Showing 12001 words to 15000 words out of 30722 words

Chapter 5 - Marubuciya Complete Hausa Novels by autar Marubuta .pdf

mu da sharrin hajjiya Aisha."

Matar tashi ta amsa da
"Amin dai wallahi, ai ni tunda ta d'aga hannu zata mareka na tsani matar nan , banda ma ta'be

wa irin tata , mene na zama a gidan babu d'a babu jika."

Ya ce .
"Allah dai ya kyauta."




Fitowarta daga bandaki ke nan Hadiza, ta ajiye buta kana tayi mika
Karima ta kallah dake gefen mahaifiyarta tana cewa.
"Aunty Karima naga fa yau duk sai a hankali ke , kodai kodai an samu karuwa ne ."

Cikin yanayin mutuwar jiki Karima ta ta'be baki tana cewa.
"Hmmm."

Umman ta ta ce .
"Kyaji dai da rashin kunyarki."
Hadiza ta ta'be baki tana cewa.
"Kai Mama kwana nawa ne na bar miki gidan , kinga dai Sultan ya turo, yana dawowa zaku sha
biki ."

Da gudu Hadiza ta fad'a daki jin wayarta na ruri.
Karima kam ta tashi ta shige lungunta domin sam yau bata jin dadi , ta dauki wayarta da nufin
zuwa tirkot tai kalloh .


Bayan Hadiza ta dauki wayar cikin raha ta fara cewa.
" 'Kawata Ruma kwana biyu ya garin ko online bana ganinki."

Daga can bangaren Ruma ta amsa mata da cewa .
"Ai baki da mutunci wallahi, sati biyu ke nan da sace min waya."

Hadiza ta ce .
"Ohh Allah sarki Allah maida alheri, ke yarinya an sa mini rana fa ."

Dariya Ruma tai tana cewa.
"Kai haba dan Allah ki ce lokacin zuwana sokkoto ya yi , da Sultan din aka sa ."?

Hadiza ta ce .
"Kwarai kuwa yaron hutu ba , ai yana dawowa daga Jemani zaku sha biki."


Ruma ta ce .

"Tom Allah ya kaimu kawata gaskiya ina missing dinki da novels dinki ."

"Yawwa kin ga wata marubuciya Autar marubuta, Littafin ta na Fatima da zarah, kin tuna Littafin
da Salma ta taba yi, shegiya ashe satar ilmi take ."


Dariya Hadiza ta kwashe da ita tana cewa.
"Aiko na gani , na rasa inda nasan Littafin to Allah ya kyauta ko ta dawo garin ne ."


Ruma ta ce .
"A'a wallahi , an yi nisan kiyo ai waya sani ma ko karuwanci ta tafi kuma dazu babansu ya rasu
."

Hadiza ta ce .
"Tab to Allah ya kyauta."


Tunda Karima ta bude data ta ci karo da rasuwar kanin babanta wato Malam Aminu, nan ta
shiga cikin firgici da tashin hankali, Allah sarki Malam Aminu Allah jikan wanda muka rasa ,
Allah yasa mu yi kyakykyawan karshe isar annabi Muhammad.



Anan kuwa umman Salma an sha kuka an more , gashi har dare ya rufa , yau dai Malam Aminu
Allah ya yi , yabar mana duniya, shima Umar ya shiga yanayi mai matukar girma domin lamarin
babu wanda bai girgiza ba .
Haka Alaji Yusuf abin dai ba a cewa komai. Allah ka jikan wanda suka rigamu gidan gaskiya.


Karfe 10:02 Salma na zaune kan gado tasa laptop a gabanta , typing din ma yaki yiyuwa, samm
ta rasa inda yake mata ciwo, komai bata jin dadinsa , domin hatta abincin dare bata iya ci ba
"A gaskiya ya kamata na koma gida, nasan na yi rashin hankali ku gafarce ni Umma."

