Showing 6001 words to 9000 words out of 47460 words
Chapter 3 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf
ta miƙa mata ledar tare da cewa.
“Momyna tace idan kun zo in baku dama gashi an haɗa tun kafin kuzo”.
Karɓa Rahama tayi kana tace.
“Toh mungode”.
Sai kuma suka juya suka fita suna fita madadin Adam yabi hanyar gida sai taga ya ɗauki hanyar
gidan Hajja Umma ɗan ware idanunta tayi tare da cewa.
“Yah Adam ina zamuje”.
Yana murmushi yace.
“Wannan abin farin ciki Ni nake so inje in yiwa Hajia albishir duk da nasan cewa Uncle Naseer
da Uncle Ali nacan dasu aka ɗaura Auren amma sauri nake kada su rigani isa wajen suyi mata
albishir”.
Kai ta gyada tare da faɗin.
„Toh shikenan ”.
Koda suka isa suka faɗawa Hajja Umma farin ciki ya rufe ta atake hawaye ya shiga bin kuncinta
still tana murmushi kasancewar abu biyu ne ya haɗu mata Auren Jikarta da kuma tuno ɗiyarta
da Allah bai nuna mata wannan auren ba da take ta fata da burin ganinsa basu daɗe anan ba
suka fito suka dawo...
Acan gida kuwa kusan baki ɗaya ƴan Uwa sun hallara wannan yakira wancan lokaci ɗaya suka
taru Al'amarin auren Ishmah yazo abazata anata addu'ar Allah ya bayyana mata mijin Aure na
Alkhairi sai Allah ya saƙƙo musu da abin alokacin da basu zata ba basu tsammata ba abin yazo
musu abazata Akuma ƙanƙanin lokaci Yah Muhammad da har zuwa yanzu bai tashi gaban
Aunty Hauwa bane ya juya ya kalli sauran Ummomin sa cikin sanyi yace.
“Alamarin Ubangiji akwai bada mamaki akwai abin tsoro aciki”.
Kallon Aunty Hauwa yayi jin tana cewa.
“Sosai ma Muhammad”.
Cikin sake jinjina girman Ubangiji Aransa yace.
“Al'amarin yanda Auren nan ya kasance da yanda ya faru har tsoro ya bani”.
Hajia Aisha wacce itace babba adakin su Daddy tace.
“Babu komai sai alkhairi in Sha Allahu ”.
Ajiyar zuciya ya sauƙe da faɗin.
“Nima haka nake ji amma wani sashe na zuciyata sai ina jin tsoron yanda abin ya kasance cikin
gaggawa".
Yah Abubakar daje gefe yace.
“In sha Allahu sai alkhairi da izinin Ubangiji".
Mikewa Yah Abubakar da Yah Muhammad sukayi jin Abba na cewa kuzo mu tafi.
Sallama suka musu tare da ficewa.
Nan su Aunty Hauwa da Garkuwa Da sauran duk suka dinga al'ajabi akan lamarin Ubangiji
daya saƙƙo da Auren nan lokacin da ba'a yi zato ba ba'ayi tsammani ba...
Acan gefen su Taj kuwa tunda Abba ya danƙa masa hannun Ishmah bai sake ba kana ya kasa
buɗe baki yace mata wani abu ba...
Ishmah kam tunda ta Zaurawa ƙafarsa dake yanke ido ta kasa janyewa sai hawaye dake
kwaranya daga idanunta.
Jin ya saki nannauyan ajiyar zuciya mai haɗe da zazzafan iska daya fito daga cikin ƙahon
zuciyarsa hankali ta ɗago idanunta dake jiƙe da ruwan hawaye ta kallesa.
Kansa ya fara jujjuya mata ahankali alamar ta daina kuka so yake ya buɗe baki yace ta daina
kuka amma yana jin harshensa yayi nauyi ta wace siga ta wane yanayi kana da wani furuci ko
laɓe ko harshe ko kalmar zai fara gabatar mata da tsananin sonta da yake yi kana da bata
hakuri bisa laifin daya mata na aura masa ita batare da saninta ko amincewar ta ba, abubuwan
sun taru sunyi masa yawa azuciya haka yasashin jin ya rasa ta ina zai fara bata haƙuri.
Ga kuma Babbar damuwar dake tattare dashi na abubuwa uku fushin ya Abana! Batun cikin
Laylah!! Da lamarin wannan karuwantacciyar yarinya Adaya, da ya baro a Ethiopia wanda ya
danne ko wanne kuzari dake cikin zuciyarsa arayuwarsa hakan sai yasa ya zuba mata idanun.
