Showing 18001 words to 21000 words out of 30722 words
Chapter 7 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf
zo ba , tun shekaran jiya na dawo , ammma babu kafar
ka cikin gidan me yake faruwa."?
Saida Aliyuu ya yi nannauyar ajiyar zuciya yana kallon matarshi, sannan ya ce .
"Baba , dan Allah ki zauna mi magana zaki fahimce ni ."
Tsawa ta daka masa da cewa.
"Ina wasa da kai Ali, wa ce ce wannan yarinyar kuma tana ina."?
Murmushi Fatima tai tare da nuna farin ciki.
"Abin da yake faruwa Baba, wannan yarinyar bata da lafiya tsawon watanni 3 yanzu ke nan."
Aliyuu suna tsaye kemm ya gama bawa mahaifiyarshi labarin Salma tun a ranar da ya ganta
kofar gidansa, har zuwa wannan ranar."
Salma dai tana daki tana kuka tare da tunanin idan tabar nan ina zata nufa a wannan
mawuyacin yanayin .
"Ina yarinyar take ."
Baba ta tambaya bayan ta gama sauraran labarin ta .
Da hannunsa Aliyuu ya nuna mata dakin Salma, kana Baba ta taka ta shiga dakin, suka bita a
baya .
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 27&28
"Assalamualaikum."
Baba ta fad'a tana shiga cikin dakin
Idanun Salma kamar mai gani cike da hawaye ta amsa sallamar
Baba ta dubi hannunta ta dawo ta dubi idanunta
"Innalillahi wa innailaihir rajiun."
Abin da ta fad'a ke nan ganin yadda Aliyuu yake bata labari lamarin duk ya wuce nan .
"Ba kwa gyara mata daki , dubi sai zarni, barinta kuke tai Kashi da fitsari anan ."?
Tai tambayar tana kallon Fatima
murmushin farin ciki ne ya rufe Aliyuu ganin yadda mahaifiyarshi ta fahimta, domin a kullum ita
ke fad'a masa ya yi adalci ya yi taimako tabbas zai ga cigaba a rayuwar shi .Gashi kuwa bata
ba shi kunya ba
Kusa da Salma ta matsa tare da d'ago ta suka fito waje, kai tsaye ta wuce ban daki da ita ,
ruwan zafi ta samu ta wanke Salma tass har kanta saida ta wanke , sannan ta debo kayanta
nan ma ta wanke su, bayan ta gama ta share dakin nata , ta yayyafa ruwa ta goge shi, sannan
ta shiga dakin Fatima ta dauko turaren wuta ta kunna cikin dakin Salma. Duk Aliyuu yana tsaye yana bin mahaifiyarshi da kallo ta gama wannan aikin, domin ta matukar
faranta masa rai sosai ba kadan ba .
Bayan duk ta gama wannan ta maida Salma daki, ita kanta taji dadin jikinta sai murna take tana
godiya.
Hatta wajen sana'arshi Aliyuu bai iya fita ba , saboda wannan yanayi
Baba ta zauna dakin Salma, Aliyuu ma ya shigo tare da Fatima tana ta fishi .
"Bazan iya dena godiya ba , na gode sosai Baba."
Salma ke nan
Murmushi Baba tai tana cewa.
"Babu komai yarinya, ai duk wanda ya taimaki wani , to shima Allah bazai barshi ba , sannan ni
suna na Baba Laure wato mahaifiyar Aliyuu, saboda haka ina nan zan kula dake harki samu
lafiya."
Jin hakan yasa Salma ta fashe da kuka
Aliyuu ne ya rarrasheta ya kwantar mata da hankali
Jimmm Baba Laure tai tana kallon Salma
"Baba ko akwai wani abin ne."?
Inji Aliyuu
Baba Laure ta d'ago kai tana cewa.
"Dama kin ta'ba yin irin wannan abin ne ko yaya."?
Salma tana share hawaye ta ce .
"A'a Baba, lokaci guda abin ya sameni ."
Jin amsar salma yasa ta kalli Aliyuu.
"Yanzu wanne maganin ake yi."?
Cikin karfin gwiwa ya ce .
