Showing 30001 words to 33000 words out of 47460 words

Chapter 11 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6558

yaƙinin in kinjin zaki ruɓanya kulawarki gareshi, zaki tausashi zuciyarsa ki sama mishi
farin ciki koda kaso 30 cikin 100 daya rasa, to dan Allah ki taimaka kiyi azama da hikima sashi
bacci, domin zuciyarsa da kwakwalwarsa su samu su huta da azaban damuwar dake cikinsu”.
Wani irin fitinenne rauni tausayin Taj ɗinne ya rinƙa narke zuciyarta wanda har ya tsinko mata
hawaye.
Garkuwa ko kai take jinjinawa cike da tausayi, sai kuma suka kalli Addawa ganin ta riƙo hannun
Ishmah tare da cewa.
“Ya nemi kusanci da kene da yaƙinin duk duniya kece kaɗai farin cikinsa, burin zuciyasa, kuma
sanyin idaniyarsa, na fahimci cewa yana jinki a jiki da zuciyarsa da yarda ko kowa zai juya
mishi baya a duniya ke zaki fuskanceshi.
Please Ishmah dan Allah ki kular min da Tajuddeen ki ɗebe mishi kewa ki sashi farin ciki, ki
mantar dashi abinda ya faru dashi kwanaki goma sha biyu da suka shuɗe, ki kusantar dashi da
bacci dan zuciyarsa ta huta sannan ki kula da cikinsa kada yunwa ta lahantashi”.
Cikin sanyi murya cike da aminci tace.
“In sha Allah”.
Sai kuma ta ɗan kalli Garkuwa dake cewa.
“Kin dai ji ko, dan Allah ki watsar da raunin kin nan, na koke-koken kin bar Hamisu ƙaton gardi,
ki ruggumi mijinki ki faranta mishi rai sai kema Allah ya faranta miki”.
Sai kuma tayi ɗan kasake tana jin Garkuwa na bata dabarun samawa miji bacci da dai
sauransu, yayinda Addawa ta ɗaura da nata.
Kusan 30 minute sukayi suna ƙarfafa mata guiwa.
“Yauwa tashi kije yana jiranki, dama na kirashi nace ya bani 30 minute zaki fito.”
Cewar Addawa tana miƙe tsaye tare da kamo hannunta.
Ita kuwa Garkuwa cikin juya harshe zuwa hausar da tasan Addawa bataji tace.
“Ya batun kayan ɗa'a da kullaccar sirri da shu'umar humra in baki sune”.
Cikin yarda da kai tace.
“Ai kullacca da humra akwaisu a hand bag na, kaya kuma barsu, in sha Allah gobe zamu bar
hotel ɗin zamu dawo gida, dan zanfi samu nitsuwar nesantashi da yunwa da kusantashi da

bacci”.
Kai Garkuwa ta jinjina cike da gamsuwa.
Daga nan suka fito ta sallami su Aunty Amina kana ta wuce ta fita.

Su kuma suka zauna a Parlour sukaci gaba da hira.

A Corridor ɗin sukayi kiciɓis da Adam da Bilal, hannu Adam ya bata sukayi musabaha kamar
yadda mafiya akasarin lokuta haka suke gaisawa, sai kuma ta amsa gaisuwar da Bilal keyi
mata, cikin murmushi tayi tare da cewa.
“Wai ya naga ka zama wani ƙaramin ba Ethiopia ne kam”.
Cikin ɗaga kai Adam yace.
“Aha wani ba Ethiopiaye ko! Ba Balarabe ba, ba kullum tsiya kukemin kuce duk cikin
mahaifiyarmu nine baƙi ba, ina gaya muku ni kalata mai tsadace tamafi ta larabar kyau tunda
kin yarda nayi kalar Ethiopia yawa”.
Tana Murmushin tace.
“Yaban kai dai...”
Da sauri ya amshi mgnar tare da cewa.
“Ilimi ba”.
Kusan a tare suka juyo suna biye da ita a baya. Bilal ke cewa.
“Yauwa dama Uncle Taj yace ki fito ku tafi”.

