Showing 24001 words to 27000 words out of 30722 words

Chapter 9 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

shiga gidan mata ."
"Ni dai ba ruwana." Cewar Karima
Mikewa Adam ya yi ya dauki jakar shi ."Tom ni dai zan tafi my love ki kula da kanki ." Nan ta
mike sukai sallama sannan ya wuce gun aikinshi na asubiti

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 35&36

"Jama'a anan muka kawo karshen wannan Littafin namu mai suna Fatima da zarah."

"Na wannan shahararriyar marubuciya Autar marubuta."
Umman Salma ke nan dake sauraran redio.
Nan ita ma Karima tana zaune tana bude WhatsApp take sauraran wannan gidan redio, daidai
lokacin da yake cewa.
"In sha Allahu gobe misalin karfe 4 na yamma zamu kasance tare da wannan marubuciya a
wannan gidan mai albarka." "Ga duk masu son turo sako zasu iya fara turowa tun yanzu a
wannan number kamar haka."...
Sai ga Hadiza ta shigo
Firgita Karima ta yi ganin Shigowar Hadiza, domin kullum Karima bata barin Hadiza taji tana
sauraran Littafin Autar ,
"Gaskiya ne Aunty ki ce kema kina yin wannan marubuciya." Cewar Hadiza
Hade rai Karima tai sannan ta ce ."Ina fa , kawai ina kamo tashar naji ana fad'a, to amma naji ya
ce za a gayyato ta , taji sauki ke nan."?
Ajiyar zuciya mai zafi Hadiza tai , sannan ta fara cewa.
"Shegiya ba , ai Aunty Karima ki bari kawai, gobe ranar aure na , kuma gobe sai na yi ajalin
wannan yarinyar, farin ciki biyu, ki duba fa wannan fim din da ake mai suna Zumunci ita ce
writer fa ."

Murmushin yake Karima tai sannan ta kashe redion.
Hannun Hadiza ta ja wo tana zaunar da ita ."Haba Hadiza, me ne wai wannan marubuciya tai
miki, kisa fa ba abin wasa bane ."
Hadiza ta janye hannunta tana cewa.
"Wannan yarinyar sunanta Salma Aminu kuma 'yar tarauni ce a Kano, shekara wajen biyu ke
nan da guduwa daga gidansu , dan kawai tana so tai gasa dani a duniyar marubuta, na tsaneta
wallahi Aunty."

Wani faduwar gaba Karima taji da tashin hankali.
"Salma kuma ."
Ta maimaita sunan cikin tashin hankali
"Eh sunanta Salma a tarauni take . Ko kin santa yar Kano ce ."

Sai da Karima ta fara mutuwar zaune, kana ta jingina da kujera."A'a bansan ta ba Hadiza,
amma yanzu ta ya zaki kasheta kanon zaki je ke nan."?

Jin hakan yasa Hadiza dariya ta ce .
"Haba Aunty, nima fa yar kano ce , kuma ita yanzu tana Gombe, amma gobe zata zo gidan
redio, kuma nasan wanne gidan redion ne , shi yasa tun jiya na kira wani domin a gama da ita ."

Karima jin kanta tayi ya kuma mata nauyi sosai .
"Kamar ya to."?
Ta tambayi Hadiza
"Zai tsaya da babbar mota, nasan da cewa a mota zata zo Kano , kafin ta karasa gidan redion
ta mutu , shi kuma ya fito ya gudu , zan kasheta tun kafin iyayenta su san tana raye , domin har

yau bata koma Kano ba ."Tana gama fade ta mike tsaye
"Aunty zanje salun ne fa , zuwa anjuma zan dawo ."
Karima ta ce . "Tom Allah ya kaimu."
Kana ta fice Karima na binta da kallo
Kanta taji ya sara mata kamar zai fashe
"Daman Salma ce wannan, innalillahi wa innailaihir rajiun, meke shirin faruwa ne."?
Karima tai maganar cikin sabon tashin hankali
"Tabbas Hadiza bazan bari ki kashe yar uwata ba , ke azzaluma ce Hadiza jahila mara ilmi, to
wallahi ko hakan zai sanadin rabuwata da Adam sai na tona asirinki."