Ta fashe da kuka yayin da take maganar a cikin zuciyarta

"Allah ne yasan halin da suke ciki, tabbas ni Mahaukaciya ce."
Ta sake fashewa da sabon kuka, tunanin gida Salma ta ringayi a daren yau, ta kasa aikata
komai domin tana tunanin ya kamata ta koma gida, ko dan tafiyar da Aunty Hauwa zatai ta
barta, haka har bacci ya dauketa a wannan wajen.


Yau da asubar fari Karima da mijinta suka tafi Kano, Umman Hadiza ta ce idan sun isa sai a kira

ta tai musu gaisuwa.

Gida ya cika da maza da mata masu shigowa suna yin gaisuwa, idan Umma ta tuna babu
Malam Aminu babu Salma sai ta sake shiga cikin tashin hankali da matukar rauni.

Allah ya horewa Salma saurin typing da hikima cikin rubutu, hakan yasa marubuta da yawa
suke zuwa domin su yi Littafi tare .Tana daukar wayarta Facebook ta shiga kai tsaye , bayan ta
ga yadda akai mata comments sosai yasa ta fito domin gamawa da na WhatsApp.
Wata number ce mai 56 karshe ta fara bude sakonta.
"Ke Mahaukaciya karuwa kawai, kina tunanin ban gane ki ba ne , wawiya mara hankali."

Abin da Salma ta gani a rubuce ke nan, mamaki ne ya rufe ta tare da tunanin tabbas wrong
number ake nema akai mata magana.

Autar marubuta ce .

https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I

*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~


Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 19&20

Salma jimm ta yi tana tunanin wannan sako, ba tare data fice daga ciki ba , hakan yasa ta sake

ganin shigowar wani sakon .

"Kina magana da Hadiza RM, kin gudu daga gidanku to asirinki ya tonu."
Salma ta sake karantawa
Hadiza kuwa Shahada kawai tai ta tura wannan sako ga Autar marubuta, domin bata da
tabbacin Salma ce , sai dai wannan Littafin na Fatima da zarah yake bata yakinin wannan
Salma ce , idan kuma ba ita bace hakuri Hadiza zata bata kawai.
Murmushi Salma tai kafin tai mata reply ta ce .
"Lallai yarinyar nan ta ya ta gano ni , tabbas Hadiza bata kaunata, ai ba komai bane danta gano
ni , daman gida zan koma ."

Typing Salma ta fara mata tana rubuta .
"Hmmm."
Abin data tura mata ke nan

Ran Hadiza ya baci da ganin wannan reply, hakan yasa ta sake tura mata da cewa.
"Karki damu, ni bazan tona miki asiri ba, amma ki sani nayi miki nisa nayi miki rata, alkalamin ki
bazai ta'ba taddo nawa ba ."

Ta tura mata, sannan ta shiga channel din Salma wanda ta ga an yi sharing dinsa a group
dinta,abin da ya fara d'aga wa Hadiza hankali ganin tarin followers dake wannan channels sun
ninka nata sun kuma ninkawa , tsaki tai ta fito daga ciki ,kana ta goge Link din a cikin group
dinta sannan tai remove din wacce ta turo . Salma kam kawai sakon ta bude tai shiru ba tare da amsa ba , hakan yasa Hadiza ta gamsu
Salma ce .

Wata wutar kiyayyar Salma ta sake ji tana ruruwa a zuciyarta, ganin yadda Salma take matukar
samun masoya da yadda ake son Littafin ta .

"Na tsaneki Salma, bana kaunarki wallahi, ni ce ajalinki duk inda kike anan zaki mutu, dani kike
zancen."
Sannan ta rafka wani uban tagumi tana tunani
Umman ta ce ta shigo dakin tana cewa.
"Lafiya Hadiza."
Hadiza ta d'ago kai cikin rashin jin dadi tana cewa.
"Dazu Inna ta kira waya , ta ce ba yanzu zata dawo ba tana gidan Baba Musa , Yayan baban
yayaUmar ."

Umman Hadiza tai dariya da cewa.
"Allah sarki Inna masu yaya da yawa."
Hadiza ta sake zabga tagumi, ganin halin da take ciki yasa Umman ta cewa.
"Wai lafiya Hadiza na ."
Hadiza tai nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce ."Umma burina zai lalace, kinga kudin da nake

samu zan dena samu , sannan shaharar da zan yi ita ma lalata min ita za tai."