Idanu Ishmah ta zuba masa tana kallon yanda ya rame du-du-du da komarsa kwana talatin da
biyu ne amma yayi wata ramar data firgitata ta ruɗa mata hankalinta acikin kwanaki talatin da
biyun ma du-du-du sati ɗaya ne baiyi Update na new video saba a Tik-tok wanda har take
tunanin meyesa bayayi.
Sosai zuciyarta ta raunata saboda ganin yanda fuskarsa ta rame da kuma yanda sajensa ya
burkice ga kuma idanunsa da sukayi Jawur suka sauya launi daga ainihin launin data sansu
cikin rauni mai ɗauke da rawa murya tace.
“Tajjjj”.
Kallonta yayi amma baice komai ba saboda bazai iya amsa kiran da take masa ba.
Ahankali ta janye idanunta dake cikin nasa ta mayar kan ƙafarsa dake kumbure yana ƙyalli ga
kuma tafin ƙafar da ƙirjin ƙafar da yayi wani irin yanka ahankali taja hannunta dake kusa da
ƙafar ta manna akan ƙafar cikin sauri ta Runtse idanunta jin ƙafar tayi zafi jau.
Cikin rauni da bugun zuciya ta maida idanunta cikin nasa tare da cewa.
“Tajj”.
Sai kuma ta fesar da sassayan numfashi tare da lumshe idanunta wanda hakan ya bawa
hawayenta damar ci gaba da tsiyayowa.
Shi kuwa Taj tsira mata idanunsa yayi tamkar wahayin kallonta akayi nishi.
Murya ciki da rauni, kulawa, tausayawa da taushin lafazi mai cike da jinƙai tace.
“Tajj me yake faruwa?,Me yasameka?,Tajj meke damunka!?”.
Kai ya girgiza mata kasancewar bazai iya cewa komai ba.
Ganin haka ne yasa ahankali tasa hannunta ta ɗauki wayarta dake gefenta number Rahama ta
kira.
Adai-dai lokacin kuma Motarsu Rahama ke shigowa gidan jin Rahama ta ɗauka tace.
“Rahama kawo min First aid box”.
Kai Rahama ta gyaɗa tare da cewa.
“Ina yake Aunty Ishmah?".
Cikin sanyi tace.
“Yana ɗakina”.
“Ok bari na kawo".
Dai-dai lokacin kuma ta shiga cikin Falon bakinta ɗauke da sallama tana shiga Aunty Amina
wacce itama ƙanwar Daddy ce ta amsa mata sallamar tare da cewa.
“kin dawo?”.
Kai ta gyaɗa sai kuma ta mayar da kallonta kan Garkuwa dake cewa.
“Ya kuka daɗe haka Rahama?”
Ta ƙare maganar tare da amsar ledan hannunta ahankali tace.
“Wallahi Yah Adam ne yace dole sai mun biya gidan Hajia munyi mata albishir ɗin wannan
auren”.
Garkuwa na bude ledar tace.
“Kai haba Shiyasa mana naga kun daɗe baku dawo ba”.
Murmushi Rahama tayi tana kallon Ummominta tace.
“Gaba ɗaya Hajia na gaisheku ta kuma ce tana tayaku farin cikinki Auren ɗiyarku”.
Murmushi Aunty Amina tayi tare da faɗin.
“Mun gode mata itama mun tayata farin cikin Auren Jikarta"
Murmushi Rahama tayi tare da nufar bedroom ɗin Ishmah...
Ita kuwa Garkuwa Da sauri ta miƙe tare da kallon Aunty Nana tace.
“Aunty Nana”.
Aunty Nana dake magana da Aunty Maryam ta ɗago tare da faɗin.
“Na'am”.
“Zan samu kaza?”.
Cewar Garkuwa tana sake buɗe ledan.
Kai Aunty Nana ta gyada tare da cewa.
“Eh akwai wani iri kike so?,na gida kike so ko kuma”.
Shiru tayi sai kuma tace.
“Eh toh tun da dai abin gangawa ne duk wanda ya samu amma in so samune ai Zabuwa muke
buƙata”.
Murmushi Aunty Maryam tayi kana tace.
“Ai akwai a wajena”.
Dai-dai lokacin Rahama ta fito daga ɗakin Ishmah hannunta riƙe da First aid box murmushi tayi
tare da faɗin.
“Aunty Garkuwa ke dai kinyi farin jini Aunty Maryam bata Miki rowa”
Dariya Aunty Maryam tayi kana tace.
“Rahama cigaba da samin sunan Marowata.