A bakin motar suka tsaya, sai kuma suka ɗan fara jujjuya kai, can gefen motar suka hangeshi
zaune bisa kujerun silver dake jere a wurin.
Bilal ne ya buɗe mata marfin motar, Adam kuwa wurin Taj ɗin ya nufa jim kaɗan suka dawo tare.

Baya ya shiga gefentan, kana driver'nsa dake can bakin gate wurin mai gadi ya taso da sauri
yazo ya shiga, kana yaja suna tafi.


A hankali ya ɗan juyo ya kalleta dai-dai lokacin da suka fita harabar gidan, cikin kulawa da
tasayawa tace.
“Kanka na ciwo ko”. Tayi mgnar tana kallon yadda idanunsa sukayi da kuma yadda jijiyoyin
kansa suka ɗan tashi, kai ya ɗan jujjuya mata alamar a'a.
Sai kuma ya ɗan kalli wayarsa dake ringing.
“Ka ɗauka mana”.
Ta faɗa tare da gyara zamanta.

Sallamar da Dr Abbas yayi masa ne ya amsa cikin sanyi da rashin bacci ya sakar masa da
cushewar zuciya gami da tunani dan har wani juyawa yakejin kansa nayi.
“Afif wai me nake ji ne?”.
Cewar Dr Abbas yayi tambayar cike da damuwa.
“A ina ɗin!”.
Taj ɗin ya amsa mishi tamyarsa da tambaya.

Murya cike da ruɗani yace.
“Dazu da Yamma Yah Aryan da Kabir suka zo da Malam, sun cire komai na sunanka sun meye
gurɓinshi da sunan Kabeer TAJMUH CONSOLATION HOSPITAL ma sun maida shi
ARKABMUH CONSOLATION HOSPITAL sun haɗe sunan Aryan Kabeer dana Malam, sannan
sun soke sunanka a komai, kai kuma nayi maka text message ba amsa meke faruwa, harfa da
cireka a matsayin Dr asibitin an meye sunan Kabeer a gurbinka shida yaushe ma ya gama
karatunsa”.
Yana ɗan lumshe idanunsa yace.
“Eh na sani, ba matsala ai”.
Da sauri Dr Abbas yace.
“Zurfin ciki ko? Wai ni kake cewa ba matsala, bayan duk abinda ya faru Yah Aryan ya gaya min!
Sannan kuma naga kabar ƙasar ka koma Qatar harma da ɗiban ma'akata sama da mutum 100.”
Shiru Ishmah tayi domin tana iya jiyo duk abinda Dr Abbas ke faɗa can ƙasa.
“Eh na bar wannan asibitin ne, na dawo nan Qatar zan kula da sabon Asbitin dake wurin”.
Da sauri Dr Abbas yace.
“Ok nima zan bar musu aikinsu na nan, zan dawo Qatar ɗin mu kula da wannan”.
Da sauri Taj yace.
“Please Abbas kada muyi haka da kai, ka zauna ka taya Kabeer kula da nan”.
Tsaki mai tsawo Dr Abbas yaja tare da cewa.
“Anƙi zaman, ai kai kasan dama dan kai nake aiki a nan, Dr Farida ma tuni tayi ajiye musu
aikinsu.
Nima kuma na rubuta takardar barin aiki nama tura musu.
Kuma ina nan tafe Qatar”.
Ya ƙare maganar tare da katse kiran.
Kanshi ya ɗan jingina jikin kujerar motar a kuma dai-dai lokacin suka shiga cikin hotel ɗin.


