Showing 39001 words to 42000 words out of 47460 words

Chapter 14 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6562

ta gyara zamanta tayi, dai-dai lokacin kuma Dr Amdaz ya fito daga Consultings
room 1, ganinsa yasa duk suka nitsu.
Patients insu wanda a ƙalla sun kai 16 ya kalla tare da yi musu, ya masu jiki.
Kana ya wuce ya nufi inda Dr Abbas yake gaisawa sukayi tare da juyawa suka nufi hanyar fita.
A bakin ƙofar fita Reception ɗin suka tsaya tare da zuwa aminin nasu idanu suna sakin
murmushi.

Shi kuwa Taj cikin nitsuwa ya fito daga cikin motar, tare da miƙawa Ishmah hannun, hannun ta
bashi, haɗe tafukan hannunsu yayi tare da harɗe yatsunsa cikin nata, kana yayi mata nuni da
hannunsa ɗaya tare da cewa.
“Bismillah fito Babey”.

Sassayan numfashi ta fesar tare da ziro sawunta waje.
A hankali ya ɗan matsa kaɗan tare da jawota ta ƙarasa fitowa.

Dai-dai lokacin kuma Bilal ya buɗewa Laylah dake gaba, marfin motar tare da cewa.
“Sai na fito da kene?”.
Kai ta ɗan jujjuya kana ta fito, ta tsaya gefenshi.

Shi kuwa Taj da Ishmah, tsayuwa sukayi a jere kai kace, wata da zahara ne, sai wani irin ƙyalli
da sheƙi gami da sassayan ƙamshi da suke bazawa cikin shigar su da tayi kamanceceniya.
Shi Taj cikin shigar farin wondon jeans ne sai long sleeve shirt black blue color mai masifar
kyau da sheƙi, daga sama can wurin wuyansa bai maƙala botur ɗin ƙarsheba hakan ne ya bawa
farar fatar wuyansa zuwa saman ƙirjinaa mai ɗauke da yalwataccen gashi kwance lip-pli ya ɗan
bayyana. Daga ƙugunsa tsadadden belt ne shima Black blue ne ɗamare da ƙungunsa wanda hakan ya
bawa surar jikinsa damar ƙara bayyana cike da haiba.
Sai siririn glass irin nasu na Doctors dake manne da idonsa, wani irin kekkyawan sheƙi da ƙyalli
lips in shi keyi, hakama sajensa da yake kwance lip-pli gwanin ban sha'awa.
sai kuma Half cover shoe dake sawunsa, na kamfanin Gucci shima Black blue.
Ita kuwa Ishmah wata tattausar rigace fara ƙal a jikinta, short sleeve shirt, sai kuma wondon
pallazo shima fari, ta ɗaura wandan kan rigar saman cikinta kaɗan hakan ne ya bawa lafeffen
cikinta bawa ƙirjinta damar bayyana ra'anul ain.
Sai kuma after dress, black blue collar, data ɗaura a saman shigar tata, wacce ta ɗan haɗe
igiyar tsakiyarta kaɗan, sai farin glaye tsiriri da tayi rolling kanta da shi, wanda ya bawa
kekkyawar fuska tsaro na musamman da fidda haibar kyanta, pink lips inta kuwa sai sheƙi
sukeyi, hakama gashin girarta dake kwance lip kana ya ɗan haɗe a tsakiyar saman hancinta ya
bada siffar W. Farin idonta ya ƙara bayyana ne, sabida ɗan kollin data zizara.
Sai kuma siririn glass fari ƙal mai garai-garai data manna a idonta.
Sai takalmi cover shoe mai ɗan karen tsini Black blue da tasa, sai wayarta dake hannunta na
hagu yayinda hannunta na dama ke cikin hannun Taj ɗin ya harɗe yatsunsu gam, yana
murzawa a hankali.

