Showing 12001 words to 15000 words out of 47460 words

Chapter 5 - In Da Rai Book 2 Complete By Garkuwa.pdf

Advertisement

06 Jul 2025

6569

daɗi ta riƙa ƙyalƙyala dariya had’i da cewa.
“Alhamdulilah munji daɗi kuma in sha Allah sai mun sa Uncle Afif ya ɗauko mana Aunty
Rahama ma ko Addawa”.

Fuska ɗauke da Murmushi Addawa tace.
“Aikam munji daɗi tashi ku kawo musu ruwa”.
Ta ƙare maganar tana kallon Zulaihat.
Kai Zulaihat ta gyada kana ta miƙe ta kawo musu ruwa, dasu drinks,snacks,fruits ta jere
agabansu.

Kallon Aunty Amina Addawa tayi jin tana cewa.
“Tafiya dai ko yaya tana da wuya”.
Kasancewar da Fulatancin tayi maganar yasa Addawa ta fahimta kasancewar itama
Bafulatanan Ethiopia ce cikin mutumtaka tace.
“Sosai ma kam gashi kuma na tsaidaku a falo baku samu kun shiga ba Zulaihat maza-maxa ku
dauki kayayyakin su ku shigar musu ”.
Sai kuma ta maida kallon ta kan wanda adai-dai lokacin yake shigowa da jakankuna cikin
alamun dan sanin juna tace.
“Bilal ka shigar da jakunkunan ciki kasa wasu ɗakin nan wasu kuma dakin can”.
Sai kuma ta Kalli Aunty Amina tare da cewa.
“Aunty Amina wasu su shiga ɗakin nan wasu su shiga wancan wasu kuma suzo nan”.
Kai Aunty Amina ta girgiza tace.
“A'a ai biyun ma sun ishe mu ai”.
Murmushi tayi tare da faɗin.
“Toh bari in kawowa Adam key”.
Ta faɗa tare da shiga dakinta Jim kaɗan ta fito ta miƙawa Adam key tace.
“Akwai wani ƙofa da yake kallo. Ƙofar dama ka buɗe ka shiga ciki”.
”Toh”.
Ya faɗa kana ya juya ya fita dai-dai lokacin suka miƙe aunty Amina,Goggo Dijah daƙi ɗaya suka
shiga Aunty Nana, Garkuwa, Khadijah suma daki ɗaya suka nufa...

Koda suka shiga wanka suka farayi kana suka cac-canza kayansu kasancewar duk sunyi sallah
acikin jirgi yasa suka fito falo bayan sun gama komai.
Ganin sun fito yasa addawa sauke ajiyar zuciya tace.
“Yawwa Bismillah ku iso dining tunda kuka zo ba kuci komai ba”.

Kusan baki ɗaya atare suka zauna a dining ɗin kallon Laylah Addawa tayi tare da cewa.
“Ɗauki ki kaiwa Uncle Adam”.
Kai ta gyada tare da ɗaukan Food flask, da kuma plate bowl spoon da aka jera acikin basket, ta
nufi dakin Adam tana shiga ta sameshi zaune a Parlour bisa alamu yayi wanka ya shirya cikin
Black jallabiya, cikin girmamawa tace .
“Uncle Adam ga abinci ”.
Kai ya gyada kana yace.
“Sannu Laylah”.

Acan gefen su Garkuwa kuwa sosai suka yaba da mutunci da karramawar Addawa bayan sun
gama cin abincin ne kuma suka dawo tsakiyar Falon.

Sai alokacin Addawa tace.
“Yawwa yanzu sai mu gaisa ko?”.
Murmushi Goggo Dija tayi tare da cewa.
“Aidai kam sai mu gaisa tun da tun da muka zo bamu gaisa ba mun bige da cin abinci”.