A hankali suka kutsa kai cikin Parlour,
Numfashi mai sanyi ta fesar tare da lumshe idanunta saboda sanyin wurin yafi na cikin gari ta
fahimci cewa suma watannin sanyinsu da zafi da damuna kamar namu ne, dan yanzu kusan
ƙarshen damune dan yau ne 12 September.
Ido ta ɗan zuba mishi ganin ya zauna bisa kujera tare da sa hannunshi duka biyu ya riƙe ƙansa.
Bedroom ta wuce, tana shiga ta faɗa bathroom broch ta farayi kana tayi wanka tare da al'walan
bacci.

Tana fitowa ta tsane jikinta da baby towel, sannan ta murza kullaccar sirri tare da ɗan shafa
shu'umar humra.
Wasu tattausan riga da wondo na bacci maroon color ta ɗauka wondon bai sauƙan mata har
ƙasa sosai ba, da kaɗan ya wuce guiwa, rigar kuma mai gajeren hannunce, tayi cib da jikinta sai
hular kayan da ta naɗe gashinta ta cusa a ciki.

Dai-dai lokacin kuma ya shigo.
Ba tare da yace mata ko ƙalaba ya wuce bathroom.

Ita kuwa a hankali ta zauna bakin gado tare da haɗe tafin hannunta tayi addu'o'in kwanciya
bacci, ta shafa kana ta miƙe ta fita Parlour.
Jin wayarta na tsuwa ganin Maryam ce yasata amsawa da sauri.
“Amarsu ta ango duk kin mance damu kin ruggume miji, su da sukaje rakiyarma gudunsu kukayi
bare mu da muke nan ko”.
Dariya tayi tare da cewa.
“Sherrin Aunty Nana nefa”.
Itama Maryam dariya tayi tare da cewa.
“Toh a dai ragewa arnan Qatar dangi kaɗan kada a ƙarardasu a mako ɗaya”.
Tana lumshe idanunta tace.
“Toh ai dama Qatar ba ƙasar zamansu bane, gwara kawai mu kashesu duka a mako ɗaya mu
samu ladan jihadi”.
Cikin ƙelkel Maryam ta fashe da dariya mai sauti har Saida Yan Abubakar yace.
“Ke lfy kuwa”.
Ganin haka ne yasa ta fito Parlour.

Bayan sun gama wayarne kuma tayi saurin juyowa ta kalli wayarsa dake ringing.
*Arfah* ta gani a fuskar wayar.
Haka yasa ta ɗauka tare da nufar bedroom ɗin.
Wani irin ni'imtaccen ƙanshin ne ya bugi hancinta da zuciyarta har yasata lunshe idanunta, kana
a hankali ta buɗesu a kansa.
Tsaye yake cikin wata tattausar jallabiyarsa Morning sky mai masifar sheƙi da sulɓi, sai baza
ƙamshi yake tamkar fure, ido suka zubawa juna tamkar yau suka fara ganin juna.

A hankali ya ɗan fara taka ƙafarsa yana tahowa gabanta.
Wani nannauyan numfashi ta kuma fesarwa tare da fara kallonshi daga saman rumfar sawunshi
tanayin sama da idanunta a hankali.
Shi kuwa Taj tafiyar yake cikin sakewa da jin daɗi da yake ji a duk lokacin da ya kasance daga
shi sai jallabi ko giltan baccinsa da yake ɗaurawa, Allah ya sani shi baya iya kwana da wani abu
a jikinsa, jallabiyar ma da yake sawa dan itane, tunda ya kai shekaru takwas daya koma gidan
Addawa kasancewar dakinsa shi kaɗai yake kwana da giltan, giltan ɗan wani tattausan fellen
yadukane masu masifar taushi wasu daga ciki kuma masu sulɓi so su yake ɗaurawa yayi bacci
dan bayi son takura Taj ɗinai.
Tafiyar da yake yi ne kuma ya bashi damar motsawa da bayyana kansa sosai a cikin jallabiyar
wanda ganin haka ne yasa Ishmah saurin rumtse idanunta tare da kauda kanta.
Sai kuma ta miƙa mishi wayar jin kiran ya kuma shigowa.

