Showing 27001 words to 30000 words out of 47460 words

Chapter 10 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6560

cike da mamakin ganin tsinkensa basu taɓa ba. A fili
yake faɗin.
“Duk da dai hakan ya zama sanadin kareni da yin dakon zunubin cutar da ita wurin raɓa mata
HIV, Allah ne ya kareta, Afif ya zame mata Garkuwa Yah Allah ka bani dai-dai dani mai irin
ciwona mu rufawa juna asiri.

Ethiopia.
Kwance take tayi lip ta rufe jikinta daga sama har ƙasa, wayartace a hannunta hotonshi dake
fuskar wayar tata ta zubawa idanu babu ko kiftawa cikin murya mai cike da yanayin muradi
tace.
“Kai wannan na mijine, cikekken namijin duniya, duk inda Namiji yake ya kai namijin da ko
wacce mace take fatan mallakar irinsa Ya Allah kasa in samu na Habibina ma haka yake”.
Sai kuma ta fesar da numfashi tare da juyawa ta kwanta a kife cike da begen makusanci a
gareta Allah ya sani ita macece mai muradi.

Doha Qatar.
a hankali ya ɗan yunƙuro kanta saboda jin yadda take sauƙe numfashi alamun bacci ya fara
nasarar yin awon gaba da ita, kanshi ya ɗan ɗago matso da lips inshi yayi dai-dai kunnenta
cikin raɗa yace.
“Babe! Babe!!”.
Sai kuma ya ɗan ƙara matsota cikin sanyi ya kuma kiranta yana mai ɗan ɗaura ƙafarsa ɗaya
kan cinyoyinta.
“Hmmmmmm”. Tayi sauti alamun ta amsa.
“Babe zan rage Miki kayan nan sunyi miki yawa a jiki”.
Ya ƙare maganar yana zame mata hannunta cikin after dress ɗin.
“Hmmmmm”.
Ta sake faɗi Murmushin gefen baki yayi domin ganin yadda duk jikinta ya sake.
A hankali ya zare mata ɗaya hannun ma.
Ya zamana tana kwance ne kawai a samansa.
Komawa yayi ya kwanta tare da jawota jikinsa ya ɗaurata kan cikinsa ya manne kanta bisa
ƙirjinsa.
Sai kuma yasa hannunsa ɗaya ya tattare after dress ɗin ya cilla shi can bisa kujera, blanket ɗin
ya jawo ya rufe musu jiki, kana ya ɗaura tafukan hannunsa bisa bayanta yana ɗan shafawa a
hankali yanayin sama da ƙasa dasu tare da ɗan mammatse wuyanta kamar maiyi mata tausa.

A hankali yaji idanunsa na lumshe,
ƙamshin jikinta ya kuma shaƙa a karo na barkatai tuni bacci yayi awon gaba dasu manne da
juna.

Ethiopia
Washe gari da safe misalin ƙarfe tara.
Yah Aryan ne, zaune a Parlour Ummu Aryan ɗin, bisa alamu waya yakeyi da ɗansa Arfah cikin
takaici yace.
“Wai ni Arfah anya kuwa ko ni ubanda da na haifeka kana sona kamar yadda kake son Afif
wannan wanne irin nacin tsiyane da jarabar mayata shi yana can yana harkokinsa da
karuwansa yama mance daku, kai ka buwayeni”.
Cikin takaici Arfah yace.
“Wlh Uncle Taj ba mazinaci bane, Dad ka daina faɗan haka”.
Cikin tsawa yace.
“To ubana yanzu dai saura ka rufeni da duka kawai ko. Maza gimtse wayar wlh in ka sake min
mgnar Afif cin ubanka zanyi hegen yaron mai nacin jaraba”.
Jin haka ne yasa Arfah katse kiran kana yayiwa Imaran bayanin yadda sukayi da mahaifinsa ya
ɗaura da cewa.
“Nifa gani nake kamar Abba na baya son Uncle Taj”.
Da sauri Imran yace.
“A'a Arfah kada ka faɗi haka, ya zaiyi ya ƙi ɗan uwansa yanzu bari in sake gwada kiran Uncle
Taj ɗin”.
Ya ƙare maganar da kiran Taj ɗin, a hankali ya juyo ya kalli Arfah cikin sanyi yace.

“Layinsa baya shiga bari sai anjima in sake gwadawa”.
ranar dai haka sukayi ta gwadawa Amman bata shiga.