Dariya Addawa tayi tare da faɗin.
“Ai dai kam matafiyi sai da abinci”.
Cikin mutumtaka da girmamawa suka gaisa bayan sun gama gaisawa tace.
“Na sani yau kam kun ɗebo gajiya ku shiga daga ciki ku samu ku huta in Sha Allahu muna nan
tare zamu sha hira kam”.
“Toh shikenan”.
Suka faɗa tare da mik’ewa.

Aunty Nana ce ta kalli Aunty Amina tare da cewa.
“Aunty Amina nifa shiru har yanzu fa basu iso ba”.
Ɗan hararanta Garkuwa tayi kana murya kasa kasa tace.
“Ina ruwanki da jiran sai sun iso mata da mijinta tana tare da mijinta kice sai kin jirata taxo?”.
Murmushi tayi kana tace.
“Ai Yakamata dai mu san inda suke kuma gashi har yanzu basu zoba har zamu kwanta kallifa
yanzu kusan ƙarfe biyun dare”.
Dariya Aunty Amina tayi mai haɗe da hamma tace.
“Um wannan dai damuwar kune”.
Ta ƙare maganar tana jan hannun Goggo Dijah suka wuce dakinsu...

Khadijah na dariya tace.
“Toh bari na gwada kiran Addah Ishmah ”.
3 missed calls tayi mata amma duk ba'a ɗaga ba.

Adai-dai lokacin kuma Taj ne zaune yana karatu kasancewar yana karatun da ɗan sautine yasa
baiji vibrating ɗin da wayar Ishmahn keyi ba duk da yana gefensa.

Aunty Nana kam dariya tayi tare da zama abakin gadon tare da cewa.
“Hmmm ai waɗannan tsofaffin tuzuran sai dai Allah ya taro manasu nifa karfin halin Taj na gani,
mutum shiru-shiru fa Ustaz-Ustaz naga mota tasha kwana hanya daban ko ina sukaje suka
buya sai Allah watofa gani yake in munzo nan tare ba lallai ne ya samu matarsa kusa da shiba”.
Garkuwa na gyara kwanciyarta akan gadon da yasha shimfida na alfarma tace.
“Koma dai ina suka nufa matarsa ce ba ruwanki”.
Cikin dariya tace.
“Wallahi ji nake kamar in zama ƙuda in liƙu a jikin blanket nasu inga wainar da za'a to”.
Cikin dariya Garkuwa tace.
“Wato ke Bama a ɗakinba har cikin blanket kike son shiga”.
Dariya mai sauti tayi tare da cewa.
“Hmmm ba doleba zan samu ƙarin darasi Ishmah fa da kike ganin halittar soyyayace shiyasa
duk wanda ya taɓa koda hiran sone da ita baya yanke alaƙa da ita dan gwanace a iya tattalin
miji wani lokaci har Maryam tai ta mata tsiya tana cewa muda muke matan aure ba ma tattalin
mazanmu da riritasu kamar yadda takewa Tajjj. To kuma shima Tajj ɗin naga alamar Tattabarane shi kuma ɗawisu a fagen iya love ke kiga
randa aka ɗaura auren mana da suka ƙule BQ sai Magrib suka fito”.
Sai kuma tayi shiru jin yadda Garkuwa keta dariya.
Hira kaɗan suka taɓa kana daga bisani suka kwanta su kayi bacci...

