Showing 27001 words to 30000 words out of 30722 words

Chapter 10 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf


"Wallahi dubu dari biyu aka bamu, aka bamu hoton yarinyar da zamu kashe, motar ba tawa ba
ce yalla6ai, mun dade a gurin muna jiransu, hakan yasa dayan yayi shigar tsofaffi domin samun
damar lekawa kowanne mota , idan yaga akwai wacce aka bamu hotonta sai ya mini a lama na
taho na danne motar , daga nan sai mu gudu." Cikin jigata ya karasa maganar "Wa ne ne ya saku aikin ."? Cewar DPO
" Wallahi yalla6ai Daga sokkoto ne , sunanta Hadiza." Inji shi
Dpo ya kalli kofur sani yana cewa. "Ka dauki bayanansa yanzu a kawo mini officer."
Dpo ya wuce ciki, yayin da wannan yake ihu yana fad'in.
"Yalla6ai dan Allah ka ce su dena dukana, wallahi ban taba kashe rai ba ." Kofur sani ya ce ."Yi
mini shiru ."
DPO yana shiga office, babu dadewa kofur sani ya Kai masa wannan bayanai , ganin hakan
yasa DPO yin waya ga abokan aikinsu zuwa Sokkoto birnin shehu .


Misalin karfe 1 mai tattaunawar mai suna Muhammad Ayuba ya fara hira da Salma, babu
boyeboye Salma ta bayyana cikakken sunanta da tarihinta
Tattaunawar ta yi nisa har ta zo gangara, kallon Salma ya yi yana cewa. "To hajjiya Salma,
akwai maganar da take yawo cewa. Kina daga cikin sahun marubuta matasa masu shahara da
kuma arziki, alhalin baki dade cikin duniyar marubuta ba ."

Murmushi Salma tai sannan ta ce . "To ai ita shahara ko daukaka daga Allah ce, ba boka babu
Malam, kuma arziki na kasuwanci ne , duk da cewa ina samun wani abu daga rubutu, to amma
bai kai kasuwanci na ba ." Ta aje maganar tana kallon shi, hakan ya tabbatar masa ta gama
bashi amsa , ya dubi takardar dake hannunshi , kana ya d'ago yana cewa. "To autar marubuta
mun saurari, kalubalenki kafin ki kawo wannan matsayi, mun ji kuma tarin nasarori da jeren
littattafan ki ."
"Wacce shawara zaki bawa marubuta masu tasowa da kuma wanda suke cikin rubutu ka'in
dana 'in."
Ajiyar zuciya Salma tai tana gyara zaman gyalen abayarta

Sannan ta fara cewa."Tom har ila lau dai shawarar guda daya ce zuwa biyu."

"Marubuta su ji tsoron Allah, su rubuta abin da zai amfani al'umma, kar si hassada a junansu ,
su jayo kananun marubuta a jika , tabbas yin hakan zai kawo babban cigaba."
Muhammad Ayuba ya ce .
"Tom ko mu dakata ne , anjuma sai mu cigaba, domin ba kai tsaye bane ."
"A'a haba dai a cigaba ai kadan ya rage ." Cewar Salma
Dariya Muhammad Ayuba ya yi , sannan ya ce ."Okay wa ne ya ce miki sauran kadan , ki gaji
ke nan."
Salma tai dariya
Hankalin shi ya mayar ga aikin yana cewa." Tom yanzu zamu amsa sakonni masoyanki."

"Wannan take cewa , gaskiya Autar marubuta Allah ya kara daukaka da nisan kwana muna tare
da ke . Daga Basira Hudu
Salma ta ce . "Amin summa Amin ina godiya."
Sannan ya kuma karanto wani sakon yana cewa.
"Aslm, nima marubuciya ce , dan Allah Autar mu, ki bamu shawarar yadda zamu magance
marubutan batsa da masu tura mana abin banza a cikin group, saboda sai mun sakankance
ake tura mana abin da bai dace ba na gode."