Qatar
Ƙarfe Goma dai-dai jirginsu Aunty Amina, Goggo Dija, Aunty Nana, Garkuwa, Khadija, Adam.
Ya ɗaha daga Doha Qatar zuwa Abujan Nigeria.
Sai da suka ga tashinsu kafin, Taj da Ishmah suka fito Airport ɗin suka nufi gida.

Bayan sun dawo gida
Kwaɓe ta tsuke tare da tura baki, ɗan gajeren murmushin yayi tare da cewa.
“Afwan laifin me nayi ne wai?”.
Ya ƙare maganar yana ɗan zamewa ƙasa ya zauna gabanta bisa kujerar.
Murya can ƙasan cikin dishewa alamun tayi kukan tafiyarsu ta ɗan kalleshi kana tace.
“Shike nanfa sun tafi sun barni ni ɗaya, yanzu bani da kowa a ƙasar nan”.
Da sauri yace.
“Babe ba gani ba, Taj ɗinki fa, bakiji me Abba yaceba”.
Cikin sanyi tace.
“Naji”.
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
To taso muje mu kwanta ki samu ladana Inyi bacci Kinga sai naji ɗimin jikinki nake iya bacci”.
Cikin ƙasa da murya tace.
“To Amman banda cire kaya”.
Hancinta ya ɗan lakace tare da cewa.
“Jiyama ke da kanki kikace in cire miki, da izininki na cire Miki ai kuma ai ba kaya na cireba”.
Ya ƙare maganar da jan hannunta suka nufi Bedroom.

Alhamdulillah washe gari ranar Monday aka buɗe Al-AHLI AFISHA HOSPITAL, lfy duk Doctors
and Nurse's da cliners sun fara aikinsu babu kama hannun yaro buɗe asibitin kuwa yazo da
gagarumin nasarar da tasa duk Qatar aka san da asinitin saboda wata balarabiyar da aka
cirewa yara tagwaye biyar reras uku maza biyu mata, kuma duk suna lfy.
Acan Nigeria ma Alhamdulillah sun isa lfy ko wacce ta koma gidanta sai Khadija da Goggo
Dijan ne da suke ɗan ƙara huce gajia kafin su koma Gombe.


Bayan kwana uku, wanda ya kama yau kwanansu goma kenan da zuwa Qatar.

A Parlour suke shi da Ishmah da Addawa yayinda Zulaihat da Laylah suka fita suna can baya
suna lilo.

Ido Addawa ta ɗan zuba mishi saboda ganin yadda ya zauna yayi tagumi da hannun biyu.
“Zuwa yanzu dai ya kamata ace, ka bar duk wannan damuwar tunda Ishmah dai tayi maka

kekkyawar fahimta.”
Nannauyan numfashi ya sauƙe tare da cewa.
“Ya za'ayi hankali na ya kwanta bayan kuma ance Laylah nada ciki, kinga tana cikin matsala an
cuceta anyi mata fyaɗa da ƙanan shekarunta, sannan ance tana da ciki”.
Cikin kaɗuwa da tsoro Ishmah ta ɗan zaro idanunta waje tare da cewa.
“Innalillahi ciki kuma Addawa, to wai wanne mara imanin ne yayi mata fyaɗen nan kuma ace
harma da ciki?”.
Cikin sanyi Addawa tace.
“Abinda kenan har yau bamu ganoba, mun kasa gano ko binciko wanda yayi mata fyaɗen har
ya narka mata ciki”.
Cikin tausayawa da ƙunan rai hawaye na cikowa Ishmah tace.
“Ba komai wlh na rantse da Allah in sha Allah sai na binciko wanda yayi mata cikin nan kuma
sai an gano shi ya amshi hukuncinsa in sha Allah zan yi bicike kan lamarin”.
Ta ƙare maganar da yaƙini.
Addawa kuwa bayanin duk yadda abubuwan suka faru ta labartawa Ishmah sai dai bata faɗi
mata sharaɗin Malam na cewa muddin Taj ya bari ya haɗu da wani dangi nasa ko yayi
mu'amala da ahlinsa ba, a bakin auren Ummeeysa.
Tadai gaya mata yace ya ciresa a yaransa baya kuma bukatar sake ganinsa ya kuma ce ya
raba sunansa da nasa kasake tayi tana jin Addawa cike da nazari da zurfin tunani a hankali
tace.
“Tajj anya kuwa ka gwada Laylah da kanka? Anyama akwai wannan mgnar, nifa gani nake
nakircine kawai da iya tsara gadar zaren kai kuma ka rubta ciki kuma ka rasa mai tayake
warwarewa”.
Cikin sanyi yace.
“Ma'eesha kiga yadda Laylah ta sauyafa duk alamun ciki bayyana gareta”.
Cikin nazari tace.
“Hmmm Tajj kamar ba likitaba kawai sun haɗa ma zafi kan zafine da fushin Yah Abana shiyasa
baka iya tuna komai ba.
Amman in sha Allah zan nazarci lamarin”.
Kiran salla Magrib da shigowar su Laylah ne yasa suka watse taron nasu.