Sai wani irin ni'imtaccen ƙanshin mai masifar daɗi sha suke bazawa, na turaren kamanin Gucci,
intense Oud.

Kusan duk a tare Ƙananan ma'aikatan nasa sukayi mishi zobe, suna kwasar gaisuwa kamar
yadda ya saba yiwa ma'akatan TAJMUH, haka ya fara, amsawa yana mai jinjina musu da basu
ƙarfin guiwa yake cewa.
“Aikinku yayi, manyan ma'aikatana”.
Yayi mgnar da iya kar mutumtaka tare da ɗan jujjuya ƙwayar idanunsa ganin ko ina na cikin
Hospital ɗin yayi fes-fes gwanin kyau sai ƙyallin sabunta yake.
Bilal ya ɗanyi murmushi tare da gyara riƙe hannun Laylah kana yace.
“Yah Afif karfa su Yah Amdaz suce kana bawa cliners matsayinsu fa”.
Kai ya ɗan jinjina tare da cewa.

“Hmmm Bilal ai matsayin su ya ɗara na Doctors da Nurse's, domin in babu su a asibitin,
ƙazanta zata sa babu Dr da zai yarda yayi aiki anan, bare kuma patients su zo ko ba haka ba
Ma'eeshah?”.
Yelwataccen murmushin da yasa dimples ɗita duka biyu lotsawa tayi, tare da amsa gaisuwar da
cliners ɗin keyi mata kana tace.
“Sosai ma kuwa, dan duk Kyan wuri in ba gyara lalacewa yakeyi”.
Cikin jin daɗin karramasun da sukayi, suka rinƙa godiya kana suka juya kowa ya koma bakin
aikinsa.

Shi kuwa Bilal kai ya jinjina cike da gamsuwa.

Shi kuwa Taj juyawa yayi ya ɗan fuskanci gefen gabas, inda wani tamfatsen gini na musamman
yake shimfide daga sama an rubuta Reception. Da manyan baƙi,
Cikin sauƙe numfashi suka nufi ƙofar shigan. Bilal da Laylah na biye dasu a baya, riƙe da
briefcase inashi.

Murmushin mai nuna cikar jin daɗin Dr Abbas da Dr Amdaz sukayi tare da cewa.
“Wow Masha Allah, kaga wani haɗin Allah a nan”.
Kai Dr Abbas ya jinjina tare da zaro wayarsa ya fara yi musu hoto, a duk taku da motsin
tafiyarsu suna masu nufarsu.

Shi kuwa Taj tsuke fuska yayi dai-dai lokacin da suka isa gab dasu, cikin sanyi yace.
“Kai kana nan kamar yaro duk motsin ka sai kayi hoto”.
Murmushin Dr Amdaz yayi tare da cewa.
“Alhamdulillah patients ɗin yau zasu samu ganin Sheykh Dr Afif dan da yawa ma suna zuwa ne
da yaƙinin zasu samu ganinka, dan haka yau zamu huta tunda ga uban gayya”.
Shi kuwa Taj fuskarshi ya ɗan kwaɓe tare da yi mishi irin kallon nan na.
“Toh bani hanya”. Fahimtar hakan ne yasa Dr Abbas yin saurin juyawa suka shiga cikin
Reception ɗin.
Yana faɗin.
“Ya naga kamar Madam ɗin ma tamuce”.
Da sauri suka kalli juna jin Taj yace.
“Tawa dai”.
Cikin sakin fuska Dr Amdaz yace.
“Eh yana nufin kamar itama likita ce ko?”.
Ɗan mirza tafin hannunta yayi cikin nasa tare da cewa.
“Itace ma mai Hospitals ɗin ai”.
Kai suka jinjina tare da biyo bayansu.

Sassayan ajiyan zuciya, Ishmah ta sauƙe lokacin da taga duk ma'aikatansu suna ta fitowa.
Ido ta zuba wa, gabansu inda nanne Registry, sai kuma gefen hagu inda Nurse's Station ke jere
da Pharmacy, sai kuma gefen dama inda Consultings room 1 2 and 3 ke jere, sai kuma Pay
Point, dake tsakanin su.