"Baba wani magani ne , saboda munje asubiti har guda biyu , amma sun ce ba ciwon asubiti ba
ne ."
Baba ta girgiza kai tana cewa.
"To babu ko shakka wannan sihiri ne akai wa wannan yarinyar."
Gaban Aliyuu faduwa ya yi .
"Sihiri kuma Baba, me wannan yarinyar ta tsarewa wani ."
Baba ta ce .
"Aliyuu mu muka san duniya babu inda bamu shiga ba , saboda haka ina tabbatar ma wannan
sihiri ne aike ne akai mata."
Wani iri Salma taji a ranta , to waye zai mata wannan abin, babu wanda yasan da zaman ta,
tunanin da take yi ke nan
"To mene abin yi yanzu."?
Aliyuu ya tambayi Baba Laure
Girgiza kai Baba tai kafin ta ce .
"Akwai wani babban malami a Katsina naga irin yadda yake aiki sosai kan irin wannan matsalar,
indai ya yi maka magani baka warke ba , to tabbas cutar ajali ce ."
Rassss Salma taji a zuciyarta
"To mu kaita mana Baba."
Da sauri Baba ta kalleshi.
"Kai baka da hankali ina muka ga kudi , yana karbar kudade sosai."
Salma ta sauke ajiyar zuciya yayin da shima Aliyuu ya zube tashi
"To haka zamu barta yanzu ke nan Baba."?
Ya tambaya cikin damuwa
Kafin Baba Laure ta ce komai Fatima ta ce .
"To ai naga cewa tai Auntinta wata biyu zatai ta dawo, yanzu gashi har wata uku sai ta koma
garinsu ."
Aliyuu ya jefawa matarshi wani kallo
Baba ce tai magana da fad'in.
"Tom babu inda zata , mu zamu nemi kudin gurin yan uwa da abokan arziki ai mata magani,
yaushe kika zama mara tausayi Fatima, ke yanzu ace ke ce cikin wannna halin a dauke ki
akaiwa yan uwanki dadi zasu ji , bari wannan yarinyar da bata da gata sai Allah."
Salma tai kasa da kai tare da hawaye
Aliyuu ya yi murmushi ya ce .
"Allah yaja da ranki uwata , Allah sa aljanna makoma ."
Baba Laure ta ce .
"Amin dan albarka ta shi ka tafi wajen nemanka , nima zan fara samo wani abin."
Aliyuu ya ce ."To Baba nima akwai wasu sittiru na masu kyau, zan kaiwa Salisu mai dinki ya
siyar dasu , a yi a had'a kudin nan ."
Baba tai murmushi tare da fad'in.
"Yaron kirki ka gado mahaifinka, Allah ya jikanshi da rahma, Allah ya yi wa nemanka albarka."
Ya amsa da."Amin babata saina dawo."
Sannan ya wuce ya tafi
Sokkoto ❤️
Karima ce zaune cikin falonta, yau kimanin wata uku da kwanaki bata ganin posting Littafin
wannan marubuciya, har number ta ta dauka ta ce ."Aslm."
Ammma har yau babu alamun hawanta, sau da yawa tana gwada kiran number ta, amma bata
samu, tana tunanin ko a wanne irin hali take ciki Allah masani .
"Salamu alaikum Aunty."
Hadiza ta shigo ta zauna a kujerar kusa da ita , da sauri da firgita Karima ta tashi , sannan tai
ajiyar zuciya
"Wai Aunty tsoro na baki ne haba ."
Murmushi Karima tai tana cewa.
"Eh mana bansan kin shigo ba ."
Dariya Hadiza tai , sannan Karima ta zame ta zauna a kasa tana dafa kirjinta, domin ita Karima
yanzu tana matukar jin tsoron Umma da Hadiza, hatta hira bata sakewa su yi kamar daah.
Wayarta Hadiza ta cigaba da dannawa
Sai dariya take ganin irin yadda ake tambayar cigaban Littafin HIJIRA na Autar marubuta,
mutane ba adadi
"Aunty Karima sauran wata 4 fa biki, dazu sultan yake cewa na gashsheki, kin ga yadda ya kara
kyauu kuwa, gaskiya Germany ta yi, ya ce sai mun yi aure zamu koma tare ."