Yana amsar wayar ta wuce ta gefenshi a bakin gadon ta zauna tare da jawo pillow ta kwanta.

Shi kuwa kashe wayar yayi baki ɗaya, kana ya dawo ya zauna a ƙasa bisa Carpet ɗin a hankali
ya jingina bayanshi da jikin gadon sai kuma ya ɗan juyo ya kalleta murya a sanyaye yace.
“Babey Kiyi addu'a ko”.

Kai ta jinjina mishi tare da buɗe hannunta ta fara addu'an.

Shi kuwa Taj a hankali ya ɗan gyara zamansa tare da fara karatu cikin sassayan muryar da
yasata lumshe idanunta.

Ethiopia Yah Hafiz ne riƙe da waya murya cike da rauni tausayi ido na tsatstsapo da wahaye ya
ɗanyi gyaran murya tare da kiran ɗan nasa da suke waya dashi.
“Imran! Imran!!”.
Ina Imran ya kasa amsawa sai kuka shesh-sheƙan kuka da yakeyi.
“Imran”. Ya sake kiransa a karo na uku.
Murya na rawa yace.
“Na'am Abba”.
Cike da lallashi yace.
“Imran kayi shiru ka dena kukan ya isa haka, zai sa maka ciwon kai, ina Arfah?”.
Cikin kuka Imran ya fara magana cike da rauni.
“Abba ko yanzu nayi ta kiran Uncle Taj baya ɗagawa, nayi mishi text ba amsa yau kusan kwana
takwas kenan dani da Arfah duk muna kiranshi ba amsa yanzuma Arfah ya kirashi Amman sai
kashe katse kiran fa yayi.”
A sanyaye Yah Hafiz yace
“Ai bazai ɗagaba Imran saboda, Malam yace bai yafe mishi ya sake mu'amala da kowaba a
cikin family'nsa kuma muma ɗin yace mana baiyafe mana muyi mu'amala da shi daba”.
Da sauri yace.
“Wallahi mu dai bai isa ya rabamu da Uncle Taj ba, ku da ya haifa kuke ganin zakuyi mishi
biyayyar ya raba zumuncin ku da ɗan uwanku mai sonku mai tausayinku, mai son ƴaƴanku
tamkar yadda kuke sonmu koma fiye da haka, in kunga zaku iya kuyi masa biyayya, Amman
wlh tallahi nida Arfah da ƴan uwanmu mata da sukayi aure muddin mazansu basu hanasuba,
zamuyi zumunci da Uncle Taj, domin shine kaɗai Uncle namu da yake tamkar uba, amini,
malami, kuma jigon mu, ni dasu duk Allah ya isar Malam bazata yi mana komaiba, Ni matsala ta
shi Uncle Taj wanne hali yake ciki? A ina yake? Dasu waye yake rayuwa? Su waye zasu zame
mishi madadinku, duk da nasan duk duniya babu masu zame mishi madadin Ummeeyshi da
Yah Abanansa”.
Yanayin mgnar ne cikin kuka da hawaye kasheɓar.
Yayinda Arfah ma dake zaune a gefensa yake kuka mai raunataccen sauti.
Ji sukeyi Mexico City tayi musu ɗaci da duhu saboda nesantasu da wanda yayi sanadin
zuwansu ƙasar.
A hankali Yah Hafiz ɗin yace.
“Imran kamar tuhumata kakeyi kan na gaza ƙarfafa zumunci na da Afif ne, shin ka mance yadda
Afif yake a rai nane,
Imran ko a hospital na wuni jinina ya hau, ya kake son inyi in har kai ɗan da na haifa kana
tuhumata na gaza gyara komai.
Ina shiga damuwa in na tuna ba wanda yasan inda Taj yake, naje gidan Addawa kusan sau
huɗu Amman itama cemin take bata san inda yakeba, kwana kusan shida kuma in najema bana
samunta, gashi Malam yace bai yaffe muyi mgnar Shiba”.

