Showing 33001 words to 36000 words out of 47460 words

Chapter 12 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6557

raraɗin damuwarsa yace.
“Babey kin tashi lfy”.
Sai kuma ya ɗanyi ɗan guntun Murmushin gefen baki yace.
“Wuyanki na ciwo ko?”.
Kai ta jujjuya mishi alamar a'a.
A hankali yace.
“Kin samu lada, kin sani nayi bacci har na tsawon awa uku, kusan mako biyu kenan baccina
baya wuce 30 minutes nake farkawa shima sai in ina karatune nake samun ya ɗan fizgeni,
shiyasa nake kwana a zaune, Amman yau nayi mai yawa Allah yayi Miki albarka”.
A hankali tace.
“Amin ya Allah”. Sai kuma ta ɗan kalleshi jin yana cewa.
“Miyi du'a Azkar, sai muje Restaurant muyi breakfast”.
Kwaɓe fuska tayi cikin sanyi tace.
“Taj mu koma gida”.
A hankali yace.
“Kin gaji da zaman nan ne!”.
Cikin sanyi tace.
“A'a kaga gobe su Aunty Nana zasu, koma ina son ɗan zama tare dasu”.
Yana ɗan gyara zamansa yace.
“to Saida yamma ko!”.
Da sauri tace.
“No ai in mun kai 12:00 AM
sai ka ƙara biyan kuɗin yau, ni mu tafi yanzu kaji ko dan allah.”
A hankali ya gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Hmmm ai dama na kuɗin two weeks na biya. Amman zamu tafi tunda hakan kikeso”.
Daga nan sukayi addu'o'in su.

Ƙarfe goma dai-dai ta samesu a cikin gidan.
Bayan ya gaida dasu Aunty Amina da duk suke Dinning area.
Ya wuce ɗakin Addawa.

Ita kuwa Addawa da kanta ta haɗa musu breakfasts ta miƙawa Ishmah tray.

A bisa kujera ta sameshi zaune, yayinda Laylah ke zaune can gefen gado ta takure jinkinta
daketa karkarwa tamkar wacce taga dodo.
Shi kuwa Taj ido kawai ya zuba mata cike da ƙuna da ƙuncin zuciya yana ɗaya daga cikin
abinda yasa yakejin kamar zai raba musu gida da Addawa ta riƙe Laylah saboda yadda Laylah
ta kasa sakewa dashi a fili yake ganin tsananin tsoronsa a kwayar idanunta wanda hakan ke

sashi jin ya tsani kansa da kansa.

Ajiye Tray Ishmah tayi a gabansa tare dasa hannunta ta jawo Laylah da jikinta ke karkarwa
tamkar mazari, a hankali tace.
“Ya dai Laylah me ya sameki? Ya kike firgice haka?”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Taj ɗin daya taune gefen lip inshi na ƙasa kana ya zura idanunsa wuri
ɗaya.
Cikin mamaki tace.
“Taj wai me ke damun Laylah ne, me take tsoro haka?”.
Cikin sanyi ya miƙe tsaye tare da zura hannunshi cikin aljihunsa suit inshi a hankali ya juya ya
nufi hanyar fita tare da cewa.
“Ni take tsoro”.
Ya ƙare maganar tare da ficewa, side ɗinsa ya wuce kai tsaye.

Yana fita Addawa kuma na shiga dai-dai lokacin da take cewa Laylah.
“Laylah wai Uncle Taj ɗinki kike tsoro? Me yayi Miki?”.
Cikin sanyi Addawa ta zauna gefensu tare da yin ƙasa da murya tace.
“Eh shi take tsoro Ishmah!”.
Da sauri tace.
“Saboda me?”.
Tana mai ɗan taune lips inta duka biyu tace.
“Tun sanda maganar cewa Taj yayi mata fyaɗe ta fit.”
Da sauri Addawa tayi shiru ganin Ishmah ta sa hannunta duka biyu ta toshe kunnuwanta kana
ta miƙe tsaye tana mai girgiza kai tare da jujjuya idanunta da sukayi jazir gaba ɗaya jikinta rawa
ya farayi tamkar mazari.
Ita kuwa Addawa sai yanzu ma ta tuna da kashedin Taj da yayi mata na kada ta gayawa Ishmah
komai shi da kansa zaiyi mata bayanin.

Sai kuma tabi Ishmah da idanu ganin ta fita.

Sauri-sauri gudu-gudu ta nufi Corridor ɗin, steps ɗin hawa saman ta fara takawa da sassarfa
har Lau hannunta na toshe da kunnenta kamar tsoron buɗe kunnuwanta ma takeyi.