Ta ida maganar tana fita tare da nufar ƙofanta...
Rahama kuwa direct BQ ta nufa abakin Kofar ta tsaya tayi Knowking jin shiru yasa ta sake
sallama tare da ɗan ɗaga saurin murya.
Daga ciki Ishmah tace.
“Shigo”.
Shiga tayi ganin Taj yasa ta saki Murmushi lokaci ɗaya fuskarta ya koma kalan rauni ganin
yanda fuskar Taj ya rame cikin sanyi ta ajiye First aid box kusa da ita kallon Taj tayi cikin sanyi
tace.
“Uncle Taj Barka da Yamma”.
Cikin sanyin murya mai gauraye da tarin damuwa ya motsa Lips ɗin sa tare da cewa.
“Barka dai auta”.
Tana tanƙwashe ƙafafunta tace.
“Yasu Ummeey?”.
Kai ya gyaɗa batare da yace komai ba.
Tana sauƙe ajiyar zuciya tace.
“Uncle Taj ina Laylah?”.
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa sai kuma ya kalleta yace.
“Tana gida”.
Cikin farin cikin kasancewarsa mijin yayarta tace.
“Uncle Taj Allah ya sanya Alkhairi Allah ya baku zaman lafiya”.
Wannan kalmar ne yasa ya ɗanji sanyi Aransa kallon idon Ishmah yayi sai yaga bashi take kallo
ba first aid box take buɗewa sai kuma ya kalli Rahama dake cewa.
“Uncle Taj sai anjima”.
Kai ya gyada a sanda take rufe musu Kofar...
Ishmah kuwa tana buɗe box ɗin taga duk wasu abubuwa da take buƙata suna ciki ɗaya gefen
kuwa magunguna ne buɗewa tayi tare da ɗaukar hydrogen kana ta Ciro auduga da karamin
almakashi ta kama auduguar kana tasa acikin hydrogen ɗin ahankali ta daga Idanunta ta
kallesa sai taga shima ita yake kallo. Ahankali ta motsa Lips ɗin ta still hawaye na zuba musamman idan ta kallesa sai taji wasu
sabbin hawaye na zirya a kuncinta cikin sanyi tace.
“Tajj”.
Zanyi maka dreesing”.
Idanunsa ya lunshe tare da buɗewa alamar tayi.
Baya tayi kaɗan kana tasa ya tsarta manuniya da babbar ta riƙe babban yatsarsa na ƙafa na ta
jawo.
Tare da ƙunsa
hauhawar tausayisa cikin zuciyarta da yake motsa mata rauninta
Jin ta jawo ƙafar ne yasa ya ware ƙafan tare da miƙa mata sai ya zamana kafar yana gabanta.
Ahankali ta gyara tankwashe ƙafafunta da tayi ta jawo pillow dake kam kushin ta ɗaura ƙafarsa
akai.
A hankali tasa ya tsarta inda taga yankan, ɗan dannan gefe-gefen ya kan tayi.
“Shythhmmmm”. yaja wani daskararren sauti wanda yafi kama da ajiyar zuciya.
Wanda yasa ya daki dodon kunnen Ishmah amma ta gaza fahimtar sautin na menene.
Ɗagowa tayi ta kallesa shima itan yake kallo.
Sai kuma ya nuna mata cikin box ɗin da hannunsa alamar ta ɗauki hangloves ta saka.
Kai ta gyaɗa kana ta janyo hangloves ɗin ta sanya tare da ɗaukar almakashin mai audugan
data sama sa hydrogen ta saka abakin yanka.
Atake ciwon ya fara fitar da kumfa duk da cewa bawai datti ciwon yayi ba ga dai yanda yankan
yayi ja alamar danye ne babu datti ko alamar ƙura, sai dai saboda bacteria bashi da ƙanƙantar
shiga jikin mutum.
Ganin yanda ciwon yayi yasa ta daga Idanu ta kallesa Araunane tace.
“Ka gani fa , Amatsayin ka na likita kaji ciwo kana wasa da lafiyarka da, kake dauka kamar bata
da muhimmanci”.
Sai kuma ta lumshe raunatattun idanunta dake cike da hawaye tana sharce hawayenta wasu na
turo wasu murya cike da tausayawa taci gaba da cewa.
“Kuma idan ma bata da muhimmanci awajenka tana da muhimmanci awajen Ummey da Yah
Abana, Ma'eesha kamata yayi ka kula da kanka ko dan Ummey, Ma'eeshah Meymer, Adaya da
kuma Laylah”.