Parlour ƙatone wanda ke ɗauke da wasu irin tsala-tsalan kujeru na al'farma, masu taushi, ke
jere daga tsakiya, wanda zai iya ɗaukan mutum 20 zuwa 30, sai kuma babban TV dake manne
jikin gini, sai AC daga can sama dake fesa sassayan iska mai sauke ƙasala.
Cikin yin ƙasa da murya yadda shi kaɗai zaijita tace.
“Masha Allah komai yayi kyau”.
Yana ɗan ƙara jawota kusa dashi yace.
“Alhamdulillah tunda kin yaba nasan kowa zai yaba”.

Kusan duk a tare suka fito, yayinda har hada baki sukeyi wurin cewa.
Good morning sir. Morning sir. Kai yake ɗan gyaɗa musu tare da ɗan motsa lips inshi a hankali
yana faɗin.
“Morning”.
Daga nan kuma suka nufi Office ɗin Dr Abbas dai-dai lokacin kuma Dr Farida ta fito daga cikin
Office ɗinta.
Da sauri ta mara musu baya.
Ta shiga da sallama tare da faɗin.
“Good Morning sir”.
Ta ƙare gaisuwar cikin yauƙi da kwarkwasa, sai kuma ta tsaida idanunta kan fuskar Ishmah
dake ɗauke da yelwataccen murmushin mai fidda haiba da kwarjinin da yasata dole ta janye
idanunta, ta maidasu kan Taj ɗin tare da yi mishi kallon dake bayyana zafin sonshi dake cikin
zuciyarta. Sai kuwa tayi saurin
rumtse idanunta tayi da ƙarfi ganin Taj ɗin ya ɗan jawo hannun Ishmah ya ɗaura kan lips inshi
tare da ɗan sumbata kana ya ɗan fara goga bayan hannunta kan sajensa zuwa saman lips
inshi, sai kuma yasa hannunsa ɗaya ya jawo kujerar baya kaɗan, kana ya ɗan juyo ya kalleta
cikin narke ido da murya ya ɗan motsa lips inshi a hankali tare da ɗan ɗaga sauti yadda Dr
Farida zata iya jinsa yace.
“So sorry Babey na barki a tsaye ko, Afwan my life zauna”.
Wani irin yam yam tsikar jikinta ya amsa saboda jin sautin muryasa har cikin kwanyarta.
Dr Amdaz kuwa kauda kai gefe yayi.
Shi kuwa Dr Abbas ido ya zuba wa Dr Farida data ƙara diriricewa tuni launin fuskantar ya
sauya.

Shi kuwa Tajj har ranshi yana hakane dan Dr Farida ta samawa ranta salama ta daina bibiyarsa
da kallon kura yaga ɗanyen nama.

Bilal da Laylah kuwa gaida Dr Farida sukayi sai dai ina ta gaza amsawa saboda firgincin ganin
kyaun sura da haibar Ishmah da kuma ganin zallan zazzafan so da ƙaunarta cikin ƙwayar
idanun mutumin da tafi so fiye da kowa a duniya.

A hankali ta zauna tare da kallon Dr Farida cikin girmama kai tace.
“Dr Farida ko?”.
A diririce Dr Farida ta gyaɗa mata kai tare da gaida ta, ta ɗaura da cewa.

“Kin sanni ni kuma ban san ki ba”.
Da sauri ta maida kallonta kan Taj ɗin daya ɗan shafi gefen fuskar Ishmah yace.
“Matatace. Aysha Abdallah Matawalle, Mrs Dr Afif Muhammad Taj.”
Wani zazzafan numfashi Dr Farida ta fesar tare da rumtse idanutan kana a hankali tace.
“Masha Allah”.
Ta ƙare faɗar hakan da nazarin, to dama wannan ce matar da mahaifinshi ya aura masa, kuma
Dr Abbas yace mata baya sonta bata sonshi, kenan ƙarya Dr Abbas yayi mata, ai waɗanan ko
mahaukaci ne ya kallesu yasan akwai true love a tsaka ninsu.”