Gaba ɗaya idanunta basa iya gani, shiyasa ta gaza hango shi inda yake Dinnin area yake
zauna bisa kujerar tare da kife kansa a kan Table ɗin.

Cikin rikitaciyar murya da alamun tsananin girgiza gami da son hafimtar abinda taji ta fara kiran
sunansa murya a hargitse.
“Tajj! Tajj!! Tajjjj! Ina kake”..
Ta ƙare maganar muryarta na rawa hawaye na zubo mata.
Cikin sanyi ya miƙe tsauye yayinda zuciyarsa ke duka tara-tara farga da kiɗimar kaddai Addawa
ta gaya mata cewa yayiwa Laylah fyaɗe harma tana da ciki ne suka diro mishi in one second.
A sabule ya taho gareta, murya a daskare yace.

“Gani”.
Da sauri ta juyo ta inda taji muryarsa hannunta tasa ta kamo hannunsa kana ta jawoshi zuwa
tsakiyar Parlour sake hannunsa da tayi da kuma mutuwar da jikinsa yayi ne ya sashi zamewa
ya zauna bisa kujerar 3 sitter dake bayansa.
Ita kuwa zubewa tayi bisa guiwowinta cike da tsoro murya na rawa tace.
“Taj me nakeji? Me gaskiyar abinda Addawa ta faɗa?”.
Cikin wani irin matsanancin fargaba da tashin hankali gami da tsoron, kada itama Ishmah tayi
mishi irin hukuncin da Yah Abana da Ummeeynshi sukayi masa, yana taraddadin kada tayi
mishi yakicewar da zaisa ta nesantasu da juna, itace kaɗai sauran yaƙininsa a duniya, ya zata
ɗauki waɗanan kalaman in ta gujeshi ina zai saka ransa?. Jin ta daura hannunta kan guiwowinsa tana jijjigawa da ƙarfi tare da fashewa da kuka tana
faɗin.
“Tajj ka gaya meke faruwa? Please kayiwa Allah da Manzonsa kada ka ɓoye min komai
meyasamu Laylah?”.
Kanshi ya ɗago tare da zuba mata ido cikin Tsananin damuwa da fargaba yace.
“Ma'eesha nayiwa Laylah fyaɗ....
Da sauri ta tsananta jijjiga guiwowinshi ba tare da ta bari ya ƙarasa faɗar abinda yake son
faɗamatan ba domin heart and brain ɗinta bazasu iya ɗaukar nauyi da munin kalaman ba ji take
zuciyar tamkar zata fashe cikin tsananin kiɗima gigita gami da tashin hankali da tsananin tsanan
furucinsa na karshe da ta katse shi ta hanashi ƙarasa tayi wani irin miƙa tare da jujjuya kanta
tana yarfa hannunta na dama na hagu kuma ta ɗaurashi kan ƙirjinta dake barazanar fashe cikin
rawar murya tace.
“Wallahi tallahi bazan ci gaba da zam....



*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170
GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276
in kuma Niger kike 1000fc ne jaka ɗaya kacal kenan zaki biya. In kuma baki biyaba kika karanta
min littafina wannan kuma kede Allah*


By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286:

*INDA RAI*
*BOOK 2 PAGE 8*

Irin zazzafan ajiyan zuciya mai fizge numfashinta.
Da sauri ta miƙe tsaye saboda jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta.
Ita kuwa Laylah da sauri ta nufi Parlour da gudu tana kiran Addawa da ƙarfi.
Wanda har Taj dake sauƙowa daga sama ya jiyota cikin mamakin yaxu gaba da sauƙowa
saboda jin yadda Laylah ke aunawa Addawa kiran mafarauta, sai kuma ya fara sassarfa tare da
sauƙa cikin kaɗuwa sabido jin Laylah na cewa Addawa.
“Aunty Ishmah ne tana ta kuka, Addawa ta kasa zama numfashinta fita da ƙarfi”.