Cikin kuka Arfah ya amshi wayar tare da cewa.
“Big Uncle dole duk mu zargeku akan nesanta Uncle Taj damu da kanku”.
Sai kuma kawai ya fashe da kuka.
Cikin rarrashi Yah Hafiz ɗin yace.
“Kuyi haƙuri kunga kwanaki ne suka rage muku, ku zaku fara jarrabawa, kada kusa damuwar
haka a ranku! In sha Allah komai zai dai-dai”.
Haka dai yayi ta kwantar musu da hankalinsu.

Qatar a hankali ta ɗanyi miƙa saboda baccin da ya fara surarta, na yadda ta lumshe idanunta
tana jin sautin muryarsa na ratsa kunnuwanta na kusan tsawon 28 mutane.
Sai kuma dukkan kalaman Addawa da Garkuwa suka fara dawo mata.
A hankali ta miƙe zaune, tare da zura sawunta ƙasa kusa dashi.

Buɗe idanunsa dake cike da gajiya, bacci, damuwa, da hawayen ƙuncin zuciya.
Dai-dai lokacin kuma ta zame ta zauna kusa dashi, har kafadarta na ɗan taɓa kafaɗarsa, ɗan
gajeren hamma tayi tare da yin mgna a hankali.
“Please Taj kayi bacci, ka bar karatun nan haka ga idanunka fa suna cike da bacci”.
A hankali ya ɗan miƙe tsawunshi tare da sa hannunsa ya jawota jikinsa kan cinyarsa ya ɗaura
kanta zuwa kafaɗunta.
Sai kuma yasa hannunsa na dama yana shafa rabin sumar kanta da hular ya zame, a hankali
yaci gaba da karatun domin so yake ya kai ƙarshen Suratul Yaseen. Alamun saura masa izufi
15 ya sauƙe Qura'an ɗin a kwanaki uku da ya faro daga Baqara.

Numfashi mai sanyi ya fesar lokacin da ya dire ayar ƙarshen surar.
Iska mai sanyi ya ɗan hura mata cikin kunnenta jin tana mgna ƙasa-ƙasa.
“Kiyi bacci kada kanki yayi ciwo”.
Yayi mgnar yana shaƙan sassayan ƙamshin kullaccar sirri da shu'umar humra dake cikinta,
wanda yasashi lumshe idansa.
A hankali ta juya ta ɗan mirgina kanshi tare fuskantarsa, sai kuma ta ƙara lafewa jikinsa murya
a tusashe tace.
“In dai bakayi bacci ba. Nima bazanyi baccinba”.
Ta faɗa cikin narkekkiyar murya da tasashi ƙara sunkuyowa a kanta bisa kafaɗarta ya ɗan kife
kansa tare da sakin nannauyan numfashi.

Ita kuwa Ishmah cikin sanyi ta gyara kwanciyarta a jikin nasa, tare da sa hannunta ɗaya bisa
cinyoyin nasa tayi pillow dashi ɗaya hannun kuma a hankali ta ɗan yi sama dashi kaɗan kan
kan ƙeyarsa ta kife tafin hannunta sai kuma ta ɗan zora babbar yatsarsa cikin kwarmin ƙeyarsa
inda wani irin tattausan gashi mai sulɓi dake kwance lip-pli a wurin a hankali ta ɗan murza
yatsar.
Wani irin lumshe idanunsa yayi tare da fesar da sassayan numfashi.
Mutsu-mutsun da sukeyi ne, yasa tattausar jallabiyarsa fara tattarawa kasancewarta mai tsulɓi
Gyara zamansa yayi ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, hakan yasa tayi tudu sosai tudun da ya
bashi damar gyara kifa ƙirjinsa da kansa bisa kafaɗarta ya cusa kansa tsakanin wuyanta da

kanta, tare da manna hancinsa dai-dai ƙasan kunnenta da yake zuba ƙamshi kulaccar sirri cikin
sanyin murya da kamar raɗa-raɗa ya fara karanto suratul Mulk dan ɗabbagar sunan da ɗibi'arsa
na karantarta surar duk daren duniya, domin itama surace maiyin ceto ranar gobe kiyama.