Da sauri Salma ta ce .
"Wannan abu ne da kullum nake bawa marubuta shawara, da farko dole ya zama kanmu yana
hade ne , duk marubuciyar batsa ku hana ake sako muku novels dinta cikin group,duk wanda
ya sako ku cireshi koda ita ce , sannan zancen masu tura abin batsa cikin group."
"Gaskiya wannan ruwan dare ne cikin group din marubuta, Allah ya shirya masu yi, abin da
zaku yi anan shi ne , ba wai iya marubuta ba , duk inda kuka ga an tura irin wannan, sai ku yi
saving number wannan wanda ya tura din, Tom da zarar ka ganshi cikin group kai maza kayi
reporting admin su cire shi, su ma marubuta idan sun yi saving number irin wannan mutanen, to
da zarar ya turo request a group zai shigo,sai ai cancel din shi kar a yi approval nashi ." "Idan ta
kama su ringa saving numbar tasu irin daya , kamar kawai si yi saving da A, ko Y koma mene,
to duk inda ka gansu zaka ganesu. Domin masu wannan halin kullum yawa suke karawa."
"To Ina tabbatar muku idan kun dauki wannan shawarar wannan matsalar ta kau sai dai wata ."

Sokkoto
Yanzu misalin karfe 1:47, an taru sosai a cikin masallaci, wakilin Hadiza ake jira domin a daura
aure,
Nan gidansu Amarya kuwa, sai farin ciki ake ana ta hidima da Kai kawo, su Umman Hadiza an
sha kyau sosai uwar Amarya, ana ta yin hotuna da 'yan uwa , motar yan sanda ce ta tsaya a
kofar gidan, kana yan sanda uku suka fito, macen cikinsu ce tasa kai, Kai tsaye cikin gidan ,
hakan yasa 'yan uwa aka fara binta da kallo.

"Ina Hadiza."?

Cewar 'yar sandar da hausa bata wadaci bakinta ba
"Gata can amaryar ." Cewar wata mata , ganin wannan 'yar sandar yasa Karima isowa wajejen
gurin da sauri .
Bayan ta ishe Hadiza da ta ci kwalliya ta ce . "Ki wu ce muje zuwa office akwai tambayoyi da
zaki amsa ."
'yar sandar ta sake magana
Hankalin kowa ya yo wajen caaaa ana mamakin meke faruwa
"Kamar ya na wuce , bikina fa ake babu inda zani mene nai muku , ." Inji Hadiza
Umman Hadiza ce dake dakinta ta fito da sauri tana cewa. "Ina zata je , ranar auren nata ma sai
an yi mata bakin ciki da hassada , to wallahi Allah yafi karfinku ."
Jin hakan yasa wannan 'yar sandar daba bahaushiya ba fad'in.
"Babu ruwanmu da biki, zami aikinmu ne , idan baza ki taho ba zami sa miki karfi , muna da
yawa a waje ."
Hankalin Hadiza taji ya tashi sosai


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________


Page 41&42

Bayan Salma sun gama wannan tattaunawar, har abinci suka samu suka ci, sukai sallah,
sannan suka hau mota.
Ganin Aunty Hauwa ta murza kan mota sun jiya yasa Salma cewa.
"Aunty wannan titin ai bazai kai mu Tarauni ba ."
Aunty Hauwa ta kalleta tana cewa.
"Eh zamu je station ne , sun kira mu , domin an taho da Hadiza daga sokkoto." Salma ta aje
numfashi mai nauyi , Aunty Hauwa ta cigaba da tafiya.

Nan kuwa hankalin mutane duk ya tashi, ko aure ba a daura ba an tafi da Amarya har Jahar
Kano, hakan yasa ango da zugarshi suka bisu , jingum-jingum kowa ya yi a cikin gida , saboda
labari ya zo musu cewa ana tuhumar Hadiza da kisan kai ne ..
Sai da wajen misalin karfe 4:30 su Aunty Hauwa suka samu suka taho, bayan Hadiza ta amsa
laifinta tare da nadama, sai dai babban abin da ya Sanya Hadiza amsa laifinta babu bata lokaci,
ganin Sultan da Alaji Babawo a wannan gurin, domin a tunanin ta tabbas za ai mata uzuri da
alfarma, domin babban mutum ne Alaji Babawo. Sai dai aka sin haka ne ya faru , domin kuwa yana jin hakan ya yi Allah Wadai yaja zugarshi
suka koma sokkoto .domin ya ce yarinyar da zata iya wannan, to tabbas zata iya kashe masa
sultan.
Anan kuwa umman Salma tana cikin matukar tashin hankali, domin tunda ta fara sauraran hirar