Karima ta dafe kai tana tunanin yanzu me ya kamata ta yi , wayarta ta dauka tai sauri ta bude
WhatsApp, kafin ta nemo number wayar Salma nertwork ya dauke baki daya .haka Karima ta
ringa sintiri cikin tashin hankali, babu wanda ta iya fad'a wa wannan maganar
Nertwork bai dawo ba duk irin zaman da Karima ta zauna jira har karfe 12 bacci ya kwashe ta
Washe gari da safe kuwa, Karima harta zuge ta rame , anjuma za a daura auren Hadiza da a
karfe biyu, domin kuwa har baki sun fara zuwa.
Tun asuba ta fara yiwa Salma magana a WhatsApp, amma Salma ta hau bata duba ba , hakan
yasa ta ringa mata flashing na company, amma Salma bata biyoba , da sassafen nan Karima ta
fita ta siyo Kati .

Ita kuwa Salma tun da ta tashi da asuba hankalinta yake tashe , shi yasa ko damar duba waya
bata dashi , sam ta kasa samun sukuni, hakan yasa ta nufi dakin Aunty Hauwa
Tana zaune tana jan carbi , tasan sam bata ganin Salma a dakinta a irin wannan safiyar.
"Salma lafiya meke faruwa, kar dai ki ce mini Kano ne baki son zuwa." Cewar Aunty Hauwa
dake kan sallaya , yake Salma tai ta zauna cikin mutuwar jiki.
"A'a Aunty ba haka ba ne , ina son fad'a miki wani abu."

"A'a mene haka kuma Salma fad'a mini da sauri mene ne ."? In ji Aunty
Idanunta Salma kamar zatai kuma ta ce .
"Amma ki mini alkawari, baza ki juya mini baya ba , ko ki kasa fahimta ta ."
Jin hakan ya sa hankalin Aunty Hauwa ya tashi.
"Haba Salma mene haka, fad'a mini mene ne."?
Salma ta sunkuyar da kai kasa duk ta tada hankalin Aunty Hauwa
"Ina jin ki ." Cewar Aunty Hauwa da matukar 'kaguwa taji wannan maganar
D'ago kai ta yi tana cewa.
"Da farko ki yi hakuri, na shirya karbar duk kan hukuncin da zaki mini Aunty." Taja numfashi
sannan ta cigaba da cewa. "Aunty Hauwa mahaifiyata da mahaifina suna raye a wannan
duniyar."

"Kamar ya."?
In jita
Salma ta ce . "Kwarai kuwa na yi miki karyar cewa kanin babana ne ya koreni a gidansa,
maganar gaskiya babu wanda ya mini hakan, nabar gida ne saboda kanin babana baya son na

zama marubuciya, hakan yasa yake zuga banana."

Cikin sabon mamaki Aunty Hauwa ta ce .
"Ni fa ban fahimta ba Salma." Nan Salma ta zage ta warware mata komai da ya baro da ita
daga gidansu har da yin kuka
Shiru Aunty Hauwa tai ranta babu dadi , cikin wata irin murya ta ce . "Kina nufin karya kika mini
a komai, har zuwa Bauchi ke nan da cewa kin makance ."?