Washe gari da safe Ethiopia
Aminullah ne zaune agaban Ummi yayin da Abpu ke gefe idanunsa alumshe kamar mai bacci
saidai ba bacci yake yi ba, bisa dukkan alamu breakfast suke.
Anutse Aminullah ya kalli Ummi tare da cewa.
“Ummi Aunty Ada fa?”.
Ummi na ɗan gyara zamanta tace.
“Aunty Ada na kirata amma naji tana waya da Izzin”.
Numfashi ya sauke kana yace.
“Ummi idan munyi Sa'a fa Allah ya kawo sauki, baki ga tun randa mutumin nan yazo ya saki
Aunty Ada har yau bata sake fita rawan nan ba”.
Cikin jin daɗi da alamun farin ciki tace.
“Nima abinda nake ta tunawa kenan Aminullah in Allah yaso ma sanadin sakin nan za tayi sanyi
ta daina abinda take yi, kasan shi saki yanada zafi da kashe jiki da cushe zuciyar mutum koda
ko yana son a sakeshin wannan alƙawarin Allah ne domin abinda zai girgiza al'arshin Allah ai
ba wani zuciyar dake da kafircin da zai hanashi girgiza sai dai in bashi da ɗigon imani, gashi
kuma tace min ta faɗi ƙugunta ya bugu sosai”.
Cikin jin daɗi Aminullah yace.
“Allah yasa ta shiryu kenan”.
Ummi na Murmushi tace.
“Ameen ya hayyu ya ƙayyum Aminullah abinda muke ta fama kenan Allah ya shirya mana ita”.
Yana gyara zamansa yace.
“In sha Allahu ai Allah sami'uddu'a ne zai amsa mana addu'o'in mu, in Sha Allah watarana
zamuyi farin ciki da rayuwar aunty Ada”.

Abpu da tunda suka fara Magana baice uffan ba ya buɗe idanunsa cikin rauni yace.
“Kayya ina wani shiryuwa awajen Adaya wataƙil ciwo ne kawai yasa ta lafa wataƙil kuma wani
abu na daban take shiryawa wanda bamu sani ba”.
Ya kai ƙarshen maganar cikin rauni da takaicin halin data jefa rayuwar ta”
Da sauri Ummi tace.
“Kada kace haka in Sha Allahu Adaya zata shiryu kawai mu cigaba dayi mata addu'a ”.
Cikin sauri Aminullah ya karɓi maganar da cewa.
“Sosai ko Abpu addu'ar mu Aunty Ada ke bukata in Sha Allahu zata shiryu kada ka karaya”.
Murmushi mai ciwo yayi tare da cewa.
“Ina fatan haka ina rokon Ubangiji ya nuna min ranan da za'a ce Adaya ta nutsu ta zama
kamilalliyar mace mai nutsuwa zuciya da jiki”.
Haka dai suka ci-gaba da tattaunawa.

*Nigeria*
Abbane zaune afalonsa yayin da Yah Muhammad, Yah Abubakar ke gefensa sai kuma Hamisu
da yanzu ya shigo gefen Abba ya tsugunna.
Kansa Abba ya shafa tare da cewa.
“Ya dai Hamisu?”.
Kansa ya gyaɗa kana yace.
“Lafiya lau Abba?".
Cikin kaunar su Abba yace.
“Ya kewar Boɗɗi?”.
Cikin sanyi da kuma rauni yace.
“Abba akwai ina kewarta gidan ba daɗi ji nayi kamar na ƙaura".
Cikin sauƙe ajiyar zuciya da kewar ɗiyarsa Abba ya saki nannauyan ajiyar zuciya kana ya
kwantar da kan Hamisu kan cinyarsa tare da cewa.
“Toh ina zaka kaura inda yafi nan Hamisu? Ai duk duniya babu inda zaka je inda yafi nan. In
Sha Allahu zamu saba ai abin farin cikine ya samu Addarka. Aure tayi fa sunnar ma'aikin Allah
abinda muke mata fata tsawon shekaru kai kafi son ta zauna anan tare damu ba tayi Aure
bane?”. Kai ya girgiza kana yace.
“A'a Abba bana fatan haka.
Hakan shine abu mafi a'ala in Sha Allahu zan yi ta addu'a Allah ya bata zaman lafiya acikin
rayuwar aunrenta”.
Atare Abba Yah Muhammad,Yah Abubakar suka amsa da Ameen.

*Qatar*.
Baki ɗayansu zaune suke bayan sun gama breakfast tare da kimtsa wa sai Adam ne dabai nan
wanda suka fita tare da Bilal.