Shi kuwa Taj files ɗin patients dake jibge kan Table ɗin Dr Abbas ya kalla kana ya kallesu tare
da ɗan gyara zamansa yace.
“Kamar akwai patients da yawa, ayiwa Dr Priter mgna taji dasu, ku kuma ga patients ɗin ku.”
Ya ƙare maganar da nuna musu Laylah dake gefen Bilal.
Sai kuma ya miƙa Bilal key tare da cewa.
“Kai kuma kaimin briefcase ɗin Office na sai kaje ka dauko Dr Priter”.
Da sauri Bilal ya amshi key ɗin tare da cewa.
“To”.
Kana ya juya ya fita,

Dr Amdaz kuwa da ido ya rakashi kana ya jujjuya kai tare da cewa.
“Hmmm Bilal ya samu abinda yakeso shiyasa ko gida baya komawa, shi a rayuwarsa in dai za'a
bashi mota yayi taja to burinsa ya cika”.
Kai Taj ya jinjina tare da cewa.
“Naji kuma ya yace min ya kusa komawa school”.
Da sauri Dr Abbas yace.
“A ina yake karatu ne?”.
Dr Amdaz na ɗan riƙo hannun Laylah yace.
“AL-Jami'atul Madina yake, karatu ni naso a rinƙa hanashi zuwa hutun ma”.
Cikin sauri Dr Abbas yace.
“To ku daina biya mishi kuɗin dawowa mana”.
Juyowa yayi ya ɗan kalli Taj jin yana faɗin.
“To ai hukumar makarantar ne suke biya dalibansu kuɗin zuwa Hutu suga iyayensu duk
shekara-shekara kuma ma yaro nason ganin iyayensa a hanashi dawowa.”

Murmushin Dr Amdaz yayi kana yaja hannun Laylah tare da kallon Dr Farida dake kallon
Ishmah tamkar madubi yace.
“Mutafi ko”.
Da sauri tace.
“Ok Laylah zo mu tafi”.
Ɗan kwaɓe fuska Laylah tayi tare da kallon Ishmah cikin sanyi tace.
“Aunty Ishmah muje tare”.
Cikin kulawa Ishmah ta miƙe tsaye tare da cewa.
“To Laylah”.

Cikin ɗan tsuke fuska Dr Farida tace.
“To ke me kika sani akan aikin likitanci? Ai sai dai Dr Afif yazo muyi aikin tare dashi”.
Cikin tsuke fuska Taj ya ɗan kalleta a fakaice kana yace.
“She's a big Gynecologist Dr, ki san abinda zaki faɗa”.
Yayi mgnar cikin kausasa murya.
Da sauri ta ɗan rusunar da kanta tare da cewa.
“Sorry Sir”.
Kai ya kauda gefe tare da kallon Ishmah Innocent face ɗinta ya kalla tare da sakin murmushi
gefen baki kana ya kalli Dr Abbas da Amdaz yace.
“Kuje kuyi aikin da kulawa”.
Sai kuma ya ɗanyi ƙasa da murya yace.
“Babey kuje, Allah yasa muyi farin ciki da zuwan”.
Ya ƙare maganar tare da ɗan jawota yayi mata yar ruggumar gefen nan da yasa Dr Farida juwa
ta kama hanyar fita.
Ita kuwa Ishmah murmushi tayi tare da cewa.
“In sha Allah zamuyi farin ciki”.
Daga nan taja hannun Laylah suka bi bayan Dr Farida, da Dr Amdaz,. Dr Abbas kuwa ya mara
musu baya.