Kusan a tare suka shiga ɗakin.
Cikin tashin hankali ganin yadda numfashi Ishmah keyi sama da ƙasa ne, yasashi saurin isa
hareta dai-dai lokacin da jiri ya fara ɗibanta.
Da sauri ya tallabota ta afka cikinsa, da ƙarfi ya ruggumeta tsam a jikinsa.
Addawa kuwa salati ta saka cikin kaɗuwa take kiranta.
“Yah Salam Ishmah meke damunki? Afif mu tafi asibiti da sauri”.
Cikin ji muryar Addawa can sama-sama, da ƙarfi ta rumtse idanunta dake kwaranyar da hawaye
tamkar an buɗe igiyar ruwa, murya na rawan kuka tace.
“No Taj bana so, kada ka kaini hospital, ni lafiyata ƙalau”.
Ta ƙare maganar cikin yayyankewar numfashi.
Da sauri ya tallabo kanta da tafukan hannunsa duka biyu, idonsa ya zuba cikin nata cikin
muryar dake nuna damuwarta itace damuwarsa yace.
“Ma'eeshah numfashinki baya fita, ki bari muje asibitin, bana son rasaki, bana kuma son
Ummeeyna ta ratsani ba tare da Yah Abana da Ummeyn sun yafe min ba”.
Ya ƙare maganar da sunkuceta tsam kana ya nufi hanyar fita da ita, itama Addawa bayansu tabi
da hanzari tare da juyowa ta kalli Zulaihat lokacin da suka fito Parlour.
“Zulaihat ku zauna a gida bari muje asibiti, ki kula da Laylah”.

Cikin sanyi Zulaihat tace.
“Toh Addawa sai kun dawo”.

Dai-dai lokacin da suka shiga Corridor ɗin da zai fiddasu wajen.
Da sauri Ishmah tasa hannunta na dama bisa ƙirjin Taj ɗin tana ɗan bubbuga cikin alamun a
ɗimauce take mgna da fizgo murya.
“Yah Sheykh lfyata ƙalau please dan Allah dan Annabi kada ka kaini asibiti bana so”.
Wani irin kallo ya zubawa fuskantar domin ya sani a iya tsawon zamansu in dai ta kirashi da
Yah Sheykh to tabbas mgna ce ta gsky takeyi mishi, ba wasa ko ƙarya ciki kuma muddin ta
haɗashi da Allah to yasan babban abune da take son a bari ko ayi shi, dan yana cikin abinda
yasa bai taɓa cewa yana sonta ba, kafin aurensu domin da ake ta cewa son juna suke, yake
cewa to ko dai gsky ne, ranar tayi ta roƙonshi da Allah da Manzonsa kada ya kawo
makamanciyar mgnar nan a abotarsu ta rantse cewa, ba wannan mgnar shiyasa bai samu
damar ida ƙudurinsaba saida tura ta kai bango.

Da sauri ya juya ya nufin kan steps ɗin da zai sadashi da part ɗinsa, saboda jin yadda taketa
ɗan bubbuga kafaɗarsa tare da magiya gami da haɗashi da Allah.

Da sauri Addawa ta mara musu baya.

Suna shiga Parlour ya kwantar da ita bisa 3 sitter, sai kuma ya dire guiwowinsa ƙasa tare da
ɗan ɗaura hannunshi kan goshinta kana ya ɗan sunkuyo kanta, tare da mannan lips inshi kan
hancinta.
Hmmmmmmmmm taja wani irin na kasashshen numfashi saboda jin yadda yake bata taimakon
gaggawa dan hana numfashinta ɗaukewa.
Zazzafan numfashi ya fesa mata kana ya zuƙo nata sassayan numfashi dake gab da komawa
cikinta ya fizogoshi da ƙarfi.
Wani irin miƙa tayi tare da sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya da ya tabbatar da daidaituwar
numfashinta.

Kusan a tare Addawa da Taj ɗin duka dire ajiyar zuciya dake nuna samun nitsuwarsu.
A hankali yake ci gaba da shafa goshinta tare da ɗan sa yatsarsa manuniya yana ɗan kwantar
da gashin girarta ɗaya da ya hautsine.

Gefen kanta Addawa ta zauna bisa hannun kujerar murya cike da kaɗuwa da kulawa tace.
“Kina da Asma ne?”.
A hankali ta jujjya mata kai alamar a'a, shi kuwa Taj yatsarsa yasa kefen kuncinta ya goge mata
hawayenta dake kwaranya, cikin sanyi murya yace.
“Ma'eesha meke damunki? Meya saki kuka? Ki gaya min koma menene zanyi maganin abin
bazai sake sa min ke kuka ba”.
Ido a lumshe tace.
“Taj Laylah ke ƙara tabbatar min wai da gaske anyi mata fyaɗa wai ka maida ita tamkar matar
aurenka, tun sanda kuka dawo Nigeria, Laylah tace min a ɗakinta kake kwana, saboda duk
sanda kake Ethiopia ne ake kwana mata a ɗaki, Laylah tace min bindiga kake nuna mata
kasata dole ta tsiraita, kuma kaima ka tsi...” Ina ta kasa ƙarasa kalmar dan tayiwa harcenta nauyi.