Murmushi Addawa tayi tare da kallonsu tace.
“Toh nima dai tun juya nake kiran Afif bai ɗauka ba gashi Ni kaina na matsu ya kawo min
Ishmah kuma shiru dai har yanzu”.

Dariya Aunty Nana tayi tare da cewa.
“Hmmm ai muma mun kira Ishmah Addawa ba'a ɗauka ba wannan dai sai mu zubawa sarautar
Allah ido.
Allah andi inda suka ratsa”.
Dariya Khadijah ta sanya tare da cewa.
“Allah dai yasa ba ƙasan suka bari ba”.
Murmushi Addawa tayi kana tace.
“Ya isa ya bar ƙasar da ita bai kawo min ita mun gaisa ba?,Ko zai bar ƙasar ai sai ya kawota
mun gaisa”.
Cikin sauri Goggo Dijah ta ɗan zare idanu tace.
“Toh ma sai ya iya barin ƙasar da ita toh su tafi ina?”.
Zama Addawa ta gyara tace.
“Duk inda tace masa tana son zuwa zai Kaita in dai Tajju ne".
Kai ta jingina tare da faɗin.
“Lallai dai kam”.

Adai-dai lokacin kuwa a hotel ɗin da suka sauƙa Ahankali Ishmah ke ɗan jujjuya Idanunta cikin
ɗakin jikinta sanye da bathrobe fari kanta naɗe da towel wanda shima ya kasance fari bisa duk
kan alamu yanzu ta fito wanda.
Ahankali ta shaƙi numfashi tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin da jikinta ke fitarwa buɗe
idanunta tayi kana ta lumshe aranta tace to ina na wurga hand bag ɗina juyawa tayi ta kalli kan
gadon kana ta maida idanunta tsakiyar falon still babu, numfashi ta fesar asaman Lips ɗin ta
murya araunace tace. “Toh bari in duba falo ko acan na bari in ɗauko brush in samu inyi, nayi wanka kuma bazan iya
brush da wannan brush d’in nasu mai laushi kamar na jariraiba”.
Ahankali ta ɗan tura ƙofar ta leƙa ganin ko Taj na falon.

Jin Parlourn shiru alamun ba kowa sai sanyin Ac dake ratsa ko ina sai kuma wuta dake kunne
wanda ya bawa falon wani haske na musamman da yayi masifar kyau yana sheƙi ahankali ta
fito saɗaf-saɗaf ta nufi inda ta hango jakarta akan 2sitter tana buɗe hangbag taga Maclean da
brush ɗinta da ta saka, ajiyar zuciya ta sauƙe ta kana ta ɓare ledan brush ɗin ta zato brush ɗin
tare da matsa Maclean ɗin juyawa tayi zata koma bedroom sai kuma ta tsaya jin kamar motsin
mutum agefen hagunta da sauri ta zira idanunta kan labulayen cikin sauri mai haɗe da tsoro ta
zare idanunta muryanta na ɗan rawa tace.
“Waye?”.
Shiru ba wanda ya amsa ahankali ta nufi wajen ganin yanda labulayen keta motsi kamar mutum
ne a ciki, saɗaf-saɗaf ta isa wajen sai kuma ta tsaya cikin sanyi tace.
“Taj”.
Sai kuma tayi shiru ganin har zuwa lokacin labulayen na motsi ahankali ta sanya hannunta ta
ɗaga labulayen da sauri ta saki sanyayyan ajiyar zuciya ganin ƙoface awajen kana iskane ke
kaɗa labulen, wanda tayi zaton Taj ne zai gwada tsoronta, ahankali ta riƙe Handle ɗin tare da
murdawa ga mamakinta taga ya buɗu cikin sanyayyan sauti tace. “Wowww Masha Allah”.