Kai tsaye ɗakin gwaje-gwajen su na musamman suka nufa wanda yake tsakanin Laubor room,
da ɗakin Tiyata.
Ɗakin ɗauke yake da sabbin gadaje biyu, sai sabbin na'urorin na musamman, na gwaje-gwaje
da kuma na haske.

Cikin 40 minutes suka gama shiryawa komai da zasu buƙata.

Cikin kulawa Ishmah ta jawo Laylah tare da yin hikinar ɗan ɗaure hannunta ta samu ta debi
jininta.
Shett tace lokacin da taji zafin zira mata allurar da akayi.
Shafa kanta Dr Abbas yayi cike da tausayawa yace.
“Sorry”.
Ita kuwa Ishmah miƙawa Nurse's ɗin dake gefentan tayi tare da bata umarnin taje a goda komai
na lfyar jikinta tana jiran result.
Amsa tayi ta fita, daga nan su kuma ita da Dr Farida da Dr Amdaz suka fara bincikan lfyar
budurcin ta...


Shi kuwa Taj, tunda suka fita ya koma ya zauna bisa kujerar, tare da lumshe idanunsa ya fara
karanta suratul Yusuf daga forkonta.
Haka nan yake jin masifar bege da kewar iyayensa na sakar masa raunin dayayi sanadin
sinkowar ruwan hawayensa.
Sosai hawayen nasa suka tsananta zuba a dai-dai lokacin da yake karanta aya ta. 11.
“Qaalu yaa Abana malaka laa ta'amanna alaa Yoosufa wainna lahu lanasihuu”.

Kalmar Ya Abana da kuma fassarar ayar da take mgn kan yayun Annabi Yoosufa d suke yiwa
mahaifinsu daɗin bakin ya basu Annabi Yoosufa suje kiwo dashi, yasashi tsananta rauninsa da
hawayensa.
Suma kenan Banu Israel bare kuma yayunsa da ba komaiba mai zai hana shaiɗan nasara a
zuƙatan wasunsu.

Da sauri yaci gaba da karatun domin baya son ya zargi wasu daga cikin yayunsa akan
ƙaddararsa,
Musamman da yayi tuni da hadisin nan da Manzon Allah Sallallahu alaihi ke cewa.
“Azzannu zambu walau kana haqoon”.

Ethiopia.
Malam ne zaune a tsakiyar Parlour'sa yayinda duk ƴaƴanshi mazan ke zagaye dashi duk suna
zaune gabansa sunyi ƙasa da kawunan su.

Doha Qatar.
Bayan fitarsu Ishmah da kamar awa ɗaya da rabi.
Yaji an banko ƙofar Office ɗin da ƙarfi.
Cikin sauri ya ɗago kansa,
Idanunsa ya zaro baki ɗaya ganin wani irin taku da Ishmah keyi tare da nufosa gadan-gadan.

Tana riƙe da takardun Result's ɗin gwaje-gwaje da sukayi wa Laylah.

Wani irin kiɗimemmen numfashi ya fesar da ƙarfi tare da rumtse idanunsa da azaban ƙarfi
lokacin da yaga ta watso mishi ta....!


Kuyi haƙuri ba editing zakusha typing errors.

*Littafin INDA RAI na kuɗine 1k ne kacal ki biya ki karanta cikin aminci ba haƙƙin kowa a kanku
0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number
09097853276.*