Murmushin yake Karima tai tana cewa.
"Tom Allah ya kaimu musha biki."
Kano State
Tarauni
Anan kuwa umman Salma ana zaune ana hutawa, an gyara gida , gida yayi matukar kyau sosai
, an sha kyau an gyara koina an yi fenti an sa tayil, har babbar waya Umar ya saiwa Umma,
suturu kuwa kala kala alhamdulillah.
Umma ganin karfe 4 ta yi yasa ta mike ta dauko redionta , kana ta kamo daya daga cikin tashar
da take yawon sauran.
"Assalamualaikum masu saurare yau zamu fara kawo muku sabon Littafi, duk da cewa ba
sabon Littafi bane a gurin mutanen da sukai following YouTube channel din mu , aje ayi
subscribe a danna mata kararrawa mun gode." Kana aka saki wani sauti mai taushi
Umma tana zaune tana kasa kunne domin jin an fara wannan labarin, tsabar kewar Salma yasa
Umma ta koyi sauraran novel, saboda Salma kullum sai tasa wannan redio ta saurara, daga
lokacin tafiyar Salma zuwa yanzu taji su da dama , kuma taji tabbas akwai Basira da tarin
nasihohi da tarbiya harda zaman ta kewa da ake dauka , ba kamar yadda Alaji Yusuf yayan
baban Salma ya fahimci marubuta ba .
"Fatima da zarah.
Mallakar Autar marubuta."
"Kashi na daya ."
Kan Umma ne ya sara mata, har saida tasa hannu ta rike , cikin wannna yanayin
Umma ta cigaba da saurarar labarin da aka fara shi da kasar saudiya.
"SAUDIYA."
"Dawowarsu ke nan daga asubiti , Najib da Ahmad tare da mahaifiyar su da bata da lafiya, eh
tabbas wannan iyalin kana iya ganin tsantsar soyyayar mahaifiyarsu..."
Umma ta kasa kasa kunne don jin yadda wannan labarin zai kasance....
Autar marubuta
MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________
Page 29&30
Baba Laure ce zaune tsakar gida tana yi wa Salma kitso, zanen hausa take rangada mata a
kanta mai matukar kyau, gefe guda kuma ga Fatima can tana iza wuta
Aliyuu ne ya shigo yana yin sallama, murmushi ya jefawa mahaifiyarshi da cewa.
"Babata ta kaina." Kana idanunsa suka kai kan Salma idanunta sama kamar shi take kallo, sai
dai bata iya ganin komai.
Shagala ya yi da kallon Salma irin yadda wannan kitso yayi matukar fito da kyawunta "Allah ya
yi halitta, kodai kyan wannan yarinyar ne yasa akai mata wannan sihiri."
Abin da Aliyuu yake fad'a ke nan a zuciyarshi, ganin yadda ya shagala da kallon Salma yasa
Fatima ta taso ta bangaje shi ta wuce tana harararshi.
A wannan lokacin ya dawo hayyacinsa yana murmushin ya'ke
"Tom mene ne ya dawo da kai ne ."?
Cewar Baba Laure, saida ya sosa 'keya sannan ya iya cewa.
"Baba daman kawu Tanimu ne ya kirani , ya ce ya turo dubu 20 a had'a ai wa Salma magani ."
Baba Laure ta ce .
"To Masha Allah, Allah ya saka muna godiya, amma banda abinka basai ka bari saika dawo ba ,
sai kawai ka kamo kafa ka taho ."
Ya murmusa yana sunkuyar da kai
"Da Allah kama hanya ka tafi mana, kasan muna neman kudi gashi yanzu har an sake wata
guda wannan kudin basu hadu ba ."
Wayar Aliyuu ce ta fara ringin , yasa hannu ya cirota a aljihunansa
Dariya ya yi yana cewa.
"Baba mutuminki ne Sa'adu yake kira." Ya d'aga wayar yana sata a spiker Baba tana dariya
"Salamu alaikum."
Sa'adu ya yi sallama, Baba ce ta amsa masa tana cewa.
"Sa'adu ya gidan ya katsina."