Addawa kam ido ta rumtse da ƙarfi, don ta fahimci kenan Laylah tayi mata cikekken bayanin
kamar yadda tayi mata cikekken bayanin yadda Taj ya maida ta, tamkar matarsa.

Cikin zubda hawayen ta miƙe ta fice daga Parlour'n tana mgnar zuci.
“Na sani Tajuddeen Namijine daya amsa suna na miji, na kuwa san cewa lafiyeyyene da yake
da buƙatar mace a kusa dashi, wacce yake so take sonshi wacce zata iya ɗaukar nauyin
buƙatar sa, a matsayin halittarsa ta cikakken namiji, duk da na ɗan fahimci ƙarfin tattalirsa da
buƙatarsa gadon kakansa ne, gashi an aura mishi wacce baya so bata sonshi, ban yarda ko
amincewa hakan zaisa Tajuddeen yayi fatali da iliminsa nutsuwarsa, kamalarsa har ya lalata ƴar
da ya ɗauko amana daga hukumar kula da marayun Palastine ba, Tajuddeen an cuci yarinyar
nan, an tozarta rayuwarta an liƙa maka baƙin fenti.

Amman na sani in sha Allah gskya zatayi halinta domin da wuya haƙƙinta da kai da zuciyata taƙi
yarda zaka aikata ya bari waɗanda sukayi wannan makircin su samu zaman lfy.
Ko dan haƙƙin tarwatsa tsakaninka da iyayenka da matarka duk da muna kyautata zaton zatayi
haƙuri da kuskurenka inma kai ka aikata”.
Koda ta iso Parlour bata iya amsa mgnar da Zulaihat da Laylah sukeyi Mataba, saboda ɓacin
rai da mgnar zuci da take yi.

A can Parlour Taj kuwa, kife kansa yayi a gefen kanta, so yake yayi mgna Amman ina ya kasa
sai wani irin rawa da lips inshi keyi kamar wanda aka saka cikin dusar ƙanƙara.

Ita kuwa Ishmah idanun ta dake zubda hawayen ta zuba mishi tare da ci gaba da yin sassayan
kuka tana faɗin.
“Taj kayi mgna mana”.
Cikin fizgo mgnar zuci yace.
“Kiyi haƙuri Babey wlh ni n...”
Da sauri tasa yatsunta ta toshe kunnuwanta tare da fashewa da kuka tana faɗin.
“No! No!! Nooooo!!! Taj kada kace min da gaskene”.
Kife kanshi yayi ya kasa mgna sai karkarwa da jikinsa keyi.

Ita kuwa Ishmah kukan taci gaba dayi.

Ethiopia
Adaya ce kwance bisa gadon ta, sai juyi takeyi, tare da jan gajerun tsaki a jere a jere, hannunta
ta manna bisa wuyanta.
Da sauri ta cire hannun saboda yadda taji jikinta, yayi zafi.
Juyawa tayi ta gefen hagunta tare da lumshe idanunta tana mai jin ɗan karen gajiya da
zazzabin da yakeda nasaba da rawar data wuni yi kai kace injice itan.

Da kyar dai ta samu wuraren ƙarfe ɗaya. bacci yayi awon gaba da ita.

Doha Qatar.
A hankali take sauƙe ajiyan zuciya a jere a jere bisa alamu tana cikin kukan ne, bacci ya sureta.

Shi kuwa Taj ɗin a hankali yake sauƙe numfashi tare da taune lips inshi na ƙasa, so yake yayi
bacci ko ya suma ko Allah zaisa yaji sauƙin zafi da ƙuna gami da raɗaɗin da zuciyarsa keyi
masa, to ya zaiyi da rayuwar sa, ina zai shiga ya samu sassauci, kullum tabbatar a yiwa Laylah
gyaɗe ƙara bayyana sukeyi ga batun cikin da akace tana ɗauke dashi, shine babbar matsalar
rayuwar sa, ganin cewa ya cinye fiye da rabin daren a nazarin da bai samu mafita bane, yasa
ya miƙe yaje yayi al'wala kana ya dawo Parlour ya rinƙa nafilfili tare da tilawar Qura'ani mai
girma gami da tasbihai da neman sassaucin zafi da ƙunar ƙadaddarorinsa.