Ta'be baki Ummanta ta yi , kana ta ce .
"Wa ce ce kuma ,me yasa zata miki haka."
Hadiza ta ce .
"Hmm Mama akwai matsala dai kawai , shi ke nan tawa ta kare , kudin da muke dan samu ma
yanzu ba zasu zami ba ."
Umman nata ta rike kugu tare da fad'in.
"Tab aiko ta yi kadan, batasan dawa take yi ba , shirya yanzu muje wajen Malam Zarto, kafin ta
hanaki ke kin hanata."
Hadiza tai jimm kana ta kara da cewa.
"Allah ko Umma, amma zaki gane gun Malam din."?

"Ayyuririri."
Umma tai bud'a sannan ta kuma cewa.
"Ke Hadiza nifa haifaffiyar sokkoto ce , kina gani nan nayi aure, har na haifi Adam , abin da ya
kaini zaman Kano auren babanki ne , kuma bayan babu shi ,gani na dawo sokkoto, mu muka
san koina shirya kawai."
Tana gama magana ta fad'a daki
Kafin Hadiza ta motsa daga inda take sai ga sallamar Karima
Murmushi Hadiza tai tana cewa.
"Ahh mutanen Kano an yi 7 an dawo sannu da zuwa Aunty."
Karima cikin gajiya ta aje jakar dake hannunta tana cewa.
"Yawwa sannu Karima ina Umman."?
Hadiza ta kalli kofar dakin Umma kana ta ce .
"Yanzu ta shiga daki, shima Yaya Adam bai dade da fita ba , yau ba shi da aiki ."
Tana gama magana Umma ta fito da fad'in.
"Sannu da hanya Karima ya aka ji da karin hakuri."?
Karima ta ce .
"Mun gode Allah Umma wani gun zaki ne ."?
Ta tambaya ganin ta sako takalmi da hijabi
Hakan yasa Hadiza ita ma ta dauko nata hijabin...

Gombawa d'ibar fari , ba a kwana daku ba an tashi daku

Ta shirya tsaf Aunty Hauwa, domin har tasa akwatin ta a mota ,sun fito harabar gidan ana
bankwana jikin Salma a matukar mace da kasala
"Aunty har wata biyu."?
Abin da take ta fad'a ke nan tun jiya da take tayata shirya kaya
Anas ne ya ce .
"Ni fa Aunty har airport zan kai ki , saina dawo da motar ."
Aunty Hauwa ta ce .
"A'a rufa mini asiri inà ka iya wata mota , acan gun aiki zan barta kayi zaman ka ."

"Ni fa gaskiya Aunty zan raka ki ."
Ta sake fad'in.
"Anas muna da yawa fa ka barshi."
Ya shige gaban motar yana cewa.
"Ni dai sai naje har sai naga tashin ku."
Aunty Hauwa tai dariya da cewa .
"Tom ai shi ke nan."
"Tom ni zan koma ciki, Allah ya tsare Hauwa aje lafiya a dawo lafiya sai mun yi waya ."
Cewar hajjiya Aisha
Ta maida mata da cewa.
"Tom mommy nagode zan yi kewarku."
Kana tana murmushi da d'ago hannu hajjiya Aisha ta koma ciki

Falll hawaye idanun Salma ta kalli Aunty Hauwa.
"Haba Salma kuka zaki kuma , kar ki yi dan Allah."
Ta fara rarrasheta, Salma cikin kukan ta ce ."wallahi Aunty baza ki gane ba amma Allah ya
dawo dake lafiya."
Kafin ta bata amsa Saida ta duba agogon hannunta kana ta ce .
"Yawwa Salma sai mun dawo, idan akwai wani abin ki kirani, idan mun je zan kiraki , sannan na
tura miki dubu 30 a opay din ki."

Salma ta ce .
"Tom shi ke nan na gode Aunty."
Ta shige motar suka tafi tare da Anas tana musu bye-bye.

