salma kin bani labarin ki, a gaskiya yayan babanki bai kyauta ba , ta ya zai kore ki a gidansa
kawai dan kin zama marainiya."
Wani dassss Salma taji a ranta , domin batason Aunty Hauwa tana tuno labarin data bata na
karya da gaskiya.
Cikin yanayin tsoro Salma ta ce .
"Aunty wallahi ma irin yadda 'yan fashi suka tare mu , suka ringa kashe mutane shi ne yake cina
."
Ta fashe da kuka tana cewa.
"Allah sarki Salma, cann nabar gawarta aunty babu yadda na iya ."
Aunty Hauwa tasa hannunta kan kafadar Salma tana cewa.
"Ki yi hakuri Salma, in sha Allah komai ya wuce , sai dai yayan babanki duk sanda na samu
lokaci zamu je gurin shi a Kano."
Salma tai murmushi mai yake kana ta sunkuyar da kai.
"Ammm Salma mene ne burinki , kin gama makaranta ne ."?
Salma taji tambayar a kunnuwanta
"Aunty na gama makaranta."
"Sai dai bani da burin da ya wuce na zama marubuciya."
Murmushi Aunty Hauwa tai tare da cewa .
"Masha Allah, buri mai kyau ke nan Salma, kina da baiwar rubutun ko zaki shiga makaranta ne
."?
Cikin jin dadin maganar Salma ta ce .
"Aunty basai nayi makaranta ba , domin lokuta da yawa nakan kirkiro labari."
."Ina son zama MARUBUCIYAR online, mai ilmantarwa Sosai."
Aunty Hauwa ta ce .
"Allah sarki Salmana karki damu."
Hadiza tana zaune rike da wayarta, kashe datar ta ke nan ta fito daga Facebook
Kana ta shiga app din da take rubutu, ba tare da bata lokaci ba ta fara rubutu kamar haka .
"Aure dadi
By
Hadiza RM
Paid book."
Ba tare da tasa kudin littafin ba ta cigaba da rubutu kamar haka.
"Page 67."
Mahaifiyarta ce ta katse ta da cewa .
"Hadiza ina bayi kina ta kirana lafiya."?
Hadiza ta ce .
"Muna waya ne da amaryar Yaya Adam, na ce ki zo mu gaisa baki zo ba ."
Umman nata ta ce .
"Tom ni dai bari naje gidan wannan kawar tawa Saude, domin biki kwana kadan ya rage ."
Hadiza ta maida mata da cewa.
"Tom a dawo lafiya."
Ta maida kanta kasa ta cigaba da rubutun .
Autar marubuta
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️
Masu YouTube na baku damar karanta wannan Littafin kar a yi kuskuren canza mini duk
abin da aka gani a wannan labarin ✍️
A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...
*AUTAR MARUBUTA CE*✍
______________________________________
_Faduwar wani tashin wani_
_Yau ake yi, gobe sai labarin_
_Burina Rayuwata, rubutuna dan masoyana_
_Cikawa da imani fatana_
<><><><><><><><><><><><><><><><><><><>
Ku yi mini subscribe Something big is coming....
https://youtube.com/@fatimaismailabdullahi?si=l3dnPNRKygK5lG4g
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 13 & 14
Ga kayan lefe nan kota ina birjik Dactor Adam ya yi kokari sosai .
Amarya Karima abin da ya bata mata rai kuwa , irin littattafan da ta ga Hadiza take rubutawa.
Sakamakon tana yawan ganin littafinta ana sharing din shi , sai dai sai yau tasan kanwar Adam
ce .
Wato Hadiza RM , ta tara masoya sosai da tarin mabiya , an santa sosai tayi kaurin suna a
rubuta littattafan batsa
Washe gari
Bayan Aunty Hawwa ta shirya tsaf domin tafiya gurin aiki , sai sukai sallama da Salma sanna ta
wuce , Salma harda rakota falo
Anas dake zaune tare da mahaifiyarshi yake cewa.
"Aunty Hauwa a dawo lafiya, Allah ya tsare."
Ta maida masa da cewa.
"Ameen Anas."
Tana murmushi sannan ta wuce, tana farin cikin yadda ta ga Anas kwana biyu yana girmamata .
Haka Salma ta koma dakinta Anas yana binta da kallo
Hannu hajjiya Aisha ta sa ta makeshi tana cewa.
"Kai wanne sabon hauka ne ke damunka kwana biyu, sai shishshigewa Hauwa kake , karka ce
mini waccen tsintacciyar yarinyar kake so."
Ta aje maganar tana nuna hanyar da Salma tabi
Dariya Anas ya yi yana cewa.
"Haba mommy, me zan yi da waccen yarinyar ."
"Kawai abin da nake so ki gane , Aunty Hauwa da kuma ke , ku zauna lafiya, saboda naji Aunty
Hauwa tana cewa.
Zasu je Dubai su yi wata biyu ."
Sannan ya sake fuskaantar hajjiya Aisha yana cigaba da fad'in.
"Kin san wannan yayan baban nata , yana gaf da cewa mu tashi, to wallahi mommy mu yi
biyayya mu ci abin da zamu ci , in ba haka ba mun zama sorry, mu zauna lafiya har lokacin da
zata tafi Dubai ."
Hajjiya Aisha tai shiru tare da tunanin gagarumin shawarar da Anas ya kawo mata .
Salma kam tana kwance kan gado , domin kuwa babu aikin fari bare na baki , sai zama da
kwanciya.
"Allah sarki Umma, dan Allah ki yafe mini ."
Salma tai maganar tare da tunanin gida .
Mikewa tai sakamakon yunwar da taji tana ji , ta fita zuwa kichin domin samo wani abu.
Sai dai gashi har yanzu Suwaiba yar aiki baza zo ba , ga rana tana yi sosai.
Hakan yasa Salma tai tunanin yin taliya jollop
Tukunya ta dauko tare maimakon ta