Washe gari ranar Friday, kasan cewar yau ba aiki dan a tasu doka da ƙa'idar ƙasar Jumma'a da

asabarne ranakun hutun mako, ranar Sunday to Thursday ne ranakun aikinsu.

Tsaye take a tsakiyar Parlour, tare da lumshe kumburarrun idanunta, ringing ɗin da wayarsa
keyi ne yasata buɗe idanunta.
“Dr Abbas”. Ta furta saman lips inta lokacin da taga shine mai kiran.
“Na rasa meyasa Taj baya son riƙe wayar nan yanzu wayarda yasha cemin ta family insa ne da
shaƙiƙansa makusanta shiyasa bai rabuwa da ita, yanzu kuma sam bai riƙeta ma, sai dai ya riƙe
waccar da yake cewa layin ciki na al'ummar duniya baki ɗaya ne.”
Sai kuma tasa hannunta ta ɗauki wayar ganin kira ya kuma shigowa.

A dai-dai lokacin kuma Taj ɗin ne zaune, a balcony dake bayan dinning area ɗinsa, zaune yake
bisa kujerar sai System nashi dake gabanshi bisa ɗan madaidacin table ɗin dake gabansa.
Yayinda ya kafa wayarsa yana video, a shafinsa na TikTok inda yake karanta suratul Khaff
kamar ko wacce ranar Friday domin tunasarwace ga al'ummar musulmi, kasan cewar yana bin
ayoyin daki daki ne, so daga aya ta 59, 60, 61, 62. Yayi kana yayi saki video bayan ya ɗanyi
rubutu a sama kaɗan, Don't forget to read suratul Khaff on Friday. Jumma'at Mabrooq to all
Muslims Ummah.
A hankali ya gyara zamansa tare da lumshe idanunsa kana ya buɗesu yana kallon fuskarsa a
cikin Camerar wayar tasa da yatsarsa ta ɗan taɓa, ya shiga kamar zai yi wani video ɗin.

Cikin sanyi ya kuma lumshe idanunsa da suka sauya launi tun ranar da Yah Abana ya koreshi
basu sake dawowa asalin launinsu ba.
Wani irin rauni, bege, so, ƙauna, gami da kewar iyayensa da ƴan uwansa da ahlinsa baki ɗaya
yakejin.
Ji yake tamkar yayi fiffige ya ganshi a tsakiyar Parlour Yah Abana wanda ya sani yanzu haka
suna can suna cike a Parlour, sun sashi a tsakiya, ji yake tamkar zuciyarsa zata fashe dan so
da begen ganin Ummeeynshi da Yah Abana, so yake ya ganshi a tsakiyar yayunsa da
ƙannensa, ji yake yi yayi rashin da bazai manceba, da ya kamata yaye kansa da kare kansa da
haka bata faruba da yau shi ya limancin Yah Abana kamar yadda ya saba tsawon shekaru in dai
yana Ethiopia.

Ishmah kuwa a hankali ta ɗan haura saman dinning area ɗin, ido ta zuba wa ƙofar da zai sadata
da balcony ganinta kamar a buɗe da ɗan sauri ta isa gaban ƙofar, tana ɗan jan handily ɗin
kuma taga ashe a buɗe take.

Shi kuwa Taj haka nan yakejin.
Wasu irin zafafan hawaye masu masifar ɗumi suna tsatstsapo mishi cikin jijiyoyin idanunsa,
haka nan yaji wasu baitukan na dira kan harshensa cikin harcen Amharic murya can cike da
sanyi gami da rauni ya fara baitukan.
“Da Babana nake, nakayin tutiyyyyah”.
Yaja ƙarshen baitin cike da raunin da yasa hawayensa bayyana cikin ƙwayar idanunsa da hakan
yasa idanun nasa yin wani irin sheƙi da ƙellin hawayen suka bada wani special collar mai tafiya
da hankalin.

Dai-dai lokacin Ishmah ta ƙarasa fito hango shi zaune, ya dasa waya a gaba, kana ga wasu
amintattun baitukan da yake yi wanda suka sa zuciyarta raunata har ta kai ga jikinta yayi sanyi,
a hankali ta nufi inda yake zaune yana fuskantar ta, sai dai sam bai gantaba saboda zuciyarsa
data raunata ga ruwan hawaye daya cika mishi ido.
Sassayan numfashi ta fesar tare da lumshe idanunta saboda taushin da zaƙin sautin muryarsa
da ya wadaci jinta, a hankali ta zauna

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login