Lokaci ɗaya ya Runtse idanunsa sunan Ummey data kira yasa yaji zuciyarsa ta karye har yana
ji kamar wani abu ya fito daga cikin ƙwaƙwalwarsa ya faɗa zuciyarsa sai kuma sunan Meymer
da Adaya data kira kansa ya bada sautin Dimmm wanda har kunnuwansa sukayi Dimmm na
dan wani lokaci hakan yasa baya jin zafin hydrogen ɗin ahaka ta cigaba da wanke wajen. Sai yatsunta daya tsurawa ido.
Zazzafan Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗago idonsa, tsirawa sirrin sajenta yake kallon yanda
ya sake ƙawata kyawun fuskarta.
Sanyayyan ajiyar zuciya ya sauƙe kana ya maida idanunsa kan zara-zaran eyelashes ɗin ta da
suka jika da ruwan hawaye da kuma yanda take ƙifƙiftasu.
Wani irin sanyi da nusuwa ne yaji yana dirar masa tabbatas Ishmah ta musamman ce
azuciyarsa da rayuwarsa tana da wani irin matsayi da harshe kansa bai isa ya fade sa ba...
Ishmah kuwa cikin nutsuwa take gyara masa ƙafar bayan ta gama wankewa tasa auduga tare
da bandeji ta matse.
Ahankali ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya a lokacin da yaga ta rufe First Aid box ɗin.
Anutse ta ture First aid box ɗin tare da juyawa ta kalli kan dining idanunta suka sauka akan
Warmers data shiryasu ne sunan Bappa Kawu da komai da komai da ke kai.
Miƙewa tayi ta ɗauko try ta ajiye agefensa kana ta buɗe fridge dake dining ɗin ta dauko plate
data haɗa friut da kuma Fresh da Swan water sai Cock bayan ta ɗauka ta zauna a gabansa.
Shibkuwa kallon wayarsa yayi dai-dai lokacin kiran Abokinshi Dr Amdaz ɗan Qatar ya shigo
wayarsa.
Kansa ya kawar gefe.
Ita kuwa Ishmah hawayenta yaƙi tsayuwa ahankali ta cire ledan data rufe fruits ɗin sai kuma
tasa fork ta tura masa Bowl ɗin kusa dashi.
Idanu ya zuba mata batare da yace komai ba ganin haka yasa ta ɗauki glass cup ta zuba masa
ruwa ta miƙa masa...
Cikin sanyi ya ɗaga kansa ya kalleta sai kuma ya sunkuyar tare da karɓan cup ɗin ya kai
bakinsa shi kansa yasan cewa akwana biyun nan da ruwan ne yake rayuwa dashi a cikinsa sai
kuma ɗan fruits da yake sha time to time ahankali ya ajiye cup ɗin bayan yasha kusan rabin
ruwan.
Kallonsa tayi bayan ya ajiye cup ɗin tace.
“Taj”.
Idanunsa dake cike taf da tarin damuwa ya dago ya kalleta da ido ta nuna masa Bowl ɗin fruits
dake gabansa.
Kansa ya jujjuya mata.
Da sauri ta girgiza masa kai murya cike da sanyi kana hawaye na taruwa tace.
“Na roƙe ka da Allah koma menene matsalar ka, kada ka hora kanka da yunwa, Please dan
Allah kaji tausayin zucciyata.
Kaci abinci kada kayi fushi da ƙaddarar da zata iya riskarka a ko wani yanayi a ko wani lokaci
Kaci abinci ka samu karfin da zaka yiwa Allah godiya da addu'a sannan ya kawo maka sauyi
acikin rayuwarka”.
Jin abinda ta faɗa yasa ya zuba mata idanun batare daya iya cire idanunsa akanta ba yana
kallonta.
Ganin haka yasa ta ɗauki fork ta soka yankekkekken kankana data zuba madara akai ta ɗago.
Idanunsa ya ɗaga ya kalleta sai kuma ya sunkuyar da kansa ahankali cikin rauni tace.
“Karɓi”.
Ta ƙare maganar tana miƙa masa fork ganin yanda tayi maganar da kuma yanda hawaye ke
zuba a idanunta yasa ya karbi fork ɗin yasa abakinsa.
Ahankali ta sauƙe ajiyar zuciya ganin yasa abakinsa shi kuwa Ahankali ya tauna ya hadiye yana
ji kamar maganine sai kuma ya sake soko kankanar saboda ganin ta tsareshi da ido, ahaka yaci
kusan yanka biyar Na kankanar kana ya ajiye fork ɗin.