Da sauri Salma ta girgiza kai tana cewa. "A'a wallahi Aunty, wannan gaskiya ne , har zuwa
Gombe da nayi a kafa , nasan nayi kuskure dan Allah ki yi hakuri." Cikin kuka tai magana
Yadda ta ga fuskar aunty Hauwa yasa Salma sake rudewa da kuka .
"Salma wannan ai yarinta ne da rashin hankali, tsawon lokaci da duk irin wahalar da kika sha,
amma baki koma gida ba , wannan wacce irin zuciya ce dake , baki tunanin halin da iyayenki
zasu shigaba Salma, shekara biyu harda watanni , ko dan kina da iyayen ne kike haka , ." Cikin
zafi Salma ta ga Aunty Hauwa tana maganar
Da sauri Salma ta sake matsawa kusa da ita tana sake rushewa da kuka , ta rike hannunta.
"Wallahi ba haka bane Aunty, wallahi ba haka bane , ina kaunar iyayena, babana yana jin duk
maganar da yayanshi ya fad'a masa, yana girmamashi sosai ."
Cikin sake turo sabon kuka Salma ta cigaba da fad'in. "Hakan yasa ya ce zan koma gidanshi,
wallahi idan na koma gidanshi burina bazai taba cika ba , yana da zafi yana da tsauri."
Ta aje ajiyar zuciya ta cigaba da damke hannun Aunty Hauwa tana cewa.
"Sannan ina son tabbatar wa mutanen da suke tunanin marubuta ne ke lalata tarbiya, ba haka
bane,mutane da yawa suna mana wannan kallon , cikin burina harda tarwatsa alkalamin
marubutan batsa, shin ba babban abu bane Aunty, ko kuwa ya dace su hanani."? Cikin jajayen
idanu Salma ta gigice da kuka tana kwanciya a kafarta. Jinkin Aunty Hauwa taji ya mata sanyi , ta sa hannu ta d'ago Salma dake sharar kuka tana
cewa.
"Haka ne Salma, amma tuntuni da kin fad'a mini , sai naje na same su , da duk haka basu
faruwa."
Salma da shashshekar kuka ta ce .
"Wallahi baza su amince ba , domin ya canza musu tunani, amma Aunty gani , ki hukunta ni dan
Allah kafin mu je Kano si mini nasu, ki hukunta ni Aunty." Jin wani kuka mai gwanin ban tausayi
yasa Aunty Hauwa ta rumgumeta. Sunyi wajen minti guda a haka, tana sauraran kukan Salma
Daga bisani ta d'ago Salma tana murmushi da cewa.
"Shi ke nan, ya isa , ta faru kuma ta kare Salma, sai dai kin yi kuskure amma ni na yafe miki."
"Ta shi kije ki yi wanka , gashi har 7 ta yi ."
Salma ta share hawaye da cewa. "Bazan ta'ba mancewa dake ba Aunty, ke ce nasarata kuma
rayuwa ta."

Aunty harara ta jefa mata kana ta ce ."Tom gwana sarkin barin gidansu ai mini shiru."
Dariya Salma tai hakan yasa itama tai dariya tana cewa.
"Ki tashi fa zuwa 12 nake son muje gidan redion nan mu gama komai ."

Salma da jajayen idanu ta ce . "Ke nan hirar ba kai tsaye ba ce ."?
Aunty ta bata amsa da fad'in.
"Eh sai karfe 4 zasu sake ta ."
Aunty Hauwa ta mike tsaye tare da cire hijabi tana cewa. "Okay yanzu na gane abin da yasa ba
kya hira da kafafen sada tsumunta , Allah ya shirya ki ."
Salma tai dariya gami da hawaye.


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 37&38


Karfe 8 suka shirya tsaf domin tafiya, tun a wannan lokacin Salma bata duba wayar taba , tana
gama shiryawa ta jefata a cikin jaka , falon suka fito da akwati sun sha abaya ruwan toka iri
daya .
Aunty Hauwa ta kalli Salma tana cewa.
"A'a har Yanzu Farida bata fito ba , kota tafi ne ."?
Dariya Salma tai tana cewa.
"Ta tafi fa tun dazu."
Sannan suka fito , Aunty Hauwa ta tsaya rufe kofa , ita kuma Salma take sanya akwati a cikin
Booth, suna gamawa suka shiga , sai aka dau hanya , ni ko nace Allah ya tsare .
Karima kamar hawan jini zai kamata , ta yi harta gaji, amma Salma bata dauki waya ba, bata
duba maganar ta a WhatsApp ba , ta yi mata text amma Salma shiru, hakan yasa Karima take
tunanin to ko dai har an kashe Salma ne, ta yi tunanin sanar da Yaya Umar amma ta ce babu
abin da zai iya akai. Matukar tashin hankali Karima ke ciki, hakan yasa ta cigaba da kiran Salma voice call ko Allah
zaisa hankalinta ya yo wajen .
Gidan biki kam ya fara cika, sai hayaniya ake .
Anan kam tafiya ta mika musu sosai, domin Aunty Hauwa sun kusa Kano, iskar da Salma take ji
yasa ta take jin bacci , amma batai wannan bacci ba , kamar an tsikareta tasa hannu a jaka ta
zaro wayar ta.
Tsaki taja ganin wata number 21 missed call, kawai ta bude data, nan ma karo ta ci da wannan
number an yi sako ta WhatsApp sau 13
Kawai Salma taji gabanta ya fadi, tasa hannu ta bude wannan sakon .
"Aslm."
"Salma babu lafiya wallahi."
"Kina magana da yayarki Karima daga kano"
"Karki mamakin ta yadda akai na gano ki."
"Rayuwar ki na cikin hatsari karki shigo Kano, domin an sa a kashe ki ."