Misalin ƙarfe tara na dare.
Zaune take a bakin gadonta yayinda Laylah ke gabanta cikin nitsuwa da kuma son kwantar da
hankalin Laylah da son gane abinda ke ɓoye tace.
“Laylah tashi in aikeki wurin Uncle Taj.”
Da sauri ta zazzaro idanu tuni jikimta ya fara rawa murya a firgice tace.
“Afwan Aunty Ishmah ina tsoro, ni bazan jeba”.
Cikin tsareta da ido tace.
“To Laylah me kike tsoro wai? Uncle Taj ɗinkin nefa, me zai Miki?”.
Cikin rawan murya da jiki ta ƙara matsowa jikin Ishmah cike da tsoro tace.
“Ni dai ina tsoronsa tunda yake cemin zai yankani in ban bari yayi min cikiba”.
Ya Salam shine abinda Ishmah ta faɗa cike da ɗimuwa da mamaki gami da firgici tace.
“Laylah Uncle Taj ɗin naki ne yake cewa zai yankaki in baki bari yayi miki cikiba, cike da gskya

da gskya tace.
“Wallahi shine tunda mukaje Nigeria muka dawo, duk randa ya dawo Ethiopia a ɗakina yake
kwana kuma sai yace in nayi ihu zai kasheni kuma in bari yayi min ciki, wai kuma kar in gayawa
Aunty Meymey”.
Far-far jikin Ishmah ke rawa da tsuma, da sauri tasa hannunta duka biyu ta riƙe kanta saboda
zafi da raɗaɗin kalaman Laylah yasa kan nata fara sarawa da ƙarfi, sai kuma ta buɗe bakinta da
ta samu numfashi ya dai-dai saboda jin numfashinta na cizga.
“Yah Salam wannan makircine aka ƙullawa Tajj aka ɓatashi a gaban ƴar da yakeji shi ya haifa” .
Ta ƙare maganar zuci tana mai rumtse idanunta saboda jiri data fara gani.
Ita kuwa Laylah cikin Tsananin kukan rauni da ruɗu taci gaba da cewa.
“Har bindiga yake nuna min, yace min in cire kayana”.
Da sauri Ishmah ta riƙo hannun Laylah cikin son gano gskyr da takejin tsoron in ya tabbata
cewa anyiwa Laylah fyaɗe nan tabbas zuciyarta zata buga domin tasan har abada yarinyar
bazata yarda ba shi bane.
Murya na karkarwa tace.
“So sorry Laylah, kiyi haƙuri daina kuka, gaya min gsky tsakanin ki da Allah Uncle Taj ɗin ne,
yake miki haka kin ganshi da kyau da haske lokacin da yake shiga?”.
Cikin shesh-sheƙan kuka ta fara gyara murya cikin gskyar lamarin da fahimtar yarintarta tace.
“Eh ko na kashe wutama, yana shiga yake kunna wuta, ya cire kayansa yace nima na tuɓe,
kuma ya kwanta kan g...”
Da sauri tayi shiru ba tare da ta ƙarasa mgnar ba, saboda jin Yadda Ishmah ta saki wani irin.....