A hankali take shaƙan ƙamshi turarensa tare da da gyara hannunta na hagu kan cinyarsa ta
tallabe fuskantar ɗaya hannun kuma tana murza ƙeyarsa a hankali wanda tuni hakan yana sako
mishi wani irin amintaccen sanyin da lunshin ido.
A hankali ta lumshe idanunta, yayinda shima ya lunshe idanunsa tare daci gaba da karatun
yana mai jin ɗumin jikinta da ƙamshimta suna fizgo mayataccen baccin dake damunsa.
Cikin 6 minutes bacci yayi awon gaba dasu, wanda zuwa lokacin tuni ƙarfe biyu ta gota.


Ƙarfe biyar dai-dai ya fara buɗe ifanunsa a hankali, tare dayin addu'ar tashi daga bacci,
da sauri ya sake rufe idanunta saboda ganin yadda ta jawo jallabiyarsa ta tattareta ta yi filon
gefen fuskantar dashi, a hankali yake sauƙe numfashi dake nunin da ya samu sassaucin azabar
rashin baccin, dai-dai lokacin kuma ta buɗe idanunta tare da yunƙurawa alamun zata taso, still
tana riƙe da jallabiyar tasa wanda hakan yasa gaba ɗaya cinyoyinsa bayyana a fili zura
idanunta tayi bisa tattausar farar tatarsa da gargasa ke kwance lip-pli a kanta tamkar anayi
masu bayin ruwa, so take ta lunshe idanunta Amman ta gaza, saboda kyaun surar cinyarsa.

Shi kuwa Taj cikin sanyi yace.
“Yah Salam Babey mun makara fa”.
Ya ƙare maganar da sa hannunsa ya tattaro gashin ta ya meda mata shi gefen wuyanta, wanda
hakan ya bawa fatar wuyanta dama bayya, kusan a tare suka Lumshe idansu lokacin dayayi
kissing ɗin wuyanta.
Jan numfashi tayi tare da miƙewa zaune, ta haɗe sawunta tare da kife kanta bisa guiwowinta.

Shi kuwa Taj a hankali ya miƙe tare da nufar Bathroom, wanka yayi kamar yadda ya saba kana
yayi al'walan, yana fita itama ta shiga.

Yadda yayin haka tayi, tana fitowa ya miƙe ya nufi Parlour tare da cewa.
“In kin gama kizo muyi jam'i muyi salla ko!”.
To tace tare da nufar drower.

Wani kayan ta jawo riga da wondo ne, sai dai rigar chort sleeve shirt ce, fara ƙal mai ɗan wuya,
sai wondon kuma brawn collar ne mai ratsin fari sai doguwar abayar kalan wondon mai igiyoyi
biyu.
Sai kuma ɗan gyale fari.

A hankali ta kimtsa kanta cikin kayan.
Masha Allah, tace lokacin da ta tsaya gaban mirror tana rolling gyalen a kanta, domin sosai
kayan suka zauna ɗas a jikinta kai kace, dan ƙirar jikinta aka haliccesu, igiyoyin rigar taja ta ɗan
ɗaure daga tsakiya wanda hakan ya bawa ƙirjinta damar bayyana, kana tayi rolling kanta ta

fidda fuskantar fasalin 0 turaren ta fesa.

A hankali ta fito Parlour, kan sallayan dake can shimfiɗe a gefen sukayi salla bayan sun idar ne
ta ɗan juyo ta kalleshi.
“Barka da safiya”.
Ta faɗi tare da kallon fuskarsa, cikin jin sassauci da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login