Showing 1 words to 3000 words out of 47460 words
INDA RAI
BOOK 2 PAGE 1
AYASHA ALIYU GARKUWA
Yar uwa kinsan illar dake tareda infection kuwa,to bari kiji kadan daga cikin illar da infection
yake da ita,kinsan cewa infection yana hana haihuwa,yana hana ma'aurata jindadin mu
amala,yanasa warin gaba kowane irin tirare kika sa bazai hana wannan warin fita daga jikin kiba
fitar farun ruwa kaikayin gaba tusar gaba duk suna daga cikin illar da infection yakewa lfyr ki. Ina masu fama da ulcer, Asthma,sickle, ina matar dake fama da fibriod, matsalar rashin
haihuwa ko bushewar jiki da fata haddake mai son hibs da breas ina uwar gida maison faranta
ran oga a othe room kema ba abarkiba jawarawa da yanmata ku garzayo kuma ku kwada ku
gani da ikon Allah da izinin Allah munada VIP chair akwai blood circulatory machine kedai kira
number nan domin karin bayani 07035275119 ko kiyi joining group dinmu dan gani da ido sai
kunzo ngd https://chat.whatsapp.com/LqcXIrhogcQC1iLdGGNJcZ
Spjg
“Ban fahimci me ɗaya kake son bayyana mana ba Tajudden kana neman mu baka izinin fara
neman Mamana ne ko,ko kana gabatar da soyayyar kane? Ko neman Aurenta kakeyi gaba
ɗaya!?”.
Ya kai karshen maganar yana kallon Taj kallon cikin ƙwayar Idanu saboda tuna cewa shin
meyesa Tajuddeen bai zo da iyayensa ba saboda duk cikin falon baiga ɗaya daga cikin wanda
zai iya kasancewa mahaifansa tunda dai yasan shi ɗan ƙasar Ethiopia ne waɗanan kuma duk
yasan mutanen ƙasarmu be kuma sanannun ma, sai kuma ya juya idanunsa ya kalli Tajj jin
yana cewa.
“Duk abu uku nake haɗewa awaje ɗaya Uncle Bello idan zan samu duk abinda kuka min akai ku
mallaka min Ishmah shine burina da Fatana shine kaɗai abinda zai samar min nutsuwa ita kaɗai
ce zata zame min tsagi da zai cike gurbin da na rasa, itace kuma zata zeme min inuwa da zan
samu in fake”. Cikin rashin walwala da jin wani irin kallo mai nuni da bincika yace.
“Kuma sai gashi banga waliyyanka ba ko kuma ince magabatan kaba”.
Cikin sauri Sheikh Tijjani Taju Usman Bauchi yai gyaran murya wanda shine Babban ɗa ga
Sheikh Tajuh Usman yace.
“Gamu nan mune matsayin waliyyansa kuma magabatansa kuma shaƙiƙansa”.
Anutse Abba ya gyara zamansa tare da sakin wani lallausan murmushi.
Atare suka juya suka kalli Sheikh Tajuh Usman Bauchi jin yana cewa
“Ni da kaina zan wakilci Aurensa sannan in daura auren zan kuma yi farin ciki idan kuka bashi
Auren Ishmah zan kuma shugabanci al'amarin in shige masa gaba akan komai saboda
matsayinsa mai girma ne awajena nima kuma matsayina halattaccene a wojensa”.
Cikin sanyi suka sauƙe numfashi sai kuma suka kalli juna tare da yin ƙasa da kansu jin Dottijon
nayi musu kalamai masu kama zuciya.
Cikin sanyi suka fara yunkurin miƙewa tsaye jin Sheikh Taju Usman Bauchi na cewa.
“Ku tashi mu tafi saboda lokacin sallah ya ƙara to”.
Daga nan suka fita suka bar gidan...
Acan cikin gida kuwa Ishmah ce zaune a falo yayin da akwatina set biyu ke gabanta set ɗaya
Maroon color set ɗaya Milk color suna zaune ta juya ta kalli Aunty Nana tare da jan gajeren
tsaki saboda wani irin iska mai sanyi da take ji yana ratsa jikinta haka nan kawai take jin
zuciyarta yana mata sanyi haka gangar jikinta yayin da jikinta ke amsar baƙon yanayi wanda
yafi kama da samar da nutsuwa da kwanciyar hankali wanda batasan sanadinsa ba cikin sanyi
tace.