By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: *INDA RAI*

*BOOK 2 PAGE 10*

*Yauwa Lahadi 28/04/2024. Wanda yayi dai-dai da cika watanni uku cib da rasuwar ɗan
uwana! Ƙanina Hamisu Aliyu Garkuwa, Yah Allah kaine mahaliccinmu kuma kai mai yawan
gafara da rahama ne a garemu duk da yawan zunubanmu. Ya Allah ka jiƙan wannan bawa naka
Hamisu kayi mishi gafara da rahama ka yafe mishi kura-kuransa ya rabbil alamin ka yalwata
makwancinsa ka faɗaɗa mishi ka haskaka mishi, ka ni'imta mishi kasa kushewarsa ta kasance
mishi dausayin Jannatul Firdausi dashi da mahaifiyarmu da ƴan uwanmu Abubakar da Auwal.
Ya zuljalalu Wa ikrami ka yafe dukkan magabatanmu musulmai*
*mu kuma ka bamu lafiya da nisan kwana da imani da dauwamemme. Ka bamu kekkyawan
rayuwa da ƙarshe kasa mucika da kyau da imani. Ya Allah kasa mana haƙuri da juriyar rashin
iyayenmu da yan uwanmu yan uwa makaranta inayiwa Ɗan uwana Hamisu barar
addu'a Qulhu ƙafa uku uku a gareku Allah ya kai haske kushewarsa*

*Dan Allah in dai kinsan baki shirya sayaba kada kimin mgn, masu cewa wai sun goda suga
number'n nayine, ko kuma a'a bari dai in na shirya zan sake miki mgn, ko kuma yanzu dai kuɗin
bai cikaba tukun sai sun cika, ko kuma a wanne gari kike, kai munyi nisa, toh in ba iyayiba ai
duk nisan state da kike ba ruwan mota ba inda bazai kai mikiba, nake turawa ƴan ƙasashen
wajema. Kuyiwa Allah da Manzonsa in dai in kinsan Baki shirya sayan kaya ba ku daina min
mgnar ku bari sai kun shirya,kada kizo ki ɓata min lokaci a banza, wlh ni na tsani harkar
karanta, duk bayani na gamayi in dai saya zakiyi ga kuɗin kaya ga account no ga numberta ai
sai ki biya kawai kafin kimin mgn. Tunda dai ga alamominshi da duk illar da yakeyi na faɗi in
kina dashi faƙat in babu kada ki wani zo kice min bayani dan ko kinzo iya bayanin da zan miki
kenan*
Alamomin infection sune kamar haka. Rashin sha'awa. Ƙaiƙayin gaba Kiji idan ya fara miki
ƙaiƙayi kamar zakiyi hauka. Warin ko ƙarnin wurin. Fitar farin Ruwa mai fatsi-fatsi. Ƙurajen su
ɗan fetso ƙananan ko ƴan manya, melewar fatar wurin, Tusan gaba. Bushewar gaba, Rashin
ni'ima. Buɗewar gaba, domin har budurwa infection na iya buɗata. Ciwon mara ko ciki mai
tsanani yayi al'ada, rashin haihuwa, domin har baƙin mahaifa take toshewa. Ko kirinƙajin wani
abu na miki yawo ƙasan mara, ko jin zafi yayin yin fitsari, da kuma saduwa, da dai sauran
abubudann ban lissafa. Sune manyan alamomin infection.
Shin kin kuwa san illar da infection keyi miki, amman kinajin ɗaya daga cikin alamominta kinyi
bulum buƙui da ita a jikinki. To bari kiji illolin infection wato cutar sanyi.
Rashin haihuwa, ƙyara da hantara a wurin miji domin muddin kina tare da ita baki da wata
daraja a idanu nai, sabida ƙyamas kike ba damshi bare wata ni'ima mai Taste, Kinga kenan
shinfida ta lalace, in kuwa shinfiɗa ta lalace dole kiga sauyin fuska, domin su maza dole
sunason wurin da kwaranya, zaki kasance baki da wani daɗi da ɗumin da mai gida ke buƙata.
Kinga duk tsabtarki da kyanki da iya girkinki shinfidarki ta zama lami. Kiyiwa Allah ki nemawa
kanki lafiya ki samawa mijinki da ke kanki nitsuwa.
KADA KUJI IYA WANNAN DOMIN AKWAI MUGUN INFECTION

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login