da aka saki cikin gidan wannan redion ta kasa sukuni
Hakan yasa ta kira Umar yana cann kallon Ball
Da sauri ya iso gida, domin ya ga irin Kiran da take masa, yana shiga a tsaye ya sameta
"Umma lafiya, me yake faruwa ne."?
Umman Salma ta nuna masa redion tana cewa. "Wallahi Umar yanzu naji anan gidan redion,
wannan Autar marubutar Salma ce , Salma ta ce ."
Jin wannan batu yasa Umar rike haba tana cewa. "Salma kuma Umma? Ko dai mai irin
sunanta."?
Umma ta ce . "Ka tsaya ka sauraran Umar wallahi wannan yata ce Salma, muryar ta ma bata
canza ba har irin dariyar ta."
Shi dai Umar lamarin ya daure masa kai , baisan ta Ina zai fara ba
Da kyar Salma ta iya gane gidansu, saboda gyaran da yaji da kuma tarin sabbin gine- gine .
"Assalamualaikum."
Salma ta fara shiga cikin falon tare da tashin hankali, Umar da Umma suna tsaye
Babu Wanda ya amsa sallamar duk a cikinsu, har ita ma Aunty Hauwa ta shigo .
"Salma."
Cewar Umar, murmushi mai ciwo Salma tai sannan ta ce .
"Na am Yaya Umar." Yayin da idanunta suka kawo ruwa , Umma take kallo cikin matukar tashin
hankali da tsananin kewa da kauna har hawaye suka fara zubo mata, ita ma Umma hawaye ne
suka zubo mata , amma ta share su cikin kwarin gwiwa.
Da sauri Salma tai yunkurin sunkuyawa gaban Umma
Amma Umma cikin izza ta dakatar da ita tana cewa.
"Dakata anan."
Jin hakan yasa su duk mamaki
"Dakata anan ." Ta sake fad'a, sannan ta cigaba da cewa.
"Ya kamata ki nemi izini yayin shigowa gidan mutane, domin kina daya daga cikin Wanda ba
muharraman wannan gida ba ."
Cikin wani sabon tashin hankali Salma ta zaro idanu tana cewa.
"Umma me kike fad'a ne , baki gane ni ba ne? Salma ce fa yarki."
Jin wannan maganar ya sake fusata Umma.
"Bani da wata 'ya a wannan duniyar, Ina so ki fitar mini a gida yanzu."
Kuka Salma ta rushe dashi mai matukar gwanin ban tausayi, aunty Hauwa babu abin da ta iya
fad'a a wannan yanayi
"Ba haka Ummana take ba wallahi, Ummana nasan tana kewar gani na kuma tana kaunata "
Cewar Salma cikin kuka
Babu annuri ko kadan a fuskar Umma ta ce. "Salma burinki ya cika ,kin samu daukaka kin samu
kudi, babu abin da ya rage fa ce ki canja iyaye da zasi daidai da kudi da daukakarki."
Umma taja numfashi na bacin rai sannan ta cigaba da cewa.
"Kin tafi kin bar gida babu tunanin wanne hali muke ciki , babu neman mu har Saida burinki ya
cika , ki fitar mini a gida Kona miki abin da baki tunanin shi ba ."
Kuka ta sake kecewa dashi tana faduwa kasa tana cewa."Haba Umma, Haba Umma."
Zazzafar ajiyar zuciya Umar ya sauke sannan ya ce . "Haba Umma, idan rai ya baci hankali ba
ya gushewa."