Ta kare faɗan Masha Allah ɗin tana ƙarasa fitowa kan ɗan baranda dake zagaye da ƙarafunan
silver, a huta isa kusa da ƙarafun, kana tasa hannayenta ta dafa ƙarfen da aka yiwa Farandar
garkuwa dashi idanunta ta lumshe tare da tsira wajen daya fi kama da akira sa da forest dan
yafi karfin akira da garden saboda subiruni ne da kuma tsirran da suke bakin kogi wanda
akanshi akayi Hotel ɗin duk inda ta ƙyalla idanunta kore ne shar da wani iska mai masidar daɗi
dake busawa wanda ke sanya nishadi..
Wani irin shauƙi da farin ciki na musamman take ji wanda yake ratsa sassan jikinta da zuciyarta
lumshe idanunta tayi tare da sanya brush ɗin abakinta batare data fara gogawa ba.

Dai-dai lokacin kuma Taj ya buɗe kofar falon ya shigo bayansu kuwa home Deleviry daya kawo
musu breakfast ne suna shiga ya nuna masa kan dining ɗin falon alamar ya ajiye abincin akai
wanda abinci da sukayi order ne yana ajiye wa ya juya ya fita.
Taj kuwa har ya nufi bedroom ya hango alamar Kofar abuɗe yake ahankali ya nufi Kofar.

Yana isa yasa hannunsa ahankali ya ɗan ɗaga labulayen.

Idanunsa ya sauƙa akan Ishmah data juya baya tana kollon forest ta ɗan Dafa jikin karafunan
kana ta ɗan jingina kadan da jikin ginin sam bata ji motsinsa ko alamarsa ba.

Ahankali ya ƙara sa shiga dai-dai bayanta ya tsaya Anutse ya sanya hannunsa ya zagaye
dai-dai kan ƙugunta.

Cikin sauri da tsoro ta ɗago kanta ta kallesa ta gefe wanda ya bawa bayanta damar mannuwa
da ƙirjinsa a hankali ɗaya ta saki sanyayyan ajiyar zuciya ganin shine dan da farko ta tsorata.

Kanshi ya ɗan zuro ta gefen fuskarta tare da ɗan manna sajenshi da gefen fuskarta ta murya
can ƙasan maƙoshinsa a hankali yace.
“Afwan na baki tsoro ko”.

Sassayan numfashi ta fesar tare da ɗan lumshe idanunta tana mai jin yadda ni'imtaccen sanyi
ke ratsata ga kuma ƙamshin jikinsa.

Taj kuwa hankali ya murza hannayensa tare da murza ƙugunta ya juyo da ita suna fuskantar
juna har lau kuma hannunta na kan Brush ɗinta.
Ahankali ya sanya hannunsa dai-dai haɓarta na dama, gefen fuskantar ya ɗan shafa tare da
ɗan sayatsunsa biyu yana ɗan shafa sajenta tare da ɗan kwantar dashi, sassayan numfashi
suka fesar a tare, sai kuma duk suka ɗan tsaida idanunsu cikin na juna.
A hankali ya ɗan kamo kunnenta kaɗan ya shafa zuwa ƙasan habarta cikin wani irin yanayi ya
tsira mata idanu yana mai sakin sanyayyan numfashi.
Itama Ishmah idanu ta tsira masa tana mai jin wani abu mai masifar nauyi yana fita daga cikin
ƙwayar idanunsa zuwa nata.
Cikin wani irin yanayi Taj ya saki nannauyan ajiyar zuciya, sai kuma yasa hannunsa na dama ya

zaro brush ɗin daga bakinta.
Ido ta ɗan lumshe kana ta buɗe.
Shi kuwa ɗan murmushi gefen baki yayi tare da sanya broch ɗin cikin bakinsa.
Ɗan wara idanunta tayi kana muryanta can kasan maƙoshi mai cike da shauƙi da kuma sanyi ta
fesar da numfashi laɓɓanta ta motsa tare da cewa.
“Brush ɗina kuma kasa abakinka?”.
Idanunsa ya tsayar akanta batare da yace komai ba yana dan motsa hannunsa kamar yana
goga Brush ɗin murmushi tayi cikin mmkin lamuransa, shi kuma cikin jin sanyi a rai ya ɗaga
mata girarsa ɗaya tare da zaro Brush ɗin daga bakinsa.
Ahankali ya motsa Lips ɗin sa alamar ya ɗan tsosti zaƙin brush ɗin da kuma garɗin yawunta.