“Aunty Nana ki gani fa har yanzu babu wanda yazo kuma fa sun san munyi dasu ƙarfe uku
zamu tafi mu kai kayan saboda mu samu kafin huɗu mu dawo muyi sallar la'asar agida kuma
har yanzu basu zoba”.
Juyawa aunty Nana tayi ta kalleta tare da cewa.
“Wallahi fa nima abinda nace kenan?,Shiyasa ma kika ga nayi abinci da yawa saboda ina
tunanin za'a zo muci abincin rana ne anan kafin mu tafi”.
Maryam dake shigowa ne ta karbi maganar da cewa.
“Ai dama sai da nace miki Kada kiyi wani abinci ki wahalar da kanki saboda Nasan da wuya azo
da wuri kasancewar yau juma'a kuma in munje can ma Nasan abubuwan da zasu bamu in mun
dawo shi za'a cicci abinci anan shiyasa ni ban shiga kitchen Bama”.
Ta ƙare maganar tana zama gefen Ishmah.
Dariya Rahama dake fitowa daga bedroom tayi tare da cewa.
“Ke dai Aunty Maryam kina nan wani lokaci idan mutum yace Miki marowaciya bai kyauta ba
kina nan kamar Gajimare saboda kyauta, wani lokaci kuma in kinyi magana kamar ta
marowata”.
Murmushi Maryam tayi kana tace.
“In kinga dama ma kice ni marowaciya ce”.
Dariya Rahama ta sanya tare da faɗin.
“Kuma kona faɗa babu yanda zakiyi dani tunda nice Autah shiyasa nake fadan abinda naga
dama kuma in kwana lafiya”.
Murmushi sukayi dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamar Garkuwa.
Cikin jin daɗi da farin ciki Ishmah ta miƙe tare da amsa mata sallamar kana ta nufi Kofar Falon
ta rungumeta fuskarta ɗauke da Murmushi tace.
“Sannu da zuwa kece kika riga kowa fara zuwa”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Aikuwa dai na riga kowa zuwa dama cewa nayi sai an saƙƙo Daga sallar Juma'a in zo”.
Hannunta Ishmah ta riƙe suka zauna akan 2sitter tace.
“Gashi kuma kinga nima har yanzu babu wanda yazo yanzu nake ta faɗa”.
Kai Garkuwa ta gyaɗa tare da faɗin.
“Eh toh kin sani mafi akasari lokacin Sallar Juma'a yayi mafi akasarin tituna an rufe Nasan da
yawa shine abinda zai hanasu fitowa may be idan an idar da sallar juma'a zasu zo kinga kafin
su zo ukun zaiyi sai mu tafi”.
Daga nan suka Cigaba da hira...
Acan cikin Yola kuma a masallacin Lamiɗo Aliyu Mustapha bayan an idar da Sallah har da yawa
daga cikin mutane sun fara yunƙurin tashi zasu tafi.
Suka jiyo limamin na cewa akwai Ɗaurin Aurerrakin da za'a yi dan Allah jama'a su zauna.
Hakan ne yasa da yawa daga ciki suka koma suka zauna sai ƙalilan ne daga ciki masu manyan
Uzurarrika suka tafi...
Cikin nutsuwa da kamala kana da mutumtaka Liman yayi gyaran murya kana ya sanar da
ɗaurin Auren da za'a yi bayan an ɗaura aure na ɗaya anyi na biyu Liman ya gyara zaman
microphone ɗin hannunsa cike da farin ciki yace.
“Yanzu kuma in sha Allah akwai ɗaurin Auren da za'a gabatar wanda zamu iya cewa mun
godewa Allah da wannan al'amarin”.
Akuma dai-dai lokacin Bappa Kawu ya gyara zamansa wanda yana ɗaya daga cikin mutanen
dake cikin masallacin...
*Ethiopia*
Adaya ce kwance agefen gado tana lulluɓe da bargo saboda zazzaɓin da ya rufeta tun daren
shekaran jiya bata warware ba.
Ahankali Ummey ta tasa hannu ta taɓa wuyanta cikin tsananin zazzaɓin da take ji ta buɗe
idanunta da take jin suna rufe wa ta sake lumshewa.
Ummey kam wasu siraran hawayene suka zuba ta gefen idanunta.
Asina dake gefenta ne ta sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa.
“Sannu Adaya Ubangiji Allah ya baki lafiya”.
Cikin ruwan murya irin na wanda zazzaɓi ke bugunsa tace.
“Ameen”.