"Kayi mini shiru Umar tun kafin na bata maka rai ." Inji Umma
Umar ya sake ajiyar zuciya tare da fad'in."Ki gafarce ni Umma, amma bazan iya shiru ki cigaba
da cutar da kanki ba, domin kullum kina addu'a Allah ya kare Salma ya kuma dawo da ita zuwa
gareki "
"Ki yi hakuri Umma ga Salma ta dawo, tabbas kina da damar hukunta Salma, sai dai karki
hukunta kanki , domin har yanzu kina kaunar Salma fiye da komai, har sauraran gidan redion
novels kike saboda kewarta."
Umma ta sunkuyar da Kai kasa, yayin da Salma take mikewa tsaye tana ci gaba da kuka
"Yanzu da zarar Salma ta juya , kuncin da zaki kuma shiga Allah ne masani Umma, Dan Allah ki
yi hakuri, yanzun nan fa kika kirani cewa kinji Salma gidan redio, kin kasa samun sukuni, to me
yasa ta zo gabanki zaki mata haka ."?
Jin wannan zan tuka na Umar yasa jikin Umma sanyi ta fara kuka
Da sauri Salma ta fara fad'in. "Dan Allah Umma ki dena kuka, wallahi Umma ina kaunar ki,
rayuwar masifar dana shiga ta hanani zuwa gareku shekara biyu da watanni kuna zuciya ta,
dan Allah Umma ku yafe mini dan Allah Umma."
Da sauri Salma ta fad'a jikin Umma tana kuka, jin Salma a jikinta yasa Umma ta rumgumeta ita
ma tana kuka
Aunty Hauwa tai murmushi tare da kallon Umar
Kuka mai gwanin ban tausayi Salma take yi tana cewa."Ki yafe mini Umma, ki yi hakuri, tabbas
nayi ba daidai ba wallahi, amma badan kudi ko daukaka ba Umma, ki yi hakuri Umma ki yi
hakuri."
Umma jin Salma tana wannan maganar cikin kuka ya sake karya mata zuciya tana sake
rumgumeta
"Na ga rayuwa mara adadi Umma, banyi zaton sake ganinki ba da Baba, amma cikin ikon Allah
Aunty Hauwa ta zame mini gata , wallahi Umma na yi kewarku ki furta kin yafe mini dan Allah."
Cewar Salma ke nan cikin kukanta
"Na yafe miki Salma, wallahi na yafe miki." Jin hakan yasa Aunty Hauwa da Umar wani
murmushi suna ta ya Salma farin ciki
Sakin Umman nata tayi , tana kallonta cikin idanunta da har sun kunbura tsabar kuka ."Umma
ina Baba nasan zai yi fishi dani sosai fi ye da ke , ku hukunta ni Umma amma karku mance ni
'yar ku ce , da ta yi kuskure ."

Taja numfashi tana kallon Umar, "Yaya Umar ina baba yake ."?
Umar ya kalli Umma yayin da suke had'a idanu, ganinsu kamar marasa gaskiya yasa Salma
rudewa
"Umma ina Baba ya ke ." ? Cikin tashin hankali ta sake tambaya
Babu wanda ya bata amsa cikinsu, hakan yasa take jin tabbas wani abin ya same shi
"Ko ya mutu ne ."?
Cikin tashin hankali ta fad'a tana rike baki, da sauri Umma ta matsa ta bude wata dirowa tana
dauko wata takarda, ta mikawa Salma
Da sauri ta karbe jikinta da hannayenta na rawa ta bude takardar

Autar marubuta

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 43&44. End.