*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne rak 0661110170
GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276
mutanen Niger kuma 1000fc ne jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076
idan kika karanta min littafina baki biyaba wannan ke da Allah*


By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286:

*INDA RAI*
*BOOK 2 PAGE 6*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*



*Bononza! Bononza!! Bononza!!! Kayan Mata na musamman. Kuɗi nake nema wuri janjau
yaseen saboda inada abin yi dasu!!! Yoh ace min turo account no ma kaɗai yana sani farin ciki,
inaga kuma inga alerts na zubowa kamar ruwan sama, toh wannan shine sirrin rashin raina

Customers ɗina, ina yinku ina ganin girman yardar da kuke min saboda wasu ko mgna bata
taɓa haɗani da suba sai kawai su turi dubban juɗaɗensu kafin ma suzo suce min ga abinda
suke, wlh hakan kan sani jin in mutuntasu sabida ai yardace ta kawo haka, yinku ina sonku
domin kuna sani farin ciki. Shiyasa nake sake muku Garaɓasaa kamar bansan cewa komai na
rayuwa ƙara tsada yake ba. Kuɗi nake so da zafi zafinsu, Ku zo ku sayi kayana.Yauwa kina ji ko
ni ba bashi ko maula ko alfarmarku nake nemaba!!. A'a talla nake muku ku bani kuɗi niko in
baku kaya ɗa'a.*
*Da ɗumi-ɗuminsa Set ɗin mgnin infection 8k kunga garaɓasa har 2k half 4k Dadiharmadiga 4k
maliƙi 5k ragi har na 2k robar Ƙasaitacciyar mace 5k ragi har 2k botikin gumbar 9k a 8k
ƙananan robobiin garuka gumbunan da tsumi na 3-3k duk a 2,500 kunga ragin dari biyar biyar
ai ba wasaba, haɗin kazar 20k a 17k na 15k 13k garin babambaɗe 4k al'ajabu 4k idan kuma
kayanki ya kai na 50k zuwa sama in dai arewa kike to Free Delivery ne sis. In kuma na 40k 35k
30k 25k ne kuwa gareku Kanawa, Gombawa, Josawa, Jigawa, Bauchi, Taraba, duk Free
Delivery ne kuma! In kuma kayanki ya kai na 60k 70k 80k 90k zuwa 100k kinada tukuicin ɗan
haɗin humra da kulacca da turaren wutan ga kuma free delivery. Nace ba tsaya mana kiji, inafa
araha kam Amman ina hana bashi, kuma wannan Garaɓasar daga yanzu ne yau ɗin nan laraba
24-01-2024, zuwa 01-2-2024 cib Garaɓasar zata sauƙa so ko kada ki karanta tallan bayan nan
kizo kice ai naga kince kaza da kaza da Free Delivery da sauƙin farashi, ɗaya ga watan biyu na
shekara dubu biyu da ashirin da huɗu na gotawa koda one minute ne to fa garaɓasa ta fece. In
a shirye kike ga account no. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki hankaɗo min
shaidar biyanki ta Whatsapp number na 08069423567. Maliƙi da ddhmdg abin 12k Amman a
10k Garaɓasar ma ai tayi yawa gaky, 10k fa wannan kayan alkhairi Please dan Allah in kinsan
baki shirya sayaba, kada kizo ki ɓata mana lokacinmu ki hutar da kanki nima ki hutar dani.*



Ya ƙare maganar da narke kwayar idanunsa cikin nata, wanda hakan yasa jikinta yin wani irin
fitinenne macewar da har yasa muryarta narkewa can ƙasan maƙoshinta tace.
“Tun yanzu?”.
Yana mai zira mata wasu fitinanuna lamura ta cikin gajiyayyun idanunsa ya motsa lips inshi a
hankali yace.
“Eh muje”.
Ya ƙare maganar tare da juyawa ya kalli su Addawa da Goggo Dija da Aunty Nana dake cewa.
“Maza tashi ku tafi”.
Ɗan rusunar da kansa yayi tare dayi musu sallama kana ya nufi hanyar fita.

Ita kuwa Ishmah ƙara matsowa tayi a jikin Aunty Amina tayi tare da yin rau-rau da ido sabida jin
Aunty Amina na cewa.
“In sha Allah Jibi da dare dai zamu tafi, in Allah ya yarda sai kizo gobe mu wuni!”.
Cikin sanyi tace.
“Dan Allah ku bari mu ƙara sati”.
Ɗan ture kanta Aunty Nana tayi tare da cewa.
“Tafi daga nan, da muke nan ɗinma tunda muka zo, bamu ga idonki ba sai yanzu, ke gaki yar

miji daɗi, muma da mazanmu, dan haka baza mu zama ƴan amshi shata ba”.
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Garkuwa kuwa hannun Ishmah taja tare da cewa.
“Zo muje daga ciki”.
Da sauri ta miƙe sai kuma ta kalli Goggo Dijan dake cewa.
“Kada dai ki mance mijinki na jiranki a waje”.
Da sauri Aunty Nana tace.
“Laa dama kinyi shiru Goggo ai bazata manceba”.
Khadijah ne ta ɗan harari Aunty Nana tare da cewa.
“Uwar sa ido ba”.
Sai kuma duk suka kalli Addawa ganin ta miƙe tsaye tare da cewa.
“Ai gwara ta bada himma ta kular min da jikana ta sama mishi farin ciki, in tayi mana haka mu ta
gama mana komai na rayuwar duniya”.
Cikin gamsuwa da hafimtar kalaman Addawa Garkuwa taja hannunta suka nufi ɗakin.