Ta ƙare maganar tana murmushi,irin murmushi dake nuna jin daɗin cikar buri..
Ita ko Ummey cikin sanyi da rauni ta mike ta koma bedroom ɗin ta.
Adaya kuwa cikin zazzaɓin da take ji da ƙarfin hali ta juya ta kalli Asina.
Da damuwa Asina tace.
“Wannan mutumin bai kyauta mana ba Adaya bai mana adalci ba ya mana tabon da baza mu
taɓa man tawa ba yazo ya tafi ya barmu da abinda har mu mutu ba zai fita cikin rayuwar mu
ba”.
Murmushi Adaya tayi kana tace.
“Ni dai ya gamamin komai tunda ya ban takardan saki ko abinda ya min ma sai naji banajin
komai akai tunda ni na jawa kaina, wlh bashi da laifi nice nayiwa kai kuma, nayi hakane saboda
burina ya sakeni dan in samu damar cimma babban burina na in ciyo mana gasar rawa ta
duniya baki ɗaya kuma Alhamdulillah tunda ya sakeni ya gama min komai Nagode mishi, duk da dai ya sabaibayi rayuwata Amman wlh na san ba laifinsa bane”.
Kai Asina ta gyaɗa cikin fesar da numfashi tace.
“Gaskiya kam nima abinda nake tunawa kenan inji sanyi araina saboda already kafin ya tafi ya
ajiye mana takardan saki kinga yanzu kina warware sai muci gaba da harƙoƙinmu kuma yanzu
ina da tabbacin Abpu da kansa bazai sake sha'awar jo gana Miki Auren dole-dolen nan ba
tunda gashi yaga zahiri an Aurar dake ɗin kuma mijin yazo ya sake ki yayi tafiyarsa”. Cikin jin daɗi ta ɗan runtse idanunta kana ta miƙe ta jingina bayanta da gado saboda tana jin
wani irin azabebben zazzaɓi dake cinta daga cikin ƙasusuwan jikinta tunda ziyarar Taj da yayi
mata hankaɗar kob ɗaya, take jin wannan ciwon bayan da ɗan zazzaɓi wanda har yanzu bai
sake taba... Cikin sanyi tace.
“Wannan ke nuna min in sha Allah inada sa'a da rabon ciyowa ƙasata gasar, in sha Allah sai Na
zubar da india a wannan shekarar”.
Cikin jin daɗi da karsashi Asina tace.
“Sosai ma dan wlh ko ni in naga yadda keda Izzin kuke juya gabbai tamkar baku da ƙasusuwa a
jiki ji nake in sha Allah mune da nasara”.
Rumtse idanunta tayi tare da cewa.
“Ke kina ganin yadda naki ɗaukar hankali kowa”.
Murmushin sukayi tare da tafa hannun.
Agefen Ummi kam kuka take tayi acikin bedroom ɗin ta dai-dai lokacin kuma Aminullah ƙanin
Adaya ya shiga ya sameta tana kuka da damuwa ya zauna gefenta daga ƙasa kana ya daura
hannunsa Kan gwiwoyinta ahankali Ummi ta ɗago ido ta kallesa cikin sanyi da tarin tausayinta
yace. “Ummi kiyi haƙuri duk kan abinda yayi tsanani ina da tabbacin in Sha Allahu yana tare da sauƙi
ki daina kuka in Allah yaso kuma ya yarda za muyi farin ciki matsalar Aunty Ada in Sha Allahu
zata zama kamar ba ayi ba mu cigaba dayi mata addu'ar shiriya kuma shima da yayi wannan
abin mu kyautata masa zato bamusan dalilinsa nayi haka ba kuma Ummi dama ai. Dole na zargi haka zai kasance saboda duk namiji mai mutunci da daraja in dai yaji kuma yayi
bincike akan Aunty Ada Nasan dole zai iya sakinta koda anyi Auren”.
Sai kuma ya ɗan furzar da iska mai zafi daga bakinsa cikin tausayi da takaicin halin da ƴar
uwarsa ke ciki ya cigaba da cewa.
“Gwara ma in ace shi ya ganta duk da halayenta da ɗabi'unta ahaka ya ganta yace yana sonta
ya Aureta amma mutumin da bai santa ba bai taɓa ganinta ba mahaifinsa ne yasa akayi Aura
mishi ita sannan kuma ke kanki kin sani na sani duk duniya Aunty Ada bata da kowa sama
damu kuma muma bamu da kowa sama da ita aduniya amma mu kanmu mun shaida halayenta
ba masu kyau bane duk da bata kasance mazinaciya ba wannan Allah ya sani mu mun sani ba
mazinaciya bace. Amman ai tana da ɗabi'un da dole mutane zasu ƙyamaceta dayi mata
munanan zato”.