Allah - Allah Salma take ta fara karantawa cikin zuciyarta ba tare da nutsuwa ba ta fara karanta
rubutun mai blue biro .
"Assalamualaikum 'yata Salma, nasan komai dadewa zaki dawo wannan gidan, ni kuma wata
kila kafin wannan lokacin bana raye, hakan yasa nake son sanar dake cewa, ban ta'ba kyamar
rubutun da kike yi ba , na biyewa yayana ne matsayinsa na babba da yake da wahalar fahimta,
amma sai gashi matsalar ta kai ga har kin bar gida ." Salma ganin wata fuska da aka zana tana kuka ne yasa hankalin ta sake tashi tana rudewa da
kuka, a wannan yanayi ta cigaba da karanta wannan takardar
"Duk inda kike Allah ya kare ki , ki girmama yayana domin shima mahaifinki ne , na yafe miki
Salma duk abin da kikai mini , Bissalam."
Karshen rubutun ke nan , kudundune takardar tai cikin hannunta tare da shiga wani sabon
yanayi, hakan yasa Umma jin tausayin Salma
"Baba ya rasu ke nan Umma, ya rasu ke nan Umma, innalillahi wa innailaihir rajiun, innalillahi
wa innailaihir rajiun."ν ½νΈ­
Maganar Salma ke nan cikin sabon yanayi mara dadi
Aunty Hauwa hawaye taji sun zubo mata, saboda irin yadda Salma tai matukar bata tausayi
"Allah ya yi masa rasuwa Salma, yanzu shekara 1 ke nan, yana sauran kwana biyu zai rasu ya
bani wannan takardar." Inji Umma cikin damuwa
Sunkuya Salma tai bisa jirin da take ji , ta zauna a kasa tana dafa kanta tana cewa.
"Allah ya jikanka Baba, babu rabon mu sake ganin juna , Allah sarki babana."
Ta mike tsaye kamar an tsireta tana kallon Umar da cewa.
"Yaya Umar ina son zan je kabarinsa, ka rakani dan Allah."
Umar ya ce . "Tom shi ke nan."
Umma ce ta kalli Aunty Hauwa tana cewa.
"Baiwar Allah ki karaso ki zauna mana".
Hakan yasa Aunty Hauwa zama tare da gashshe da Umma tana mata ta'aziyya tare da rarrashi
.
"Umma wannan ita ce Aunty Hauwa." Cewar Salma
Nan shima Umar ya zauna Salma tana basu labarin irin rayuwar data shiga tunda ta fice a
wannan daren , Umma ta tausaya mata sosai, sannan ta jinjinawa aunty Hauwa tare da mata
godiya sosai,
Wajen karfe 6 Yaya Umar yake kiran Alaji Yusuf yake sanar dashi dawowar Salma, a cikin dare
kuwa sai ga zainab ta zo , bayan an sanar da ita

Aunty Hauwa ita ma a wannan gida ta kwana da sassafe Umma ta tashi ta dora musu doya da
kwai , Umar ya siyo breadi

A social media kuwa babu abin dake yawo kamar irin yadda marubuciya Hadiza RM ta yi
yunkurin kashe Autar marubuta, abin da yake yawo ke nan a duk inda ka shiga , sai dai a halin
yanzu an tura Hadiza zuwa kotu, Umman Hadiza tana cikin matukar damuwa, domin Karima
babu tsoro ta bayyana cewa wannan Autar marubuta da Hadiza tai yunkurin kashe wa , to 'yar
uwarta ce , shi kanshi Adam ya yi mamakin irin yadda bata ta'ba bashi labarinta ba.
Umman Hadiza kuwa tsanar Karima ta yi sosai, domin yanzu bata son jinin wannan Autar
marubutar ,
Da safe Karima ta shirya tsaf domin tafiya Kano, nan Umma babu abin da ta iya cewa da ita ,
domin asan samun Umma, Adam ya saki Karima, sai dai bazai iya hakan ba , wai a hakan ma
Umma tana yin haka ne ba tare da tasan Karima ce ta yi sanadin tonon asirin Hadiza ba , da
abin yafi haka kam.
Da safe suna gama karyawa sai ga Alaji Yusuf nan, nan ya zo gurin Salma suka gaisa harda
bata hakuri, domin tun daga rasuwar kanin shi yayi sanyi sosai, har albarka ya sa mata sannan
ya koma .
"Salma yau zamu je Bauchi fa , domin babu lokaci." Cewar Aunty Hauwa
Umma ta ce .
"Yau kuma daga zuwa ."
Salma tai murmushi ta ce . "Eh Umma ai Aunty Hauwa bata da lokaci sosai, wannan ma sa'a
aka ci ya zo kan ga'ba ."
Salma ta kalli Yaya Umar.
"Tare da kai fa zamu tafi."
Zaro idanu ya yi yana cewa.
"Tare dani kuma , yau ina da aiki fa ."
Harararshi Salma tai tana cewa ."To wallahi sai kaje babu ruwanmu da aikinka."
"To ko dai an samu wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login