"Dan Allah yar uwata karki shigo Kano."
Abin da Salma ta gani ke nan gutsutstsuran sakonni harda voice call
Gabanta taji ya Fadi, ta sake komawa tana kara karanta wa.
"Tsaya tsaya Aunty Hauwa."
Cikin tashin hankali Salma ta fad'a, babu musu suna gaf da shiga Kano Aunty Hauwa taja gefe
ta tsaya
"Mene ya faru Salma."?
Ta tambaya yayin da take cire facemask, har Salma ta had'a gumi
"Dubi dubi dubi Karima."
Aunty Hauwa ta aje numfashi tana cewa.
"Kimin yadda zan gane Salma."
Cikin sarawar ciwon kai ta mika mata wayar tana karantawa sannan ta Dora mata da cewa.
"Tun asuba take kirana Karima ce ita ce 'yar yayar babanmu."

"Wannan zancen kuwa Salma gaskiya ne,? amma kirata kiji." Ta mika mata wayar
Karima ganin Shigowar kiran Salma yasa zuciyarta wani irin bugun tsoro da fargaba, ganin
koina ya tara mutane yasa ta shige lungunta ta shiga bandaki ta rufe, kafin ta d'aga kiran ya
katse, yana sake shigowa tai saurin d'aga wayar tsabar farin ciki yayin da Karima taji muryar yar
uwarta sai ga hawaye "Salma ni ce , ni ce nan Karima." Cewar Karima yayin da Salma tasa wayar a spiker
"Karima ya kike , ina kika samo ni da har kika san wannan zancen."?
Cikin kasa kasa da murya Karima ta ce . "Duk ba lokacin wannan maganar bane yanzu Salma,
kina ina ."?
Salma ta ce "Gamu mun kusa shiga Kano ."
Ajiyar zuciya Karima tai kafin ta ce . "Tom ina cikin tashin hankali Salma, kinsan Hadiza ko."?
Salma ta ce. "Wacce Hadiza Karima."?
"Hadiza RM marubuciya."
Dasss Salma taji a ranta , bayan Karima ta bata amsa.
"Eh Karima." Ta bata amsa jiki a sanyaye.
"Tom ita ta shirya yadda za a kasheki Salma da zarar kin shiga Kano daidai titin da ya shiga
gidan wannan redion, akwai wani da babbar mota ta shirya kasheki Salma."
Salma ta kalli Aunty Hauwa cikin matukar rauni da tashin hankali, Karima ta cigaba da cewa.
"Ba wasa nake miki ba Salma akwai hatsari a Shigowar ki Kano , akwai maganganu sosai."

Jin hakan yasa Salma cewa. "Tom ke Karima duk ina kika san wannan."?
"Ina auren yayanta Adam na yi aure Salma, gidanmu daya dasu , sun dawo sokkoto." Inji
Karima
Girgiza kai Salma tai tana cewa. "Gaskiya Karima hankali na ya tashi , me nai mata haka ."?
Da saurin baki Karima ta ce . "Salma ina ce kin yi cuta, kika makance kika kuturce , to wallahi
duk ita ce , duk ita ce ta aikata miki wannan bata kaunarki Salma."
Girgiza kai Salma ta sake yi cikin tsananin mamaki tana kallon Aunty Hauwa, duk sun kasa
cewa komai tsabar mamaki da rudanin da suka shiga , hakan yasa Karima sake fad'in."hello
Salma."