"Sa'adu ya ce lafiya lau babarmu ya mutanen gidan."
Ta ce .
"Alhamdulillahi Sa'adu ya manyan naku."
Ya mayar mata da fad'in.
"Lafiya lau, daman na kira na fad'a miki ne gobe Malam Shafi'u zai tafi Niger, to naji kuma kina
cewa zaku kawo yarinya ai mata magani, nace bari na sanar dake."
Da sauri Baba Laure ta saki kan Salma ta mike tsaye tare da cewa.
"Niger zai tafi gobe kuma ."?
Ya ce .
"Eh wallahi Baba Laure."
Ta ce ."To shi ke nan Allah ya kaimu goben." sannan sukai sallama ya kashe , cikin tashin jin
dadi Aliyuu ya ce .
"Tom Baba mene abin yi ."?
Ta kalleshi da cewa.
"Mene abin yi kuwa Ali , yanzu yanzu sai Allah zamu tafi katsinan , kaje tasha ka samo mana
mota ."
Zaro ido ya yi yana cewa."Yanzu kuma baba kudin fa basu hadu ba ."
"Babu wannan zancen Ali , tashi Salma."
Ta d'ago Salma tsaye
"Kaje ka samo mota , kudin ko a can zasu hado."
Aliyuu ya juya da sauri yana cewa.
"Tom bari na samo mai motar."
Masha Allah Hadiza an yi kiba bulbul, sai shirin aure ake , irin yadda take son Sultan ba a cewa
komai , mu dai sai dai mu ce Allah sa a yi damu wannan gagarumin biki .
Washe gari
Katsinawan dikko, kunya gareku badai tsoro ba
A daren jiya su Baba Laure suka isa garin Katsina, aiko gari yana wayewa tun asubar farko
suka nufi gurin Malam Shafi'u, sun tarar da layi sosai kafin a zo kansu .
Bayan Malam Shafi'u ya ga Salma ya tabbatar musu sihiri ne gami da aiken àljanu akai wa
Salma.
Sai dai Salma abin yana matukar bata mamaki, wane zai mata sihiri a wannan duniya me take
dashi
Malam Shafi'u ya debo ruwa cikin wani 'ko'ko , kana ya zuba ganyen magarya ciki, ya kaishi
gaban Salma tare da fad'in.
"Karanta ayatur kursiyu ki tofa a ciki ."
Kamar yadda ya bukata haka Salma tai kana bayan ta gama ya ce tasa hannayenta a ciki,
bayan ta zasu ya dauki carbi yana ta ja , ko mene yake cewa Allah masani
"Rufe idanunki."
Ya fad'a
Ta rufe , cigaba ya yi da jan wannan carbin wajen minti talatin, daga bisani ya fara karanto wasu
ayoyi da surori cikin Littafin Allah mai girma.
Kuka Salma ta fara yi , sakamakon irin zafin da take ji a duk jikinta, jinta take kamar ba ita fa ,
wajen awa daya da rabi sukai a haka , sannan ya ce ta cire hannunta ciki, ta cire aka dauke
'ko'kon daga gun
Hannu Malam Shafi'u ya d'aga sama yana addu'a yana kuka
Shi dai Aliyuu yau yana ganin abin mamaki, ita ko Baba Laure ta saba ganin wannan lamarin
tun tana karama
Bayan ya gama wannan addu'a ya aje carbin a gefe ya kalli Baba Laure yana cewa.
"Wallahi aike ne , sai dai mu munfi karfin duk wani àljani , da ikon Allah da manzonmu
Muhammadur...."
Baba ta girgiza kai
Mikewa ya yi ya debo wani kullin magani guda biyu, ya mikawa Baba.
"Ku karbi wannan, saboda tsarin jikinta ga duk wani shedani, sannan a ja mata kunne ta dage
da addu'a."
Tasa Hannu biyu ta amsa tana cewa.
"To malam."
"Sannan kuma zatai cuta mai tsanani sosai, daso samu ne yau ku koma Bachin, sai dai in baku
koma ba babu matsala, amma idan aka koma zai fi."
Baba ta ce .
"In Sha Allahu kuwa daga nan sai gida."