Cikin sakin sanyayyan Murmushi mai haɗe da wani irin shauƙi na musamman ta fesar da iska
mai sanyi tace.
“Ka bani tsoro”.
Fuskarta ya shafa yana mai jin wani irin yanayi na musamman atare dashi yace.
“Farar kura ga tsoro ga ban tsoro”.
Ya ƙare maganar yana haɗe yawunsa daya haɗe da zaƙin makilin da garɗin yawunta.
Sai kuma yasa hannunsa na dama ya tallaɓe fuskantar ido ta tsira mishi shima tsira mata nasa
yayi, da sauri ta lumshe nata saboda ganin ya haɗe bakinsu wuri ɗaya.
“Yah Salam wai ni kam me lips ɗina sukayiwa Tajj”.
Tayi mgnar zuci sabida jin yadda yakeyiwa lips inta wani irin fitinenne lasa kamar ya samu
lollypop”.
Sai kuma tayi saurin zamewa daga gareshi tare da juyawa tana kallon Forest ɗin still fuskarta
na ɗauke da Murmushi.
Sake matsar da ita jikin ƙarafunan yayi kana yasanya hannunsa ya shafa lafeffen cikinta cikin
sanyi sauti yace.
“Jiya ba kiyi Lunch ba gashi yanzu har kusan ƙarfe goma bakiyi breakfasts ba, muje Kiyi in baki
abinci, kada Ulcer ta illata min ke”.
Cikin lumshe idanu da yanda hannunsa ke yawo asaman cikinta ta saki sanyayyan numfashi
tare da faɗin.
“Toh”.
Kana suka fito falon ƙofar yaja ya rufe.
Ishmah kuwa kai tsaye bedroom ta wuce tana shiga ta wuce bathroom tayi brush tana fitowa ta
ganshi tsaye.
Cikin lumshe idanu tace.
“Ya dai?”.
Da hannu ya nuna mata durowa dake cikin dakin yace.
“Ga kaya acikin nan ki saka”.
“Toh”.
Tace dama aranta tana tunanin wani kaya zata saka.
Shi kuwa Taj juyawa yayi ya fita kana ita kuma ta buɗe durowar ɗan wara idanunta tayi tare da
faɗin.
”Wow Masha Allah”.

Ganin kayan dake shaƙe ajiki an shiryasu gwanin ban sha'awa wanda bisa duk kan alamu
dogayen rigunane masu masifar kyau da sheƙi.
Sai kuma wanduna masu kamar Palazo da top wanda suma suke shirye gefe ɗaya sai kuma
takalma wanda mafi akasarin su Snickers ne da hill masu shegen tsini.
Murmushi tayi aranta tace lalle ma Taj zan iya tafiya da wannan takalmin ne ahankali ta zaro
wata tattausar abaya mai laushi ƙiran samfurin Qatar Abayas Maroon color ta ɗaura gefen gado
sai kuma taja drawer ƙasa nan kuma Undoies ne kama daga Brassier, Pant, Skin tied, Boxer na
mata, da dai sauransu ahankali ta zaro Brassier cikin mamaki ta wara manyan Idanunta tare da
jujjuyawa asaman Lips ɗin ta tace.
“Ya akayi Taj yasan Size ɗin Brassier na?”.
Ta ƙare maganar cikin matsanancin mamaki ganin gaba ɗaya Brassier size ɗin ta ya sayo sai
kuma ta janyo Pant cikin sauri ta rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login