Su Hadiza suna tafiya suna hira har suka isa suna zuwa suka shiga ciki , kamar yadda ya
bukaci su zauna kan wata tabarmar kaba ,nan suka zauna kana ya saka hularshi ya dauki carbi,
sannan kasar dake gabanshi yasa hannu ya share samanta , sannan ya d'ago ya kalli Umma.
"Kwana biyu Mero, shekara da shekaru."
Umman Hadiza tai murmushi da cewa.
"Lafiya lau ai kasan mijina ya mutu, tom sai muka koma Kano."
Ya ce .
"Allah sarki mijinta ce baban Adam ."
Umma ta ce .
"Yawwa akwai abin da ke tafe damu."
Tasa hannu ta dunguri Hadiza alamun tai magana
"Ita ma wannan yarki ce , naga Kun yi gama wajen idanun."
Ya fad'a yana dariya
Umma cikin raha ta ce .
"Ehhhh."
"Tom yanzu me kuke so a yi ."?
Ya tambaya
Hadiza ta ce .

"Akwai wata da nake so a tabbar min tana raye kota mutu . Kuma a wanne hali take ciki."
Ya shafa saman kasar tashi yana cewa.
"Ya sunanta dana babanta , awanne gari take."

"Sunanta Salma Aminu, tana garin Kano karamar hukumar tarauni."

Ya rubuta Salma Aminu kan kasar tare da wani jagwalgwalon rubutu.
Jimm ya yi yana kallon kasar , daga bisani ya d'ago yana cewa.
"Sunanta Salma Aminu Waziri, wacce ake kira da Autar marubuta, kuma yanzu haka tana cikin
garin Gombe."
"Cikin daula da wadata."

Da sauri Hadiza ta kalli Umma jin ya bayyana Salma, domin tabbas tuaninta , ya zama gaskiya
"Me kuke so a yi mata yanzu, ko kuna so ta dawo inda kuke ."?

"Ahhhhhh."
Cewar Hadiza
"Kawai dai ina so a hanata sukuni , kuma wannan rubutun ta dena yi , a makantar da ita kuma a
kuturtar da ita ."
"Makanta da kuturta ko."?
Ya fad'a
Hadiza ta ce.
"Eh."

Ya shafa kan kasar tashi , sannan ya ce .
"Zaku kawo kofaton jaki guda daya , da kuma idonsa guda daya."

Hadiza ta kalli Umma


Ina cigiyar book dina na DAJIN MUTUWA

Autar marubuta
07040805269
WhatsApp only

https://whatsapp.com/channel/0029VasuzYr6rsR0bxO94J1I
*SADAUKARWA GA Marubuta masu tsaftataccen alkalami*✍️

Kaggagen labari ne ✍️

A yi hakuri masoya wanna lokacin ma babu editing❌
~Ba labari ba ne mai tsayi~

Autar marubuta ce
MARUBUCIYAR .....
Gubar rayuwata
Kawar karuwai
Dajin mutuwa
Fatima da zarah
Mahaukacin so
Dangin dalas...

MARUBUCIYA ✍️
Na
Autar marubuta
________________________________________

Page 21&22

Tunda Salma tai alwalar magariba ta shiga daki ta kulle, duk da cewa tunda Anas ya tafi raka
Aunty Hauwa bata sake jin motsinsa ba
Wajen karfe 8 taji ana kwankwasa mata kofa .
"Waye ."?
Suwaiba dake tsaye kofar dakin ta ce .
"Ni ce nan hajjiya ce take kiranki a falo."
Salma ta ce .
"Tom gani nan ."
Ta tashi tasa hijabiinta kana ta fita zuwa falon , tana zaune ta harde a kujera, ganin wannan
yanayi yasa Salma ta durkusa a kasa tana cewa.
"Gani hajjiya."
D'ago kai ta yi , sannan ta ce .
"Ki tattare kayanki a wannan daren kibar gidan nan ."
Dasssss
Zuciyar Salma ta bayar
"Mommy ina zani kuma."?
Cikin tashin hankali Salma tai maganar
"Ki tafi duk inda zaki je mana, wannan gidan daga ni sai my son dan kuwa na sashi a kasuwa ,
gobe da safe muma zamu tashi ."
Jin hakan ya sake sa Salma cikin tashin hankali
"Assalamualaikum."
Anas ya shigo rike da wayoyi guda biyu a hannunsa, guri ya samu ya zauna yana cewa.
"Mommy kin ganni sai yanzu ko, ai yanzu ma sun je, har airport naje ."
Hajjiya Aisha da duk hankalinta ke kan hannun Anas ta ce .
"Ya nake ganin kamar wayar Hauwa kuma."