Runtse Idanu Ummi tayi tana mai jin zafi akasan zuciyarta Aminullah kuwa cikin sanyi ya cigaba
da faɗin.
“Kuma kina ma sane Aunty Ada ita kanta take ƙoƙarin watsa Auren da Abpu ke shiryawa akanta
so wannan mutumin bashi da laifi akan wannan al'amarin abinda Abpu ma da kanshi ya faɗa
yanzu yace ya sani baza arasa.
Makircin da Aunty Ada ta ƙulla ba shine sanadin da bawan Allah nan ya saketa”.
Zazzafan Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare da girgiza kai tace.
“Aminullah Ni kaina nayi zargin haka nayi tunanin haka Nasan Wacece Adaya Nasan tasan duk
wata hanya da zatabi dan ta lalata auren nan Shiyasa nake ta jin tsoro da taraddadi nake ta
fatan inga anyi an tare”.
A hankali ta furzar da iska mai zafi hawaye na cigaba da zuba tace.
“Yau da muke da wowo nan da muka haɗu dashi suna fita ba ƙaramin farin ciki nayi ba amma
sai gashi abin takaici Mahaifinku na baisan Angon ba baisan fuskarsa ba wai abin takaici mai
gadin daya samu agidan ma baiga fuskarsa ba ita kanta Adaya da suka zauna awaje ɗaya
cewa take batasan fuskarsaba saboda bata ƙare masa kallo ba ko za'a kasheta ita ba zata gane
kamanninsa ba da yake shashace”.
Sunkuyar da kai Aminullah yayi yana mai jin zafi a ƙasa zuciyarsa yana so yaga Yayarsa ta
inganta rayuwar ta ta dawo nutsatstsiyar mace mai aji da kamala ta rabu da ballagantar da
kanta, kansa ya dago jin Ummi na cigaba da cewa.
“Yazo duniya ta shaida an daura mata Aure sannan yanzu duniya ta cigaba da ganinta tana
zaune agida tana fita tana raye-raye da rawa,tana yawo gari harda ƙasa da ƙasa, wannan
al'amari yana yimin ciwo yana ƙona min raina Aminullah al'amarin Adaya yana yimin ciwo”.
Cikin ƙarfin zuciya Aminu yace.
“Bakomai kiyi haƙuri kada abin ya mana yawa kinga yanda Abpu yake fama yau lafiya gobe ba
lafiya sannan matsalar Aunty Ada ya sake ingiza rashin lafiyarsa musamman ma jin batun sakin
nan”.
Sai kuma ya ɗan dakata kafin ya cigaba da cewa.
“Da farko Dr da kanshi yace za'a sallamesa amma jin abinda ya faru yasa jikinsa ya kara
rincaɓewa dole an ɗaga batun maganar sallama dan Allah ki kwantar da hankalinki kar in rasa
inda zanji sanyi inje wajanta in kalli rayuwar da Aunty Ada ta ɗauka ba daɗi in duba mahaifin mu
inga ba lafiya sannan in tuna Miyminmu ta rasu keda kike madadinta in kin kwanta ya zanyi? Ko
domin Ni ki cire damuwar aranki”.
Cikin sanyi tace.
“In sha Allahu Aminullah zanyi dangana zan cigaba da yiwa Adaya addu'a Ubangiji Allah ya
kawo mata sauƙi ya kuma shirya mana ita”.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum ”.
Ya amsa...
*Nigeria*
Daga harabar gidansu Ishmah motocine guda takwas wanda suke jere bisa duk kan alama
akwai wani ɗan ƙwarya-ƙwaryan hidimar da za'a yi yayin da can cikin falon kuma yake cike da
mutane wa'anda sun haɗu ne saboda kai kayan Auren Adam can cikin Yola.
Mafi yawan su Ummomin Ishmah ce da kuma ƴaƴayen su da kuma friends ɗin ta ƙarfe uku
dai-dai suka shirya suka kai kaya.
Bayan sun kai kaya sun dawo duk sukayi alwala sukayi sallah kana suka baje abubuwan da aka
babbasu wanda na tukuicine.
Ajiyar zuciya Aunty Hauwa ta sauƙe tare da cewa.