Banana ta ɗauka ta bare masa sannan miƙa mishi.
Amsa yayi tare da fara ci.
Ita kuwa fork ɗin ta ɗauka ta soka shi jikin apple, kana ta miƙa masa kansa ya girgiza ya kalli
grapes yanzu yana jin zai iya shan grapes.
Ganin haka ne yasa ta kama saman Nonon grapes ta mika masa ahankali ya amsa kana ya
maida kansa ya jingina da jikin kujeran ya cigaba da tsinkar ƴaƴan grapes yana tauna yana
hadiya.
Ita kam idanu ta zubawa ƙafarsa tana kallon wani irin tausayinsa na bin magudanan jinin jikinta
zuwa zuciyarta tuni lokacin Maghiba ta ƙara to....
*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170
GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.
Mutanen kasar Niger kuma 1000fc jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy
+22790899076 Please Dan Allah da Manzonsa kada ki karanta min littafina in kinsan baki biya
ba, in kuma kika biya kika rinƙa turawa wasu ko groups wannan kuma keda Allah*
Acan cikin gida kuwa Garkuwa ce tsaye a kitchen yayin da Aunty Maryam ke gefenta cikin
dariya sosai tace.
“Wai nikam dan Allah Garkuwa me haka son kai afili so nake na ture Ishmah in maye gurbinta
ajikinki amma kinƙi, kuma fa nima yar ɗakinki ne tunda dai Makkan nan tare mukaje ɗaki ɗaya”.
Murmushi Garkuwa tayi tare da cewa.
“Toh son kan me nayi
Maryam kemafa kadaki manta lokacin aurenki haka Naita dibi-dibi dake yanzu ke kin tsufa gashi
har kin bugo Hafiz da Hafiza”.
Maryam na gyara tsayuwar ta tace.
“Ki gani fa daga ji an ɗaura auren Ishmah kiga wasu abubuwa da kike ki dafa wannan ki ajiye ki
dafa wancan yanzu wannan me yenene dan Allah in ba son kai ba tunda ni lokacin zabuwa
kawai kika dafa min”.
Ƴar dariya Garkuwa tayi tare da sauƙe tukunyar data dafa Zabuwa a ciki wanda yaji hadin
magunguna na musamman masu kama jiki sauƙe wa tayi ta juye a Warmer kana ta kalli
Maryam tare da cewa.
“Ba wani son kai aciki ita fa Amarya ce ke kuma amarya ce. kuma ita Ishmah abu yanzu a
ƙurarran lokacin da son samune in tsumata na wata ɗaya zuwa biyu, to wannan Tajj ɗin yayi
mana shigar sauri, dan ma dai Allah yayi kwanaki mun ɗan fara kaɗan akan batun Dr Nafi'u da
magana ta fara rawa kuma dole muka bari”.
Maryam na matsar da warmer gefe tayi Murmushi tare da cewa.
“Aikuwa tare dani za'a ci”.
Wara Idanu Garkuwa tayi da faɗin.
“Ki yiwa Allah da Annabi ki bari ita kaɗai zata cinye Kuma yau bazan bar gidan nan ba sai ta
cinyesa a Idona yanda Auren nan yazo mana a bazata in ba dage mata akayi ba bazata ciba”.
“Kar ki damu ai Maryam na nan zata nace mata dan Maryam nada naci akan magani babu
kamar ita duk da cewa itama batasan maganin amma idan ta nace mata dole sai taci”.
Cewar Aunty Nana dake shigowa yanzu.
Cikin jin daɗi Garkuwa tace.
“TOh Alhamdulillah”. Ta ƙare hamdalar suna
ƙarisabfito falon ta ajiye akan dining tana ajiye wa ta fito tare da kallon Rahama tace.
“Ki miƙo min ruwa mai sanyi a fridge”.
Kai Rahama ta gyada tare da ɗauko mata goran ruwa a fridge dake dining tana kawo mata ta
karba tare da buɗe ledan da suka kawo mata ta fito da wani ɗan kwanon China tare da cewa.
“Ina su Aunty Amina fa?”.
Rahama na ɗan danna wayarta tace.
“Sun shiga ɗakin Daddy zasuyi alwala sallan Maghiba ya ƙara to”.
Kai ta gyaɗa tare da faɗin.
“Nima bari nayi sauri na dama lokaci ya ƙara to".
Juyawa tayi ta kalli Maryam dake gyara zaman da Kulolin data kawo kan Dinnin table.
“Yauwa Maryama gwara fa ki matson nan dan abubuwa nake so in bar Miki aiki zan baki na
bawa Ishmah