Salma tai ajiyar zuciya tana cewa. "Ina jinki Karima, abin ne ya bani mamaki, nasan cewa
Hadiza bata sona , amma ban yi zatan abin yakai haka ba , karki damu Karima, na gode sosai
yar uwata, zami waya ."
Karima ta ce ."Tom shi ke nan." Sai a lokacin Karima taji sanyi a zuciyarta da walwala

Salma ta kalli Aunty Hauwa da ta yi jimm tana cewa. "Aunty mene abin yi ."?
Kawai Aunty Hauwa ta ja motar suka cigaba da tafiya

Karima ba karamin farin ciki ta tsinci kanta ciki ba ,duk ta saki jiki sai annushuwa take , su
Hadiza an sha kunshi an yi kyau, har wasu kawayen ta marubuta sun zo domin ta ya ta murnar
aure, su Ruma ma an zo tun jiya aka yo Shigowar dare .


Gaban Salma matukar faduwa yake sosai ,haka suna cikin tafiya har suka hau kan wannan titin
da zai kaisu gidan wannan redionqq,ql1qadi , hakan yasa Aunty Hauwa ta tsaya domin karta
take shi, babu wanda ya fita cikinsu har wannan tsohon ya mike da sanda da robarshi ya matso
kusa da murfin kofar tasu yana fad'in. "A taimaka mana da na Allah da annabi, a taimaka mana."


MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 39&40

Wani iri Salma taji irin yadda wannan tsohon yake kallonta, juyawar da zatai ta ga wata babbar
mota ta yo kansu gadan gadan
Ihu Salma tasa tana cewa. "Wayyo Aunty Hauwa gata nan."
Sai ji suke "Tau tau tau 'dau ."
Karar bindiga ana harbata 'yan sanda ne da farin kaya .
Jin hakan yasa wannan mai shigar tsofaffi ya ke ce da gudu yana cillar da sandar, shima mai
tuka wannan babbar mota ya diro , Allah ya bawa wani dan sanda damar cafke shi , ya kaishi
kasa yana bangare shi tare da sa maka ankwa.
Salma matukar rudewa ta yi jin wannan karar ta bindiga, karo na biyu ke nan data ta'ba jin irin
wannan, sai da Aunty Hauwa ta nutsar da ita sannan ta dawo hayyacinta, domin tana ganin
kamar za a kuma irin lokacin da zata je Zaria, haka wannan 'yan sanda suka tafi da shi , duk da
cewa wasu sunbi dayan amma basu samu damar kamashi ba .
Haka su Aunty Hauwa suka isa gidan wannan redion, sai dai Salma duk ba a daidai take ba ,
har saida aka zubo musu shayi ,kana ta ga fuskoki kala kala suna kawo mata gaisuwa sannan
ta fara nutsuwa

Bayan wannan driver ya ci duka sosai , ya fara basu hakuri.
Sun yi masa jina- jina yaji jiki. "Zaka fad'a mini me ne ne yasa zaka kashe mutane har guda biyu
ko kuwa , daman ka saba kashewa ko." Cewar wani kofur din yan sanda dake rike da kulki .
"Wallahi yalla6ai ba haka bane , motar ma ba tawa ba ce dan Allah ku yi mini rai." Jin haka yasa
wannan kofur cigaba da lafka masa sanda ta koina.
Dpo ne ya tsaya daidai bakin kantar yana cewa'
"Kai kofur sani , sashi a bakin daki ."
"Okaysir ." Cewar kofur
Ihu wannan matashi ya saka yana cewa."wallahi yalla6ai zan fadi gaskiya, ku yi mini rai karku
rufe ni ."
Dpo ya ce .
"Muna sauraran ka ."
Yana haki kamar zai shid'e ya ke cewa.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login