“Kai gaskiya mutanen nan sunyi ƙoƙari”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Toh Aunty Hauwa ba dole suyi ƙoƙari ba ai muma kayan da aka kai musu munyi ƙoƙari sannan
babu kayan ƙaranta aciki gaba ɗaya”.
Murmushi Ishmah tayi tare da cewa.
“Duk da haka sunyi ƙoƙari tukuicin da suka bada har yayi yawa ai”.
Kai Aunty Maryam ta gyaɗa kana tace.
“Gsky dai tukuicin yayi yawa dubu ɗari fa tukuicin”.
Garkuwa ce ta karɓa da cewa.
“Aikam sun kyauta tukuicin dubu ɗari a wannan marra da ake ciki gashi komansu ba ƙaranta”.
Ta ƙare maganar tana buɗe Cooler paper chicken sai kuma na gabansa Donut, Cake da sauran
abubuwa kana ga Catoons² na juice da faro water da dai sauransu.
Juyawa Aunty Nana tayi jin Ishmah na cewa.
“Aunty Maryam da an ɗauko plate an sassakawa mutane su suci”.
Kai ta gyaɗa Aunty Nana kuwa saurin cewa tayi.
“Yawwa ga nan abinci na ma kafin kuci nasu sai kunci abincina”.
Ta ƙare maganar tana nufar kan dining tana kwaso Warmers tazo ta ajiye atsakiyar su kana ta
dauki tirurrika ta ajiye da plate ta zubawa Aunty Hauwa nata daban kana ta zubawa Hajia Aisha
wacce itace ƴar farin su Daddy cike da girmamawa tacem
“Ga naku”.
Murmushi Ishmah tayi tare da cewa.
“Mu ma dai in Allah ya yarda mun kusa mukai wannan matakin in da zamuje surai sukarrama
mu su bamu komai namu daban Aunty Nana keda Maryam in banda wulaƙanci Babu abinda
kuke mana agidan nan”.
Dariya Maryam ta sanya cikin fahimtar junansu tace.
“Toh ba dole muyi muku ba kufa ƙannen Mijine sai ki bari idan Adam ɗin yayi aure nan ne zaku
samu Power tunda kun fara zama yayun miji”.
Dariya suka sanya Garkuwa kuwa kafaɗar Ishmah ta dafa kana tace.
“Ishmah kwantar da hankalin ki kwana nawa ne ma ya rage matar Adam ta ware Miki kwananki
da ban”.
A dai-dai lokacin kuma Adam ya shigo duk haɗa baki sukayi wajen cewa.
“Ango!, Ango!!, Ango!!”.
Idanunsa ya wara tare da cewa.
“Ina anata Angwaye wa yake ta angoge aini angoge ne ba Ango ba”.
Duk juyawa sukayi suka kallesa kana suka ce.
“ kamar ya Angoge”.
Murmushi yayi mai nuni da zallan farin ciki da tsananin annurin dake nuna madaukakin jin
daɗinsa yace.
“Ai Ango yana waje ba kuji yadda gidan yaketa baza ƙamshi ba ga Amarya agefenku”.
Da mamaki Garkuwa tace.
“Wace Amaryan kuma?”.
Still fuskarsa ɗauke da Murmushi yace.
“Ƴar ɗakinki Aunty Ishmah mana”.
Cikin mamaki suka hada baki wajen cewa.
“Ishmah kuma?”.
Kai ya gyaɗa cikin tabbarwarta yace.
“Eh Ishmah mana”.
Kafin suce wani Abu Yah Muhammad ya shigo yana shigowa ya durƙusa gaban Aunty Hauwa
da Hajia Aisha da kuma Aunty Amina ƙannen Daddy da yayarta kenan
Wasu hawayen farin ciki suka fara zuba akuncinsa cikin sauri Aunty Hauwa tace.
“Muhammad ya dai?”.
Cikin matsanancin farin ciki yace.
“Aunty Allah ya ƙaddara Allah ya nufa yau an ɗaura Auren Ishmah yau Allah ya nufa Ishmah
tayi Aure”.
Da wani irin sauri suka haɗa baki wajen cewa.
“Ishmah?”.
Ishmah kuwa zamewa tayi ta zauna sandan-dam tamkar an daskarar da ita sai kuma ta juya ta
kalli Adam dake cewa.
“Tabbas Alhamdulillah”.
Cikin al'ajabi Aunty Hauwa tace.
“Muhammad Bama haka da kai