Ya kallesu yana cewa ku je waje ku jira ta
Su baba suna fita minti biyu, me yayiwa Salma Allah masani , ta mike ta fito idanunta a bude
hannayenta sun dawo daidai.
Kuka ta fashe dashi yayin da suka had'a ido da baba Laure, Salma ta zube kasa ta sume .
Bayan kwana biyu
Bauchi
Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah, sai dai godiyar Allah, Salma a halin yanzu tana shan
jinya Sosai da sosai, domin yanzu haka jini ake kara mata
Irin yadda Fatima take ganin ana kulawa da Salma sai duk tsantsar kishi yake damunta, domin
tana ganin karshen wannan lamarin to Aliyuu auren Salma zai .
Bayan an cire mata wannan Karin jini bacci ne ya kwashe ta , ba ita ta farka ba sai karfe 9 na
dare, abin yana matukar bawa Salma mamaki, wai idanunta sun dawo daidai, hannunta ma
babu abin da bata yi dashi , duk da cewa tana cikin jinya Sosai amma idan ta dubi yadda take
tana jin dadi ta gode Allah. Bayan ta tashi tashi aka bata ruwan zafi tasha, kana aka soya mata kwai kamar yadda ta nuna
tana bukatar ci .
Har kowa na gidan ya yi bacci, amma bata iya baccin nan ba , farin ciki da mamaki, bata ta'ba
zaton zata tsinci kanta cikin wannna yanayi ba .
Washe gari da safe , Baba Laure kamar wacce ake kora, tai wanka ta hado kayanta , tana
gama karyawa ta ce yau sai gida , tsakar gida ta fito rike da jakar kayanta, hakan yasa duk suka
fito
"Baba yanzu fa karfe 8:45. Dan Allah ki bari rana tayi , ina nan ina gidanki." Cewar Aliyuu
Baba ta ce .
"Tom ai kaji mene ka ce , ina nan ina gidana, daman jinyar wannan yarinya ce ta zaunar dani."
Ta nuna Salma
"Yanzu kuma jiki Alhamdulillah zan koma zuwa gobe ko jibi nazo naga jikin nata ."
Salma durkusa wa tai gabansu tana cewa."Baba hakika kun yi mini abin da bazan ta'ba
mancewa ba , kuma kun yi mini sanadin farin cikin da bazan ta'ba gushewa ba , bani da abin da
zan gode muku , Allah yabar zumunci ya bani ikon saka muku ."
Murmushi Baba Laure tai tana cewa."Karki damu Salma, ki ci gaba da kula da kanki, idan kinji
sauki kuma sai Ali ya kawoki gidana."
Salma ta kalli Aliyuu tana murmushi da fad'in.
"In sha Allah kuwa zan zo Baba."
Baba ta ce .
"Masha Allah, yarinya mai hankali da tarbiya, kowa zai so kizo a sirikarshi ko yarsa."
Salma ta sunkuyar da kai.
Wani mashi Fatima taji ya sokar mata zuciya, sabuwar kiyayyar Salma taji ta sake samun guri a
zuciyarta
Nan Baba tai sallama dasu kana ta wuce gidanta
Salma shigewa daki ta yi ta samu guri ta zauna
"Idan har sihiri akai mini wannan abin ya faru dani , to wane ne ? Na baro gida , kan karamin
dalili,kamar dai mara hankali."
Maganar da take cikin ranta ke nan sai ga Aliyuu ya shigo , matarshi Fatima dake biye dashi ta
tsaya kofar dakin
"Salma ya jikin."?
Salma cikin girmamawa ta kalleshi da cewa.
"Da sauki Yaya Aliyuu."
Ya zura hannu a aljihunansa yana cewa."Allah ya kara lafiya."
Wata kifat din Tecno ya zaro ya mika mata, kana ya mika mata sauran SMS dinta guda biyu da
ya shigo dasu .
"Ga wannan wayar second ce , ki yi hakuri da ita sai kisa layukanki ciki ."
Hannu biyu tasa ta karba tai godiya tana cewa.
"Na gode Yaya, Allah ya saka da gidan aljanna."
Sannan ya fice ya tafi
Cikin farin ciki Salma ta bude wayar tana