Salma ta kalli hannunsa
"Eh mommy wayar ta ce wallahi, sam'bad'ota nayi , wannan wayar ta kai dubu dari biyu da
hamsin , nasan tun a jirgi zata neme ta, sai sun sauka ta ga babu ita ."

"Innalillahi."
Salma ta fad'a a fili ba tare da tasan sautinta ya fito ba
"Wannan yarinyar me take yi anan ne."?
Anas ya tambayi hajjiya Aisha
"Na ce ta kwaso kayanta tabar gidan nan , shi ne take mini gaddama da futsara."Mommy ta ba
shi amsa

Cikin hassala ya mike tsaye tare da fad'in.
"Zaki tashi ko kuwa yar mutumarrr..."
Da sauri Salma ta nufi daki ta fara had'a kaya tana zu ba wa a cikin jaka , tasa laptop da
wayarta , hijabi kala biyu kawai tasa sai wasu dogayen riguna guda biyu, sai ga Anas ya shigo ,
firgita ta yi da gudu ta dauki jakar ta fice , haka ya biyo bayanta har waje .
"Ke garin nan ma zaki bari yau din nan kuwa, muje bakin titi."
Cikin tsoro ta bishi , bakin titi yaje ya tsaya tare da ita , ammma babu wata mota da take
tsayawa ,ganin ya gaji yasa ya tsayar da irin babbar motar nan wacce take cike da shanu .
"Yaa mai gida dan Allah kara mini wanna yarinyar mana ka sauketa duk inda ka tsaya."
Ya mika masa wasu kudade .
"Ni fa Bauchi na nufa kai tsaye."Cewar mai tuka babbar motar
"Ehh ba matsala ga wannan kasa mai."
Ya karba Salma ta fashe da kuka , haka ta hau gaban wannan mota daga ita sai mai tuki sai
shanu ga dare yayi, kana ya tuka motar suka tafi
Kuka Salma ta ringa fasawa a wannan lokacin, sai dai bai ce da ita komai ba kawai taba yake
sha abinsa .
Haka suka tafi kwana tafiya, wajejen karfe 5 na asuba wannan mutum ya karasa Jahar Bauchi,
sauke ta kawai ya yi yanufi cikin kasuwa.
Cikin tashin hankali Salma tana kuka ta rasa meke mata dadi, ta fara tafiya har ta fara gano
gidaje
Wani kofar gida kawai ta samu ta zauna, babu abin da take so illar a halin yanzu ta koma gida,
sai dai rashin kudi, samm ta manta da kudin da Aunty Hauwa ta ce ta tura mata .
Kiran sallar asuba aka fara , sai dai sai kuka take Salma domin babu inda ta sani , ana cikin
haka sai ga wani saurayi ya fito daga kofar gidn da take zaune, bai ce da ita komai ba , kawai
ya wuce masallaci yana tafiya yana waigenta , dawowa ya yi saboda yana tunanin zata shiga
gida tai masa sata. "Ke me kike yi anan ne tashi ki bar mini kofar gida." Ya fad'a cikin masifa
Mikewa tai Salma cikin kuka tana magana tana hardewa .
"Dan Allah ka taimaka mini wallahi nasha bakar wahala, babu wanda na sani anan , daga
Gombe nake , tun daga Kano nake haduwa da jarabawa babu yadda zan yi ka taimaka mini."
Ta kai kasa tana kuka, tausayin ta yaji ya rufe ta sosai , hakan yasa ya ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login