Showing 30001 words to 30722 words out of 30722 words
Chapter 11 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf
ne acan, sai a fadan na nemi daidai ni." Inji Umar
Dariya Umma da Aunty Hauwa suka yi , nan sukai ta wasa da dariyar su, har lokaci ya ja ,
sannan suka tashi sukai wanka , Aunty Hauwa da Salma suka hau mota daya , sannan Umar
yaja motar da za a kai wa Aliyuu
Sun isa Bauchi cikin farin ciki da walwala, nan suka sauka gidan Aliyuu, aiko Baba Laure ma
tana wannan gida, sakamakon Fatima ta haifi na miji kwana biyu yau ke nan, Salma tai matukar
farin ciki, haka ita ma Baba Laure sai murna take da ganin Salma, aikawa akai aka kira Aliyuu
can gurin shayi da burodi, mamaki ne ya ishe shi da ganin Salma a wannan lokacin, nan Aunty
Hauwa tai ta koda Salma gabansu tana tabbatar musu wannan makauniyar tasu ita ce Autar
marubuta fa, farin ciki da mamaki ya kama kowanne a cikinsu, haka aka sha wasa da dariya har
sukai canjan numbobinsu, haka Fatima ta roki alfarmar Salma ta yafe mata saboda irin
abubuwa data aikata mata , Salma ta ce babu komai.
Da suka tashi tafiya Aunty Hauwa ta bawa Fatima dubu 50 asai wa jariri fanfas, sannan ta sake
bawa Baba Laure dubu 50 ta ce ta yi hakuri a haka .
Sannan suka rankaya suka fito waje domin rakasu, nan ne Salma ta mikawa Aliyuu mukullin
wannan mota , sannan take tabbatar wa da Baba Laure hajjin bana tare da ita za ai, murna kam
ba a cewa komai, duk sun kasa zaune sun kasa tsaye ganin wannan arziki a gidansu, bari Baba
Laure da taji zata hau jirgi a je ga ....
Haka sukai musu addu'a suka hau mota suka juyo Kano
Anan kuwa umman Hadiza ta samu ta kawowa Hadiza ziyara
Tana zaune tana ta jira domin ganin an fito da ita . Da gudu Hadiza ta nufi Umma tana kuka
kafin ka ce komai ita ma Umma ta dau kuka
"Innalillahi wa innailaihir rajiun, Umma kinga yadda duniya take yi dani, sultan ba ya nan , kotu
yanke mini hukuncin zama a gidan yari za tai , shi ke nan rayuwa ta ta lalace Umma, innalillahi
wa innailaihir rajiun."
Haka Hadiza tai ta sunbatu Umma tana kuka , Allah yasa mu dace , Allah ka raba mu da sharrin
zuciya.
Karima harta iso Kano da dare , aiko tana zuwa gidansu, ta taho tarauni gidansu Salma
Nan su Salma suna dawowa suka tarar da Karima, aiko aka sha hira sosai , irin yadda Karima
ta gano Salma duk ta sanar da ita , farin ciki dai yau cikinsa aka kwana
Har Salma take cewa da Umar tana son za ai rijiya ko masallaci domin mahaifinta, ya ce mata
ai shi ke nan
Da safe suna karyawa Aunty Hauwa tai wanka ta shirya
"Tom Salma ni zan koma ." Cewar Aunty Hauwa
Murmushi Salma tai tana cewa."Babu dadewa zan biyoki kuwa Auntyna , gaskiya zan yi kewarki
."
Aunty Hauwa ita ma tai murmushi tare da fad'in."Tom ina nan Ina jira , amma da Allah ki amsa
tambayar da akai miki zuwa BBC."
Salma ta ce . "In sha Allahu Aunty duk zanje har ma da gidan TV da suka gayyace ni ."
Aunty ta ce .
"Tom shi ke nan sai na jiki ."
Nan ta shige mota, suna tai mata addu'a, Salma harda kuka sannan Aunty Hauwa ta wuce
Gombe.
Bayan kwana biyu
Salma tana zaune tana rubutu , sai ga Umar ya shigo
Salma ta kalleshi tana murmushi
"Ni fa na zo na hanaki rubutu, domin soyayya nake so mu yi ." Cewar Umar
Ajiyar zuciya Salma tai tana cewa.
"Tom zaka ga soyayya ni Gombe ma zan tafi gobe , domin shagona da Auntyna." Inji Salma
Umar ya jefa mata wani kallo yana cewa."To yaushe ne auren namu."?
Salma ta kifa laptop cikin kunya tana durkusar da kai .
Alhamdulillah masu sauraro, nan na kawo karshen Littafina mai suna MARUBUCIYA ✍️
Wanda ni Autar marubuta na rubuta , Allah ya bamu ikon ganin kuskureen mu , abin da ba
daidai ba Allah ya ganar damu, godiya ga d'imbin masoyana a duk inda suke , sai Allah ya sake
had'a mu cikin wani sabon labarin ✍️.
Bissalam.