A bakin gado suka zauna cikin kulawa da fahimtarwa ta tsare Ishmah da ido cikin yin ƙasa da
murya tace.
“Da alama dai kin gaza kwantar da hankalinki bare ki kwantarwa mijinki nashi hankalin”.
Ajiyan zuciya mai nauyi Ishmah ta fesar tare da gyara zamanta kana a hankali tace.
“Na rasa me yake damun Taj, sam ba haka yakeba, na fahimci yana cikin tsananin damuwar da
ko bacci baya iyayi fa my Aunty”.
Ta ƙare maganar cike da damuwar hakan.
Tsuke fuska Garkuwa tayi tare da cewa.
“To ai duk laifinki ne Ishmah, ace kina mace macen ma data san zaman duniya da haƙƙin miji,
ace ki kasa kwantar masa da hankali da sama masa nutsuwa zuciya, har damuwa ta hanashi
bacci kina kuma tare da shi a muhalli ɗaya anya kuma Ishmah baki zama lusarar maceba.
Kin kuwa san tabbas ya ɗaukekine ya tafi Hotel dake dan ku samu hutun jiki dana zuƙatane,
keda kanki kika cemin yana cikin damuwa mai tsanani fa,
Kin kuwa ga kenan ya nemi kusanci da kene domin yana zato da yaƙinin kece farin cikinsa,
kece zaki sawa zuciyarsa nitsuwa da tausarsa ki kwantar mishi da hankali ki cire masa
damuwar dake tare dashi, Amman ace haka ya gagara kina tare dashi wuri ɗaya, ɗaki ɗaya, kai
gado ɗaya ƙarshenta ma pillow ɗaya, cikin blanket ɗaya, Amman ki kisa zama ƙasaitacciyar
macen da zata sa mijinta bacci wlh Allah kin bani kunya Ishmah.”
Cikin sauke numfashi tace.
“A'a my Aunty wlh tunda mukaje iyakarsa a ƙasa bakin gado, ko gefen bai taɓa zamaba.”
Sai kuma ta ɗan lumshe idanunta kana ta buɗesu ta zubasu kan Garkuwa dake yi mata kallon
mamaki a hankali tace.
“A zaunefa yake kwana yana karatu, wani lokacin ma kuka ne yake fizge muryarsa.”
Cike da takaici Garkuwa tace.
“Innalillahi Ishmah dan Allah ke bakya jin tausayinsa, kinfi kowa sanin Taj kin dai ga zahiri
damuwa tare dashi wai ke wacce iriyar mace ce?”.
A sanyaye tace.
“Ni nayi zaton yana damuwa ne da auren bazata da yayi min, dan akan haka yaketa bani

haƙuri, yana jaddada min shi masoyine a gareni”.
Sai kuma sukayi saurin kallon bakin ƙofar jin sallamar Addawa.
A tare suka amsa mata, jin sun amsa mata ne, yada ta shigo fuska ɗauke da Murmushi, a gefen
Ishmah ta zauna ya zama sun sata a tsaki cikin sanyi tace.
“Ishmah wurinki nazo”.
Tana ɗan juyowa tace.
“Toh Addawa gani”.
A hankali ta ɗan sauƙe numfashi kana ta kalli Garkuwa tare da cewa.
“Aysha, ƴar ɗakin kin nan fa tana bukatar tunasarwa”.
Da sauri Garkuwa tace.
“Sosai ma kuwa Addawa”.
Kai ta jinjina cikin hikima ta fara mgna.
“Kallo ɗaya nayiwa Tajuddeen na fahimci cewa har yanzu yana cikin damuwar data samu baro
Ethiopia zuwa nan Qatar, damuwar da take sirri a gareshi, ya kuma roƙeni da in sirranta masa
shi, da banyi mishi wannan al'ƙawarin ba, da zan baku dukkan labarin abinda ya faru, wanda
nakeda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login